← Book details Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 162 OF 226

Sashe 162

Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

         Minti talatin ya dawo a sanda yake zaton tayi bacci,sai ya janyo kujerar soso ya dawo da ita gabanta bayan ya kunna qwan dakin,qaramin qur'ani ya dauka cikin ma'ajiyarsa ya bude ya dora da tilawarsa daga inda ya tsaya cikin zuciyarsa yake yi,saidai lokaci lokaci yakan daga kai ya dubeta,fuskarta ta sake wani haske,kamar yadda kan hancinta da saman idanuwanta suka yi ja sabida kukan data sha,hakanan tausayinta ya dinga ratsashi,baisan tausayin na meye ba,ya dinga tuna wasu abubuwa da ya gani game da ita tun daga sanda igiyar aurensa ta hau kanta zuwa yau,yasan dai koma me yayi halalinshi ya karba,amma baisan me yasa yake jin wani bawai ba,ganin bai fahimatar karatun sai kawai ya rufe qur'anin yaci gaba da kallonta,har yanzu akwai lema kan zara zaran gashin idanuwanta,dan qaramin bakinta wanda kalarshi take pink ya kalla,sai ya lumshe ido yana jin wani sabon shauqi na taso masa,ba shakka tilas su bar hotel din nan su koma gidansa kowa ya kama dakinsa,idan ba haka bai baijin zai iya jure ci gaba da zamansu a muhalli daya ba tare da faruwar wani abu ba,bazai iya kallon giftawarta ta gabanshi ba tare da yaji komai ba,murmushi ya kufce masa sanda ya tuhumi kansa yaushe ka koma haka almustapha?,bai mancewa yakan jima baiji wani abu akan su'ad ba,wani lokaci har sai ta nemeshi sannan zaiyi ashe akwai feeling tattare da shi,har qorafi take masa bai zuwa wajenta saidai idan ita ta matsu ta biyoshi,hannunsa ya sanya qasan gadon ya ciro wayarshi wadda tun jiya ta fada,yama manta da su hakanan baibi ta kansu ba sai yanzu,kunnasu yayi baki daya har ta hannunta wanda ta soma karanta mishi saqo,murmushi ya sake saki sanda ya tuno yadda take karanta saqon a tsare cikin muryarta mai dadin amo,yadda kowanne harafi take furtashi cikin qwarewa,baisan yaushe yakai gareta ba,murmushi ne kwance saman fuskarshi yana zancan zucinsa shi kadai,saqonnin su hamza lamin musaddiq ne suka dinga shishshigowa a jajjere,dan qaramin tsaki ya ja,baki daya ya mance da cewa ya musu alqawarin zasu hadu a masaukinsu jiya da daddaren,baibi ta kan saqonnin nasu ba ya soma lalaubar lambar kamfanin da suka yi mishi aikin ginin gidansa,ba bata lokaci suka daga ya basu umarnin qarasa dukkan sauran abinda ya rage cikin gidan tare da basu kalolin furniture din yake so a zuba dakinsa da daya dakin
"Sir sauran dakin fa?" Waiwayawa yayi ya dubeta,baison wanne kala tafi so ba,dauke kanshi ya sakeyi
"A sanua orange da fari" ya amsa musu,bai ajjiye wayar ba sai da ya musu transfer na dukka kudin da ya rage.

      Yana shirin ajjiye wayar kiran baba ya shigo,a ladabce ya daga kiran yana gaida baban,yayin da yake amsawa shima tare da tambayarsa harkokinsa,ya tabbatar masa komai lpy
"Masha Allah,ina fatan komai yana tafiya dai dai ko?"
"Komai lafiya baba"
"To madalla,kadai kula da amana,Allah yayi maka albarka ya sake hada kanku"
"Amin ya Allah,Allah ya qara girma,ya jiqan mahaifa ya saka da alkhairi" ya samu kanshi da kwararowa baban addu'o'in
"Amin ya Allah,ga umminka ita keson magana da kai" ya fada yana miqawa ummeee wayar,cikin girmamawa ya gaidata ta amsa tana fadin
"Ina amirata?" Sake dubanta yayi,tana baccinta cikin nutsuwa,karon farko daya taba ganin wani mutum wanda bacci ya yiwa kyau irin haka
"Nace ina amira?" Ummen ta sake maimaitawa jin shiru bai amsa ba,sam ya mance tan kan layi
"Tana bacci ne ummee"
"Ba rana ta soma fitowa ba nan?,Ina fatan dai lafiyarta qalau ko?" Kunya ta kamashi,yana ganin kamar ummeen zata fahimci wani abu,cikin qoqarinsa nason boye komai yace
"Lafiyarta qalau,kawai batai isashshen bacci bane jiyan....." Da hanzari ya katse maganar da yake sanda ya soma fahimto zaiyi baran barama
"To madalla,ka gaisheta idan ta tashin,anty maamaa tana gaidaku"
"Zataji insha Allah" ya fada yana datse layim cikin hanzaei,idanuwa ya fitar waje yana furzar da iska daga bakinsa.

       Daya wayarce ta soma ringing,da sauri ya amsa kiran yana duban sumayya dake kwance,haka kawai baya son ta tashi,hamza ne tashi yayi ya koma saman doguwar kujera ya miqe a can sannan yace
"Lafiya malam da zaka damu mutane da kira da sassafe haka?" Dariya hamza ya bushe da ita
"Wai ko ba musty na kira bane?"
"Ban sani ba dan iska,da bakasan waka kira ba?"
"Dole na fadi haka,amazingly na kiraka kana na tasheka da sassafe,naga kai din baka da lokacin kira,any time ur available" yasan tabbas magana ya gaya mishi don hakan yake,su din ne har basu so a fiddasu daga gida da daddare ko a sasu tashin wuri,hakanan yau yake jin kansa shima as magidanci ,yake jin kansa wani na daban,ashe haka suke ji idan aka kirasu da sassafe haka,shi daya ne baya damuwa saboda baisan ana jin haka ba idan aka kira mai iyali da wurwuri ko idan dare ya fara turawa ba
"Naga alama ka fara rainani wallahi hamza,ni kake gayawa am available always?"
"To qarya nayi,idan banda rainin wayo jiya saika shanyamu muna ta jiranka har sha daya na dare na baro abida ita daya a gida?"
"Sannu tattabara sarkin aure,to nima fitarce bazan iya ba na bar....." Idanunshi ya dauke ya dora a kanta yana ware mata kallo,sai ya rasa sunan da zaya kirata da shi,dariyan da hamza ya qyace da ita ta sanyashu runtse ido,hayaniyar har tsakiyar kansa
"Hey,ar u mad,a kunnena kake wannan gadar?"
"Aci amarci lpy my maan,sai ka fito" ya fada yana datse kiran,maimakon yaji haushi yadda suka saba yi da hamzan sai murmushi ya subuce masa,ya sauke wayar daga kunnensa yana kwanciya rigingine yana kallon saman dakin,hannunshi kan sumarshi yana shafata a hankali,jinsa yake fresh tamkar wani sabon mutum,wani farinciki ke ratsashi
"Iyalina,matata,mata ta na bar ta ita kadai,matata bata son wannan,mata ta tana son abu kaza,mata ta tana buqata ta,mata ta ce ta kirani,mata ta ce ta yimin,ina son naji muryar mata ta,nayi kewar mata ta,iyalina sunyi kewata,mata ta zan siyawa,mata ta tace na siyo mata,mata ta tana neman izini na" dukka wadan nan lafuzan a bakin hamza da sauran abokai yake ji,dai dai da kalma daya cikin jerin gwanin wadan nan kalmomi baisan da zamansu ba aduniyar ma'aurata,duniyar zamantakewar aure,sai gashi cikin watanni hudu ya soma sanin wasu daga cikin kalmomin,kamar jiya da ya kasa fita saboda karantar wani yanayi na takura da rashin sakewa tattare da ita,ajiyar zuciya ya saki yana sake maida idonshi kanta,maganganun da baba ya gaya mishi ke masa bita daya bayan daya cikin qwaqwalwarsa.

          Cikin jin kunya da nauyi take komai,duk inda ta motsa tana jin idanuwanshi a kanta,har ta kammala azkar dinta ta miqe ta nade sallayar bata dubeshi ba,rabonta da kallonshi kwanaki hudu kenan,duk abinda zaice mata saidai ya fada tana duban wani gun,sauqin abun ma kwana biyu suna wani taro na mutanen da suka mallaki kamfani a qasar,bai shigowa sai bayan magariba,takanyi qoqarin yin bacci ko na qarya ne kafin ya shigo din,bata san me ya sanya take jin kunya da nauyinshi ba,irin nauyin da bata taba jinsa ba tattare da sauran mazan data aura,shima qoqarin tura mata saqo sau biyu a rana najin lafiyarta,duk don kiyaye amanar da aka bashi,bata bata dubawa ba sakamakon tana tunanin duka saqonnin nashi ne,saidai abu daya daya tsaye masa a tunaninsa wanda ya rasa dalilin haka,dare qwaya daya tak wanda yayi karen tsaye a tunaninsa,har yau yaqi goguwa daga idanuwanshi,sau tari tunanin wannan dare yakan wafci duk aikin da yake ya fado ciki,saidai ya tsinci kansa ya saki murmushi yana girgiza kai,yayin da hamza aka sa masa ayar tambayar wai me ya maidashi haka?,harara yake watsa masa yace zai daddaki hancinsa idan bai fita sabgar rayuwarshi ba,dariya yake masa tuburan ya bashi waje,yasan dai tabbas ruwa baya tsami banza,haka nan ya samu kansa da yin addu'ar Allah ya sanya canjin da suke fata ne ya soma samuwa.

      Qoqari yake su hada idanu amma abun ya faskara taqi yadda,duk inda ya kalla sai ta kauda kai,tun daga ranar taqi yadda ta dubeshi,har abun ya zame musu tamkar game,shi ya dage sai yaga qwayar idonta ita kuma qememe taqi,kamar yanzun data gwammace ta zubawa t.v idanu,wanda yasan hakan ba al'adarta bane,tunda suka zo bata taba kunna tv don radin kanta ba,dan qaramin murmushi ya saki na gefen baki,sai ya miqe ya isa ga makunnin tv ya kashe,janye idanuwanta tayi,ta rasa inda zata tsoma ranta,yayin da shi kuma bai fasa kallonta ba,shigarta qarewa kallo yana ambatar bahaushiya cikin ranshi,atamfa ta sanya dinkin zani simple,sannan ta saka riga halp buba wadda iyakarta gwiwa,kayan sun mata kyau duk da cewa baki dayan dinkin simple ne
"Miqo min ruwa" ya fada wai ko zata kalleshi,miqewa tayi tsam ta isa ga freezer tana mamaki,don bai taba sata yin wani abu ba saidai idan tayi niyya don radin kanta.
Chapter 162 · 0% Book details