← Book details Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 197 OF 226

Sashe 197

Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

      Kitchen ta shiga tana yin sallama,mai aikin ummi uwani na tsaye gaba gas tana fere dankalin turawa ita juyo cikin sakin fuska ta amsa,hakanan take son sumayyan,ta yaba hankalinta sosai,sam basu taba jin dadin zama da abokiyar zamanta ba shi yasa suke mamakin halayyarta,hasalima umarni ne kawai tsakaninsu,ka saba kuma taci mutuncinka ko gaban waye,kaman bayi take daukansu,gefe daya eesha ce sanye da kayan bacci tana jingine da freezer,hannunta daya riqe da cup,daya hannun kuma waya ce tana amsawa,uwani duka ta girme musu don ta kusa sa'ar ummi,mai aikinta ce da suka jima tare,amanarta da hankali yasa tasu tazo daya da ummi,tunda sumayya ta dawo wajen ummin ita kewa sumayya komi duk abinda take da buqata,fuskar sumayya qunshe da murmushi ta qarasa kusa da uwanin sanda take yunqurin gaida sumayyan tayi maza cikin girmamawa ta soma gaidata,ta amsa tana fadin
"Halan wani abun kike da buqata uwar dakinmu?" Murmushi sumayyan tayi
"Ai naga ma kaman aiki kike ko?"
"Ba matsala fadi abinda kike so sai ayi miki ai......"
"Ba aikin wanda zakiyi har sai kin gama min nawa" eesha ta fada tana sauke waya daga kunnenta idanunta a akansu
"Ai duka zan iya hajiya aisha....nata aiki yafi mu....."
"Bakiji me nace bane?,ko sai na sake maimaita wa?" Ta kuma fadi a gadarance,murmushi sumayya ta yiwa uwani
"Kada ki damu baba uwani...ci gaba da aikinki" ta fada tana matsawa gaba,ta samu tukunya ta dauraye ta zuba ruwa da duka kayan qamshin da take buqata ta dora saman daya gas din,sannan ta bude freezer ta fitar da nama ta zuba masa ruwa don ya narke ta janyo kujera ta dawo gefan baban ta zauna suna hira jefi jefi,wannan dabi'a ta sumayyan na daya daga cikin abubuwan da ya sanya baki daya ma'aikatan ke qaunarta,bata dauki rayuwa da zafi ba,komai nata a sauqaqe yake,idanuwan eesha na kanta,baqinciki ya cikata,so tayi taja zancan da tsaho ta yayyaba mata magana ta qona mata rai,saidai anyi katari sumayyan bata bi ta kanta ba,wani wawan tsaki ta ja sannan tace da baba
"Saura bayan fitata ki kama aikin wasu,zan shiga wanka kafin ma fito a shirya min saman dining"
"To" kawai baban tace da ita,sai ta juya ta fice tana wani taku tana jin kanta dai dai da kowa,da kallon takaici sumayya ta bita sai data fita ta dauke kai,batasan me ta dauki rayuwa ba,yanzu kaman baba data yi sa'a da uwarka idan ba dole ba ma yaushe zaka sanyasu wani aiki
"Kiyi haquri baba don Allah" sumayyan ta fada cikin rashin jim dadi,dariya baban tayi
"Banda abinki uwar daki ai babu komai,tana cin albarkacin hajiya ne da alhaji,dukkansu su da yaransu an shaida mutanen arziqi ne,don wannan tayi ai ba komai na lokaci ne zata koma inda ta fito" kai ta jinjina kawai suka ci gaba da hirarsu,kusan tare suka gama,wanda hakan yayi dai dai da shigowar sauran ma'aikatan,suka gaisa baki daya sannan ta fice ta basu waje,bayan an kai kayan karin dining saboda harda ummi tayi,gasashshen nama ne da kayan lambu,sai breadin inibi da ruwan shayi,na eesha kuwa chips ne da qwai sai nata ruwan shayin.

          Ta tadda sajida ta farka harta gama gyara dakin tayi wanka abinta,sam yarinyar anty farida bata yi mata rainon yaran masu kudi ba,ta iya qananun aikace aikace dai dai da ita,ta iya shata tsaf da gyaran gado,ta gaida sumayyan sannan ta shige toilet tayi nata wankan,ta shirya sannan suka sauko,sun tadda ummi itama ma saukowa a dining suka hade baki daya harda eesha,a ladabce sumayya ta gaida ummi ta amsa fuska sake tana tambayarta ya jiki tace alhmdlh
"Amma dai ai zuwa yanzu amai ya tsaya ko?" Kai eesha ta dago tana duban sumayyan,tunda tazi take zargin hakan dangane da sumayyan saidai bata da tabbas sai yanzu,kanta a qasa cikin jin nauyi ta amsa mata da eh
"Alhmdlh haka ake so Allah ya qara afuwa"
"Amin" tace da ita,kafin ta sake cewa wani abu yaron gidan da ummi ta aika ya soma danna qararrawa daga bakin qofar falon,sumayya zata miqr ummin ta dakatar da ita,ta miqe da kanta ta tafi amsowa,jawo kwanukan data yi abincin tayi ta soma budewa tana zubawa cikin plates uku,nata ummi da sajida,yayin da eesha ke gefe daya tana jefa chips bakinta,gaba daya abincin yayi mata,hakan ya sanya sumayya na gama zubawa ta kai hannu ta bude ta janyi wani plates din
"Ci zakiyi ne?" Sumayya ta tambaya,don tana so ya kai mata ne har wajem sha biyu zuwa daya kafin nan an gama girkin rana,din bata fiya son wahalar da masu aikin ba tayi ta sasu dafa mata abinci kamar kanta aka soma ciki,banza tayi da ita kaman ba da ita take magana ba,sai ma fara yunqurin diba da tayi,hakan ya qona ran sumayya,hakan ya sanya ta sake maimaitawa
"Magana nake dake" sai a sannan ta daga kai ta dubeta
"Tunda ba abincinki bane saiki sauraramin ko?"
"Gaskiya kika fada,amma kiba nawa bane ni na dafa saboda haka sai wanda naga dama sannan zaici" ta fada tana janye flask din ta maida murfin ta rufe shi ruf,sajida ta miqawa tace ta kai mata daki,ta amsa kuwa tana murna ta haye saka da shi,din jiya itama eeshan sai data zalunceta don kawai ta takata bata sani ba,hakan ya bata ran eeshan matuqa,tana ganin kamar ita zata sumayyan zata yiwa haka?,idan ma da tasan cewa ita tayi da ba zata nuna kwadayinta a kai ba,amma tunda har hakan ta faru dole ta taka mata birki ko don gaba
"Kece matsiyaciya,ba sabanba,duk inda dan talaka yake sai ya nuna hali?" Idanunta ta watsa mata,a fuska zaka rantse bata damu da maganar data watsa mata ba,a nutse tace da ita
"Ko 'yar qaruna?" Isowad ummi wajen yasa sumayya ta ja abincinta ta soma ci,cikin murmushi ummi ta dubi nata plate din ba tare data lura da sauyin yanayin fuskar sumayya ba
"Wannnnan dai ba girkin uwani bane....sumayya ya aka haihu a ragaya?" Ta fahimci sarai me take nufi,tuni ta hanata yin komai,itakam bata iyawa ta wuni sur ba tare data tsinana komai ba,murmushi tayi kanta a qasa
"Ummi na gaji da kwanciya ne,sai naje ja tayata muka yi"
"Ki dai dinga kula,don wannan mijin naki wallahi yazo yaga ba dai dai ba sai ya daga hankalin kowa" ta warashe tana dariya,ta ja plate dim gabanta ta soma ci cikin zuciyarta taba yaba qwarewar girkin sumayya,gefe daya na zuciyarta kuma yana tausayawa almustapha,tasan ko ba'a fada ba yayi kewar abinci mai kyau dadi da tsafta.

        Eesha na gefe ta cika tayi bam,gani take maganar ummin na qarshe ma kamar da ita take,wato ciki ne da ita shine take wannan iskancin?,jan kujerarta tayi baya sannan ta miqe,binta da kallo ummi tayi sannan tace
"A'ah,ya haka"
"Na qoshi ne ummi,zan koma bacci" ta fada tan zare jikinya daga wajen
"Aikin kenan fa,sam baku gajiya da bacci,kudai rago ko don saboda aure"
"Uhmmm....." Kawai ta fada tana nufar daki.

        Ko data shiga kasa zaune tayi bare tsaye,ta kai ta kawo ta rasa sakat,zuciyarta kaman ta fashe,batasan kishin sh'ad da takeyi salama bane akan na sumayya sai yanzu,wayarta ta cilla saman gado sannan tabi lafiyar gadon tana tunanin ina mafita?,tilas ta samawa kanta qofar shiga gidab mustapha koda tsiya koda tsiyatsiya.

       Itakam bayan sun gama wucewarta tayi wajen anty maamaa,dawowarta kenan daga sashen mai gidan wanda yanzun ya fita
"Uwar biyun mu" anty maama ke tsokanarta,dariya ta saka,tana jin kunyar antyn ita kanta
"Baki gajiya kullum sai kinzo gaidani?,da kinyi zamanki ma" ta fada suna gaisawa da sajida data rakota,hira sukayi sosai abinsu,anty maama babu ruwanta,tana da sauqin kai da dadin zama tun asali,abinda yasa zamansu yayi qarko kenan da ummi.

      Suna tsaka da hira mahmoud ya shigo,ya sake wata qiba da haske,ta jima rabon data ganshi,fuskarshi qunshe da murmushi yake fadin
"Antynmu matar yayanmu"
"Ka fadi haka mana tunda kayi wuyar gani kai da mus'ab,amaren ma rowarsu ake mana har yau ba'a kawo mana su ba" ta fada cikin sigar tsokana,anty maama na gefe tana dariya
"Habba anty,sashen naku ne kaman wani tsaro naga yaa man ya qara masa,tunda ya fahimci alqasim abokina ne shikenan naga ya soma nima ciccije min,kinsan halin mutumin sai a hankali,dama yaya lafiyar kura" ya fada bayan ya zauna daura da anty maama yana dariya
"Kaci gidanku,yayanka ne,sannan banda tsaurin ido a gaban mace ka dinga sille mata miji ha'an?" Dariya suka sa baki dayansu sannan suka fara gaisawa ya dora da cewa
"Amare gobe zasu zo dukansu,sun so zuwa dubaki ance bakiji dadi ba,to sai naji ya man ya koma dubai na tsammaci tare kuka koma"
"Kace gobe muna da manyan baqi,to Allah ya nuna mana"
"Ke tsohuwa,yaiushe sirutunki ya ragu ne?" Ya tsokani sakida dake zaune gefe,dariya ta saki
"Yana nan bai ragu ba"
"Au to,na fasa tayaki murnar da nayi niyya" dariya sunayya tayi,akwai wasa tsakaninsu,shikam mahmoud ba ruwanshi,wani lokaci akwai ban dariya sumayya ta fada tana dariya,hira sukayi abinsu sosai kafin daga bisani ta musu sallama ta koma wajen ummi.

       Data koma eesha ce kawai a falon,itama bata zauna ba daki ta koma ta nade kan gado,saboda lokacin yin wayarsu da almustapha ya kusa.

********   *****   *********

        Washegari akayi rasuea maqotan gidan baba prof,hakan ya sanya duka ummi da anty maama basa nan suna gidan rasuwar,gidan daga ma'aikata sai ita sai eesha,sajida ma ta bisu,ga baqi da zasu zo matan mus'ab da mahmoud,hakan ya sanya bayan sun gana wayarsu da mama,zainab,halima,abdallah da yaya yahansu,kowa sai data kirashi suka sha waya sosai,credit mai yawa ta qarar,sannan ta tashi ta shiga wanka kasancewar bata yi wanka da wuri ba tana fitowa a wankan ta shirya cikin wani yadi mai azabar kyau cikin lefanta,ta dubi kanta a madubi,ta zama wata classy sumayya,ita kanta tasan ta sake kyau da sauyawa sosai,hannunta ta dora saman cikinta data fara jin alamun dagawarsa,murmushi ta saki har cikin ranta tana jin farinciki,tana qissima yaya almustapha zaiyi duk randa yazo yaga cikin nan ya fito?,turare ta fesa ta yane kanta da siririn mayafi medium size ta fito daga dakin.
Chapter 197 · 0% Book details