← Book details Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 226

Sashe 92

Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

        Tun sumayyan na janye jikinta har ta saki jiki,nafisan ita ta soma koya mata cumputer,ta naqalceta sosai,itama halayen nafisan sun burgeta,yadda ta tsammaci halin masu kudi duka guda ne ashe ba haka abun yake ba,taga misali daga kan nafisa da kuma amira,a yanzu haka amiran ko yaushe na kan kiran sumayyan,har tana mamakin bata ganin kudin da take qonewa wajen kiran nata?,kullum nafisan na kan qorafi da mitar yadda sumayya taki sakin jiki da ita bayan ta dauketa 'yar uwa,kan hakan har tasowa sukayi takanas ita da mai gidanta suka zo suka kawowa uncle farouq qarar sumayya wai bata sonsu,wanda tilas hakan ya sanya ta soma sakin jiki da itan,shima mijin nata auwal da yake dan taya bera bari ne ya biye mata,akwai tsantsar qauna shaquwa da fahimtar juna tsakaninsa da matarshi,qauna ce mai yawa da tsafta tsakaninsu,wani lokaci idan sumayyan taje taga yadda ake zuba soyayya kunya kamata take,takan ce bari naje gida,bazan iya wannan badalar taku ba,dariya nafisa ke saki
"Wallahi sister(haka take ce mata)sai kin fini tsula tsiya,bari kiyi auren" kyabe baki sumayya keyi
"Wane aure,ai mu mun bar muku shi,mu da shi sai a qiyama" kalaman da sun jima suna daurewa nafisa kai,ga tsammaninta sumayyan budurwa ce bata taba aure ba,sau tayi yunqurin tambayarta sai kuna taja bakinta ta tsuke,ba kasafai take son yiwa mutum shishshigi cikin lamuransa ba,randa taga sumayyan na waya da abdallah a ranar ta kasa daure tarin tambayoyinta
"Ke wallahi baki isa ba,kullum ki sani a duhu ki gudu,to yau kam sai kin gayan wace ke" nafisan ta fada cikin yin kicin kicin,dariya tayi mata
"Wace kuwa ni din bayan sumayyan da kika sani" sakinta nafisan tayi tayi baya ta zauna
"Shikenan tunda haka kika ce,na fuskanci baki daukeni yadda ni na daukeki ba,inda kin daukeni yadda na daukeki da ba zaki boyen komai dangane da ke ba,tunda dan uwa bai boyewa dan uwansa sirrinsa,naga har shawara nake dake sumayya kuma ina ganin haske cikin dukkanin shawarar da kika bani" shiru tayi ganin yadda fuskan nafisan ta nuna rashin jin dadi qarara,babu shakka dukkan wata qauna ta fisabilillahi nafisan ta nuna mata,bata shayi ko shakkar yin kowacce shawara da ita,ajiyar zuciya ta saki
"Shikenam kiyi haquri mom khalid,yanzu ki bari naje gida na yiwa anty abincin dare kinga bata nan sun fita da uncle,amma na miki alqawarin idan na kammala zan dawo na baki labari na" sake hade rai tayi don ta nuna mata gaskiyan abinda take fada
"Na amince saidai da sharadin idan kinzo nan gidan zaki kwana,tunda kin sani yau dadyn khalid bai gida kwanan makaranta zaiyi" dariya sumayyan ta bushe da ita ganin yadda ta hade rai tana mata muzurai kamar wadda ta hadiyi kunama
"Idan anty ta barni zan kwana"
"Zata ma barki saidai baki so ba" bata qara cewa komai ba ta miqawa khalid hannu dake kallonta,jira dama kawai yake tace su taho,wani shaquwa sukayi sosai da yaron,ganinsa take kamar abdallanta,ta sabi khalid din suka fice nafisa na binsu da kallo,murmushi ta saki tana jin dadi,jin sumayya take kamar ciki daya suka fito,Allah shike hada qauna da soyayya a tsakanin mutane har ma da jinsin dabbobi,haduwar jini wani abu ne na daban daga Allah.

      Tana zaune kan sofar dake dakin baccin nafisan sanye da nata kayan bacci cotton masu kauri riga da wando wadatattu,khalid na saman cinyarta yayi bacci,hannunta na saman sumar kanshi tana shafawa don bai jima da yin baccin ba,lokaci lokaci takan daga kai ta dubi nafisa dake tsaye gaban madubi tana ta faman shafe shafe da goge goge bayan fitowarta daga wanka,mamaki duka ya cikata bacci akewa wannan hidima haka,gaskiya mana ko yaushe fatar nafisan kamar ta dan jariri,duk da fara bace choculet ce,har haqurin sumayyan ya qare ta tanka
"Wai duka wannan wankan naki meye amfaninshi bayab wanda ake mawa baya nan mrs auwal kamar zaki sauya fata?" Murmushu tayi tare da ajiye body mist da ta fesa ta dubi sumayyan
"Au sai noor yana nan sannan zanyi haka,ai ya riga da ya zame min al'ada ta"
"To ai saiki bada himma,nikam na fara jin bacci,ina jin labarin nan bai yiwuwa sai gobe" ta fada tana gyarawa khalid kwanciya saman gado,da sauri ta zura 'yar saman rigar baccin nata ta qaraso inda sumayyan take itama ta haye gadon tana cewa
"Sorry,na kammala,kema dab kike daki fara wannan sanaben ai" baki ta kama
"Niii,rufan asiri,ku din dai sai kuyita yi,haka naga laila ma 'yar qwailarta da ita ta fara daukan course" dariya nafisa tayi
"Wallahi da gaske nake,jiya na hau internet,naga D&G sunyo sabbin mai na gyaran fatar fararen mata,set ne harfa perfume,sure,da subulunshi,na riga ma da na siya miki,jiran isowarsa kawai zamuyi,a yadda suka ce gobe zasu kawo min" shiru tayi tana saurarenta,wannan wace irin qauna nafisan ke mata haka?,daga ganin abu babu wanda ta tuna sai ita din?
"Am ready fa,ke nake jira" ta katsewa sumayyan tunani tana dubanta.

       Gyara zamanta tayi bayan ta jingina jikinta da bango,a hankali ta soma warware mata wace ce ita,babu abinda ta boye mata,sumayya kuka nafisa kuka,babu wanda zai rarrashi wani,bala'in tausayin sumayyan ya kama zuciyar nafisa,yayin da sumayya ta tsokano wani danqararren tabo da dama har yau bai ida warkewa ba,janyo sumayya tayi ta kifa kanta saman cinyar nafisan tana ci gaba da kukan tana bubbuga bayan itama tana tayata ba tare da ta tsaidata ba,cikin zuciyarta taba cike fal da mamakin irin rayuwar da sumayya tayi,bata taba hasashen zata iya yin rayuwa irin wannan ba,shi qunci da matsin rayuwa gami da QADDARA hadi da JARRABAWA kenan babu ruwansu da girma ko qanqantar shekaru?.

Sai da zuciyarta ta samu salama sannan nafisa ta soma magana
"Ashe akwai irin wannan rayuwar a duniya?,rayuwar da mutum mai kimanin shekaru kwatankwacin nawa zaya fuskanceta da tsanani har kamar haka?,na jinjina miki sumayya,Allah ne kadai yasan me ya tanadarwa rayuwarki,irin wannan yarda da qaddara da karbarta hannu bibbiyu bau tashi a banza,Allah ya jiqan mukhtar ya raya mana abdallah,kici gaba da haquri,amma kada ki sake hasashen ba zaki sake yin aure ko jin dadin rayuwarki ba,kin sani kowanne bawa da yadda Allah ya tsara masa zai rayu,dole kowa ya rayu bisa tsari da doron da mahalicci ya QADDARA,kici gaba da addu'a,zan tayaki da yardar mai duka,yayi miki zabin kyakkyawar rayuwa,ya cire dukkan qunci da damuwa da kika taba tsintar zuciyarki a ciki",ta jima tana fidda hawaye masu dumi wadanda suka dinga wanko zafi da radadin dake cikin zuciyarta maganganu ta dinga bata masu kwantar da hankali har ta samu nutsuwa cikin zuciyarta.

Washe gari ta tashi fuskarta ta dan tasa saboda kukan data raba dare jiya tana yi,baki daya nafisa sai ta damu tana ganin kaman laifinta ne,murmushi sumayyan ta dinga tana girgiza kai tana qoqarin nuna mata ba laifinta bane,dole ne ga duk mutumin da yake da miki cikin rayuwarsa ya koka duk sanda wannan ciwon ya motsa.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

6⃣7⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

Allah madaukaki yana cewa

*duk wanda ya sallamawa Allah dukkan lamuransa alhali yana mai kyautatawa haqiqa yayi ruqo da igiya qaqqarfa wanda bata tsinkewa(yankewa/rabewa)*

_____________________________________

        Wuni nafisa tayi ta kasa sukuni da tausayin sumayya,a haka auwal ya dawo ya taddata,baki daya wani qaunarta na sake shigarta,haqiqa bata yi zaben tumun dare na aminiyar qwarai ba.

         Washegari da kanta taje gidan anty dije dauke da ledar mayuka da turarukan data siya matan,dariya sumayyan ta dinga tana kallon tarkacen kayan,ko ba'a fada mata ba tasan cewa sunfi qarfin mai rangwamen gata irinta,saboda zuwa yanzu kanta ya soma budewa,tana iya gane abu mai tsada,balle ta san nafisan sarai,komai nata designer ne,kuma komai nata a set dinsa take amfani da shi
"Wai kina nufin ni kike so na dinga amfani da wannan kayan?"
"Qwarai kuwa da wace?" Kai ta kada tana dariya
"So nake naga kin sauya sis,so nake naga kin fara sabuwar rayuwa" kai taci gaba da kadawa tana dubanta,kafin tace wani abu anty dije ta shigo dakin,kayan ta dinga dauka tana dubawa tana dariya
"Allah yasa a baki hadin kai"
"Idan ma taqi ina kallon fatarta zan gane,don sun tabbatar min suna da kyau,suna gyara fararen mata" itama ta fadi tana dariyan,godiya anty dije ta taya sumayya,sun jima suna hira kafin nafisan ta koma gida don dora abincin dare,don auwal baison take away idan ba lalura ba ta kama.

        Anty dije ke jinjina tsadar kayan
"Bansan ya zata kaya ba idan kayan suka karbeki ba,suna da kyau amma akwai tsada" cewar anty dijen.
Chapter 92 · 0% Book details