← Book details Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 226

Sashe 93

Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kiran wayar daya shigo wayar sumayya ita ta katse hirar da sukeyi din,fuskar ta washe baki bude take fadin
"Amiran baabaa ce anty"
"Kice ina gaidata" inji anty dije tana miqewa don ficewa daga dakin ta fara jiyo hayaniyar minal da khalipha da alama rigima suke shi da ita
"Autan baabaa(haka take kiranta idan taso tsokanarta)"
"Mutanen uk,wai nikam yaushe zaku dawo,nifa na gaji wlh daga gida sai makaranta,ni daya kamar mayya,idan bakuyi wasa ba fa zaku ganni wlh na biyo sahu" dariya sumayya ta dinga yi ganij dududu watansu nawa ma da tahowa
"Kamar yaune fa zaki ga mun dawo din,yi haquri takwara" dariya sukayi baki daya sannan suka soma taba hira,amiran na bata labarin abubuwan da suka faru bayan tafiyarsu
"Amiran umman khalipha,baabaa fa ya karbi kudin aurena har da sa rana watanni shida masu zuwa dai dai sanda zan kammala degree dina" ta fada cikin nuna farinciki,cikn zumudi sumayyan tace
"Kai haba dai takwara"
"Wallahi amira,amma nikam tsoron yin auren nan nakeji takwara,duk da saifullahi na matuqar sona da qaunata,hakanan na amince da tarbiyya da halayyarsa" gefe daya na zuciyar sumayya itama jimamin da take mata kenan,saidai ba lallai abinda ya samu dan uwanka kaima ya sameka ba,kowa da tashi kalar qaddarar,bare amiran ita ba mai mata zata aura ba,ita daya ce a gunsa
"Meye wani abun tsoro?misali su ummee da sukayi auren su wani abu kika ga ya samesu?" Kai ta kada kamar tana kusa da ita
"Um um,kawai banson rabuwa ne da gida,ina son family na"
"Ba shakka familynki abunda zaka yi marmari da begensu ne idan ka barsu,duk wanda ya kalli yadda kuke son juna ba zaiyi mamakin haka ba" sumayya ta zantawa ranta,amma afili sai ta bagarar da zancan da nuna rashun muhimmancinsa
"Duk mace 'yar wani gidan ce,ko su su ummeen ce miki akayi gidanku ne gidansu,suna nasu familyn fa suka baro ko?" Sai amiran ta qyalqyale da dariya
"Kinji umme tace ah to,ashe taji me kika fadi,kinsan abinda anty maamaa ta gama gayan kenan dazu" itama dariyan tayi,ta shiga tsokanar amiran
"Kawai kice mu fara shirin baki,ina ga ba zamu wuce wata guda da dawowa ba zamu shiga hidima,ummm,bari na gayawa anty dije mu fara taru"
"Ahto,don kune amarori,shi yasa na dage saidai asanya wata shidan,daa qasa da haka za'a saka,nasan kafin sannan kun dawo"ci gaba da tsokanarta sumayya tayi a haka suka rabu cikin barkwanci.

Bayan ta aje wayar ta samu anty dije na sauyawa minal kaya da alamu bata wadancan tayi don ba'a jima da yi mata wanka ba
" nikam saura qiris na sauya qawa,wannan qawa tawa qazamiya ce"sumayya tayu maganar tana duban minal tare da yamutse fuska
"Yadai fi wallahi,duk gidan nan babu mai bata kaya kamar nata"inji anty dije,fuska ta kyabe tana shirin sakin kuka
" na daina anty,wayyo Allah na"ta fada tana bubbuga qafafunta zata hau bori
"To shikenan,ya isa,ai ke qawata ce ta amana,babu mai rabamu,uwata ce fa ta kaina" sai ta soma dariya tana tsallen murna sumayya na dubabta tana murmushi,duk yaron data gani tuna mata yake da abdallahnta,dauke kanta tayi ta maida ga anty dije
"Anty an sanya bikin amira fa,wata shida mai zuwa" sakin maballin da take ballewa minal tayi dama ta kusa gamawa ta juyo tana duban sumayya
"Tabdijan,kice akwai gangami kenan,bikin auta guda?,bikin amira ni 'yasu?" Antyn ta fada cikin jinjina lamarin,kai sumayya ta gyafa tana nade qafafunta saman gado tana murmushi
"Jar uba,kice abuja zata motsa,familyn baabaa prof za'ayi bikin da aka jima ba'ayi kamarsa ba,to ai ina ga da na su mahmoud za'a hada tunda suma wata bakwai ne inaga yayi saura cikin ranar auren da aka sanya musu ko,Allah ya nuna mana,sai mu fara shiri tun yanzu,sumayya kuna da biki" inji anty tana murmushu gami da jinjina kai
"Wallahi anty haka tace,ni kam mai zan iya cikin hidimar,ni da ban taba bikin qawa ba?"
"Aikuwa dole ki ware ayi komai da ke,yadda amira ta daukeki kada kuce zaki watsa mata qasa a ido,nasan halayyarki sarai" dariya sumayya tayi ganin yadda antyn ta camfata tana kwantar da kanta saman filo
"Allah ya bamu iko to anty" kan ta gama rufe bakinta kira ya shigo wayarta,lambar alqasim ne,tana mamaki da har yau bai rabu da ita ba,bayan ta zayyana masa ita din bazawara ce har da yaro,sai ta latse wayar ta kasheta baki daya tana jan qaramin tsaki ta gyara kwanciyarta abunta,ita yanzun babu mai daga mata hankali,ko lukman idan ya kira sai taga damar dagawa,darajar yaranshi dake sonta kawai take dubawa,badur rahman je kadai ke da wannan qinar na daga kiransa a duk yayin da ya kira din.

        Cikin qanqanin lokaci da fara amfaninta da mayukan da sabulan taga banbanci,ita a karan kanta taga sauyi,wani laushi da santsi fatarta ke sake yi tamkar wadda ke zuwa gyaran jiki,baki daya qamshin jikinta ya sauya zuwa wani qamshi na musamman ma daban wanda ya kama kayanta sabida turaren da take amfani da shi set na man da sabulun,cikin watannin da basu gaza biyu ba sumayya ta sake komawa wata ta daban,komai nata ya sauya,sau tari laila na tononta tana cewa
"Wlh anty sumayya kin koma 'yar gayu" hakan ya yiwa nafisa dadi qwarai a ranta,bisa dukkan alamu zata cimma qudurinta cikin sauqi kan sumayyan,tana son sumayyan ta zama wani sashe na familynsu,dukkanin halayyarta sun mata babu na yarwa.

*******     *******    ********

         Yau da gobe kayan Allah,sannu a hankali kwanaki ke mirginawa suna wawasar kwanukanmu a duniya,da kuma kwanakin dukkan wani abu da muka sanya masa lokaci,zuwa yanzu su sumayyan na da watanni takwas cikin qasar ta uk,ba qaramin karba qasar ta yiwa sumayyan ba,bugu da qari kuma ga nafisa daga gefe data kafe kai da fata zata sauya sumayyan malam din zuwa wata sumayyan ta daban,sumayyan uk,qudirinta kuwa ya karbu,a yanzu idan kaga sumayyan zaka sha mamaki,komai nata ya sauya,wani irin kyau da da can yake boye a yanzu ya soma bayyana kansa,hutu jin dadi da kwanciyar hankali suma na bada tasu gudun mawar,hatta da anty dije kan kalleta mafi yawancin lokuta,dadi take ji cikin ranta da ta sanadiyyarta sumayyan ta soma samun canjin rayuwa,ashe da can damuwa rashin kwanciyar hanakali da tension ita ta tasamma kassara sumayyan da gurgunta tunaninta,a yanzun kai baka ce sumayya bace wadda ta taba aure,'yar shekara ashirin da biyu har da yaro ba,sai kayi zaton tana cikin shekararta ta sha shida ne,tun da can Allah ya bata sanyin murya nutsuwa da iya magana,sai abun ya sake zame mata ado,zakayi zaton daga wani babban gida ta fito.

       Gefe daya karatun ta ya kankama haiqan,turanci ba damuwarta bane a yanzu bare hausa,mai gaba dayan larabci dama ya jima da zama kan harshenta tun tana qanqanuwarta,tana daya daga cikin zaqaquran ajinsu a yanzu,zaka yi mamakin yadda harshenta ya karye,tana karbar karatunta da kyau,tuni wata daya baya ta kammala makarantar koyon girki da mu'amalar yau da kullum,ta fita da cetificate mai kyau,a yanzu kusan anty dije ta zama 'yar kallo ta fannin kitchen,kowacce rana da kalar abincin qasar da sumayyan zata girka,uncle farouq da taya bera bari shike basu kudi suje suyi siyayyan kayan da za'a buqata a ranar tunda shi bai sansu ba,laila ce 'yar rakiya,kai na rawa zata bita suje,zuwa yanzu ta sake tana iya zuwa gurare wadanda ke kusa da su ba nisa can ba,idan kuma suka so yin nisan nafisa ce jagora,zata debesu guri guri da yake ita din tamkar 'yar gari ce a garin,ranar haka zasu wuni a waje,sau tari sumayya na noqewa saboda ganin yadda nafisan ke kisan kudi idan sun fita amma taqi bata dama,duk abinda ta siyawa kanta sai ta saiwa sumayyan duk tsadarshi,dole tayi surrender ta tabbatar Allah ne yayi wannan hadin tsakaninsu.

*******     ********    *******

     Kamar ko yaushe yau ma tafe suke su shida,nafisa,sumayya,laila,khalipha,sai minal da kuma khalid dake riqe a hannu,ganyayyakin abinci suka sayo daga can suka wuce suka sha coffe a wani gun shan coffee dake daura da gun,zasu hau bus nafisa ta hana,a qasa suka dinga takowa tana nuna musu gurare tana musu bayani,sosai yanayin ya yiwa sumayya dadi qwarai,murmushi kawai ke tashi a fuskarta,sanye take da dubai abaya wadda tayi mata cif a jiki,ja ce mai dan turuwa kadan,bata yi amfani da mayafin rigar ba saboda yayi mata qanqanta,sai ta yafa wani medium vail dark blue wanda ya lullube har kafadarta.

      Idan ka kalleta dole ta burgeka,murmushin dake tashi kan fuskarta kawai abun sha'awa ne,kayan sun haskata matuqa,khalipha da minal da laila sunyi gaba abinsu suna ta tsalle tsallensu laila na qoqarin saitasu,ita da nafisan ke ci gaba da takawa a hankali suna hira tana bata labarai.

       Maganar da nafisan ta fada ta sanyata juyawa tana kallonta dariya ta kubce mata,sam bata lura da gabanta ba ji tayi ta bangaji abu,taga taga tayi zata fadi murya a sama taji ance
"Hey!" Tare da riqo hannunta,tashin farko ta gigice,abubuwa biyu cikin lokaci daya suka hargitsa ta,walainiya idanuwanta suka shiga yi zuciyarta na bugawa,man ne,mustapha,sanye cikin three pieces slim fit suit navy blue wadanda sukayi matuqar yi masa kyau tare da fidda sigar kyawunsa,idanuwansa saye cikin sun glasses,ya kafeta da tsinin idanuwanshi duk da bata iya hangosu fes amma tana ganin alamunsu,jikinta ya soma rawa sanda ya saketa sai ta sake tafiya zata fadi nafisa ta tarota tana fadin sunanta,tsaye yake qyam yana dubanta,duba mai dauke da bacin rai,tuni baturen dake tare da shi ya kammala tsince wayoyinshi da suka zube qasa yana masa sannu cikin harshen nasara,dauke idanuwanshi yayi ya maida kan wata rantsatstsiyar baqar mota data faka a gabanshi,qaramin tsaki ya ja sannan ya juya cikin takunshi ya nufi inda motar take,da alama dama ita yake jira,baturen ya mara masa baya cikin hanzari ya bude masa mazaunin baya kafin shi kuma ya shiga gaba,jan nafisa ta soma yi jiki na rawa tana waiwaye har suka shige motar suka tayar suka bar wajen.
Chapter 93 · 0% Book details