← Book details Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 226

Sashe 150

Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       A nutse yake saukowa qasa,har yanzu falon shiru yake
"Me taci tun safe zuwa yanzu bayan lawal yace ba wanda yayi kiransa" yake rayawa cikin ranshi,mutum ne mai qoqarin sauke haqqin da ya rataya wuyanshi,hakan ya sanya ya taka a hankali ya isa cikin corridor da dakunanta suke,ya murde qofar ya tura,tsaye take cikin nutsuwa saman abun sallah,sanye da yalwataccen farin hijabi wanda ya saukar mata har saman qafafunta,hannayenta na hade saman qirjinta kanta a sunkuye tana karatun sallah murya qasa qasa,sakin qofar yayi ya koma da baya idanunsa a kanta kafin ya juya baki daya ya fice,idanunsa ya lumshe kana ya budesu yana ficewa daga sashen ba tare da ya iya tuna komai ba.

     Ummeen na zaune gefan baabaan yana cin abincinsa,yayin da bangare guda kuma ya bata dukkanin kunnuwanta yana saurarenta cikin gamsuwa,sai data kammala tsaf sannan yace
"Wannam shawarar taki tayi dai dai,don nima abinda na yanke kenan cikin raina....." Sallamarsa ita ta katse hirar tasu,baki dayansu idanuwansu na kanshi wanda hakan ya tabbayar masa maganarshi suke,cike da girmamawa ya qaraso gurin,ya zauna a gabansu kamar yadda suma suke zaune saman rugs din dake wajen ya lanqwashe qafafu
"Barkanku da warhaka" kusan lokaci guda suka amsa mishi,sama sama suka fara hira da baabaa ummee na gefe tana kallonsu tare da karantar yanayinsa,tana hango irin yadda mustaphan zai koma matuqar tsarinsu ya cimma gaci,mustphan irin mutanen nan ne da basu iya so kadan ko qi kadan ba,hakanan idan abu ya fita a kanshi zaiyi wuya ya kuma waiwayarsa
"Baka son abu mai nauyi at night,gashi naga kaman kana son tuwo...."
"Barshi baabaa.....matarshi tayi masa kalar abinda yafi wayo a gun" ummee ta tari numfashin baabaa,waiwayowa yati fuskarsa qunshe da murmushi yana duban almustapha,farinciki yaji,wato hakan na alamta fara samun sauyi kenan cikin rayuwar mustaphan
"To kaji abinda ummenka tace,sai ka barmin abincin tsaffin mata na" kansa ya dan sadda qasa yana sakin murmushi
"Baabaa,ina tunanin gobe in sha Allah nakeso na wuce dubai,na baro company kan aiki,mun fara fidda sababbin design da wasu companies keso na sabuwar shekara,wannan karon harda vails mukeso mu fidda" kai baba ke kadawa cike da farinciki da kuma alfahari kan irin qwazon da Allah ya bawa almustaphan
"Masha Allah,Allah yayi albarka ya kuma taimaka,saidai ita mai dakin naka ai bata da visan shiga dubai ko?" Addu'a ya soma cikin ranshi kada baban ya ballo masa ruwa
"Baba ai nan da nakeso ta zauna......"
"Ban yarda ba,ka daga tafiyarka sai jibi ko gata zuwa lokacin na sa an buga mata visa,and then bana son zaman hotel,ina son zaman hotel ya qare maka,ka koma naka gidan" kanshi a qasa yana dawurwura,da zai iya da ya nemi alfarma wajen baaban,saidai bazai iya musu da shi ba
"Shikenan,za'ayi yadda kakeso din in sha Allah,amma baba gidan zai dauki a qalla wata uku kafin ya zaunu,saboda akwai wearing na abubuwa da za'a yimishi,kasan komai na qasarsu a tsare yake saida amincewar gwamnati zaka yi"
"Ba komai,sannan gobe ka zauna gida ka huta hakanan,ko don ciwon hannunka" baisan me zai zauna yayi a gida ba,amma ko bazaiyi komai din ba babu musu tsakaninsa da baba
"In sha Allah"
"Kira maman tawa ta kawo passport dinta idan yana kusa" rasa yadfa zaiyi yayi din bashi da numberta,baiso kuma ya fada hakan ya bata ransu,iyaye ba wasa ba tuni dukkaninsu suka fahimci hakan
"Ka amshi number wajen mamanka tunda sai an gaya maka abinda ya dace,tashi kaje ka kirata" ba musu ya miqe yayi hanyar waje,da idanu suka rakashi,kowannansu zuciyarsa cike da farinciki tare da cikakken alfahari da shi,mustapha na dabanne cikin zuriyar gidan,tsananin biyayya da qaunar iyayensa na dabanne cikin zuciyarsa.

       Riga da skert ne a jikinta na atamfa wadanda suka zauna cas a jikinta,ta rasa wanme mayen tela ne har ya iya fidda qirarta haka,ta tabbatar sharrin amira ne,gashinta ta ware bayan ta gama feshe jikinta da turaren jiki da na gashi,dariya ta subuce mata sanda take taje kan,tana kwatanta zata iya tunkarar mustapha kenan zuciyarta ke nufi.

     Turo qofar da akayi shi ya sanyata juyowa da hanzari,tsaye yake a bakin qofar hannunshi riqe da handle din qofar,janye idanunshi yayi daga cikin nata idon ya maida kan gashinta wanda ya sauka har qasan kafadunta,baki ya tabe a zuciyarsa,wato itama tana jona gashi irin wanda su'ad keyi kenan,wanda sunsha kai ruwa rana da shi akan gashin dokin,duk sonshi da gashi bai son attachmen
"Ki fito ki sameni a falo tare da passport dinki,wannan abun kuma da kika qarawa kanki ki tabbatar kinje an cire miki shi" ya nuna kanta da bakinshi,a hankali ta daga hannunta ta dora saman kanta don taji me yake nufi,itakam idan banda gashinta bata ji komai ba,bata fahimceshi ba bata kuma zurfafa tunani ba ta daure gashin nata ta zari hijabi ta zura,sannan ta janyo jakar hannunta ta fiddk passport din nata wanda dama tunda suka dawo daga uk yana ajjiye a ciki ta fito falon cike fal da mamakin me zaiyi da passport dinta kuma?.

       A tsaye ta taddashi hannayensa cikin aljuhunshi,da idanuwa yayi mata nuni ta wuce gaba,kanta a qasa tayi gaba ya bi bayanta,tamkar wanda aka sarqafe idanuwanshi haka ya dinga bin duk wani takunta da kallo,tamkar wadda ke rangaji haka take ajjiye takunta anutse,duk jin kan su'ad da jin ita din wata ce wajen iya gayu maqale magana da tafiya bai taba ganin tayi irin wannan salon ba,ko don bai kallon mata banda su'ad ne oho,shi a nashi tunanin ko wacce mace tana sane take nau'in waccan tafiyar saboda tashi madam din kawai ya sani,baisan komai da ya shafi shirgin mata ba,tsakaninshi da su ya duba su idan lalaura ta taso.

      "Wait" ya ambata sanda take gab da shiga sashen,ya qaraso a hankali ya daidaita da ita sannan suka shiga,kamar ko wanne lokaci haka ta gaida baabaan,ya miqa hannu ya karbi passport din nata
"Ki shirya in sha Allah zaku wuce dubai gun aikin mijinki,ina ga kamar hakan zaifi ko?" Kanta sunkuye cikin fargana da gaduwar gaba tace
"Duk yadda kace baba yayi" murmushi ya saki don dama yasan ba matsala tattare da ita,yana fatan hakan zai haifar da alaqa mai tsafta kyau da danqo a tsakaninsu,kai yake gyadawa cikin farinciki ya sanya musu albarka kana ya sallamesu yace su wuce sai da safe,tare suka sake jerowa,saidai suna zuwa gab da sashen ya ja da baya ya koma ya yiwa kansa mazauni kan daya daga cikin kujerun hutawar daya qawata wajen da su,daura da inda fanfunan nan suke,hannunsa ya sanya ya fidda wayarshi dake burari,hamza ke kira,dora wayar saman tebur yana kallonta har ta qaraci kukanta ta katse,sai da ya hada misscall wajen biyar sannan ya dakata,bai bi takansa ba,yana ciki da shi,ji yake kamar shi ya masa bakin da ya bishi sanda zai taho daga dubai,sai da ya mula don kansa sannan ya daga wayar ya kirashi,bai iya fushi da hamzan amini ne na qwarai
"Maan,ina ka shiga ne inata kira,ko ana angonci mode" ya fada dariya na son subuce masa
"Allah ya isa tsakanina da kai wallahi hamza shege mai mugun baki" dariyar da yake son dannewa bata barshi ba sai data subuce,wanda har sai da mustaphan ya dage wayar kadan daga kunnensa sabida dariyar da yake zabga mishi,tuni hamzan ya samu labarin komai
"Me kuma nayi,sunnar ma'aiki na maka fatan sake rayawa fa kuma ta tabbata"
"Na rantse idonka idona sai na karkatar maka da baki,idan yaso tayi jinyarka da kyau waccar 'yar kazar taka"
"Qarya kake wallahi abida ta wuce kaza a wajena giwa ce,kuma zaka bada bayani dalla dalla duk sanda ka shiga hannu wallahi,gwara ka fara saita kanka tun yanzu,ni nasan me nake aure shi yasa na sallamawa matan africa espicially na nijeria,nijerian ma AREWA,they are special over wlh"
"Close your mouth malam...yaushe zaka koma,kayan dake warehouse sunyi qasa fa sosai"
"Kai barni,haka kawai ina tsaka da shan amrcina,mun shigo abuja ni da madam dazu da zahar,gobe ma in sha Allah da yammaci zamu kawo muku ziyara daga nan muga amarya"
"Ganin amarya ko gulma?" Ya fada yana datse kiran,dariya hamza ya dinga yi abunshi,yq riga ya saba da dukka halayen mustphan,tex ya tura masa na musaddiq(daya daga cikin abokanshi)na neman wayarshi bai samu ba,pls ya kira shi,tsaki ya ja,yasan tsiya ce zasuyi mishi,don sarai yana da yaqinin hamza ya baza labarin wai an masa auren dole,kamar yadda yake tsokanarshi kenan,kiran daya daga cikin MD na kamfanonin da suke karbar riguna a wajensu ne ya shigo,nan ya jima wajen zaune suna waya,wanda sai da suka bata tsahon awa biyu kafin suyi sallama.

  *******    ******    *******

       Qarfe hudu saura ya sauko daga saman cikin sassarfa wanda tunda gari ya waye bai sauko ba din sai yanzu,sau uku tana hawa cikin fargaba tana dubashi sai ta tadda yana bacci,hakan ya sanya ko breakfast data shirya masa su daukewa tayi bai ci ba,tunda ta ganshi kwance tasan baida niyyar fita,hakan ya sanya ta quduri aniyar shirya abincin rana,sam bata ma san da zuwan baqi gidan ba.

      Yana sanye da long sleeve t.shirt baqa mai dauke da logo din armani,slim fit  jeans din jikinsa baqi ne shima,kamar yadda hight top sneakers din qafarshi yake baqi,baki daya shigar saita haska farar fatarshi sosai kamar wani jinsin ba hausa fulani ba,da sassarfa yake saukowa don bada oder na abinda za'a kawo ma su hamza idan sunxo,ya saba,ta zame masa al'ada matuqar zaiyi baqi saidai ya siya musu abin fitar kunya,masu aiki su shirya shi a gun cin abinci,yana step din qarshe wayarsa ta dauki ruri,lambar hamzan ce
"Munfa iso,a zo a qaraso da mu" inji hamzan,wayar ya mayar aljihu yana furzar da iska tare da shaqar daddadan qamshin abincin da yafi zaton kodai daya daga matan adam tazo abuja ne?,ya taka a nutse ya fice zuwa parking space.

         Suna tsaye shida abida,wadda itace matarshi,matashiya mai matsakaicin kyau,nutsuwa cikakkiyar tarbiyya da iya mu'amala,cikin shigarta ta bahaushiya zam suna tsaye da hamzan ta dan jingina da mota saboda cikinta daya soma nauyi,kana dubansu kasan akwai kyakkyawar DANGANATAKAR ZUCI data fili a tsakaninsu,a haka ya iso ya taddasu,tana matuqar jin nauyin mustapha yana mata kwarjini,hakanan tana girmamashi,saboda haka abayansu ta tsaya tana biye da su fuskarta washe da murmushi tana duban yadda take wakana tsakanin hamza da almusphan.
Chapter 150 · 0% Book details