Sashe 30
Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sallamar da ake zabgawa daga harabar gidan shi yaja hankalinsu,zainab ce ta miqe tare da ajjiye remote din hannunta ta bude qofar ta fita,fadima ce ita da jamila diyar yaya yahanasu,bakinsu a washe suka soma takowa zuwa inda take
"Ku tsaya daga nan da Allah ku cire takalmanku kada ku batawa mutane waje yanzu na gama mopping" da fari jamila tayi dum amma ganin fadima ta tsugunna ta cire nata ya sanya itama dole ta cire,juyawa tayi fuska a cusgune su kuma suka bi bayanta.
Zama tayi kan kujerar ta maida qafarta yadda take,suna shirin zama saman kujerar da sauri tace
"A'ah,da Allah ku zauna a qasa,ai carfet ne,idan kuma baku iyawa ku tafi can ga nata kujerun can ku zauna a kai" tsabar qin da suka yiwa sumayyan suka gwammaci zama a qasa,suka gaidata ta amsa da qyar,ko kusa baau dubi sumayya dake guga ba,haka suma ko qurar data kwasosu bata kalla ba
"Dama yaayaa ce ta aiko mu gun yaya muntari" inji fadima,wani kallo ta watsa musu
"Bacci yake,ku fadi saqon sai na gaya masa idan ya tashi" shiru suka dan yi sannan suka dubi juna alamar basu son fada,hakan yasa ta dubesh kai tsaye
"Sai ku tashi ku koma da saqonku,ko kuma wadda ta aiko kun tazo da kanta"
"Yaaya yahanasun?" Suka fada tare cikin mamaki
"Eh,ita din mana,to meye?,kunga ku tashi ku bani guri da Allah,muta ne sai shegen binbinin tsiya haba" ta fada tana jan tsaki tare da mai da kanta gun t.v.
Zuciya ce ta zowa jamila wuya,bayan sun miqe sai ta kasa shiru
"Kema halin fa'izan gareki?,lallai akwai butulu a duniya da yawa,to wlh bari kiji,baki isa ki shiga tsakaninmu da dan uwanmu ba wallahi"kallon banza ta yi mata sannan ta saki murmushi tana kada qafa
"A'a'ahhhhhh.....yaro man kaza,quruci dangin hauka"
"Ke za'a gayawa wannan ai mahauk......."
"Idan kika sake bakinki ya qarasa wallahi sai na tashi na tsitstsinka maki mari,na kuma tattaka ki naga wanda ya tsaya miki...." Ganin yadda ta yunquro kamar zata sanya musu dukan ya sanya fadima ta janyeta suka fice jamilan na ciccika baki tana cewa "ai umman zata zo naga uban da ya isa ya hanata ganin dan uwanta,mata duka sai shegeb butulci duk wadda ka yiwa rana sai ta yi maka dare" itakam sumayya na gefe,ci kanku bata ce ba balle ta dago ta dubi abinda ke faruwa,tana jin zainab din na ci gaba da banbaminta mai kama da jirwaye da kamar wanka
"Ni wallahi babu wata yar miji da zata shiga rayuwata tunda ba ita ke aurena ba,idan da can an saba muku toni wallahi bazan lamunci a dinga tatsemin miji ba" ita dai ko kallo bata isheta ba,cikin hakan mukhtar ya fito sanye da doguwar riga jallabiya
"Ke dawa haka ina daki ina jiyoki?"
"Ni da danginka mana,haka akeyi basu da aiki sai zuwa roqo tsakani da Allah?" Zancan sai ya baiwa sumayya mamaki,iko sai Allah,ke kudin nan ba naki bane,kuma wanda suka roqa din ai dan uwansu ne ko?.
Tsaki yaja yana zama kan daya daga cikin kujerun
"Kudi take so zata biya kudin makarantar yara,na kuma gaya mata tayi haquri ribar hannuna na baki zaki fara saida mayafai,kasuwa kuma yanzun sai a hankali ba kamar da ba amma ta qi yarda,gwara da suka tafi din don ko sun sameni ba ni babu abinda zan iya bayarwa"
"Ato nidai na kora musu jawabi" ta fada tana tafa hannuwa
"Samamin ruwan zafi du Allah" ya fada yana kashingida.
"Gaskiya muntari na fara gajiya,aikin gidan nan fa akwai wuya kawai ka sama min mai aiki" ta fada a shagwabe,murmushi ya danyi sannan yace
"Kada ki damu,kafin a kama azumi za'a samar mikin ki bada cigiya"fari tayi da ido cikin salo" kai dear na ko gode....bari na kawo maka"miqewa tayi tana wani rangwada tare da sakin wani dan qaramin fito na jin dadi,a duniya bata da burin wulaqanta sumayya,tunda ita taqi samuwa to ko ta hanyar mukhtar din kawai ya isheta tunda tana cimma burin cusguna mata.
A hankali idanunsa ya sauka kanta,tana gefe daya tana guga abinta,sai ka rantse bata cikin falon ko batasan meke faruwa ba,saidai can qasan zuciyarta ita kadai tasan meke nuqurqusar zucida da gangar jikinta baki daya,baki daya ba mukhtar dinta take ganin ba a yanzun,siffar ce kadai tasa,rabon da ta sanya shi idaunta kwanaki uku kenan,idan yaso yana iya daukar kwananta ma ya kaiwa zainab din,saidai ci kanka bata taba ce masa,ta debo idanu kawai ta sanya musu.
A nutse yake nazarinta wani abu na fisgarsa,sosai yaga ta fada ta sake haske,qirjinta ya sake cika sosai sai hancinta da ya sake fitowa saboda rama,riga mai dogon hannu da skert ne a jikinta na wani yadi mai roba,kanta na kame da ribbom don ta jima rabonta da kitso
"Sumayyah" ya furta a hankali ba tare da ya san kalmar ta fito ba,sarai ta jishi amma sai tayi zaton gizo kunnenta yake mata,saboda haka tayi banza da shi
"Sumayya ba zaki kula ni ba?" Ya kuma fada a tausashe,sosai muryar ta bugeta,murya ce irin wadda yake mata amfani da ita a zamanin BAYA,hakan ya sanya ta gaza daurewa,sai ta daga idanunta da suka cika taf da qwalla ta azasu kansa,kallon kallo suka farayi kowa zuciyarsa da gangar jikinsa na shirin motsa masa soyayyar dan uwansa da suke tunanin sunyi bankwana da ita.
Muryar zainab dake takowa daga kitchen ta raba tsakaninsu,sai ta gaza ci gaba da gugar ta zare socket din ta tattara kayanta ta wuce dakinta,kan gado ta fada ta saki wani marayan kuka,zuciyarta da jikinta na azabtuwa da qaunar mukhtar da kewarsa.
**** **** ****
Da izzarta da bacin rai ta diro gidan tun qarfe tara na safe,saidai ga mamakinta tana qarasowa cikin falon ta qwala sunan zainab din wadda ta fito cikin kayan bacci sai ta nemi duk wani bala'i da ta tanada ta rasa,hasalima ma sai ta fara gaida zainab din,sheqeqe tace da ita
"Lafiya?,me kika zo yiwa mutane a gida tun farar safiyar nan,ko farkawa masu gidan basu yi ba?"
"Haba ko hutawa ai nayi ko zainabu abu"
"Hutu kika zo yi gidan da ba naki ba?" Ta fada tana rungume da hannunta a qirji
"A'ah....to....to daka jiya na aiko yara zasu karbi kudin makarantarsu ne sai kuma basu samu ganin kawun nasu ba,shine ni na biyo sahu,saboda koda yaushe za'a iya korarsu daga makaranta" gyara tsaiwarta tayi
"Au basu gaya miki rashin mutunci da rashin tarbiyyar da suka zo suka yimin ba?" Duk da cewa tasan komai amma sai ta samu kanta da gaza nunawa
"Su su fadiman?"
"Eh su din fa,don haka ina mai sanar miki cewa sun jaza miki,ba zaki samu damar ganin mukhtar ba,bacci yake koma ba haka ba wallahi ba zaki ganshi ba,ki tashi sawunki a likkafa ki tafi,babu mai matsawa mijina da shegen roqe roqe" idanu yaya yahansun ta zuba mata,tana so tayi masifa amma ta kasa,kamar an wanke zuciyarta haka takeji.
Tunda ta idar da sallar walha ta bingire da baccin da batasan sanda ya dauketa,muryar zainab din ta dinga jiyowa sama sama wanda shi ya farkar da ita,bata da niyyar fitowa amma tilas ta fito din sabida yunwar da ta tashi da ita.
Zainab din na tsaye kan yaya yahanasun tana zubda shika shikan rashin mutunci,yaya yahan tayi muqus kamar ba ita ba sai idanu da take bin zainab din cike da mamaki ba tare da ta iya tankawa ba,fes sumayyan ta fuskanci meke faruwa tunda na jiya ma gaban idonta akayi,sosai taji ranta ya baci,a rayuwarta ta tsani wulaqata babba sam,a kwanakin quruciyarta har kuka idan taga babba cikin wata iriyar rayuwa,ko ba komai ko bata girmesu ba yaya yahanasun ai tsatson mukhtar ce duk lalacewarta,ranta taji yana baci hakan ya sanya ta gewaye ta bayan kujerun ta bude qofar da zata sadata da falon mukhtar zuwa dakin baccinsa kai tsaye ta shige,wanda hakan shi ya ja hankalin zainab,da sauri ta fara kiranta da niyyar tsaidata saidai ko qurar data kwaso bata kalleta ba bare ita,hakan ya sanya ta rufa mata baya,tana shiga falon ta bame qofar dai dai lokacin da zainab din ke qoqarin sanya qafarta a falon,tana iya jiyo hayaniyarta akan ta bude qofar kada ta tasar mata miji,banza ma ta fita saboda haka ta nufi dakin gadon.
Kan side bed drower idaninta ya fara sauka sanda take qoqarin isa ga mukhtar din wanda ke daga can saman gadon yana barci,garwashi ne tare da wani qullin tsumma a kai,a hankali ta taka zuwa inda kayan suke,idanu ta zuba musu tana nazarinsu,babu alamun turaren wuta zata sanya don bata ganshi ba,hakanan taji bata aminta da qullin ba musamman da taga launin wani irin tarkace dake ciki,sai ta kunce qullin bakinta dauke da addu'o'i ta tura bandakin mukhtar din ta shiga,cikin masai ta zazzage dukkan maganin tayi plushing dinsa.
A hankali ta soma ambaton sunansa hannayenta harde a qirjinta fuskarta a dinke tsaf,idanunsa ya soma warewa kanta kafin ya gama budesu baki daya cike da mamaki,ya manta rabonsa da ya ganta cikin dakin,zai ambaci sunanta ta dora yatsanta kan lebanta sannan kai tsaye tace
"Tashi" ba musu ya yaye bargon ya tashi,sai ga taka zuwa gefansa ta zauna,idanunta sosai cikin nashi ta soma magana muryarta can qasa
"Wacece yaya yahanasu a gunka?" Cikin rashin fahimta yake dubanta,sai kuma ya bude bakinsa a hankali
"Yayata ce"
"Zainab kuma fa" hade rai yayi yana jin qin wani abu da zai taba martabarta cikin ransa
"Mata ta ce"
"Cikinsu wa zaka iya sauyawa" take yaji zuciyarsa ta harzuqo
"Kinga....bansan....."
"Riqe maganarka tukun" itama ta katse shi
"Ka tashi ka wuce kaje tana son ganinka yanzun nan" ta fada kanga tsaye cikin bashi umarni tare da miqewa abinta tana shirin ficewa,binta yayi da ido cike da mamakin yadda yau ta dumfareshi kai tsaye a yau din tana kuma bashi umarni,hakanan yaji ya kasa musanta mata,sai ya sauko da hanzari ya zura takalminsa yabi bayanta.