← Book details Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 154 OF 226

Sashe 154

Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda ya fita wunin baki daya bai zauna ba,gagarumar matsala ce ta taso cikin companyn tsakanin qananun ma'aikata ta qabilanci,wanda hakan har ya kai kunnen hukumar qasar,tun jiya abun ya faru amma ba'a sanar masa ba sai yau yana sauka qasar,kasancewar akwai jinsin daban daban kuma 'yan qasa kala kala dake aiki qarqashin company,tunda ya fita banda coffee cup biyu babu abinda ya sanyawa cikinsa,shaf har ga Allah ya manta da ita baki daya,har sai da aka idar da sallar magariba cikin masallacin dake cikin kamfanin,yana tsaka da azkar ya tuna,katsewa yayi cikin hanzari ya soma lalubar wayarshi,sai ya tadda ya barota a office,cikin hanzari da sassarfa ya miqe ya nufi office din,inda yake rataye keys yaga key din dakin,sai a sannan ya tuna da rufeta ma yayi,hakan ya sanya babu shiri ya kira P.A dinshi yace ya sallami kowa sai gobe zasu qarasa zaman,yayi kiran drivansa yace su hadu a parking space.

A gaggauce suka tsaya wani gun saida abinci da bashi da tazara da kamfaninsa inda anan yake order din abincinsa yayi musu takeaway,sunyi mamakin ganinsa saboda kiransu yake kawai su kai masa yau sai gashi da kanshi,bazai iya jira bane kawai shi yasa yayi hakan,abinda ya saba ci da dare tayi order,ita din baisan me take so ba sabida haka kawai ya saimata abinda yaga amira tafici idan tafiya irin wannan ta kama,tafiyar minti arba'in cif tsakanin companyn da hotel din suka isa,ficewa yayi daga motar dauke da kayan yana bashi umarni cikin harshen nasara kasancewar dan india ne ya gyara parking din motar ya bada key din a reception.

Tana daga kwancen taji ana yunqurin bude qofar,sai ta sake tsurewa ta zaro ido tana duban bakin qofar,a nutse ya turo qofar ya shigo kana ya maidata ya rufe,a kanta idanunshi suka fara sauka,sai ya tako a hankali zuwa inda take kwance wanda tuni ta runtse idonta da hawaye ya jiqe zara zaran gashin idonta,durqusawa yayi ya gabanta yana sauke ledojin tare da cewa
"Na manta da ke ne,tashi ga abinci kici" haushi ya qumeta,ya manta da itama kenan tsahon awanni sabida rainin wayo,sai ya miqe bayan ya gama bude mata ledojin yana cire suit din sama
"Wannan amanar da kace zaka riqe ce?" Ta furta cikin subutar baki muryarta na rawa,batasan zai fito ba maganar,abinda ke zuciyarta ne kawai,cak ya tsaya da abinda yake,ya sake takowa a hankali bayan ya janyo wata kujera mai siffar zero wadda jikinta baki daya cushion ce katifa ce baga da nauyi ya ajjiye gabanta
"Am so sorry" ya furta yana janyo ledojin gabanshi,da mamaki ta daga idanunta ta dubeshi,batayi zaton jin kalmar daga bakinsa ba,bai dubeta ba ya fito da soyayyar shinkafa da gasashshiyar kaza,bayan ya ajiye robar fresh milk data tataccen ruwan inibi,kusan wadan nan sune abun shansa,cikin park din akwai wani dan plate na qarau mara qwari,a kai ya juye mata ya sanya cokali sannan ya daga kai ya dubeta
"Tashi kici" tazarar sakan uku kafin ta miqe cikin rashin cikakken kuzari tana goge qwalla,idonsa ya dauke daga kanta,ya tsani kuka,musamman wannan kukan da yake jin shi ya zalunceta,baison zalunci shi yasa yake jin kukan har ranshi,kaman fushin baba zai sauka a kansa haka yake ji,can qasa bayan ya kauda kansa wani sashe yace
"Stop crying" bata amsa ba illa jan plate din data yi ta soma tsakuran abincin,baifi loma biyar ta kai cikinta ba taji cikinta ya dunqule waje guda,take ta soma yunqurin amai,almustapha dake gaban t.v ya waiwayo yana dubanta,kafin yace wani abu tuni ta fara kelaya aman,a gaggauce ya qaraso ya tsaya kanta,baisan ya akeyi ba,baisan me ake cewa ba,sai data gama tsaf sannan ya miqa mata ruwa ta kuskure bakinta,ta rasa inda zata zuba yace
"Zuba anan" yana danna waya,jikinta ta janye gefe tana maida numfashin wahala,magana yayi a recption,cikin qanqanin lokaci saiga leburori,ya matsa musu yana tsaye harde da hannaunshi a qirji har suka kammala gayarawa,jifa jifa yana dora idanunshi a kanta,suna yunqurin ficewa wani ma'aikacin ya sake shigowa da butar shayi da qananun cups,sai da suka fice ya maida qofar ya rufe sannan ya nufi inda butar shayin take,ya tsiyaya cikin daya daga cikin kofunan ya qarasa inda take ya miqa mata
"Karbi" ya fada a taqaice,hannunta na rawa ta amsa sai ya bita da kallo,sai da yaga ta shanye baki daya sannan ya miqe ya shige toilet.

Tsahon awa guda sannan ya fito daure da rigar towel wanda da kadan ta zarta gwiwarsa,hakan ya sanya kwantacciyar gargasarsa data sha ruwa kwanciya luf,idanu suka hada sanda yake fitowa,ta dauke idanunta da sauri ta maida idonta ta rufe,tana jin yadda ruwan dumin ke warware hanjinta,gun jakar kayansa ya nufa sai yaji babu komai ciki,hakan ya sanya y nufi drower din ya bude,cikin mamakin yadda kayan ke jere a tsare yake kallonsu,kadan ya waiwaya yana son satar kallonta sanda ransa ya raya masa ita ta gyara,tunda dakin na rufe bare yace wani ne yayi,kayansa ya diba ya koma toilet ya saka sannan ya fito,pyjamas ne na maza me v.neck wanda igiya ce ke daure da su,wani sashi na gashin dake cike a qirjinsa kwance luf ya bayyana,dogon wando ne da ita sai takalmi slippers a qafarsa,gun ya sake dawowa ya janyo abincin ya miqa mata,da idanu ya mata nuni data ci,fuska ta soma yamutsewa tana tsoron kada ya sake dawowa,kafeta yayi da idanu wanda hakan ya tilastata yin yadda yake so din,baki daya cin abincin kawai take saboda yadda ya rutsata da idanunshi yana bibiyar motsinta,qarar wayarshi ce kawai ta ceceta,miqewa yayi daga gun ya koma gefan gado bayan ya dauki tashi ledar ya janyo center table ya dora,baki daya abincin daren nasa chips ne da hadin salad kamar ko yaushe da ruwan inibi,sai fresh milk wadda ya jima bai shata ba saboda wasu dalilai,baya kuma sha din sai ya tabbatar bai da matsala,sai da ya zauna sosai sannan ya fara amsa wayar.

Ya jima yana wayar wanda har batasan sanda ya kammala ba sakamakon gyangyadi data soma a wajen data gama cin abincin saboda wata mutuwar jiki da kasala data rufeta,wutar dakin na akashe sai hasken wasu qwayayen bacci guda biyu masu duhu,jikinta ya bata yayi bacci saboda haka ta miqe ta kunna haske wayarta ta fidda doguwar rigar baccinta wadda keda santsi,silk ce sosai mai bin jiki ta wuce bandaki,cikin sanda take takawa don kada ya motsa har ta shiga,saidai abinda bata sani ba idanunshi biyu,hakanan yana iya ganintar tar sakamakon ya jima cikin duhun dakin shi yasa bai ganin duhun sosai,so yaje yayi bacci amma abun ya gagareshi,dalilin da yasa baya shan irin wadan nan abubuwa kenan,duk sonshi da fresh milk da yoghourt ya haqura da su don ya zauna lafiya,yana son kunun aya matuqa haka shima ya ajjiye shi gefe,koda yaje gida ya tadda ummee tayi saidai yace baisha,acan ta wanke hannunta,sannan tayi brush ta sauya kaya sannan ta fito.

A hankali ta ja qofar toilet din ta rufe,idanunshi suka sauka a kanta,haske pink din rigan baccin na yawo cikin dakin,binta yaci gaba da yi da idanu har ta qarasa bakin mudubi ta dauki turarenta ta mutsetsike jikinta duk idanunshi na biye da ita,take qamshin humrar ya karade dakin ya isa har inda yaje kwance,bai san mai yaje sake jansa ga kallonta ba har ta kai saman doguwar kujerar ta haye tana karanta addu'o'i tana shafe jikinta da su,bayan ta yane jikinta da mayafi ta kwanta tana rufe idonta,baki daya abincin data ci ya sanya mata mutuwar jiki,bacci kawai take da buqatar yi.

Sai a sannan ya dauke idanunshi yana sauke numfashi hadi da ambatar sunan Allah,wani irin juyi yayi ya sauya yanayin kwanciyarsa idanunsa a rufe yana son tilastawa kansa yayi bacci,saidai yasan yaci qarya,ba kasafai a irin wannan yanayin yake iya bacci ba,yayi juyi yafi sau arba'in,take ya soma ganin baiken kansa,mai ya kaishi shan abunda yasan zai zame masa damuwa,sannan ya bige da kallon abinda baiji cikin ranshi har yanzun nashi ne,a qalla ya kwashe kusan awanni biyu a haka kafin ya fara samun sassauci,gumin da yaji yana yi shi ya tabbatar masa da komai yazo qarshe,kimanin minti talatin sannan ya miqe ya kunna qwan dakin ya shige bandaki.

Fitsari ne ya farkar da ita,ganin saman gadon wayam ba kowa ya sannan ga motsin ruwa a bandaki ya sanyata zaman jiran fitowarsa,minti biyar tsakani ya turo qofar ya fito daure da towel jikinsa jiqe da ruwa,baiyi tsammanin farkawarta ba,dauke kai yayi cikin dakewa da daure fuska tamkar ita ta kar zomon ya bude ma'ajiyar kaya,yayin da ta miqe wuf ta fada bandaki saboda wani nauyi da kunya da suka lullubeta,ganinshi a haka yayi matuqar yi mata tsauri,bata fito ba sai data bada tazarar minti goma sannan,saman abun sallah ta ganshi yana salla,da sauri ta koma saman kujerar ta qudundune bayan ta duba agogo ta tabbatar tsakiyar dare ne,ya bata aqalla awa daya kafin ya koma saman gadon ya kwanta bakinsa dauke da tasbihi a haka bacci ya daukeshi.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

8⃣1⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis,aslih li sha'any kullahu,wala takilni ila nafsy darfata aynin*
___________________________________

Qarfe takwas na safe ta farka bayan baccin data koma bayan ta kammala sallar asuba,babu kowa a dakin sai ita daya,alamu sun nuna ma ya fita,gefe daya ta tarar da kayan break fast,komai da komai irin wanda zata iya ci,toilet ta shiga tayi wanka ta dawo ta gyara dakin sannan ta sanya kayan taja kayan ta karya,kwanciya ta sake yi bayan ta gama,ba dadewa wani baccin yayi awon gaba da ita,bata farka ba sai data ji ana knocking qofar,ta miqe ta isa ga qofar,ga mamakinta a bude take muqullin ma na jiki yau bai rufe ba kenan.
Chapter 154 · 0% Book details