← Book details Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 168 OF 226

Sashe 168

Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai da komai ya kammala sannan ta farga,nauyi da kunya suka sanyata kuka,itakam me yasa sam bata da wayo ne bata ganema wayonshi sai ya gama budirinsa,yana jin kukanta a sanda yake hutawa yana sauke numfasji tare da shaqarsa d'ai d'ai,yana jin wani wasai a qirjinsa da gangar jikinsa tamkar waccan karon,wata iska ta musamman yake ji yana shaqa a qofofin hancinsa,yatsunsa ya tura cikin sumarta yana yamutsa gashin ta anutse,santsi da sulbinsa na aika saqo har cikin qwaqwalwarsa,hakanan yana sake burgeshi,salon yadda yake matan ya sanya kukanta raguwa,sannu a hankali wani irin bacci data jima bata ji irinsa ya ziyarceta.

A nutse ya zareta daga jikinsa ya kwantar da ita saman filo,hannunshi ya sanya ya yaye gashinta da ya rufe fuskarta,fuskartata ta bayyana na mai dauke da lemar hawaye
"Lazy girl" ya fada murmushi na kubce masa,a hankali ya sauka daga gadon yana maida tufafinshi,ya taka ya qarasa gaban mudubin dake dakin,hannunshi ya dora kan fuskarshi yana shafata a hankali,murmushi ya kuma subuce masa sanda ya tuna kalaman da suka dunga subucewa daga bakinsa suna fitowa cikin awannin da suka shude,shi kadai ya soma magana da kanshi
"Wai meke damunka almustapha?,kaine kuwa?,yaushe ka koyi maqalema mace?"
"There is something special tattare da ita" ya fada a fili,girarsa ya dage yana tambayar kansa tare da son tabbatarwa
"Really?" Ya kuma tambayar kansa,murmushi ya kuma saki yana dan dukan kanshi
"U r crazy man,gaskiya hamza ya fadi kenan" kafadanshi ya daga ya juya zuwa toilet don tsaftace kanshi.

Wannan karon ma haka ta dinga qunbiya qunbiya,ita kanta batasan ya akayi ta sake masa haka ba,kunyar kanta ta dinga ji,shikam yana zaune abinshi yana karyawa,yayin data kasa sakewa riqe da cup din tea tana juyashi da cokali,ta lura tun dazun yakeso ya takaleta da magana saidai taqi bashi fuska
"Hey" ya fada murya can qasa,fararen idanunta dake burgeshi ta daga ta dubeshi
"Come here" ya bata umarni yana dubanta da wani kallo qasa qasa,bata son musu tsakaninsu,sai ta dire cup din ta miqe zuwa inda yake,inda ya nuna matan gabansa ta dawo ta zauna,batasan me yasa yake yawaita son kiran sunanta ba,ci gaba yayi da dubanta kamar dalilin da ya sanya ya kirata kenan,a qalla minti goma sannan ya ture plates din dake gabansu
"Let me tell you something,baki iya making love yadda nakeso ba,sai kuka,sai kunya,wadanne irin lusaran maza kika taba aura?" Maganar ta mata zafi sai ta daga kai tana dubanshi,tuni qwalla ta cika mata ido,wannan cin fuska ne,yana nufin har da mukhtar cikin lusaran?
"Can i teach you how i want you to be?" Kai ta girgiza,sai ta saki kuka,dariyarsa yake boyewa,hawayen dama kawai yakesin gani cikin idanunta,a jiya ya kura da wani kyau da idanuwanta sukayi sadda qwalla ta cikasu,kamata yayi suka miqe tsaye baki dayansu,bai saketa ba har sai da suka isa gaban mudubi,yana tsaye a bayanta
"Look at your self,i think crying is ur hobby ko?"duban fuskar tata yayi kamar yadda yace,shabe shabe da hawaye kamar ta abdallah,sai ta dubi tashi fuskar,wata kunya ta kamata tayi qas da kanta,mannata yayi a jikinta ya dora kansa saman kafadarsa,hucin numfashinsa ya shiga kunnenta,tsigar jikinta ta tashi
"na baro wata qasa na iskeki,wannan tarbar na cancanta?,you must learn yadda zaki dinga tarbata..."
"Ai na iya" ta fada da sauri cikin subutar baki saboda yadda ya sake mannewa da jikinta,murmushi ya subuce masa ganin yadda ta amsa da gaggawa tun bai gama fadin abinda zai fada din ba,kallonshi take tana duban yadda yake murmushin,wani kyau taga yayi mata
"Daina kallona" ya fada yana dan hade rai kaman bashi ba,itama sai ta sake hade rai,juyo da ita yayi suna fuskantar juna hannayenshi aka qugunta,a hankali tamkar mai rada ya soma zayyano mata dukkan yadda yakeso ta dinga masa idan suna tare,idan ba gab da su kake ba ba lallai kaji me yake gaya mata,wayyo Allah kamar qasa ta tsage ta shige haka ta ji,idanunshi a kanta yake maganarshi kanshi tsaye,ko kunyan duban idanunta baiji,wanne irin mutum ke shi da bai da kunya,zille zille ta soma yi saboda yadda maganar ta soma fin qarfin kwanyarta,muryarshi ratsata take,salon maganarshi daban ne,murya ce mai matuqar tsada da daraja a tarihin rayuwarta,sai yayi shiru ya tsaya cak yana dubanta tana mutsu mutsu
"Haddacewa nake so kiyi,shi yasa nake gaya miki a yanayin da ba zaki manta ba" shiru tayi ta rasa abin cewa,karata yayi da jikinsa cikin qirjinsa
"Tsaya anan idan kin gaji da tsaiwa ne naga qafafunki na rawa kici gaba da haddace abinda nake gaya miki" sake sauya salon muryarshi yayi yana ci gaba da gaya mata,wannan karon hatta da bugun zuciyarta sai da ya sauya,ta rintse idanuwanta tsigar jikinta na tashi,ya kwashe a qalla minti talatin kafin ya dan janyeta
"Ina so na gani practically,zamu fara gwada wannan,shirya min ruwan wanka,zanje na dawo qarfe hudu zamu wuce abuja ki zama ready" dama neman gun kubuta take,da hanzari ta juya har qafafunta yana sarqewa har sai da yace
"Kula" bata bi ta kanshi ba ta shige toilet din,gefan bathtube ta zauna tana sauke numfashi kamar tayi gudun famfalaqi saboda yadda bugun zuciyarta ya qara gudu,maganganunshi ke mata yawo ko ina cikin sassan jikinta,muryarsa mai mai dauke da wani amo na ratsata tamkar yanzun yake maganar,curewa tayi waje daya murmushi na subucewa a tattausan lebanta.

*kuyi manage sabgogi sun sako kai,sai ranar lahadi idan Allah ya yarda*

*gareku 'yan uwana al'ummar qasata,ka sani cewa quri'arka itace 'yancinka,kana da damar zaben duka mutumin daka ga dama,quri'arka zata iya zama sanadin jin dadi da walwalar al'ummar qasarka,hakanan zata iya zama silar shigarsu qunci,saidai kar ka manta da wannan,RANAR QIYAMA ZAKA TSAYA GABAN MAHALICCINKA KA BADA HUJJARKA NA DALILIN ZABAR MUTUMIN DAKA ZABA DIN,kada ka manta tsayawa gaban wanda ya halicceka babban lamari ne,mu tsaya mu zabi shugaba na gari,wanda zaton alkhairin da al'umma suke masa ya rinjayi na sharrin,MU ZABI CANCANTA BA JAM'IYYA BA,hakanne kadai zai sanya mu saka qwarya a gurbinta,kada mu yarda wasu su shiga rigar jam'iyya su cucemu,mu duba cancanta da dacewa,mu yiwa kamu alqalanci,kada mu jefa kanmu a fitina da musibar da bamusan ranar qarewarta ba,Allah kasa mu dace ka yi mana jagoranci kada ka barmu da iyawarmu*

*muyi zabe lafiya cikin aminci da kiyayewar mahaliccinmu*

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

8⃣6⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah madaukakin sarki yana cewa*

*haqiqa muminai 'yan uwan juna ne kuyi sulhu tsakanin 'yan uwanku*
_____________________________________

           Qarfe uku saura na rana suna zaune bayan motar driva na jansu,tattausan tafin hannunshi na cikin nata,yana zaune gab da ita sabanin daa da kowa ke zama tashi shiyyar,kunya ta sanya ta maida kanta bangareb window tana duban hanya cikin baqin glass din da motar take da shi,yatsunsa ya sanya ya juyo da fuskarta gareshi,ya dage gira daya
"Ina son miki qari kan abinda na fadi miki dazu,zayyano min naji kin haddace?" Wata iriyar kunya ta kamata,ta yaya zata iya maimaita kalaman dazu masu nauyi da girma,kanta ta qwace daga hannunshi ta sake maida kanta ga window murmushi na son kubce mata,ganin haka ya sanyashi janyota jikinsa ya sanya hannu ya matseta
"Maganinki zanyi,naga alama baki fara daukan lacture ko daya ba,yadda nake daban haka nakeson matata ta zama ta daban,you must be ready,qarin karatu guda daya,dole ki koyi zama a jikina,bazan lamunci zama a mabanbantan wurare ba ba,idan baki son haka ki daina zama waje daya da ni" ya fada yana shan mur,baki ta murguda wanda yayi nasaran hangota,cikin zuciyarta tana mita,wuta ce ta dauke mata sanda taji hannayenshi cikin rigarta,ta daga kai ta dubeshi tana narke fuska,idanunshi lumsassu ya zaro mata waje yana mata nuni data daina kallonshi,tilas ta sauke qwayar idanunta,tana ji tana gani haka ta haqura ya dinga yadda yaga dama da ita,sai da yaji tsaiwar motar sannan ya zare hannunshi da jikinshi,hannun nasa ya sanya ya gyara mata rigarta da yafen mayafinta,wanda atamfa ce a jikinta ta dora mayafinta saman ka,kanta na a qasa cike da jin nauyi har ya kammala,bata dago ba sai da taji yace
"Oya,lets go".

        Tayi zaton ganinta a airphort sai ta gansu cikin wani makeken guri wanda yaso yi mata zubi da gida,mutane ke kai kawo,kama daga qananun yara saffa saffa da kuma manya,yana fitowa wasu tarin ma'aikata suka qaraso wajem,cike da girmamawa suka tarbeshi,a mutunce yake gaisawa da su,sannan ya saka hannunshi cikin na sumayyan sanda suke masa rakiya zuwa cikin wani babban gini dake gabansu,ta daga kanta a hankali a naj taci karo da wani rubutu cikin manyan haruffa daga saman gidan wanda aka rubuta MUHAMMAD ALMUSTAPHA ORPHANS HOUSE,cikin ranta take rayawa gidan marayu dama gareshi.

       Babban office aka bude wanda shine mallakinsa,office din nada girma qwarai,akwai kyau tsari da wadatar tsafta ko da yaushe,sun sani haka yake,ya saba kawo musu ziyarar ba zata,sai a gama waya da shi yau anjima ku ganshi cikin gidan,duka yana haka ne saboda ya tabbatar kowa ya riqe amanar aikin da aka bashi,saman doguwar kujerar cusion suka zauna shi da ita kafin su shiga gaisawa da wadanda ya dorawa nauyi da alhakin kula da gidan,cikin nutsuwa da sanin aiki kowa ke masa bayani kan nashi bangaren da yake riqewa,kusan mintina talatin kafin ya buqaci kewaya fadin gidan.
Chapter 168 · 0% Book details