Sashe 202
Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana tsaka da duba number ma'aikacin kamfanin jirgin fly emirate dake yankar masa ticket su'ad ta sauko,cikin taku dai dai kai tsaye ta haye dining,ta soma jawo kayan break din tana duba abinda ma'aikaciyar ta dafa ba tare data lura da sauyawar yanayin almustapha ba,tsaki taja don ita duka abincin bai mata ba,choice din almustapha ne,kenan bata mata nata ba,baki ta bude ta shiga qwala mata kira,saidai har tayi ya gama shiru maqatau ba dalilinta,sai ta miqe da niyyar shiga kitchen nemanta tana zazzaga masifa,banza yayi da ita har taje ta gama bulayinta ta dawi,zuwa sannan ya gama waya da su,saidai dole yayi haquri yabi jirgin gobe da safe shine zai sauka dubai to abuja direct,hakan bai masa ba amma tilas ya karba haka,miqewa yayi ba tare da ya damu da qarasa karyawar ba,sai daya sauka daga step din sannan yace mata
"Na riga dana sallameta,tunda ba tare na auroku ba"
"Wata zaka sauya mana?" Ta tambayeshi ba tare data fuskanci me yake nufi ba
"Ki shirya fara girki da kanki karon farko tunda kika zama matar aure" ya bata amsa yana ficewa,zumbur ta miqe ta sauko da hanzari tabiyo bayanshi tana cewa
"Haba man,ya zamuyi haka da kai?,kaima kasan abinda bazai taba yiwuwa bane"
"Saiki maidashi mai yiwuwar" ya bude motar da kanshi duk da qoqarinbda drivern keyi wajen bude masa motar ya shige abinshi tare da bawa drivern umarnin ya shiga su tafi,binsa tayi da kallo baki daya tunaninta ya koma ga kitchen,gata can gaban tukwane tana fama da gas,kai ta girgiza wlh abinda bata taba yi ba ba zara fara ba yanzu,cikin fushi ta koma ciki kai tsaye ta shiga daki ta dauko wayarta,lambar hajiya khaulat ta soma nema wanda cikin sakanni ta daga,sai ta fashe mata da kuka,daga daya bangaren ta soma fadin
"Yaya?,lafiya?,waye ya taban ke?"
"Mommy man ne,wai kinji ya kori kuka na wai na fara girki da kaina daga yau,don kawai ya siya min foam na catering school nace bana iyawa,kuma na gaya masa ya gayan nawa ya kashe na buyashi,yanzu don Allah mommy nayi kama da wadda zata shiga kitchen zafi da tururi na qonata?" Wani shegen tsaki haj khaulat ta ja
"Shegen yaro tsagera,sai shegen zafin kai da taurin zuciya,to bai isa ba wlh,bamu aura masa ke don ki dafa masa abinci yaci ba,idan ma iya daukan nauyin mai girkin ne bai iyawa ko kuma girkin ne bata iya ba,nan kusa da mu akwai qwararrun masu girki professional zan aiko muku da daya,a aljihuna zan dinga biyanta,cikakkiyar baturiya ce ba abinda bata iya dafawa ba" murmushi su'ad ta saki tare da ihu
"Shi yasa nake sonki mamana wallahi"
"Uhmmm" tace
"Ni wlh wannan yaro ba don abinda ya mallaka ba da tunu na rabaku,qabli da ba'adi iri daban daban,yau wannan tsurfar gobe wancan?,duk ya maidaki wata mara 'yanci"
"Kai mummy kada ki kwafsa mana haba da Allah,ke matsalarki kuma kenan auren mutu ka raba mukayi,kawai ki turotan ni zan biya kudin visa da ticket cikin satin nan keso tazo"
"To shikenan babu damuwa"da haka sukayi sallama su'ad na aje wayar k babu damuwa a ranta ko kadan,saima ta hura saman dining din ta soma karyawa tana tunanin inda zata musu order abincim dare kafin ya dawo.
To fans alhamdulillahi rabbil Aalamin,yau zamu tsaya anam sai kuma bayan zabe idan Allah ya kaimu,amma wannan karon zamu iya kaiwa lahadi bamu dawo ba,idan kuma ya samu lahadin to amma banyi alqawari ba kada na kasa cika muku.
Ina kira ga dukkan wani dan qasa da ya tsaya ya fidda son zuciya ya zabi shugaba na qwarai,wanda ko gaban Allah ya riqi kyawawan hujjojin da zai bawa ubangijinsa kan zaben mutumin da yayi,dukkanmu muna da hankali muna ga da tunani munsan abinda ya dace.
Ya Allah muna roqonka da kyawawan sunayenka da siffofinka wadanda muka sani da wadanda bamu sani ba,ka zaba mana shuwagabanni na gari,wadanda suke qaunarka suke qaunar fiyayyen halitta suke tausayin bayinka har cikin zukatansu,suje tsoronka da tsoron gamuwarsu da kai,wadanda suka tsaya bada wata manufa ba sai ta taimakon Al'umma,ya Allah duk wanda ya tsaya da wata manufa Allah ka karya mana shi koshi waye,Allah ka nuna isarka ka tallafi raunanan bayinka.
Ya Allah duk wanda zai kasance alkhairi a rayuwarmu data addininmu Allah ka damqa masa ragamarmu ko muna so ko bama so,Allah ka zama jinmu ganinmu dama furucinmu,Allah kayi maja jagoranci alfarmar shugaba annabi muhammad S A W
'Yan uwa da garuruwansu ake fama da rikici Allah ka tsayar da wannan tashin hankali,ka zaba musu shugaban da zai zama farincikin zukatansu,sanyin idaniyarsu alfarmar shugaba S A W.
Mu guji saida quri'armu domin kuwa QURI'ARKA ITA CE 'YANCINKA,duk dan adam din da bai da manufa akwai babban gyara cikin rayuwarshi.
Daga qarshe ina son jan hankalinmu da cewa AKWAI RAYUWA FA BAYAN ZABE kada muci mutuncin juna aibata juna ko bata ran juna sabida wanda mukeso yaci wanda baya so shi ya fadi,basu suka hadamu ba bai kamata su raba mu ba,alkhairi muke nema da kyakkyawan shugabanci,Allah kayi mana zabi mafi alkhairi ka kyautata qarshenmu.
WANNAN KIRA NE BAGA AL'UMMAR GARI NA KAWAI BA,KIRA NE GA DUKKAN WANI DAN QASATA NIGERIA,ALLAH YA TALLAFI QASARMU.
Subhanakallahumma wabi hamdika,ashhadu an la'ilaha illa anta,astagfiruka wa atubu ilaika.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
1⃣0⃣0⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*
*subhanallahi wa bi hamdih,subhanallahil azim*
______________________________________
Har yaje ya dawo abun na damunsa cikin rai,ko cikin company ranan kowa yasan lallai an tabo oga,duk wanda ya kuskure sai ya sha fada idan ma baice ya bawa mutum hutun satittika ba,har ya dawo din bai sake kiran sumayya ba ko wani cikin gidan.
Bayan sallar isha'i bayan yayi wanka,sanye yake da vest da boxer yana zaune saman dining,fitowa tayi daga kitchen dauke da ledoji niqi niqi a hannunta ta zauna saman dining ta soma fiddo da dinner din data musu order,idanu ya zuba mata yana kallonta,yasan za'a rina,lallai raina shi su'ad tayi,bata ji me ya gaya mata kafin ya fita ba kenan
"Wannan fa?" Ya fada yana nuna abincin da idanunshi
"Abinci ne na mana order"
"Shi nace miki zanci?,da na order nake so kinsan dai na fiki iyata ko?,wanda kika dafa cikin gidan nan nakeso" kai ya lanqwasar tana dubanshi
"Amma dai kai zaka bawa wani labarin ban taba dafa wani abu ba ko?"kafada ya daga in idont care manner
"Wannan ke ta shafa,tunda na baki dama ki koya,so wataqil dama can kin iya ko shi yasa kika wulaqanta foam din kanshi da na saka kudade masu yawa na siya miki"
"Iyawa ne gsky bazan yi ba,tunda nasan kana da arziqin da zaka iya dauka min kuku ko nawa nake da buqata"
"Ba kuku bane matsalata,abincin mata ta nake so naci,ke ba zakiyi min abinda nake so ba saidai ke nabi ra'ayinki.....to ba zaiyiwu ba,ni ba sakaran namiji bane,dole ki sauya,dole ki koma kan tsarin da nakeso tunda na fahimci ke bakisan lallashi ba" a fusace yake maganar,yana kaiwa nan ya miqe a zafafe ya shige dakinshi,binsa tayi da kallo har ya wuce,ta dauke idonta tana tabe bakinta,kome zayayi ba zata lamunci yin wami girki ba kamar 'yar aiki,jawo tata ledar tayi ta bude ta soma cin abincinta hankalinta kwance,
A daren da kanshi ya soma hada kayanshi cikin wata qaramar jaka mai kyau ta matafiya,ba wani kaya zai diba can ba saboda ko ina yana da kayan amfaninsa komai da komai,su'ad na nade saman gado tana kallon wani horror film,jakar da ya fita da ita ya janyo ya bude ya ciro ticket ya ajjiye gefan su'ad
"Ki shirya gobe da azahar zamu wuce nigeria" da hanzari ta dago ta dubeshi,sam bata taba zaton haka ba,itafa bataqi su dauna zuwa ba ma baki daya tunda ta daukoshi wa ta ajjiye can da zata damu sai taje
"Me zamu je yi a can din?,naga duka bamu yi cikakken wata biyu kai daya da rabi ma da dawowa ba....nikam gaskiya da ka sani na america ka siya min,tunda ina da sauran visa ta bata qare ba naje na qarasheta"
"Sai kin dawo" ya bata amsa cikin halin ko in kula,farinciki ne ya kamata
"To zaka siya min din?" Waiwayowa yayi yana dubanta
"Kudin da na miki transfer accnt dinki jiya....duka ina kika kaisu?" Fuska ta bata,ya iya saninta tunda suke da shi babu lissafi tsakaninsu,bai taba mata irin haka ba,ko yau ta nemi kudi gobe ta nema zai maya transfer ba tare da ya damu da me zata yi da su ba
"Na kashesu" shuru ya mata bai sake bi ta kanta ba yaci gaba da abinda yake,yayin da ya barta cikin qila wa qalan zai biya ne koko a'ah?.
Qarfe sha biyu na rana ta fito daga luctures,takowa take cikin yauqi da isa inda zata jira drivan ya dawo daukarta,har yau bata da walwala,ranta a bace yake,ta qullaci sumayya qwarai,ba ita kadai ba hatta da ummin ta sanya bigiren da zata sanyata,gani take ma duka ummin ce ta hana ruwa gudu,banda haka tana da tabbacin matuqar ta yiwa almustapha izinin aureta ko musawa bazaiyi ba tilas ya amince,sanda tazo mata da kukanta haquri ta bata,tana nuna mata almustaphan bai jima da yin aure ba bazaiyiwu ace ya sake wani nan kusa ba,kawai taci gaba da addu'a idan rabonshi ce ita dole zasuyi aure,sai yanzu take shinshinar cewa sonta ne kawai bata yi ta fake da haka.