← Book details Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 218 OF 226

Sashe 218

Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

      Bayyana irin farincikin da baban ya shiga ma bata baki ne,har qaramar qwalla sai da dauke yana tasbihi ga Allah,basu jima da shigowa ba anty maama ta daeo,saiga mahmoud wanda shima bakinsa ya kasa rufuwa,ko kunyar baban da anty maamaa baiji ba yake cewa ya Allah shima ya bashi kaman hakan,addu'a yayi musu baban sosai mai tsaho wadda har tasa su'ad ta soma qosawa,ta dinga sakin tsaki a boye,guda daya ya shiga kunnen almustapha ya waiwayo yana dubanta,sai ta dake ta saki murmushin yaqe cikin duniyanci sannan ta sake maida kai wajen baban,sai da ya gama ya miqa musu yaran,ya yiwa sumayyan addu'a itama sosai,tun tana amsawa har kuka ya qwace mata,alkhairai yake roqa mata na duniya dana lahira,amsawa take tana kuka addu'ar na sauka cikin zicuyarta tana fatan Allah ya amsa,sai da ya gama da ita sannan ya sanya almustaphan da su'ad a ciki,suka shafa ya jawo wani file wanda da alama musamman ya ajjiyeshi saboda wannan zaman,takaddu ya fito da su ya ajjiye gaban sumayya
"Ba abinda bazan iya yiwa yaran almustapha ba,kaman yadda babu irin biyayyar da baiyi min ba,hatta da mahaifina ya soshi tun yana tsumman goyonshi,ba don mahaifin yaran baida shi ba ko ya gaza,a'a,nayi ne saboda murnar zuwansu duniya kaman yadda nake bawa kowanne jika na,saidai su din tasu kyautar ta musamman ce kaman yadda su da iyayensu suke na musamman a wajena" a nutse yake musu bayanin abubuwan da ya mallakawa yaran,wanda duk wanda ke wajen yasan cewa eh lallai ba qaramin matsayi da alkhairi yaran suka zo da shi ba,kyautar ta girgiza su'ad har ta ringa jin kaman kunnenta ba dai dai yake jimata ba,hakan yasa ta saki duk aninda take ta tattara hankalinta tana sauraren sha tara ta arziqin da baban kewa yaran,daga bisani ya rufe da baiwa sumayyan kyautar kujerar umra da kuma sabuwar mota fil wadda take qirar wannan shekarar,koda cikin masu kudi ba kowa ya samu zarafin yin orderta ba,kyautar data sanya su'ad sakin kukan da taso dannewa,motar da take qulafucin samu?,motar da take tattalin kudinta dinta siyeta saiga haihuwa ta siyawas sumayyana bagas,miqewa tayi tana rushin kuka ta fice yayin da kowa ya bita da ido,kusan kowa yasan abinda ya taba ranta amma dattako irin na dattijon sai yace almustapha ya tashi yaje ya rarrasheta
"bata da lafiya ne zata je tasha magani ne"
"To Allah ya sawwaqe" bai iya amsawa baban da amin ba tsabar takaici,tabbas baiyi qarya ba,hassada mugun ciwo ne,hassada tana cinue kyawawan ayyukan mutum kamar yadda wuta kecinye yayi,ka tashi ran qiyama baka da komai cikin kyawawan ayyukanka duka hassada ta cinye.

        Cikin kwanaki hudu da zuwamsu duk wani dan uwa dake kusa yazo yaga 'yan biyu,yaran sunzo da wani irin alkhairi da farinjini,kowa cikin farinciki yake kaman a sannan familyn suka samu jika na farko,kullum gidan baya rabo da jama'a tako ina,ko yauahe qofar gidan a bude take,suna kuwa tun kafin ranan yinsa kullum yinsa ake,saboda ci da sha da ake yi a gidan kullum kwanan duniya,duk wanda zaizo da kyautar da zai ajjiyewa yaran,saboda kowa ya fuskancu yaran 'yan gaban goshi ne ta kowanne bangare,ita kanta ummi da kyautar data musu haka anty mama,bare manyan iyaye anty farida hida da anty ni'imah,hakan ya sake daga hankalin su'ad matuqa,har takai bata da katabus sai tagumi qunci da bacin rai,bata da magana sai da tuni ita ke amsar wannan abubuwan,da tuni itace a wannan bigiren.daga sunan akayi aka maidashi dai dai da randa yaran zasu cika sati biyu a duniya,suna saura kwana hudu saiga malam da mama,tayi matuqar mamaki da farinciki,kwana biyu sukayi,mama ta siyawa yaran barimar gwal da zobe,sai awarwaron azurfa wanda ya musu yawa saidai nan gaba sa saka,randa suka tafi washe gari saiga halima zainab data haihu wata uku kenan ta samu namiji,sai anty meena,har da abdallah,yaya abbakar ne kawai bai samu zuwa bawayyo ranar kasa cin abincin kirki sumayya tayi saboda murna,abin kam ba'a cewa komai,haka ta zauna cikinsu tana jin dadi sosai,dan uwa akwai dadi,duk wanda ya rasa dan uwa yayi kuka kam

        Ranar suna ta kasance baabbar rana ga duka ahalin,hidima akai qwarai da gaske kaman ta bikin aure,ranar har kukan farinciki sumayya tayi,babu shakka duk bawan da yayi haquri da qaddara mara kyau gaba Allah zai musanya masa,kuma Allah baya dauke maka wani jin dadi koya jarrabeka khaka kawai sai don ya musanya maka da abinda shi yafi alkhairi a gareka wanda kai bakasan da hakan ba,alkhairi kam sumayya ta sameshi wanda bata taba tsammanin samunshi ba,washegarin suna aminan qwarai musaddiq lamin hamza usman da huzaifa suka hada qawatacciyar walima,wanda iyakan abokansu ne da makusantan mai jego,ranan almustapha yaga tsiya,hamza ya kwasheshi son ranshi,cewa yake
"Iyeeeen ba,ashe dai ba jarumin qarya bane,duk tsare gidan nan ba'a banza ba,twince ne ke tafe,amma fa rashin son raini da hayaniya ya zama na banza,ashe tsula tsiyarka kake a daki kaman ba....." Duka ya kai masa wanda da qyar hamza ya kauce,su lamin suka dinga kwasar dariya,can anjima sai ya matso gefan kunnenshi
"Yallabai....a bamu sirrin mana,ga wadan nan manyan gaurayen an sanya ranar aurensu shekara daya masu zuwa(lamin musaddiq da huzaifa)"
"Zaka gane kuranke ne wallahi hamza kafi kowa sanina ban da kyau" sai da ya masa haka sannan ya shafa masa lafiya,anci am sha an rashi cikin raha da walwala,bayan kowa ya yiwa aminin masa kara da kyauta ta bajinta,don almustaphan ba baya ba,ya riqe aboka qwarai da gaske,bashi da qyashi ko hassada,komai ya taso naci gaba burinsa ya sanyasu a ciki su samu kowa ya samu ci gaba,kusan duka gaban idanun su'ad aka gabatar da komai,hakan ya sanya tun dare ta tashi hankalinta zata gida,kuka ba irin nau'in wanda batai masa ba,amma yayi biris da ita,don bata dauko hanyar da zai barta ba,lafazinta kawai ya isa ya sanya a hana mata duk wani abinda take so,qarahe ma falo ya dawo yayi kwanciyarsa,yana jin kewar sumaya,don a qa'ida kwananta ne,amma jego ya raba tsakaninsu,dako banza zaya samu kulawa da tattali,tsaki ya dinga ja yana juyi,wai dama haka jegon yake?,yanajin wannan jegon bazai iya da shi ba,idan suka hanashi tafiya da ita nan da next week ba shakka zai saceta ne su gudu,su basusan halin da yake ciki ba sai suce dai tayi wani jego.

Washegari tun qarfe tara baba ya kirayi wayarshi yace yazo yana son ganinsa,sanda ya isa shi daya ne
"Ka siyawa su'adatu ticket taje taga gida" shine unarnin da baban ya bashi,ba musu ko jayayya tsakaninsu har abada,hakan ya sanya bai tambaueshi bai kuma yi masa bayani ya amsa da to ciki girmamawa,ya kuma siya din,saidai da ya siya baban ya kaiwa ba ita ba,daga hakan baban ya gano lallai ba son ranshi bane,saidai tunda ya riga da ya siya haka ya danqa mata,har ta tafi bata ga qeyarsa ba,hakan ba damuwarta bane,tasan cewa lokaci qalilan ya rage ta samu dukkan kulawar data keso,zata shuka tsiyarta za kuma ta zuba iskancinta yadda taga dama,haka take rayawa a ranta.

Jakarta kawai ta ajjiye suka fito ita da mommyn nata,ta riga data siya musu tikitin jirgin qasa har ya zuwa unguwar da sibitin yake da zama,tafiya ce ta kusan awanni daya,wanda cikin awa daya da rabi suka isa ga ofishin ainihin likitan da suke nema,doctor james,haifaffan qasar america,mutum da ya tashi da tsantsar aqidar yahudawa ta aihini,sannan ya ginu kan qiyayyar musulunci da musulmai,ko kadan baya qaunar musulmi a zuciyarsa,qwararren likitane na gyni wanda ya qware ya kuma shahara wajen saida sperm yin dashe d'a dana qwayayen haihuwa,shahararsa ta sanya mummu kashe kudade masu yawa domin su ganshi don samun biyan buqatarsu,da idanu yake kallonsu bayan ya gama jin abinda ya kawosu,uasan tabbas ba mai yiwuwa bane,haihuwa ga macen da babu mahaifa tattare da ita kwata kwata,saidai kuma tunda aka masa transfer na sunayensi cikin system dinshi ya tabbatar da musulmai ne,baya jin kuwa zai barsu su fita a office dinsa salin alin ba tare da ya zaluncesu ba,wanda wannan shine babban burinsa,agender dake gabanshi tsakaninsa da wani shahararren mai kudi dake garin nasu ya fado masa,hakan ya sanyashi sakin murmushi,ba shakka zuwansu yayi daidai,haka faduwa tazo dai dai da zama,murmushinsa ya jefa musu zaton cewa nasara ce qarara ya hango,sai ya karkace ya zuba musu bayanin cewa zata haihu kamar kowacce mace,zasuyi mata aikin da bazata farka ba sai da juna biyu,nan da kwanaki uku ta taho asibitin zasu soma aikin nasu,kudi kadan ya yanka musu ahakan ma ya karba ne kawai don kada ya darsa zargi cikin zuciyarsu saboda yasan cewa kudaden da zaya samu zasu mai dashi cikin jerin sahun masu kudin garin,zuciyarsu fes suka bar asibitin,tun a sannan su'ad din ta fara hasashen irin abubuwan da zata shuka bayan bayyanar ciki a jikinta,bata jin zata dagawa wani cikinsu qafa,kowa sai ta takashi dai dai da abinda yayi mata.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽

✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

1⃣0⃣6⃣

*KADA KI WUCE BAKI KARANTA BA*

*SHIMFIDA MAI MUHIMMANCI*

*bismillahir rahmanir rahim*

*Allah S W T yana fada cikin qur'aninsa mai girma*

*ku koma izuwa ubangijinku ku tsarkake aiki dominsa,tun kafin azaba tazo muku,sannan ba za'a taimakeku ba(da hana saukar azabar idan baku tuba ba*

*kubi kyakkyawan abinda aka saukar izuwa gareku daga ubangiji tun gabanin azaba bata zo muku bagatatan bakuyi hasashen zuwanta ba*

*tun kafin rai bata ce ba "ya asarata/tabewa ta bisa sakacim da nayi a janibin Allah,haqiqa na kasance cikin masu wasa*

*ko tace "da Allah ya shiryeni da na kasance daga cikin masu tsoron Allah*

*ko tace lokacin da taga azaba  " da ace ina da damar komawa izuwa duniya izuwa duniya dana kasance daga cikikin mash kyakkyawan aiki*
______________________________________

*WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NE GA MEELA ADEEL DA SAURAN DUKA MASOYAN SU'AD*
Chapter 218 · 0% Book details