← Book details Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 226

Sashe 42

Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bata kammala ficewar ba ya taso da kuzarinsa ya qaraso gabanta sanda ta cire maman daga bakinsa tana gyara masa rufa,ya miqo hannunsa ta dora masa shi saman hannun nasa tana fadin
"Ga abdallah nan"sai ya cira kai ya dubeta,tabbas suna ne mai kyau da asali,ko shi din ma sunan yayi masa,baice komai ba ya koma da baya ya zauna inda ya tashin yana kallon yaron,baisan fuskarsa ta wadata da murmushi ba,baisan hawaye na bin fuskarsa ba sai da yaga digarsu kan kuncin yaron wanda hakan ya sanya yaron bude idanunsa yana kallonsa,wata qaunar sumayyan ke son dawowa cikin zuciyarsa,ko babu komai koda ta aikata laifin tayi fama da dakon wannan qaton babyn cikin cikinta tsawon watanni tara ta kuma yi naqudarsa ta haife masa,rana da wani matsayi na daban wanda babu diya macen da ta takashi cikin rayuwarsa,ita din ma dubansu take tana daga zaune,wani wawan rauni keson ziyartar zuciyarta,saidai zargin saurin yanke hukunci na mukhtar da rashin bincike ke naushin zuciyarta,sai ta dauke kai daga dubansu tana jin kuka nason qwace mata tana qoqarin maida shi.

Ya jima zaune yana aikin kallon yaron da yi masa addu'a tamkar zai maidashi ciki,sam kamar ma bashi da niyyar tafiya,har sai da aka sake yin baqi sannan ya miqe ya dora mata shi saman cinyarta,ya sunkuya ya sumbace har tana jin hucin numfashinsa wanda hakan ya sanya ta ja da baya,ya dago yana dubanta bayan ya ajjiye ledar da ya shigo da ita a gefanta ya dora kudi a sama
" ga wadan nan ko zakuyi amfani da su,ban yarda a dorawa kowa wani nauyi wanda yake nawa ne,Allah ya qara muku lafiya"ya fada yana juyawa ya fice daga dakin a sanyaye tamkar bai son tafiyar

**** ***** **** ****

Cikin kwanakin hidima aka dinga yi sosai cikin gidan,duk wani dan uwa na jiki ko aboki babu wanda baizo ya tayasu murna ba,mukhtar kuwa kullum qafarsa na gidan babu ranar da bazaizo ganin fuskar Abdallah ba,sau tari saidai sumayyan tasa a miqa masa shi tana daga cikin gida.

Yaya yahanasu tazo a kunyace saidai ita daya don sauran duk sun kasa zuwa,atamfa ta kawowa sumayya turmi biyu sai dan qaramin akwati na qarshen wanda ta cikoshi da kayan baby,ba wanda ya nuna mata komai suka karba suka mata godiya.

Suna akayi na gani na fadan tamkar tana gidanta,hatta anty dije dake abuja ba'a barta abaya ba sai data halarta ita da yaranta baki daya,duk da cewa suna tsaka da zangon karatu amma sai da suka dauki uzuri suka zo,rago da saa mukhtar ya yanka masa,sosai abdallah yaga gata,yaron yazo da farinjini da goshi mai yawa,qauna da soyayya ko ta ina,kowa gwada masa kalar tasa yake yi.

**** ***** *****

Jego take sosai irin na daa shi mama take mata,sosai take gasata ta kuma cikata da cimaka,irinsu romon nama,tuwon dawa kunun kanwa kunun gyada da sauransu,hakanan babu fashin wankan ganye safe da yamma take yinsa har sai data cika kwanaki arba'in harda doriyar kwana biyar,zuwa lokacin ta murje ta dada kyau,idan ka dubeta ba zaka taba cewa ita ta haife abdallah ba,yayin da abdallahn yayi wani irin wayau da qiba dauka da nishi ajjiyewa da nishi,kullum mukhtar na hanyar gajin yaronsa,sau tari yakan bawa mama da malam tausayi yadda baya ko gajiya,duk sanda zaizo hannunsa dauke da wani abu yace na abdallah ne,har da abinda bazai yi masa amfani a yanzu ba saidai ko nan gaba,itakam sumayyan bata ma yarda su hadu bada yaron take ta shige daki,yakan jima yana yiwa yaron wasa tare da jin qaunarsa da kewar mahaifiyarsa cikin zuciyarsa.

**** ***** ***** ****

Rayuwa ta mata kyau saboda ta samu gata yadda ya kamata,cikin watanni uku abdallah ya soma iya zama,wata na biyar rarrafe ya miqa,sosai yaron yake da shiga zuciya da daukan hankali,saboda tsafta da kukawa da yake samu,ko yaushe zaka ganshi tsaf cikin shiga ta gayu kamar wani saurayi,idan manyan kaya ta sanya masa kai kace babban mutum ne,idan kuma qananun kaya ne sai ka dauka saurayi ne,baya rabo da qamshi shi yasa har maqota aikowa suke daukarsa,zuwa wannan lokaci mukhtar wani lokacin yakan zo ya daukeshi ya jima wajensa wani lokaci har kasuwa yake leqawa da shu,tun tana bata rai mama na mata fadan na zata raba da da uba ba har ta saki ranta ta haqura,wata goma ya qware a tafiya sosai,idan ka ganshi sai ka zaci yayi shekara daya da rabi ne.



A lokacin yaya abubakar ya sama mata foam na wata makaranta dake koyar sana'o'i,ta zabi ta koyi yadda ake saqa da humra turaren wuta da na kaya da na tsugu no,hankali kwance take zuwa makarantarta ta dawo don bayan layinsu take,abdallah kuwa bai cika rigima ba sai idan yaso,saboda haka a gida take barinsa taje abinta ta dawo,koda ya sa rigima ma zainab ko halima kan daukeshi su kai mata shi,a lokacin ta sake wani kyau da cika,saika rantse da Allah bata taba aure ba balle har ta haifi yaro.

***** ****** ******

Qarfe hudu da mintuna ta iso gida a gajiye,tana sallama abdallahn ya kubce daga hannun zainab dake shafa masa hoda a wuya da alama wanka aka sake masa,riga ce mara hannu a jikinsa sai wando three quater,yayi kyau sosai,da gudunsa ya taho ya tareta yana mata gwalantu wanda ke nuna alamar fara koyon magana,daga shi sama tayi tana juya shi suna qyalqyala dariya sannan ta direshi tana amsa maganar zainab wadda ke mata qorafin yau abdallah ya bata kaya sunfi uku
"Kunfi kusa ai,bake ke kareshi ba idan za'a masa fada" tayi maganar tana qarasawa bakin fanfo don daura alwala tana sake fadin
"Mama fa?,naji gidan shiru" zainab dake tattara kayan kwalliyar abdallah ta amsa mata
"Eh sun fita ita da ya halima gidan maman shafa'atu ganin salima"
"Kice biki ya kusa kenan"
"Wlh saura 'yan satittika basu wuce uku ba"
"Allah ya sanya alkhairi" ta fada tana gyara daurin dankwalinta ta shige daki donyin sallah abdallah na biye da ita a baya yana mata surutu.

Tana kammala sallar abdallah na saman jikinta yana faman qiriniya da nuqurqusarta taji sallama kamar ta bahijja,kafin ta yunquro taji ana tambayar tana nan zainab ta amsa da eh,bahijjan ce kuwa,hannu bibbiyu ta karbeta sai da suka fara gaisawa ta sanar mata tare da abdur rahman suke yazo ganin abdallah,idanu ta zaro tana dariya
"Iyeee,kice da tare da larabawan madina kuke kada kai ace har an gama karatun?" Cikin murmushi bahijja tace
"A'h,yadai samu hutu ne yace tunda ya shekara bari yazo yaga gida"
"Da kyau.....zainab zoki dauki carfet ki shimfida masa a zaure(soro)"ta fadi tana murmushi tare da qoqarin miqewa.

Tare suka fito da bahijjan saboda abdallahn na hannunta,ji take kamar kada ta ajjiyeshi yaron ya shiga zuciyarta sosai.

Tun kafin ta qarasa soron wani kalar qamshi na daban ya ziyarci hancinta,zaune yake ya hakimce kan carfet din,yana sanye da shadda ruwan siminti sai qyalli take,kansa saye da baqar hula,baki ta riqe tana murmushi,sosai abdur rahman din ya sauya,ya zama wani babban mutum lokaci daya,kai bakace abdur rahman din dake tayata zama bane sanda tana amarya mai qarancin shekarun da basu gaza goma sha uku ba,ya zama mai cikakkiyar kamala da haiba,fatar nan tayi fresh da ita,duk yadda taso ta zolayeshi da tsokana kamar yadda suka saba sai ta kasa sanda shi yake tsokanarta da iyeeem ba,yarinya ta girma gata da yato ta zama mama,bayan sun gama barkwancinsu kasancewarsa mutum mai yawan son barkwanci sannan ya shiga jajanta mata abinda ya faru tun daga samuwar cikin abdallan zuwa haifeshi,suna tattaunawa yana wasa da abdallahn har bahijja ta gaji ta tashi ta koma ciki wajen zainab ta barsu a nan.

Sosai yaron ya masa ya tafi da shi har ya gaza boyewa sai da ya furta,murmushi kawai tayi suka ci gaba da hirarsu a haka mama ta cimmasu,a mutunce suka gaisa tana mamakin ganinsa da sauyawarsa ta tambayeshi mutanan gidan ya amsa duka lafiya ta dubi sumayya
"Amma ai abdur rahman ba baqo bane da zaki barshi a soro,maza tashi ka dawo tsakar gida" cikin tsokana yace
"Atoh mama na sani ko rowar gidan ake min,ni kuma naga gun hira kuwa har na koma,tunda nayi aboki" hararar wasa sumayyan ta masa tana cewa
"Dadinta ai na maka tayi kace a'a tunda mama bata nan nan zaka zauna" ta fada tana shigewa cikin gidan.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

3⃣6⃣

_____________________________
*Bismillahir rahmanir rahim*

*huwallazi yuhyi wa yu miit*

*sannan shi (Allah) shi yake rayawa yake kuma kashewa*

______________________________

       A tsakar gida zainab ta sake shimfida musu wata tabarmar suka koma ciki.

       Hira sosai suka dinga yi har da mama,abdur rahman na basu labarin garin ma'aiki madinatul munawwara har aka kirayi sallar magariba,tare suka fita sallar shi da malam da yaya abubakar,koda suka dawo ma bai tafi ba tare suka ci abincin dare sannan ya musu sallama.
Chapter 42 · 0% Book details