Sashe 166
Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali ya tura qofar dakin,babu haske a dakin kasancewar babu kowa,ko ina dumdum yake da duhu,kunna qwai yayi yabi ko ina na dakin da kallo,sai yaga dakin tamkar bashi ba,komai ya canza,wani fili yaga dakin ya sakeyi kamar an dauke wani abu,wata gajiya ta musamman ta saukar masa,ya taka zuwa cikin dakin ya zauna gefan gadon idanuwanshi na kan doguwar kujerar data saba zama,yana fidda takalmin qafarshi da safa yana jefarwa,gadon ya fada baki daya yana fidda iska daga bakinsa,a qalla ya kai kusan minti goma a haka kafin ya miqe ya zauna dai dai,wayarsa ya fidda ya kira ya bada umarnin a kawo mishi dinner sannan ya miqe ya cire kayan jikinsa ya fada toilet,turus yayi yana duban bathtube wanda yake wayam babu komai a cikinsa,sabanin watannin baya da idan ya dawo yake tadda shi cike da ruwa mai qamshi da dumi,cikin kasala ya soma tara ruwan kafin ya shige cike,qaramin tsaki ya ja,baki daya ruwan bai masa ba,sabanin nata da yake jin baison fita a ciki,a gurguje yayi wankan ya fito yana tsane jikinsa da towel aka yi knocking,sai daya sanya doguwan riga sannan ya bude ya karba,shafa'i da wutiri yayi kafin ya dauko computer dinsa ya kunna bayan ya jonata chargy,sosai ya zauna a qasa ya bayan ya janyo abimcin ya bude ya soma kaiwa bakinsa,lokaci lokaci yakan daga kai ya kalli inda ta saba nadewa duk lokaci irin wannan da yake zama cin abinci ko yin wani aiki,lokaci lokaci yakan kamata tana satan kallonshi da fararen idanuwanta,ko ita wani lokacin ta kamashi ko su kama juna,kowa yakan dauke kai da sunan ba kallon dan uwanshi yake ba,qaramin murmushi ne ya subuce masa,ya ture abincin dake gabanshi,yana tuna sanda tayi yajin aikin daina kallonshi tun faruwar lamarin a wannan daren,kai yake girgizawa yana sake tuna duk wani minti daya daya gifta musu a daren,cikin hanzari ya soma kokawar kauda tunanin,ya jawo computer din ya soma kunnata cikin bawa zuciya da gangar jikinsa karsashi da qwarin gwiwa,saidai duk yadda yaso da nuna jarumta lamarin yaci tura,gajiya da kasala sun mamayeshi,haka ya sanya dole ya kashe wutan dakin ya fada gado,idanuwanshi still kan kujerar tata,sannu sannu idanuwan suka dinga lunshewa bacci ya rinjayesu.
Ko da ya tashi da safe abu na farko daya fara takawa shine takalminsa,tsaki ya ja sanda ya tuna jiya bai kwashesu ba ya kaisu muhallinsu,ya saba da zarar ya cire bai zuwa ya taddasu wajen,haka ya duqa cikin kasala ya janyesu gefe sannan ya wuce,yana shiryawa yana sake duban duk wani muhalli da takanyi kai kawo a wurin da safe irin wannan,musamman inda ta saba zama tayi karatun qur'ani ko taja carbi,kai ya girgiza yana tsaki tare da tuhumar kansa me ya sameshi ne haka?,a gurguje ya shirya ya fice zuwa office.
Ko da ya dawo yau dinma kamar jiya,bai shigo da wuri ba,haka ya dinga wasiwasi cikin dukka ayyukanshi,kanshi ya shafa idanuwansa a lumshe,yana tunanin tsananin sabo ne ke dawainiya da shi,don me zata zauna cikin tunaninshi haka?,don me zai kwana ya tashi ya wuni cikin tunaninta ita daya?,bai taba fuskantar irin wannan yanayin ba tsawon rayuwarshi,to yau ko cikin baccinsa ma bai samu hutu ba,sai da ta kawo masa ziyara,wanda hakan ha sabbaba masa yin wankan tsakiyar dare,hakan kusan sai ya zame masa kamar al'ada ko wani jarrabi cikin kwanakin,idan yau baiyi ba gobe zaiyi,duka ya tattara hakan ya dora bisa mizanin sabo da kuma cikakkiyar lafiya da Allah ya bashi.
Cikin kwana na biyar da tafiyar tata cikin dare bayan yayi wanka ya dawo sai baccin yayi nashi waje,haka ya dinga juyi shi kadai,baisan me yasa garin baki daya ya daina masa dadi ba ya fita masa a kai,miqewa yayi ya janyo wayarshi ya hau binciken da baisan dalili ba,cikin haka hannunshi ya kai kan bigiren hotuna,tunani yake bari ya gwada abinda yaga rannan tana yi,yana tsammanin zasu debe masa kewa kamar yadda yazo ya tarad da ita tana kallon hotunan cikin wayarshi,hoton farko dake bangaren camera nata ne,cikin shigar doguwar riga,da sauri ya wuce zuwa hoton gaba nan ma ita ce,sai ya sake wucewa,nashi hoton ya gani,ya jima tsaye kan hotonsa sai ya samu kansa da dawo da hoton baya,kamar wanda ake umarta ya sanya hannunshi yayi zooming,komai ya fito tar cikin hoton,tana tsaye gaban mudubi tana murmushi,fararen idanuwanta zuwa dan qaramin bakinta mai dauke tattausan labba yake kalla,bai manta laushin da yaji a wajen,bai manta hasken wadan nan idanuwan ba,da sauri ya fita daga hoton ya ajjiye wayar,ba shakka sha'awa ce kawai ke fusgarsa,ita ke damunsa,amma me yasa baijin haka wajen su'ad tun asali?,shima bai sani ba,yaye bargon yayi ya koma toilet ya daura alwala ya dawo ya shimfida abun sallah ya tada nafila.
******* ****** *******
Washegari a makare ya isa office duk da sunyi da hamza huzaifa da lamin zasu hadu,dubansa lamin yake sanda almustapha ke yiwa jakarsa mazauni shima yana neman zama,yayi kyau cikin suit mint green wanda suka haska farar fatarshi data jiqu da hutu,agogon hannunsa lamin ya kalla
"Maan ban sanka da karya alqawari ba,saidai yau gashi ka saba,but idanunka suna nuna ma kamar baka samu isashshen bacci ba"
"Shi kuwa ya samu isashshen bacci,uban wa zai hanashi bacci yana shi daya a daki,d same thing fa yanzu muke" inji huzaifa yana duba wani file kamar bashi yayi maganar ba
"Gaskiya ka fada my guy" inji hamza wanda tun dazu yakeso ya takeshi dama,idanuwanshi yacu gaba da zuba musu bayan ya sarqe yatsunshi cikin juna,duka sai da suka gama iskancinsu sannan lamin yace
"Ga allocation din da gwamnati ta bamu ka duba" ya fada yana tura masa file gabanshi,banza ya masa,yaja wayar landline ya bada umarnin yanka masa ticket da zai tashi daga dubai zuwa nijeria wanda zai sauka a aminu kano international airphort kano,ji yake tamkar wani abu na janshi zuwa nijeria,baibtaba tsammatar tafiya cikin tsukin wadan nan kwanakin ba,ya kife wayar ya musu transfer kudinsu sannan ya ja file din yana dubawa ba tare da yace musu uffan,kana dubansa kasan halinne ya motsa,kusan duk sun sani,shikam hamza yaci alwashin sai ya sanyashi magana
"But maan me zaka je yi kano" sai da ya daga kai ya dubeshi
"Ka mance zan aurar da qanne?"
"Amma ai ina cewa jiya muka gama maganar next week kaman friday haka zamu wuce baki dayanmu har da su huzzy"
"I change my mind" ya fada kai tsaye
"Ko kuma she changed your mind ba" sake dagowa yayi yana dubanshi
"Me kake nufi?"
"As i said" ido ya zuba masa yana duban hamzan kamar mai nazarin wani abu,sai murmushi ya qwace masa,girgiza kai yayi ya maida kansa kan file yana ci gaba da kada kai,su huzaifa na dariya qasa qasa
"Iam telling you,he became crazy wallahi cikin watan nin nan,shi kadai sai ka ganshi yana murmushi,kun tuna yadda murmushi ke masa wuya a baya?,kana wasa da mata maan,mata ba abun wasa bane,duk yadda kake ganin u r powerfull nasu power din yafi naka,so ka bisu a hankali man tun ba'a saka ka fara kneeling ba kana begging"
"Saurara malam,naga ka fara wuce gona da iri,ni...ni zanyi kneeling ina begging,begging for what?"yayi saurin tarar numfashin hamzan
"For love ko?" Inji huzaifa yana rufe bakinsa da wata takarda saboda shegiyar dariyar dake sakadarshi
"God forbid wlh,an gaya muku kowa irinku ne?,mtsweew,kunga idan wannan ta kawoku na tashi na barmuku office din,idan kun gama kwa kirani,i have alort to do" dole duka suka zama seriouse suka hau tattaunawa kan abinda ya tarasun,kowanne yana so ne yaga yadda maan zai fara buga nashi love din da wadda yakeso,duk cikinsu ba wanda bai kwana da sanin cewa shi din mutum ne dake bala'in qaunar soyayya cikin rayuwarshisau tari idan suna hira ko siyan gift wa 'yammatansu tabe baki yake yace basu iya komai ba duk yadda suka kai ga qure adaka,wani irin mutum ne mayen love,shi yasa suka jimanta masa a sanda baiyi dace da dai dai ra'ayinsa ba,a nutse suka soma tattaunawa kowa na maida hankalinsa kan lamarin,bude sabbin reshe da suke so suyi a qasashe biyar kowanne branch zai baiwa daya daga cikinsu ya riqe ragama,bawai don kowannansu bai mallaki abun kansa ba a'ah,tsabar qauna yarda da aminci dake tsakaninsu ne,da kuma koyi da yin abota mai kyau da doctor almustapha ke da buri da kwadayin yi irin na mahaifinsa professor mukhtar.
Ga almustapha da su'ad zuwa nijeria,muje zuwa readers..............
*Ummu muhammadiyya.*
*mrs muhammad ce*👑
*Ummu muhammadiyya.*
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
8⃣5⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*
*wannan page din kuma naku ne*
*sparkling son sorians by batool mamman*
*Allah ya bar zumunci*
_____________________________________
A qalla ya kusa minti talatin zaune cikin motar a qofar gidansu,ya dubi agogo karo na kusan biyar yaja dan qaramin tsaki,baisan me ya jawoshi qofar gidan ba,to idan ya shiga yace me?,me ya kawoshi?,la'asar ne bare yace malam yazo gani,bai da tabbacin yana cikin gida a wannan lokacin,tun suna hanya ya dinga kai kawo cikin wayarsa bangaren adana lambobi baiga komai ba da zai iya amfani da shi,ya motsa labbansa da niyyar bawa drivan umarnin yaja motar su wuce sai yaga fitowar malam din,sanye da shadda milk babbar riga,fuska akwai ruwa da alama alwala ya kammala masallaci ya nufa zaiyi sallar la'asar,cikin hanzari ya balle murfin motar ya fito,dakatawa malam yayi ya zubawa wajen ido sanda yake qarasowa
"A'ah,mustapha ne?,saukar yaushe?yanzu dama tasan da zuwanka amma ta fita unguwa?" A ladabce ya fara shirin rusunawa malam ya dakatar da shi da hanzari
"A'ah,miqe kada ka bata jikinka" duk da haka sai da ya dan rage tsawonshi suka gaisa
"Bari na baka ruwa ka daura alwala idan mun dawo sai mu shiga ciki ko?" Malam ya fada yana niyyar juyawa ciki,jin haka ya sanya drivansa saurin komawa mota don dauko masa ruwan riba,da hannu ya dakatar da shi,suna tsaye malam ya iso da butar ya miqa masa,ya koma saman dandamalin qofar gidan ya fara daura alwalar,a hankali yara suna fara giftawa suna kallonshi,kafin ya kammala sai ga yara sun soma taruwa suna kallonshi,a tsakaninsu suke qus qus din balarabe ne wlh,murmushi malam ya saki don ya jisu,karbar butar malam yayi ya aiki daya daga cikin yaran ya maida gida sannan suka wuce masallacin tare.