← Book details Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 226

Sashe 48

Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*_KUJI TSORON WATA RANA DA AKE KOMAR DA KU IZUWA GA ALLAH A CIKINTA (RANAR LAHIRA),SANNAN A SAKAWA KOWACCE RAI ABINDA TA AIKATA (SHARRI KO ALHERI)ALHALIN SU BA'A ZALUNCESU BA(BA WANDA ZA'A ZALUNTA DUK ABINDA KA AIKATA SHI ZAKA GANI)_*

______________________________

Qarfe tara na safiya tayi wankanta,ta shirya cikin atamfa dinkin riga da zani,ba wani kwalliya tayi ba amma tayi kyau,dakin ta sake karkadewa ta goge sannan ta koma bakin gadonta ta sake kwanciya,idanunta ta lumshe tana saqa da warwara,kewar abdallah take ji sosai cikin zuciyarta har qwalla na shirin kawo mata,tunani ne fal zuciyarta tana wassafa yaya rayuwa zata kuma kaya mata cikin wannan gidan.

Hayaniya ta dinga jiyowa cikin falon da surutai,ta bude idanunta ta kalli agogon dakin,goma tayi har da mintina arba'in da biyu,saita bude sif dinta ta ciro hijabi ta zura kana ta sanya silifas dinta ta murda qofar dakin ta fito.

Duk uban hayaniyar da take ji yara hudu ne cikin falon,yarinyar farko wadda ita ta sake hautsina yanayin falon ma hakimce kan kujera kamar wata babbar mace duk da du du du ba zata wuce shakara sha uku ba,kallo take a tashar mbc three ta qure volume kamar ita da mutum dari suke kallon,sai yarinya ta biyu wadda batafi shekara uku ba dake zaune qasanta kan carfet taci uban indomie ta hadeta da ruwan shayi tana wasa da ita,daga can wajen step na dining kuwa wasu yaran ne su biyu,daya shekarunta goma daya takwas suna karyawa,su biyun kadai sun dame gurin kamar qanwar tasu dai,ta sake wurga idanunta,wata yarinya ce data tasamma zama matashiya wadda ta kusa shekara goma sha hudu takure a saqon kujeru,kallo daya zaka mata kasan daban take kamar yadda kamanninsu ya bambanta da sauran yaran dake falon,don dukkansu kamarsu daya ita kadaice kamarta daban kamar yadda ta fisu kyau baki dayansu.

Dukkansu sun ga fitowarta saidai babu wanda ya kulata,ta dubi qofar dakin karima wanda ke garqame ta sake dauke kai
"Ina kwana anty"
Taji an ambata daga bayanta,saita waiwaya,yarinyar dake zaune ce saqon kujera ta gaidata tana murmushi,maida mata murmushin itama tayi tana mamakin zarnin dake tasowa daga jikinta
"Lafiya qalau,an tashi lafiya?,me sunanki?"
"Nuwaira"
"Sunan mai dadi" sai tayi murmushi tana cewa
"Na gode anty".
"Ko zaki rakani wajen kakarku?"
"Wa?,hajiya"
"Eh"
"Muje in rakaki anty" ta fada tana wucewa gaba sumayya na rufa mata baya.

"Wallahi bari umma ta fito sai na gaya mata duk abinda kika yi,bata ja mana kunne ba?" Yarinyar daje saman kujera ita ta ambaci hakan tana jijjiga kai,cak yarinyar ta tsaya kamar an ambata mata mala'ikan mutuwa,idanunta na tara qwalla tace
"Kiyi haquri don Allah kada ki gaya mata"
"Wallahi sai na fada saidai ta kasheki" ta fada tana buga hannu alamun babu fashi,wani abu ya tsayawa sumayya a wuya,takaici da mamaki suka cikata,sai ta janye nuwaira tana fadin
"Muje babu abinda zai faru dake kinji kada ki damu" jikinta babu qwari ta bi sumayyan suka fice.

Kafin su qarasa gun hajiyan sumayya ta dubeta
"Me yasa kinsan kina fitsarin kwance da kika tashi baki sauya kayanki ba nuwaira?,kinsan fa ba'a son mace da qazanta" sai yarinyar ta fara qwalla ta soma sharewa tana cewa
"Wallahi anty tunda bana fitsarin kwance,saddiqa keyi sai a hadamu kwanciya gado daya,idan tayi duk sai ya jiqani,idan ta tashi ita sai nuratu ta sauya mata kaya,ni kuma ba zan canza ba har sai umma ta gama bacci tayi wanka ta fito sannan zata nunan wadanda zan sauya din,koda asuba bana samu nayi sallah sai rana ta fito" ta fada da alamu abun na ci mata tuwo a qwarya,shiru sumayya tayi tausayin yarinyar na kamata,wannan wanne irin zalunci ne,tun kallon farko da ta yiwa yarinyar ya nuna tana jin jiki a gidan,amma tana tunanin kamar ita ce yarinyar nan daya da karima jiya ta gaya mata uwarta daban,don ta tabbatar sai ta tambayeta
"Ina mamarki to?"
"Mama na tayi aure a wani gidan,tun kafin a yayeni aka karboni aka bawa hajiya ni,to da abbanmu ya sake aure ya auro umma sai umman ta karbeni nake gunta"take tsanar karima ta darsu a zuciyar sumayya,lallai ba shakka bayan shirkar tsafi ma harda azabtar da yarinyar da bata ji ba bata gani ba,wai me mutane suka dauki duniya ne?,kowacce mace son kanta ya mata yawa?,burinta ta mallaki miji ta rabashi da kowa nasa?,ta rabashi da 'yan uwansa da tazo ta samesu tare,'yan uwa da suka zamar masa bango marufar asiri tun yana zanin tsumma har kawo yau,ta rabashi da duk wani alkhairi uwa uba ta rabashi da mahaliccinsa,ta sakashi a musibar da ranar gobe qiyama bazai iya tsallaketa ba,ta rabashi da hankalinsa bare ya kula da addininsa,wanda ya cancanci a bashi haqqinsa ta hana ya basu yanzu duka wannan qauna ce?,sai tace sonshi take shi yasa ta aikata haka,wannan ko babban maqiyinka ba shakka iya cutarwar da zai maka kenan,da irin wannan tunani suka isa bangaren hajiyan.

A duqe suka sameta tana share falon nata dake malale da carfet,kallo daya sumayya tayi mata ta fuskanci shekarunta basukai ace tayi tsufar da tayi a yanzu ba,da sallama suka shiga ta dago tana amsa musu riqe da qugunta wanda bisa dukkan alamu ciwo yake mata,nuwaira ce ta gaisheta ta amsa babu yabo ba fallasa yayin da sumayya ta qarasa tana amsar tsintsiyar hannunta tana gaidata,amsawa tayi tana dubanta yayin da sumayya ke qarasa mata sharar har ta kammala sannanbta dawo inda hajiyar ke zaune tana yiwa nuwaira masifar sai zuba zarni take taje bandakinta ta wanke jikinta,mamaki ya cika sumayyar,to ko batasan meke wakana bane cikin gidan?,batasan ba laifin nuwairan bane karima ce ta cancanci fada idan da duka ma ayi mata?,tashi yarinyar tayi ya shige bandakin hajiyar sannan hajiyar ta maido kallonta ga sumayyan
"Ban gane fuskar ba wace ce ne?" Murmushi kawai tayi ta dan sad da kai
"Oho,ko amaryar lukman ce" kai sumayyan ta gyada.

Shiru ne ya biyo baya,hajiyan na dan satar kallon sumayyan,sai taji ta dan sake da yarinyar duk da ba hira suke ba zaman kurame ne,a haka har nuwaira ta fito daga bandakin sanye da jiqaqqun kayanta wadanda ta wanke bayan ta dauraye jikinta ta maida su a haka
"Wani nuwaira nikam bakuyu abin kari bane yau,gashi har sha daya na shirin gotawa yau ba'a kawo kin komai ba,ko luba mai aikin bata zo bane?"cike da madaukakin mamaki sumayya ke sauraron zancan
"Tazo hajiya,bansan ba'a kawo miki ba,don ko nima yau ban karya ba,naga dai su nuratu na karyawa ni ma ba'a bani nawa ba"ta fadi babu alamun damuwa tattare da ita bisa dukkan alamu ta riga da ta saba da hakan,yamutsa fuska hajiyan tayi
"gaskiya na fara jin yunwa wlh,wannan abu Allah kayi mana maganinsa"
"Amma hajiya ai naga kina da sauran kayan abincinki da kika ce bazaki iya ci gaba da girki ba ai abba bai debe su ba ko?"
"To idan banda abinki ina fama da lalura ina zan iya,sharar ma don bazan iya zama cikin qazanta bane nake daburtawa nake yinta" ta fada ta muskutawa da alamu yunwa na sakadarta,tausayinta duka sai ya kama sumayya ta dubeta
"To hajiya idan ba damuwa sai na shiga na girka miki ai ko?"haba ta riqe
" a'a,har kya fara shiga madafi ta sanadina?,ki barshi babu komai idan da sabo ai mun saba da irin wannan gashin,ke dai kawai Allah yayi mana magani"murmushi tayi kawai ta miqe tana tambayar nuwaira inda kitchen din yake.

Sallamar karima a gadarance ita ta maida hankalinsu bakin qofar,ita ke gaba gogan na binta a baya riqe da wani dan qaramin flask wanda bako shakka abun karin hajiyan ne a ciki,idanunsa na kan sumayya yana faman sakar mata murmushi ,wani takaici da haushinsa suka qumeta saita dauke kai tana jin kamar taje ta shaqeshi,haka nan kawai taji jarumin namiji yana burgeta,sai ta tuna sanda zainab ta fara murza kambunta lokacin tana gidan mukhtar,tabbas ko a lokacin mukhtar din kan tauna tsakuwa wani lokaci.

Hajiyan da za'a yiwa sannu a gaisheta ita ke faman yiwa kariman sannu tare da gaisheta,lukman ya koma gefan hajiyan yana gaidata cikin dari dari suke gaisawar kamar suruki da suruka duk don kada su batawa karima rai,baki sumayya ta saki tana kallon abun mamaki bayan hajiya ta bude flask din da aka kawo mata,wani gantalallen soyayyen dankali ne da rabin wainar qwai babu ko tea amma hajiyan sai godiya da sannu take mata
"Saidai yau kici haka hajiya don kafin na fito jikokin naki sun shanye shayin"
"Ai babu komai,idan baka yiwa jikanka ba wa zaka yiwa" ta fada fara'a kamar gonar auduga.

Kallon sumayya karima tayi bayan sumayyan ta gaida lukman wanda ke faman binta da kallo kamar tsohon maye
"Ke baki iya gaida mutane ba" ta fada fuska a tsuke kamar wata uwarta,waigawa sumayyan tayi ta watsa mata kallo
"Su waye mutanen?" Ta tambayeta bayan ta tsareta da ido,sai kawai taji sumayyan ta mata kwarjini da irin kallon da take mata,janye idonta tayi ta dubi hajiya
"Hajiya kina gani dai a gabanki ko?" Ta fada cikin zafin rai,lukman yayi saurin karbewa
"Bana son rashin zaman lafiya fa sumayya a gida na kinji ko?" Kallon da wa kazo ta watsa masa sannan ta dauke kai,hajiya cikin rawar jiki tace
"Ke yarinya,farincikinmu shine farincikin karima,saboda haka dole ki mata biyayya ki kiyaye" girman hajiyan take gani,saboda haka ta dan rusuna
"Insha Allahu hajiya kiyi haquri" ta fadi da sauri tana shigewa kitchen din hajiyan don bata son ma ta sake kallon fuskar lukman bare ta karima.
Chapter 48 · 0% Book details