Sashe 207
Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tunda aka jere abincin ya dinga binsu da kallo daya bayan daya,kallo daya ya musu yaji baki daya basuyi mishi ba,zuciyarshi ma sam ta kasa aminta cewa order tayi musu
"Wadan nan abincin fa daga ina?" Ya tambayeta yaba dubanta,murmushi tayi tana zaton ta burgeshi ne
"Kuku na taho mana da ita ta musamman,kuma mommy ce zata dinga biyanta" wani abu ne ya tsaya masa a wuya,baturiyar mai dafa abinci cikin gidanshi wadda baisan da zamanta ba?,babban abinda ya fara baqanta masa rai wai mommy ce zata biyata albashi,me suke nufi kenan?,ya gaza shi din,wani abu mai daci ya tsaya masa awuya,mutum ne shi da baisan raini,irin mazan nan ne da basa buqatar tsinke ki taimaka masa da shi cikin gidansa,Allah ya hore masa yafi qarfin duka buqatunshi,bai marmarin ko daga waje ayi ma iyalansa kyautar abin amfanin gida,yafiso komai suyi amfani da abinda ya fito daga aljihunsa,kallo yaci gaba da binta da shi wanda take jikinta yayi sanyi,ta rasa wanne irin kallo ne
"Ce miki akayi na gaza daukar nauyin kuku?,ke zaki bada labarin cewa babu irin kukun da bazan iya ajjiyewa cikin gidana ba ko daga ina yake daga fadin duniya,sai dai me?,banda ra'ayi,ke din ke nakeso ki shiga kitchen da kanki a matsayinki na matar aure ki dafa min" sai a sannan ta gane har yanzu yana kan bakansa,tun a can mummyn ta riga ta zigota kan kada ga yarda ya tauyeta tunda ba shi zai biyata ba,hakan ya sanya ta fara fadin maganganu,ransa ya baci ainun,ya sanya mata ido kawai,da yaga bata da niyyar saurarawa ya daka mata tsawa,wadda ta kada hantar sumayya dake cikin nata falon tana kallon film tare da shan fruit,tsoro ya kamata ra ture plate din gefe tana kiran sunayen Allah
"Na baki nan da minti goma ki tattarata ta bar gidan nan"
"Ba inda zata almustapha wallahi" ta bashi amsa daidai sanda kodaddiyar baturiyar ta fito,sanye da mini skert wanda idan tayi kyakkyawan tsuguno ba abinda zai hanaka ganin mazaunanta da t shirt mai gajeran hannu,wani baqinciki ya sake shaqeshi ya dakawa baturiyar tsawa cikin yaren da zatafu fahinta yake sanar mata ta wuce ta tattara duk abinda tazo da shi ta fice masa daga gida,tuni ta soma rarraba ido don bata taba zatar haka ba,idan ta fita din ma ina zata?,sai su'ad din ta rushe da kuka iya qarfinta ko hakan zaisa almustapha ya sauya qudurinsa,ihun kukan su'ad din shi ya daga hankalin sumayya,ta tsammaci ba lafiya,sabida haka ta yafa mayafi saman doguwar rigar dake jikinta ta fito zuwa babban falo,dai dai sanda mujadala ta harqe tsakaninsu,tuni yace ta hada kayanta itama ta bita,wanda hakan ya sage nata gwiwa,maimakon hana mai girki tafiya sai ta koma qoqarin yadda ita din zata zauna,kallo daya zaka yi masa kaga zallar bacin rai shimfide a fuskarsa,ita kanta sumayyan sai da tsoro ya kamata ganin yadda ya birkice,da addu'a a bakinta ta nufi inda yake zaune saman dining yana fuskantarsu,gefanshi ta tsaya cikin kwantar da murya
"Haba yallabai,haba.....bai kamata ba,ba fa cikin qasarmu muke ba,yanzu ta yaya don kawai ta maka laifi zaka ce tabi baquwar fuska subar gidanka?,kasan kuma yanzun qarfe nawa,a karamcinka ko mai aikin bai kamata kace ta fita ba,koba komai macace mai rauni,balle kuma matarka ta sunna....kayi haquri don Allah ka sawa zuciyarka ruwan sanyi,yanzu kaga baki daya fushinka ya hautsina gidan ummm,ina kake so musaka ranmu?" Shiru yayi yana sauke numfashi sannan ta juya ga su'ad
"Anty....tunda baiso kiyi qoqari gobe ki saya mata ticket ta koma a zauna lafiya don Allah" harara ta wurgawa sumayyan amma bata ce komai ba,saboda ko banza taji dadin ganin almustaphan yayi shiru,miqewa yayi ya dauki muqullin motarshu dake ajjiye kan freezer ya fice,dukkansu suka bishi da kallo,sai da ya gama fita kowacce ta dauke idonta,suka hada ido sumayya da su'ad,sumayyan tace
"Don Allah anty kiyi qoqari ki karanceshi ku daina musayar yawu haka da shi,gaban baquwa fa ba don Allah yasa bata jin yaren ba,haramunne mace ta dinga daga murya sama data mijinta,miji sama yake da kai dole ka saukar da kanka qasa ka bishi,tana janyowa kanta tsinuwar mala'ikun Allah" ta fada a tausashe
"Ke da Allah sauraramin,a naku tsarin ba,ba wanda yafi wani tsakanin mata da miji kowa mai 'yancin yin yadda yaga dama ne,wai wa ya saka da ke ma?" Kada kai tayi babu alamun jin haushu a fuskarta
"Allah ya baki haquri idan kinji haushi"ta juya a nutse ta shige falonta ta zauna taci gaba da binda take,saidai lokaci lokaci hankalinta na kan agogo,har ta soma gajiya da zaman ta buqaci kwanciya bata ji motsin shigowar almustaphan ba,har dare ya soma shiga sha daya da kusan rabi,duk da su a can daren ba komai bane wajensu,hakan ya daga hankalinta,ta dauki wayarta ta dinga qoqarin nemansa saidai sam bata samunshi,sai data gwada a qalla wajen sau biyar ana shida ta dace ya shiga,a jiyar zuciya ta sauke
"haba yallabai,ka tashi hankalinmu fa" shima ajiuar zuciya ya sauke,muryarta ta soma rage masa bacin ranshi
"Me ya faru?"
"Ka fita cikin iyalanka cikin fushi,sannan kuma har war haka ace baka dawo ba ai dole hankalinmu ya tashi ko?"
"Lafiya nake,kawai yau bazan kwama gidan bane,sai gobe idan Allah ya kaimu,ki kwanta kiyi bacci sosai,good night" ya katse wayar yana jin dadin yadda ra kula da shi har ta nemeshi,ya tabbatar idan su'ad ce kota nemeshi qorafi ne abu na farko da zata fara ba tare da kwantar da murya ba,ranan haka ya kwana sai da safe sannan ya dawo cikin gidan,to sai gashi yanzu tana tsaka da bacci ta soma jiyo muryansu,wanda hakan ya sanyata farkawa ba shiri,uwa uba da kuma yunwa data fara tambayarta,har ta shiga toilet rayi brush ta fito tana jiyosu,ga yunwa tana sadakarta,bata so ta fita ta taddasu haka,amma dole ta sanya hijabinta ta fice sanoda yadda cikinta ya soma motsawa saboda yunwa.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
1⃣0⃣2⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*
*ya zul jabarutu wal malakutu wal kibriya'i wal'azmati*
_____________________________________
Tunda ta fito ta fuskanci maganar dai kusan kan shiga kitchen ne,ita kanta ta gaji da wannan jeka ka dawo magana daya tak mai sauqi amma ta rasa dalilin su'ad na qin yarda da maganar tashi,har zata rabe ta wuce sai kuma ta fasa sakamakon tuna fadar Allah da tayi
"Haqiqa muminai 'yan uwa ne kuyi sulhu tsakanin 'yan uwanku", a nutse ta qarasa wajen da suke tsaye,ta sanya hannunta ta riqe hannun almustapha ta gefe ta yadda su'ad din na zata gani ba ta soma matsawa a hankali idanunta cikin nashi,cikin 'yan kwanakin nan su'ad tasa ta ga halinshi da bata taba gani ba,ta fuskanci yana da fushi saidai yakan jima ba'a ga fushinsa ba,barshi dai da miskilanci wannan tambarinshi ne,sai data fuskanci hankalinshi ya soma dawowa gareta yayin da su'ad rayi carko atsaye tana jiran kota kwana
"maan" karon farko ta kirashi da sunan da mutane ke yawan kiranshi,saidai yaji sunan ya zama wani sabi na musamman daga bakinta,a tausashe hadi da karyar da wuya tace
"Bai kamata ba....." Dakatar da ita yayi da hanzari ra hanyar daga mata hannu sannan ya waiwaya ya dubi su'ad
"Option ne na baki,na kuna rantse yau ko zaki kwanta asibiti sai kin dafa tea din nan,naga wanda zaya sake min order din abinci cikin gida na" yana fadin haka ya zame hannunshi daga nata ya wuce zuwa sashensa,da kallo suka bishi,yayin da gaban su'ad ke faduwa,ta tabbatar da cewa yau din matuqar bata yi abinda yace ba babu abinda bazqi iya faruwa ba,saidai ta yaya zata ta ina zata soma tunkarar kitchen?,sai kawai ta wuce fuuu kaman guguwa ta shige kitchen dinta,sam abun baiwa sumayya dadi ba,hakan ya sanya batayi qasa a gwiwa ba ta bishi zuwa dakinsa.
Yana tsaye gaban window,hannayenshi zube cikin aljihun wandonshi,qoqari yake yayi controlling kansa tare da hana zuciyarsa aikata abinda take raya masa,so yake yaga ta ina ya gazawa su'ad,ci?,sha?,sutura?,kudin kashewa?,walwala ko adalci,duka babu,babu ko daya daga ciki,hasalima ta wani bangaren tafi sumayyan samun wasu abubuwa,tunda suka fara tarayya da sumayya bazai iya tuna rana qwaya daya tak da ta tambayeshi wani abu ba,saidai shi don gashin kansa ya bata,ko idan su'ad din ta tambaya yayi adalci itama ya bata duk da bata tambaya ba,abinda ya lura ma shine tara su take,ba abinda take da su,shi kansa yasan babu wani anu qwaya daya da na kusa da shi bama iyalinshi ba da zasuyi kukan basu da shi ko yafi qarfinsu,shi a ganinsa babban abun kunya ne ma ace kai din wani je,ko Allah ya maka rufin asiri,ana maka kallon mai rufim asiri,a ganka cikin kama kai kyau amma iyalinka a wahale ko cikin mummunar kama,wannan shine babban abin kunyar da magidanci zai aikata wanda zai jawo masa tur da ala wadai a bakunan al'umma.