← Book details Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 226

Sashe 13

Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

            Suna kammala ci ta ja gefe ta sake sabon zama,da ido mukhtar ya bita sannan ya dauke kansa yaci gaba da abinda yake,ba qaramin tsanar falon tayi ba saboda yadda ya kere nata amma ta gwammace tayi ta zama ciki ko banza ta musguna musu ta hanasu sakewa.

        Gefansa sumayyan ta dawo ta zauna tana kallon yadda yake shigar da wasu bayanai cikin sabuwar laptop da ya siyo,tana da sha'awarta sosai hakan ya sanya ya saki aikin da yake yana koya mata.

        Sosai ta qulu amma hakan baisa ta bar dakin ba,har suka kammala ya miqe ya fita,cikin 'yan mintina ya dawo yana shigowa falon ya sunkuceta kamar dazu,har ya kai bakin qofar dakin gadon ya waiwayo ya dubeta
"Ammm,idan kin gama abinda kike yi ki rufe mana qofar,sai da safe" ya fada yana shigewa,da gayya ya dinga takalo sumayyan har sai da ya fuskanci ta fice musu daga falon ta hanyar dukan kujera tare da banko qofar sannan ya saki murmushin mugunta yana saukowa daga gadon don ya rufe dakin.

        Riqo hannunsa sumayya tayi tana masa kallo qasa qasa
"Kai ko.....ba'a haka ya mukhtar fa,nasan da gayya kake komai" murnushi ya saki har yana fidda sauti sannan yace
"Koma me nayi ita ta jama kanta,ta yaya haka kurum zaka dage sai ka cusa kanka inda baka da muhalli?,sai kayi zaman aure a inda ba'a da muradinka?" Ya fada yana sauka daga gadon tare da cewa
"Jirani nazo sai muyi hirar sosai" ya fadi yana kashe mata ido daya,dariya ta saka.

**********************

      Wani irin zama ne yake wakana a tsakaninsu,cikin abinda bai wuce sati uku ba gaba daya fa'iza babu layin da bata karade ba neman qawa,kasancewar duka maqotan nasu mutanan sumayya ne,hakan ba qaramin qona mata rai yayi ba,bilhaqqi bata qaunar sumayya ko wani abu da ya danganceta,hatta da yaran dake shigowa gun sumayyan fa'iza qorafi take a kansu,idan taso tana iya korarsu,wani lokacin idan kan idon sumayyan ne ta hanasu tafiya,tsoronta yaran keji hakan ya sanya wasu daga ciki suka janye shigowa,mutum ce ita ta jama'a hakan ya sanya idan fa'izan nason yawonta saidai tayi uwar tafiga zuwa can bayan layinsu.

         Tunda tazo gidan bata taba daukar tsintsiya da sunan shara ba baya ga ta dakinta,koda ran girkinta ne da ta kammala zata bar wajen yadda yake tayi gaba abinta,ko kadan sumayya bata lamunci qazanta ba ita zata killace komai ta gyara,ko banza tasan tana da lada.

          Ko kadan mukhtar baya daga mata qafa wannan shi ya rage kaso casa'in cikin dari na rashin mutuncinta,tun da can irin 'yammatan nan ne da basuqi su fito da daurin qirji su dambatu da namiji ba,hakan ne ya bawa yaya yahanasu sha'awa a gajeran tunani irin nata,tana ganin cewa ita daya ce zata iya zama cikin gidan muntari ta take kowa ta kuma kawo musu abinda suke so,duk da cewa fa'izar ta taba shege tuna gida aka zubar amma hakan ba aibu bane a gun yahanasu,tana ganin ma wata dama ce dake nuna zata iya haifawa muntarin d'iyoyin da take tsammatar zasu iya alfahari da su,tarbiyya cancanta kunya asali da cikakkiyar nasaba basu zame mata mizanin ma'auni ba a gareta wajen hada qanin nata da ita.

        Ko daya sumayya bata taba shaidawa muntarin fitar barbadar da fa'izan keyi ba,ta azawa ranta cewa idan kere na yawo zabo na yawo dole a hade,abu daya ne da ta tsaya a kansa shine,bata yadda fa'izan ta shiga haqqinta kamar yadda ita bata shiga nata haqqin har ma da hurumi da shirginta baki daya,sai yanzu take sake ganin alfanun shawarar anty dije gareta,tabbas gaskiya ta gaya mata,kuma gata ta mata,ba dan hakan ba da zuwa yanzu Allah ne kadai yasan yadda fa'izan zata maidata.

            Duk yadda ya dauki lamarin shigowa gidan muntarin da sauqi ya fice haka,sai ta tadda soyayyar da muntarin kewa sumayyab bairin soyayyar nan bace da tuggu ko makirci ke nasarar wargazata ba,soyayya ce mai azabar danqo da yauqi,amma ta daukarma kanta alqawarin sai ta wargaza zaman lafiyar sumayyar ko ta halin yaya,kafin ta waiwaya ta takawa su yaya yahanasu birki wadanda zuwa yanzu suka soma yi mata lissafin zuwa yaushe zata dauki ciki,bata son takura ko sanya ido cikin lamuranta,basu san wace ainihin fa'izan ba har zuwa yau

*A WANI DARE*

*_Masu karatu ku biyoni,yanzu aka fara littafin._*

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍✍✍✍
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
________________________

*bismillahir rahmanir rahim*

*inna ma'al usr yusrah,fa'inna ma'al usr yusrah*
_______________________

1⃣1⃣

*A WANI DARE*

     Tun magariba ta shige dakinta kasancewar ba ranar girkinta bane,tun wajejan yammaci take jin ciwon kai da fargaba kadan kadan,hakanne ya sanya tun tana saman abun sallarta bayan ta kammala sallar isha'i bacci yayi awon gaba da ita,ko mukhtar da yazo mata sai da safe haka ya sameta,daukarta yayi cak ya maidata saman gado sannan ya ja mata qofar ya fice.

      Kamar cikin mafarki taji ana kiran sunanta,cikin wata iriyar murya ce wadda sam bata ta dadin amo,a hankali ta dinga bude idanunta cikin duhun da ya gauraye dakin nata,tabbas sunanta ake kira cikin wata murya mai kama da amon sautin kukan kare.

      Idanunta ta ware sosai saboda wata siffa data dinga hangowa ta tokare bangon dakinta daga inda take fuskanta,wata mummunar faduwar gaba ce ta ziyarce take gumi ya rufeta baki daya,jikinta ya hau rawa
"Bismillahil lazi la yadurru ma'as mihi shai'un fil'ardi wala fissama'i wa huwas sami'ul alim" haka ta dinga maimatawa,tun tana yi cikin zuciyarta har ya fito fili,maimakon kiran sunan nata da ake a hankali sai aka koma da sauri sauri,sannu a hankali siffar halittar da take gani jikin bangon ta bace bat.

         Cikin wani irin hanzari da kuzari ta diro daga saman gadon nata hannunta dauke sa wayarta,falo tayo tana ci gaba da ambaton sunan Allah,ta kunna qwan dakin tana mai qarewa falon nata kallo,babu abinda ta gani,cikin sanyin jiki ta zauna kan daya daga cikin kujerunta dafe da kanta.

           Tsawon mintina ashirin ta dauka a haka sannan ta isa bakin t.v stand dinta,ta dauki ruwan leda guda daya da ya rage wanda tash dazu,dankwalinta ta cira ta ninka ta shimfida ta daura alwala a kai sannan ta fuskanci gabas.

          Sallah tayi raka'a hudu sannab daga bisani ta zauna,cikin surorin data haddace ta dinga karantawa daya bayan daya,har zuwa sallar asuba bata samu ta runtsa ba,a nan zaune mukhtar da ya shigo tayar da ita sallah ya sameta,yaso ya danyi mamaki amma sanin cewa wani lokaci takan tashi da wuri ya sanya boye mamakin nasa ya fita ya tafi masallaci.

           Sai kusan biyar da rabi ta koma saman kujerarta ta kwanta a nan bacci ya sureta.

          Sallamar mukhtar ce ta tasheta,ta miqe tana mutstsike idanunta,a shirye ya shigo da alama kasuwa zaya fita
"Lafiya kuwa kike sumayya,wani irin bacci yau kike haka sam ban ji motsinki ba?" Murmushi tayi tana gaida shi ba tare data amsa masa tambayarsa ba
"Ni zan fita babu wata matsala ko?" Ya fafa kamar yadda ya saba fadi duk sanda zai fita kasuwa,kai ta girgiza
"Babu komai,a dawo lafiya Allah ya bada sa'a"
"Amin" ya fada yana kashe mata idanunsa daya tare da cewa
"Yau ba rakiya my sumy?" Kai ta kada
"Kaima ka sani ba girki na bane,ka kuma san halin fa'iza sarai,ranar girkinta bata son kowa ya rabeka ko?" Kai ya kada
"Ba ruwa na da ita,tunda kafin na san ta ke na sani ko,amma tunda kince haka shikenan,sai na dawo" ya fada yana daga mata hannu kana ya fice.

            Sai da ya fita da wajen mintina biyar sannan ta miqe,daki ta nufa da nufin shiga,gab da zata shiga din abinda ya faru jiya ya dawo mata tar a kwanyarta,tsayawa tayi jim sannan ta karanto addu'o'i  ta shiga.

          Tsayawa tayi tana bin kowanne lungu da saqo da kallo bata ga komai ba saboda haka ta dauki abinda zata dauka ta fito.

        Ga mamakinta tsakar gida ta taras da fa'iza zaune saitin window din dakinta zaune,kallon juna sukayi sumayya ta dauke kanta ta nufi bandaki don yin wanka,yayin da fa'izan ta bita da kallo,har ta kammala wankan ta koma daki ta shirya ta fito ta shiga kitchen don samawa kanta abinda zata ci fa'izan na zaune,dim yawanci idan ranar girkinta ne bata baiwa sumayya abin kari,to da yake ita din ma ba gwanar abinci bace hakan baya dada ta da qasa saita hada duk abinda ya samu taci shikenan an wuce gurin.

           Yauwa kamar jiya bacci ya dauketa da wuri,kamar jiyan dai cikin bacci taji ana kiran nata,tarwai wannan karon bude idanunta nata cikin gigita,yau kam siffar macizai take gani tsaye ya mamaye bangon
"A'uzu bi kalimatillahit taammati min sharri ma khalaq" ta dinga maimaitawa da qarfinta har bata san tana daga murya ba ko kuma ta manta cewa dare ne,bat abun ya bace sama ko qasa,a bakin qofar fita daga dakin sukaci karo,mukhtar ne yana tsaka da bacci ya dinga jiyo muryarta,jikinsa ta fada gabanta na tsananin duka jikinta na rawa,janyeta yayi zuwa falon suka zauna gefan kujerar yana tofa mata addu'a.

          Sai da ta samu nutsuwa sannan ya dubeta ba tare da ya tambayeta me ya faru ba
"Muje dakina ki kwanta a can" kai ta kada tana zare jikinta daga nashi
"Kaje kawai babu komai zan iya kwanciya a nan,mafarki kawai nayi kuma yanzun nayi addu'a" idanu ya zuba mata sai ta kada kanta tana son gamsar da shi kan abinda ta fada din,kan doke saboda yadda ta kafe ya sanya shi barinta tare da sake mata addu'a sannan ya fita.

           Qarfe tara na safw tuni tayi wankanta tana zaune a falon cikin rashin kuzari da tunani barkatai,a haka mukhtar din ya taddata,bayan sun gaisa ya samu gefanta ya zauna
"Sumayya,meke damunki,na tabbata akwai abinda ke damunki,yanayinki jiya ya tabbatar min da haka,kada kuma ki soma cemin babu komai" qasa tayi da kanta don kada ya ga tsoron dake cikin idonta,sai da ta saisaita kanta sannan ta dago
"Ya mukhtar,ina zaton akwai maciji cikin dakin nan"
"Maciji?" Ya tambaya cikin mamaki,kai ta gyada masa,sai yayi shiru na wasu daqiqu kana daga bisani ya ajjiye jakar dake hannunsa yana mai miqewa
"Ina zuwa" ya fada yana ficewa.
Chapter 13 · 0% Book details