← Book details Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 205 OF 226

Sashe 205

Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*IDAN ZAKUYI UQUBA KUYI UQUBA DA GWARGWADON MISALIN ABINDA AKA YI MUKU UQUBA DA SHI(ma'ana idan zaku rama wani abu da aka yi muku ku rama gwargwadon abinda mutum yayi muku babu qaari)IDAN KUKAYI HAQURI SHINE MAFI ALKHAIRI GA MASU HAQURI*

Sadaqallahul azim
__________________________________

         Da fari labarin dariya ya dinga bashi,quruciyarta ta dinga burgeshi tana masa dadi,ya dinga leqa fuskarta yana tsokanarta,a hankali sai yanayin ya sauya ya koma na kishi,zallahn kishin mukhtar,yayi shuru yana saurarenta,daga bisani kuma sai mamaki ya bijiro masa,tausayi shi ya zama abu na qarshe,kafin ta gama bada labarin saiga hawaye shabe shabe kan fuskarta,yayin da zuciyar almustapha ta dinga motsawa,ji yake kaman ya dawo da hannun agogo baya,kamar ya dawo da baya ya ciro fa'iza zainab har ma da karima ya hukuntasu,lallai dole ta dauki eesha ba a bakin komai ba,tausayin abdallah da qaunarshi suka kamashi,ashe maraya ne,marayan da tun kafin ya iso duniya ya fara fuskantar qalubale na rayuwa,lallai dole yayi maganin eesha,bazai yarda ta sake fuskantar irin wannan rayuwar ba.

       Dubanta kawai yake bayan ya gama rarrasarta,mamakin irin rayuwar da take kawai yake,saidai zuciyarsa cike take fal kishin dukka mazajenta,ina ma ace shi ya fara samunta tun a wancan shekarun,da lallai ba shakka bazai bari tayi irin wannan rayuwar ba,saidai kuma qaddara data rigayi fata,ko a hannunshin ne tunda yazo cikin KUNDIN QADDARARTA dole hakan ya faru da ita.

        Kwanansa biyu cikin gidan baya fita ko nan da can,wata sabuwar rayuwa mai cike da soyayya da qauna suke shimfidawa cikin gidan,wata kulawa sumayyan kr bashi wadda ada can bai taba hakaito ta iya bawa miji kulawa kwatankwacin haka ba,duk sai ya narke ya koma wani shagwababben qarfi da yaji,jinsa yake tamkar qarakin yaro,irin soyayyar da yake hasashen samu ga matar aurensa ita yaje gani zallarta ba algus,shima baiyi qasa a gwiwa wajen bata kulawa ba,ji yake kaman ya lasheta ita da abinda ke cikinta,sau tari yakan sata ta saka qananun kaya kawai don yaga zaman cikinsa a jikinta,wata qimarta ke dada hauhawa cikin zuciyarshi,ta zama wata ta musamman cikin rayuwarshi,labarinta ya tsaye masa a wuya,yana jinjina mata yadda ta fuskanci duk wani qalubale na rayuwarta,yaci alwashin sai ya shafe duk wani tabo da yayi saura qasan ranta da qarfin qwanji da na zuciyarsa.

        Randa suka cika kwana uku a gidan,bayan sallar magariba ne,yana zaune a falo sanye da gajeran wando da vest duka farare qal,qafafunshi harde yana kallon wrestling,fuskarshi qunshe da murmushi duk da ba abin dariya ake ba a allon t.v,yayi shiru yana sauraren fitowar sumayya daga kitchen,wanda yasan me ya qulla maya shi yasa yake dariya,kukan shagwabarta ya jiyo tana fitowa a kitchen din,sanye take da vest itama da wando iya gwiwa baki dayansu blue da pink,kayan sun fito da cikinta muraran ya zauna das a jikinta,gashinta na daure a ribnom qwaya daya ya sauja bayanta sai qyalli yake,wanda aikin almustaphan ne shi ya gyara maya shi dazu da yamma,waiwayowa yayi yana kallonta hadi da qunshe dariya ya dage gira ya ware mata hannayeshi alamun ta taho
"Babe....me ya faru?" Harararshi take tun kafin ta iso
"Nama na.....ina nama na?" Sake qoqarin boye dariyarshi yake ya soma zagaya idanunshi sannan yace
"I think akwai bera ko mage fa gidan nan,dazun naji motso a kitchen may be su shuka janye" sai ta sake sakin kuka ta fado jikinsa a hankali,da sauri ya tarbeta yana sakin dariya,ya cusa hannunshi bayanshi ya ciro kwanan ya dire mata
"Hala baki kallon mudubi....gaba daya kina cin nama yana komawa kumatunki yana zama" ya qarashe yana dariya,dariya itama ya bata,sai ta harde hannayenta tana kallonshi
"Okey.....yanzu ya kake so ayi,na daina ci kenan?" Hannunsa ya daga sama
"Ni bance ba,ci abinki tunda baby na so...." Magananshi ta katse sanda wayarshi ta dauki ruri,ummi ke kira,sai ga miqa hannu ya dauki wayar yayin da ya maqaleta a kunne,ya soma bude plate din yana motsawa sumayya naman don ya huce yadda zai mata dadin ci.

       Gaisawa sukayi don yau duka basu je sun gaida su ba
"Almustapha ka kira gwagwgwanka hasiya ka mata jaje fa,yau kwanaki hudu ba'a ga aisha ba ba'asan kuma inda take ba,anyi nema har an gaji"
"Wace aisha ummi?"ya tambaya tamkar bai santa ba din
"Aisha 'yar gidan asiyan uncle balarabe?"
"Ohhh....Allah ya bayyana"ya fada yana miqawa sumayya naman cikin bakinta
"Nace ya kamata kasaka hannu ko Allah zai saka a ganta,barinta gidan nan da kwana uku abin ya faru,tunda Allah yasa kana da idon sani ka saka hannu ko Allah zaisa a ganta"
"Ummi....ku barta kawai,alhakine fa.....kisa taso yi cikin gidan Allah ya tsare,may be alhakin ne yake wahal da ita" ya fada kaman da gaske baisan komai ciki ba
"Almustapha......qaniyarka,qanwarka ce fa,tunda har Allah ya tsare din mai ya taso da wannan maganar?,c'mn ka sanya hannu a nemota hankali asiya a tashe yake"
"Zanyi qoqari ummi in sha Allah"
"To Allah yasa a dace,ina 'yata" murmushi yayi ya dubi sumayya dake kallonshi
"Gata nan....nama take ci"murmushi ummi ta saki cikin jin dadi
"qyaleta kar ka tseta,ka gaidamin ita,jikin nata kuma fa?,daka dauketa ka hana mai magani qarasa aikinsa" murmushi ya saki
"Zan kawo miki ita gobe,zaki mamaki ummi,ya za'a yi ina likita a kira mai maganin gargajiya ya taba min mata?"baki ummin ta riqe tana murmushi,wannan qauna ba qarama bace ta tabbata almustaphan kewa sumayya
"sannu masu mata,mu ai da yakeazanmu basa sanmu da idan irin haka ta samemu suke kiran masu maganin gargajiyar su dubamu" sai kuma kunya ta kamashi,ya saki dariya yana katse wayar da sauri.

      "Uh,me kike kallona?" Ya fadiwa sumayya yana lakace mata hanci,kai ta girgiza
"Don Allah baby ka barta ta koma gida haka" ta fada a shagwabe,fuska ya dinke
"Wa fa?"
"Aisha mana,kaga hankali yanzu ya tashi,ya kamata ta koma gida"shuru yaui kaman bazai tanka ba,yaci gaba da miqa mata naman,sai da yaga taqi karba sannan yace
"sati guda na diba mata kuma sai ta yishi,kiyi addu'a a sanda ta cika satin ta yarda ta aikata abinda ta aikata din,matuqar ta sake maimaita min abinda tayi tace sharri ne aka mata wallahi sai ta sake wani satin har sai ta yarda ta amince ta kuma nemi yafiya,zuciyata ba zata lamunci cutarwa tattare da ke ba,ki fitar da kanki daga maganar nan banson kice komai bare ki nunawa ummi na aikata hakan....kin gane?" Shiru tayi kawai ta gyada kai,don ta fuskanci ya dauki lamarin da zafi qwarai.

   *******   *****   ********

        Da yammaci suka shirya kaman yadda ya alqawarta kaita wajen ummi,tayi kyau cikin atamfa vlisco,ta cika sosai fatarta ta sake fresh,ta zama wata 'yar duma duma,duk inda ta gifata sai ta bat ragowar qamshinta,duk yadda yasi dauke idanunshi daga kanta hakan ya gagara,daga bisani janyo abarsa yayi ta sauka jikinsa tana dariya
"Baby.....so nake na gama fa mu tafi,na qagu naje naga ummi"
"Anya fitar nan kuwa yau zata yiwu?" Idanu ta zaro tana dubanshi
"Saboda me?" Murmushi ya saki,ba qaramin kyau ta sake masa ba data zaro idon,ya saka hannunshi ya ja hancinta
"Kinmin kyau,ya kamata muje mukai wa babynmu ziyara ko ba haka ba madam?" Ya qarashe yana kashe mata ido,ta fuskanci sarai me yake nufi indai yace zai kaiwa baby ziyara ne da shi yake fakewa,ta rasa ya akai ya sake ninka jarabarsa kan tada,sai ta soma tureshi tana bubbuga qafarta
"Ba wani ziyara.....yau wajen ummi kawai zamu" dariya ya soma yana cusa hancinsa lungu da saqo na jikinta yana shaqar daddadan qamshinta tare da yamutsata,tsuwwar da wayarsa ta fara shi ya sanya shi sakinta yana dubawa,ya ajjiye wayar yana dubanta da idanunshi da suka rage girma tare da sauya kala
"Hamza ya iso shi da matarshi,yace zasu wajenmu ne can gida nace masa bama nan,dazun na tura masa adress sun iso" gyara daurinta da tuni ya wareshi ta soma tana cewa
"Ok,to muje mana" kai ya girgiza yana kallonta
"A hakan zan fita?,bayan kin yamutsani,so kike hamza ya shekara yana addabata da tsokana kenan,jirani minti biyar na watsa ruwa" ya fada yana miqewa harda dan tsallenshi ta bishi da kallo har ya shige bandakin,murmuahi ta saki tana gyafa kai,wani irin mutum mai bala'in dadi zama tayi katari da shi cikin rayuwarta,sau tari idan yayi wani abun sai taga kaman ba almustapha ba,mayen soyayya ne na qarshe,yasan darajar auratayya da qimar matarshi.

        Yana maqale da hannunta suka iso harabar  gidan inda hamza ke tsumayinshi,gurim abida sumayya ta isa fuskarta qunshe da murmushi tana yunqurin amsar baby,yayin da almustapha ya qarasa wajen hamza
"Maan.....yaushe ka soma shiga cikin wannan duniyar taka?" Ya fada cikin sigar tsokana murya qasa qasa
"Lokacin shigarta ne yayi" ya fada yana fidda qaramin murmushi,dariya hamza ya saki irin ta mugunta yana dan dukan saman hannun almustapha
"Musty.....kace kawai kaima kayi dumu dumu cikin soyayya kaman yadda mukayi"
"Na sabawa Allah?....ka fita a idona fa hamza" bai fasa dariyarshi ba,yana jin dadi yaga ya kwashi almustapha
"Ina mutane na suzo suga yadda ake bugata"
"Dallah malami idan zaka shigo muje,idan ba zaka shiga ba ka sauka lafiya" ya fada yana yin gaba,wanda su abida tuni sun shige,binsa yayi yana ci gaba da dibarsa,shikam murmushi yake a boye,babu wanda ke kwasarsa son rai koda cikin abokanshi irin hamza,ya zaiyi da shi?,abotarsu haduwar jini ce daga Allah ne.
Chapter 205 · 0% Book details