← Book details Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 161 OF 226

Sashe 161

Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

      Idanunsa lumshe murya can qasa ya mata nuni da filon dake daura da shi
"Nan zaki dawo" daga kai tayi ta dubeshi,ganin idanunsa a rufe yake ya sanyata matsowa ta sake rage muryarta ganin tana kusa sosai da shi babu buqatar daga murya,don har tana iya sheqan daddadan qamshin turarensa
"A daga wayata,nasan cewa kana kusa,kana shirin wulaqantani ne kawai,kafi kowa sanin zuwa yanzu zan iya rasa kudi hannuna,naji kuma ka share baka da alamun sauke nauyin dake kanka" cikin harshen turanci ta turo wannan saqon,salon yadda take karanta saqon da tataccen engilishinta ya matuqar burgeshi,ta karya harshe sosai tamkar yarenta,sautin muryarta ya dinga ratsashi ya hanashi sukuni,jin tayi shiru yasa yace
"Uhmmm,ci gaba" ba tare da ya bude idanunshi ba,sake bude dayan tayi wanda shi kuma da hausa ne
"Kana wacce qasa?,ina son nazo na sameka mu warware sabanin dake a tsakaninmu,kafi kowa sanin bazan iya jurewa rashinka ba......"
"Is ok" ya fada yana amshe wayar daga hannunta,don bashi da lokacin saurarar shirmen su'ad din,ya lura ta maidashi wani qaramin yaro,ya tabbata buqatarta ce ta taso,mai hali baya fasa halinsa,ba zata taba canzawa ba,a hankali ta soma motsawa da niyyar sauka daga gadon,caraf taji an ruqo hannunta,da sauri ta waiwayo,still har yanzu idanunsa na rufe
"Ina zaki?"
"Kwanciya zanje nayi bacci nake ji"
"Ni kuma bana jin bacci so ya za'a yi dani?" Ya qarashe fada bayan ya ware manyan idanuwansa fes a kanta wadanda suka sauya launi,sunkui da kai tayi saboda wani abu da taji yana fisgarta,hannunta ya saki yace
"Dawo ki zauna" bata musa ba cikin mutuwar jiki ta sake dawowa gurbin data matsa,saidai wannan karon baki daya a takure take,saboda waiwayowa da yayi yana fuskantarta gami da zubo mata ido,baisan me zaya ce mata ba,baisan ta ya zai fuskanceta ba,bai taba tsammani akwai wata rana da d'iya mace zata yi masa kwarjini ba,shi kadai yasan me yake ji cikin jikinsa,meke zagawa jini da jijiyarsa,tabbas yana buqatar dauki,ya godewa Allah daya kasance akwai halalinsa a kusa,da ya tabbatar yau babu abinda zai hana ya yanki ticket zuwa america,zuwa yanzu nauyin da yake ji ya fara guduwa,ya soma daina fahimtar kunya nauyi izza da isa dake tattare da shi,zuciyarsa ta fara kaiwa maqura,ajiyar zuciya ya sauke
"Bani labari.." Ya fada yana dubanta,a wannan karon yadda mamaki ya kasheta shi ya hanata motsi bare ta dago kai
"Bani da labari" ta yanke masa hanzari tun kafin taji me yake shirin fada,shiru ya ratsa tsakaninsu,yayin yaci gaba da qare mata kallo ta cikin lullubinta wanda mayafin ba wani kauri gareshi ba,numfashi ya fitar da qarfi sannan yace
"Shekaran jiya kin yimin tayin samun 'ya'ya ko?" Ya fada yana duban sumarta wanda mayafin ya zame ba tare data sani ba,sai a sannan ta dago ta dubeshi tana mamakin me ya maido wannan maganar,kanta ta maida qasa tana murza tafin hannunta
"Ta wuce ai,tunda baka da matar da zata haifa maka din"
"Idan kuma ya kasance kece matar fa?" Gabanta ya fadi tsoro ya kamata
"Idan kuma bazan iya ba fa?"wani salon murmushi mai fidda qaramin sauti ya fitar yana matsowa dab da ita
"qarya ne,wanda kika taba haifa fa a baya?"wannan karon ma sai data dubeshi,ya akayi yasan ita ta haifi abdallahn?duk da ya gansu a tare amma ta tabbata baisan itace mamarshi ba,duba da tsawan daya taba yi mata sanda ta mareshi,tsareta yayi da idanuwanshi yana karantarta,tuni tsoro ya mamayeta,idanuwanshin kadai sun karantar da ita me yake nufi,to amma da wacce siga yake son kasancewa da ita,mutumin da bai gama aminta da cewa matarsa bace ma?,mutumin da bai taba cewa yana sonta ko yana qinta ba,ita kam wai a haka rayuwarta zata kasance,ta zama rabon mutum uku kenan nan duniya?,zuciyarta ta karye tana jin wannan karon ba zata iya ba har sai ta tabbatar da matsayi ta,da azama ta sake motsawa da niyyar sauka,saidai ina halittar ba daya bane,cikin zafin nama ya danne rigar baccin tata ta gefe daya ya aza duk nauyinsa,tilas ta durqushe,jikinta ya fara rawa idanunta suka tara qwalla
"ka yima Allah ka barni matuqar kasan ba zaka iya ci gaba da zama da ni ba har qarshen rayuwarmu,kada ka shiga rayuwata daga baya ka fice ka barta" ta fada kuka na qwace mata,baki daya jikinsa sai ya mutu amma hakan bai kashe kaifin abinda yake ji cikin zuciya da gangar jikinsa ba,tabbas ya sani ta taba aure amma baisan me ya rabata da gidajenta ba,abu daya kawai ya sani ya kuma yarda da shi,baban bazai taba zaba masa macen da bata kamaci rayuwarsa ba,tafin hannunshi ya sanya tsakiyar nata yana murzawa a hankali idanuwanshi a kanta,ya tabbatar koma mene wani miki ne dake zuciyarta me yiwuwa take amayar da shi ta hanyar hawaye,a hankali yaci gaba da mutstsuka tafin hannunsu dake hade waje guda,wani abu na yawo cikin jikinsa,sannu a hankali kukan nata ya soma tsagaitawa,har cikin jininta take jin mutstsutsukawar da yakewa tafin hannunta,cikin sanyi ta daga kanta sai ta tsinci idanuwanshi na kanta,kai ya girgiza mata alamun a'ah,sai ta maida sabuwar qwallar dake shirin zubowa,hannayensa ya bude mata baki daya alamun ta taho,haka nan wani shauqi ke jansa zuwa gareta,kai ta kawar gefe alamar ba zata iya ba,birkitota yayi baki daya tayi masauki saman faffadan qirjinsa,jikinsa ya hadu da nata,lallausan fatarta ta sake bashi gudun mawa wajen samun himmar aiwatar da abinda da kaikawo cikin jiki da zuciyarsa,tamkar wanda ake kadawa gangi haka ya dinga tsuma,cikin zafi zafi yaje aika mata da saqonni masu nauyi,wanda har suka nauyaya cikin qirji da zuciyarta,tsoro ya kamata,tunda take bata taba tsintar kanta cikin duniyar daya jefa ta ba,saqonni ne masu rikita qwaqwalwa da kashe gangar jiki,data rasa abunyi sai kawai ta sake masa kuka,sam baya son abinda zai kawo cikas ga abinda ya nufata,yayi nisan da bai tsammanin kira zai dawo da shi,bai buqatar kukanta a wannan lokaci,sai ya hade bakunansu waje guda tare da sake jefata a wata duniya mai nisan gaske wadda bata taba tsammatar akwaita ba.

      Tana kwance saman faffadan qirjinsa duk da kusan shudewar awanni biyu suna a haka amma hakan bai dameshi ba,shauqi ke shawagi dashi cikin sabuwar duniya kamar tsuntsun daya samu sararin sama,abunda bai taba faruwa ba tsakaninsa da su'ad ba,hasalima Allah Allah yake ya tashi ya tsaftace jikinsa,saidai wannan karon jinsa yake wani daban,ya kasa rabata da jikinsa,ya kasa tashi,hakanan ya kasa lallashinta kukan da take fitarwa,saboda yana da yaqinin idan ya lallasheta din akwai wani lallashin a gaba,saboda baijin zai iya barinta aziyara daya,anya daidai kunnensa ya jiyo masa sanda baban ke fadin bazawara ce da yaro guda daya tsaga jikinta ya fito?,har yau ya kasa tantance ainihin duniyar da yake,duk yadda yaso sake koyi da sunna wajen yin alwala amma ya gaza samun wannan qwarin gwiwar,burinsa kawai shine ya koma duniyar da ya fito,kuka ta sake saki sanda ya sake maidata jikinsa,tana tunanin rayuwarta kawai yau yake nema,maganin kukan ya sakeyi karo na biyu sanda ya rufe bakinta gaba daya da nashi.

  ******    *******    ********

      Ya jima zaune saman abun sallar da suka idar da sallar asuba yana dubanta,yayin da take takure waje daya itama kan abun sallar tana zub da qwalla,tasbihi kawai takewa ubangijinta tare da godiya a gareshi,tasan shi kadai ke yadda yaso da rayuwar bawa,sosai kukan nata ke sukarshi,ya rasa ta yadda zai lallasheta,yana jin tamkar bai kyauta mata bane,don me ya gaza haquri ya shiga gonarta ba tare da amincewarta ba,sai ya jingina da gadon yana qarasa azkar dinshi,ya kammala ya shafa,har yanzu bata sauya zani ba,wani mugun firgita tayi sanda taji ya sureta gaba daya,karon farko data yarda suka hada idanuwa tun daren jiya bayan faruwar abun,baki daya idanuwanta suyi luhu luhu sunyi ja,hawaye ne cike da idanun,ya fuskanci me take nufi,tana tsoron ko wani abun zai sake,shi kansa yayi makin yadda taji jiki haka,yadda ya saba tafiyar da su'ad haka yayi mata,dauke kanshi yayi yana ci gaba da takawa har kan gadon,gyara filo yayi ya kwantar da ita
"Ba abinda zan sake miki,bacci kawai nakeso kiyi" ya fada yana ja mata bargo zuwa kafadunta,luf tayi tana sharar qwalla gami da fitar da ajiyar zuciya
"I hate crying" taji ya fada
"Idan baki daina ba kuma zan miki abinda bakyaso" har ga Allah tsoronsa take ji,bata marmarin sake gamuwarsu,sai ta rage jan hancin da take,kashe qwan dakin yayi tana jinsa ya bude qofar ya fice ba tare da tasan inda zashi ba,a hankali idanuwanta suka fara nauyi,bacci mai dadi ya sureta wanda batayi tsammanin zuwanshi nan kusa ba.
Chapter 161 · 0% Book details