← Book details Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 222 OF 226

Sashe 222

Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dukkansu suna zaune a babban falon dake asibitin wanda na likitan ne ya basu su zauna,kowanne ka dubi fuskarsa cikin baqinciki take,hatta da mazan dauriya kawai suke,saidai almustapha bai iya daurewar ba,karon farko da suka soma ganin hawaye kan fuskarshi,abinda basu taba gani ba tsahon rayuwarshi da su,ummi ma hawaye take sharewa lokaci zuwa lokaci,yayin da sumayya ke kuka tuburan,idanunta da fuskarta gaba daya sun kumbura,yayin da fuskar ta hadu tayi jazur,ummi dake gefanta ita ke lallabata ta bawa yaran nono,tana shayar da su cikin hijabin tana kuka,ba shakka mutuwa kota wanda baka sami bane tana da ratsa jiki da sanya wani sabon imani a zuciyar dan adam,ballantana wadda ta sani sun zauna tare tsahon shekara nesa da juna,gab da zata tafin kuma sukayi zama irin na yaya da qanwa,yaushe zata manta haka?,haka mutuwa take,takan dauke mutum a sanda bai shirya ba hakanan masoyansa basuyi sallama da shi ba,sai mutuwar mukhtar ta fado mata,kukanta ya sake daduwa,wanda hakan ya sake karya zuciyar duka sauran,ba shakka sunga irin zaman da sukayi a tsakaninsu cikin sati uku kacal kafin ta mutu,haka suka dinga bata baki kafin su fara tattauna abinda ya zaunar da su din bayan an kai gawar su'ad mutuware.

Alhj abdus samad ne ya fara magana
"Zamu wuce nigeria da gawarta,bama gawarta ba har maman tata ma"
"Amma alhj kaji fa sunce ita khaulat ta samu stroke,haka zamu tafi da ita" cikin tsantsar baqinciki yana goge qwallarsa yace
"Daga rana irin ta yau professor na bar zaman qasar nan har abada,zamu koma qasarmu ta gado da zama,babu abinda na tsinta a zaman qasar nan banda baqinciki da tarwatsewar iyalina tunda har na kasa control dinsu,kowa yana vin gashin kanshi,Allah ya jiqanki su'adah ya gafarta miki" ya qarasa fada yana shafe sabbin hawayen da suka zubo masa da tafin hannunshi
"Hakan yayi,a mata suttura cikin dakin mijinta" inji ummi,da wannan shawarar suka soma neman izinin tafiya da gawar su'ad,cikin kwana biyu rak suka samu kasancewar abun na masu da shi ne.

Cikin dakinta dake abuja aka mata wanka aka shiryata,almustapha na tsugunne gaban gawarta yana mata addu'a,sosai yayi mata addu'a tare da jaddada yafiyarshi a gareta,sannan ya bawa sumayya guri,alhj abdus samad da duk wani makusancinta,inda aka turo mommy a keke,kuka ta saka ta soma magana,saidai maganar bata fita ba'a jin abinda take fada,sakamakon bakinta daya karkace tun faduwar data yi sanda tayi ido hudu da gawar sy'ad tana ihu tana ita daya ta mallaka ya zata yi mata haka,daga nan ta sume,bayan ta farfado kuma ta gamu da wannan cutar,sosai sumayya ta qunshe kanta a tsakanin qafafunta tana sakin kuka sanda aka dauki gawarta aka fice da ita zuwa gidanta na gaskiya,tabbas duk wanda yayi damara don duniya ya kwanceta,Allah ya bamu sa'ar tafiya,kasa mu riskeka sanda kake farinciki da mu ya Allah.

A nan gidan dake abuja suka zauna karbar makoki,kaf 'yan uwan sumayyan ba wanda baizo mata ba,haka yan uwa da abokan ariziqi suka dinga zirya,har eesha ba'a barta a baya ba,tazo jikinta cikin matuqat sanyi,tana tuna yadda suke takun saqa da su'ad din,tana tuna yadda su'ad ta dauki rayuwarta kusan dai dai da yadda itama take jin kanta,hakan ya qara mata mutuwar jiki,sai data dangana da sumayya tayi mata gaisuwa,sannan ta roqi gafararta kan abinda ta nata a baya,murmushi kawai tayi,mutuwa kadai ta ishi mai hankali aya,me ya mata zafi da zata tsaya saka wani mutum a ranta,itakam mantawa ma take da faruwar abin sai idan wani abu ya taso da zai tuna mata da hakan,tace ya wuce har abada,'yan biyu sun jima hannunta,sosai yaran suka shiga ranta,bul bul da su cikin tsafta gwanin sha'awa,duk da mamarsu na cikin alhini amma fes suke,don ummi ke sawa baba uwani ke kula da su akai akai,ba'a maidasu wajen sumayyan sai sun buqaci nono.

Kwanaki bakwai akayi kaman yadda al'ada tace kowa ya watse,aka fidda duk wani abu na su'ad din aka miqawa iyayenta,don almustapha cewa yayi ya yafe,bazai iya amsar komai nata ba,ranan mummy khaukat tayi kukan da bata taba makamancinsa ba,tayi nadamat da bata taba tsammanin akwai kamarta ba,ta dinga kallon sumayya tana son gode mata amma babu baki,iya jinyar su'ad kawai zuwa mutuwar nan ta karanci irin kyakkyawar zuciyar da take da ita,da hannu ta dinga mata godiya haka aka turata kan keken guragu suka fice a gidan.

Washegari kwana takwas kenan almustapha ya taddata tana gyara dakinta,ita daya ce su amatullah suna wajen ummi,duban junansu suke kowa na kallon irin sauyawar da dan'uwanshi yayi,shaida mata yayi zai koma america,amma baya so ta gayawa kowa can ya tafi,din su dubai yace zai koma,fatan alkhairi ta masa don ta fahimci me zai komar da shi din,itama tana goyon bayanshi,bai kamata mutane irin doctor james ace sun kubuta ba haka nan akwai.

Qasa ce da bangarorinta suke da wariyar launin fata da qyama ga musulmai,amma hakan ko kadan bai karya masa gwiwa ba,bai wani tuna cewa shi din baqo bane,ya dan sha wuya amma bai haqura ba sai da ya tabbatar an kamo doctor james an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya,sannan an qwace duk wani license nashi tare da rushe asibitin da ya gina,wanda hakan ya dauki almustaphan tsahon watanni biyar,bai waiwayi gida ba sai bayan wadan nan watanni,satin guda da kammaluwar lamarin,da wani yammaci wanda a wannan lokacin sumayyan na kwance,bata taba jinta cikin matsi da takura irin na wannan lokacin ba,rashin ganin almustapha har tsahon watanni biyar bata zaci ma zata iya jureshi ba,a kusan kullum sai taci karo da saqonshi ta email dinta na ban haquri da alqawarin dawowarshi nan kusa,bata da amsa face Allah ya bada sa'a,ta tsawaita haqurinta qwarai da gaske,saidai har zuwa yau shiru kake ji,duk sanda ummi ko professor sukayi qorafi,takan nuna ita ta bashi dama babu komai yana gab da dawowa.

Qarar wayarta ita ta dawo da ita daga tunanin da take,ta miqa hannu ta daga ta kara a kunnenta ba tare data damu da duba mai kiran ba
"Assalamu alaikum warahmatullah" muryar nan mai daraja da qima a wajenta,muryar nan da take bawa girma,muryar nan da babu tamkarta ita ta ratsa dodon kunnenta,tamkar an cire duk wata laka dake jikinta haka taji wata muvuwar kasala,zuciyarta ta karye,take qwalla ta cika idanunta
"Wa'a laikumussalam warahmatullah" ta amsa masa bayan ta sauke ajiyar zuciya,idanunsa ya lumshe daga can bangaren yana duban kansa a madubi,ya sauya kaman bashi ba,ya rame saidai ya fara cikowa cikin sati guda,zaya so ace sai daya murmure sosai kafin ya koma mata saidai dauki da son ganin ahalinsa bazai barshi ba,sautin yaji kaman na sheshsheqar kukanta
"Ya salam" ya furta yana zama gefan gado
"Ummu abdallah ki yimin rai don Allah ki daina kukan nan" ya fada a tausashe,a hankali ya dinga tsarata cikin kalamai masu taushi da di,har sai daya sauke mata duk wani abu dake cikin zuciyarta sannan ya jefeta da albishir mai dadi
"Rana ita yau,ki jirayi mijinki masoyinki,ki masa kyakkyawan tanadi da tarba ta musamman,ki gayawa daughters(amatullah da amatur rahman)duk wanda nazo na tadda ya fara gwada tafiya shine best friend dina" murmushi mai dauke da sauti ya qwace mata,ba qaramin dadi albishir din yayi mata ba,uwa uba takan yi dariya duk sanda yake magana da yaran kaman sa'anninshi,saboda tsabagen wayo hat sun soma shaida muryarshi da fuskarshi ta hanyar hoto da kuma waya da sukeyi
"In sha Allah" ta furta cikin tsantsar farinciki,a qalla sai da suka kashe awa daya cikakkiya yana sake wa soyayyarshi service kafin suyi sallama,ya jiqata ya tsumata da kalamanshi qwarai da gaske,wanda ta dinga sakin murmushi ita daya kaman tababbiya,kasa zama sashen tayi,ta zura hijabinta ta miqe zuwa sashen ummi,inda su amatallah suke can tun sassafe.

Sanda ta sanarwa da ummi zancan dawowar cewa tayi cikin zolaya
"To sai a fara shiri da kyau ko?" Kunya ta kamata ta sadda kai tana gyarawa amatallah kalbarta data soma zamewa.

In sha Allah last page na zuwa muku nan da anjima,ku zama ready........

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽

✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

1⃣0⃣7⃣

*bamu kasance masu azaba ba har sai da muka aiko da dan aike(manzo)*

*haqiqa mun aiko ka manzo(annabi muhammad)kan al'ummah,Allah ya isa shaida*

*wanda ya yiwa manzan Allah biyayya haqiqa yabi Allah*

*haqiqa mun shiryar da shi hanyoyi biyu(dan adam)kodai ya zamanto  mai godiya ko ya zamto mai kafircewa*

*haqiqa mun halicci mutum  daga digon maniyyi dake cakude da ruwan mace da namiji muna jarrabashi da takhlifi(nauye nauye na shari'a Allah na nufin jarrabarsa a sanda ya dace)saboda haka muka sanyashi mai ji mai gani*

*haqiqa wannan gargadi ce ga talikai to wanda yaga dama sai ya riqi hanya izuwa ubangijinsa*

_____________________________________

Sosai ta shiga gyara cikin satin bata zauna ba,ummu kam ta daure mata qarqashi ta kwashe mata su amatallah,duk wani abu daya kamata ta aiwatar da shi,har kwaskwarimar bangarenta sai data yi,kafin ranar dawowarshi komai ya zama neat.

Ranar da zai dawo din mahmoud ne zaya je dauko shi,kafin isowarshi ta shirya tsaf cikin shigar cikakkiyar bahaushiya atamfa,ga mata cas a jiki dinkin ya zauna mata,yaran duka ta shiryasu cikin kaya iri daya komai da komai,sun fito sak a twince dinsu,sunyi wani kyau da girma,sanda taji isowar tasu sai ta kasa zaune ta kasa tsaye,kai tsaye wajen baba ya wuce,ya taddashi tare da matan nashi,ba wanda baiyi farinciki da ganinshi ba,sai a sannan ya yiwa baban bayanin me ya zaunar da shi,shiru baban yayi yana jinjinawa namijin qoqarin da yayi cikin qasar daba tashi ba,aqalla ya kusa mintuna talatin kafin ya wuce sashensu.

Awa uku da shigowarshi amma ta kasa zama,sai qirqirarwa kanta aiki data yi,zirga zirga take tsakanin kitchen da falo,duk wani motsinta yana kan idanushi,ya ganeta sarai,tana nufin sai ya sake sabon yaqin neman soyayyarta?,kunyarta keson musu shamaki,yana zaune ne da boxer da singlet fara qal bayan yayi wanka,ba abinda ke fita jikinsa sai qamshi mai taushi na turaren safirul hubb da wasu nau'in turarukan,tuni amatallah da amatur rahman sukayi bacci kan qafarshi dake miqe,sai ya yunqura ya miqe da su saman kafadarsa sanda ta sake zuwa ta kwashe duk abinda yayi amfani da shi zuwa kitchenbda alama wanke wanke zata yi,sai da yaje ya kwantar da su din sannan ya nufi kitchen din.
Chapter 222 · 0% Book details