← Book details Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 226

Sashe 43

Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

         Hannunsa dauke da abdallah ya fito daga gudan,bahijja da sumayya na bayansa wadda ta fito don ta dan taka musu,a bakin motarsa sabuwa da ya sauya qirar range rover yaja burki yana duban sumayya
"Tsarabar abdallah bata qaraso ba,ko zaki dan rakamu waccan titin dake gabanku naga akwai wami super market na dan masa siyayya kafin su iso?". Kai ta kada tana dubansa
" haba sabida dorawa kai wahala,mun yafe duk sanda suka iso ma amsa".kunu ya dan sha yana dubanta
"Dorawa kai wahala kuma?,niba babansa bane?,ko kina so kice ba yarona bane?" Baki ta bude tana dariya tare da dubansa tace
"Ni na isa in fadi haka,kai matsala ta da kai son girma fa"
"Ban kai naso girma ba ko sumayya?" Ya fada cikin wani irin salo da ya sauya yanayin muryarsa idanunsa cikin nata,wanda ya haifarwa da sumayyan rage farashin dariyarta,karon farko da taji duban qwayar idonsa ya mata nauyi,sai ta janye idonta tana cewa
"A'ah,ai ko da sakan daya mutum ya girmeka ya girmemaka har abada" dan shiru yayi sannan ya gyara tsaiwarsa yana miqa mata abdallah
"Karbeshi yau mun wunar muku,sai kuma gobe idan Allah ya kaimu" ta amsheshi tana cewa
"Allah ya nuna mana goben" cikim zuciyarta ta dauka da wasa yake,hannun abdallahn ya bude ya sanya masa 'yan dubu dai dai guda uku yana cewa
"Kasha sweet my son"
"Habba abdur rahman...."
Katseta yayi ta hanyar cewa
"Shshshshsh!,ai bake na bawa ba ko?,kuma wai bakijin kunyar fadar suna na haka gatsal?" Galala ta saki idanu ta bishi da kallo
"Kunyar kamar yaya?" Ta fada tana dubansa,murmushu kawai yayi ya bude gaban motarsa ya zauna sannan yace
"Sai goben ko 'yamma ta?" Murmushi ta saka mamakin abdur rahman din na kuma kasheta
"Nice kuma yau 'yammata abdur rahman ga yaro na a hannu?"
"Oh,kuma fadar sunan nawa dai kika yi?" Ya tambayeta yana kada kai,shuru ta masa tana zagayawa wajen bahijja ta dubeta
"Bahijja ki gaida mama kinji,naga alama wannan yayan naki bayan karatu sa ya tafi qarowa ya qaro yadda ake canjin hali" dariya bahijjan tayi tana amaa mata da zata ji,shima dariyar yayi sannan ya tada motar tasa yayin da sumayya ta shige gida.

        Tunda ya shigo da motarsa layin su sumayyan ya hagi tsaiwar wata motar a qofar gidansu,har zuwa yanzu da motar tazo ta wuce ta gefan tashi yana binta da kallo tare da qoqarin tantance waye a ciki,saidai duk qwaqqwafinsa ya kasa gane waye a ciki saboda glasa din motar mai duhu ne,hakanan sai yaji wani abu mai tauri ya riqe masa wuya,rabin 'yar walwalar da ya samu wunin yau ta kau baki daya,a sannu yaci gaba da tuqa motar tasa har ya qaraso qofar gidan ya tsaya ya fito ya samu yaro ya aikashi ciki,ba jimawa yaron ya fito dama sun riga da sun saba duk sanda aka aika akace ana gaida mama to mukhtar din ne kuma sun san me yazo yi,sai halima ko zainab ta kawo masa abdallahnsa,nan cikin mota yake zama da shi su qaraci wasan su sannan yayi horn su fito su karbeshi da abinda ya kawo masa sannan ya wuce,sau tari yakanji sha'awar ganin sumayyan saidai babu wannan damar,rabon da ya ganta ma bazai iya tantance adadin kwanakin ba,tilas yaje danne komai don ya sani a yanzu ta fita a huruminsa.

        Yau din ma kamar kullum hakan ce ta kasance,abdallahn nata masa gwalanto saidai bai gane me yake cewa ba biye masa kawai yake,bai wani jima ba ya maida shi ya tafi zuciyarsa na sakutarsa kan motar da ya gani,ya mance cewa a yanzun sumayyan rabon mai rabo ce ba mallakinsa bace

  ****    *****   ******  ****

          *BAYAN KWANA BIYU*

      Tun daga ranar abdur rahman ya maida gidan gurin hirarsa,wani lokaci yazo shi kafai wami lokaci ya taho da bahijja,da yake su biyu Allah ya bawa mamansu,sukan dauki lokaci da sumayya suna hirarsu,yayin da wani lokaci idan ya furta wata maganar sai ta sanya ta a duhu,wani sa'in takan yi murmushi ta alaqanta hakan da girma da abdur rahman din ya sake yi,ya fara zama babban mutum shi yasa yanayin hirarrakinsa suke sauyawa,bata taba kawo komai cikin zuciyarta ba saboda ita din rainon mutum daya ce da mutum daya ta taba gina duniyarta wato mukhtar,ba komai take iya ganewa ba ko fahimta game da wasu baqin al'amura a gun d'a namiji ba.

     Sau biyu mukhtar na katarin ganin motar na tasiwa daga qofar gidansu ta fice daga layin,saidai har yau bai samu nasarar gano waye ba,lamarin ya tsaye masa a zuciya,duk da yasan baida hurumin hakan amma zuciyarsa ta gaza daurewa,hakan ne ya sanyashi cin washin zuwa ya tadda ko waye.

    Tunda ta fito daga makarantar tasu ta lura yake bin bayanta cikin mota wanda hakan ya matuqar tsorata ta musamman data lura yau unguwar tasu babu yawaitar jama'a,hakan ya sanya ta qarawa qafarta sauri.

      Ganin tana neman bace masa ya sanya shi faka motar sannan ya fito ya biyo bayanta,gabanta taga an sha wanda ya hakan ya dan tsorata ta taja baya taba dubansa,matashi ne wanda a qalla zaiyi shekara arba'ain da biyu,dogo ne baqi maras jiki sosai,za'a iya karansa da chaculet colour,babu laifi yana da kyau dai dai gwargwado,kana kallonsa kasan yana cikin rufin asiri da wadata dai dai gwargwado
"Assalamu alaikum" ya fada yana murmushi wanda sallamar ta dauke kaso mafi yawa daga cikin tsoron da ya cika zuciyarta,cikin qarfin hali ta amsa masa
"Don Allah kiyi haquri,nasan ban tsaidaki a yanayin da ya dace ba,nidai suna na lukman,na gaza daurewa zuciya ta ne shi yasa ni aikata hakan,na lura kamar a darare kike da ni,idan ba zaki damu ba ki bani lambar wayarki sai muyi magana" kamar kuwa ya sani a takuren take,saboda wannan shine karo na farko da ta fara tsaiwa da wani namiji,ga masu shugewa jifa jifa suna faman binta da kallo,hakan ya sanya cikin rudewa ta karanto masa lambar halima don bata da niyyar bashi tata,yayi serving yana murmushi gami da yi mata godiya,bata ko jirayi amsa masa ba tayi gaba da sauri shima ya wuce ya tada motarsa ya fice a layin.

        Tun daga nesa take hangowa kamar shine sabe sa abdallah ya zuba mata idanu,sai data qaraso gab da shi ta tabbatar shi din ne kuwa,hannunsa dauke da leda wadda ta tabbatar abdallah ya yiwa siyayya kamar yadda ya saba
"Waye wancan?" Ya tari numfashinta ya furta fuskarsa a dan daure ta hanyar riga ta yin magana,dan galala tayi tana dubansa cikin mamaki,sai kuma ta basar ta saki dariya cikin tsokana tace
"Bazawari na ne"
"Bazawarinki?" Ya tambaya cikin nanatawa har sau uku yayin da ta tsaya tana sake dubanshi
"Eh mana" ta fada kanta tsaye,shiru yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya sauya akalar abinda zai fada din da cewa
"Ok,muje qofar gida akwai maganar da nakeso muyi" ya fada cikin magana ta gaske yana yin gaba,kamar an qulle bakinta sai ta ja qafafunta ta bishi.

      Qofofim gaban motar ya bude ya shiga nashi mazaunin yana dauke da abdallah wanda baiko damu da ganin maman tasa ba,ya wani lafe jikin abdur rahman din yana ta fama da biscuite,dubanta yayi ganin tana tsaye qiqam a waje
"Bismillah shigo ki zauna" kafadunta ta daga
"Haba,ai kaima kasan bai kamata ba,mu shiga cikin gida kawai ko meye ai ina ga sai yafi dadin tattaunawa ko ba cikin mota ba"
"Ai nasan da cikin gidan,amma maganar bata cikin gida bace,idan kuma kina da wani gu da zamu mu tattauna kuma to" kanta ya daure tana mamakin wacce iriyar magana ce haka da yakeso suyi da sai su kadai?
"To amma kuma malam fa,idan ya dawo ya ganni cikin motarka"
"Indai malam me baki da matsala,na gaya miki hakan da gaske" dan shiru tayi sannan ta sake bude murfin ta shiga ta zauna ba tare da ta maida murfin ta rufe ba,abdallah ne ya soma yunqurin tahowa gunta hakan ya sanya ya miqa mata shi,sai da ta zaunar sa shi sosai ya nutsu a gunta sannan ya soma magana
"Sumayya..."
Yadda yayi kiranta ya sanya ta daga kai ta dubeshi
"Kinsan cewa tun kafin a haifemu Allah ke rubuta mana dukkan wani abubda zai faru da mu har ya zuwa ranar mutuwarmu ko?".kai ta jinjina tana bashi dukkan nutsuwarta
" a gaskiya sumayya bazan cuci kaina ko na zalunci kaina ba,sumayya.....haqiqa na ga dukkan wasu halayya na mace ta gari,naga dukkan wasu dabi'u na macen da za'a iya aure ta zama uwar 'ya'ya,na gamsu na nutsu,nagano alkhairai a tattare da ke sumayya,da haka zuciya ta ta fara qaunarki sumayya,zuciyata ta gamsu da ke a matsayin wadda zamu rayu tare,ina sonki ina qaunarki,ina buri ki zama mata ta,ina kuma fatan zaki amince da maganganuna,kin san ko waye abdur rahman sumayya tun ba yau ba,saboda haka mene ne ra'a yinki a kaina?"
Dariya dariya ta saki duk da tarin mamakin dake cunkushe cikin zuciyarta
"Kai abdur rahman,Allah ka iya wasan kwaikwayo,kyanka dramer"
"Sumayya!" Ya kira sunanta da dan qarfi wanda shi ya sake jan hankalinta gareshi
"Dubeni da kyau!,kinga wasa a idanu na da fuska ta bare kalamaina?,wallahi billahi babu wasa cikin lamari na,da qarfina nazo gareki sumayya ko yau kika amince a shirye nake da a daura min aure da kai".
Chapter 43 · 0% Book details