Sashe 58
Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sati na zagayowa aka maida auren sumayya da mukhtar karo na biyu ranar jum'a bayan an sauko daga masallaci,a ranar mukhtar ya matsanta mata sai ta sanya ranar tariya,sati biyu tace ya tuburr mata kan ya masa yawa,tilas ta haqura ta maida shi sati dayan,don dama tana jiran aiken da anty dije tace zata yi mata nan da kwana goma.
******* ******** *******
Juma'a asabar lahadi litinin kwana hudu da mai da auren ran litinin mukhtar yace ta shirya da daddare zata masa rakiya zai yi siyayyar kayan da yake son sauyawa cikin gidan,mama ta sanar,Allah ya tsare sai kun dawo abinda maman tace kenan.
Tana idar da sallar magariba ta soma shiryawa,kwalliya tayi wadda rabonta da yin kwalliya irinta har ta manta,tsaf ta shirya cikin material na one million stone peach ne da adon mint green,fitted gown aka mata da shi,ya masifar yi mata kyau,zainab ke dubanta tana cewa
"Kai yaya sumayya,sai kace zaki dinner,ai kya bari sai nan da kwana hudu wannan kwalliyar,karfa ki sanya ya mukhtar yaqi maidoki" daquwa sumayya tayi mata tana cewa
"Ni sa'arki ce,naga alama kin soma rainani" dariya ta sanya
"Yi haquri yayanmu,amma dai ba hijabi zaki sanya ba ko?,naga kina da mayafi kalar kayan"
"Kyaji da shi" sumayyan ta fada tana feshe jikinta da turaruka,ita kanta tasan cewa tayi kyau,sai da tazo fitowa sai taji kunyar wuce mama a haka,da qyar ta fice kanta na sunkuye mama bayan ta barwa zainab abdallah wanda yau yayi baccin wuri.
Baki kawai mukhtar ya saki yana kallonta har sai data hure masa idanu,dariya sukayi baki daya
"Ki amince kawai yau mu wuce gida my sumy"kicin kicin tayi
" amma dai unguwa kawai kace zan raka ko?"murmushi ya saki
"Afuwa ranki shi dade,na tuna,muje" suna tafe yana tuqi amma baki daya ya wani narke mata bini bini ya kalleta har suka isa gun ya kashe motar ya zuba mata ido ba tare da ya fita ba
"Sumayya,ina jin wata sabuwar qauna taki na dasuwa cikim zuciya ta,da ace a yanzu ne wani ya aureki mutuwa zanyi wallahi,ina sonki sumayya ina fata mu kasance tare har ABADAN" murmushi ta saki tana kada kai
"Nima ina fatan haka ya mukhtar"
Sai da ya sumbaci goshinta sannan ya bude motar suka fita.
Kayayyakin amfanin gida suka siya sosai,harda kayan kitchen sai da ya siya wasu abubuwa daga ciki,motarsa ta cinye kayan a ciki aka zuba masa sannan suka fito,sake tsayawa yayi a wani gu da saida kayab qwalam da maqulashe ya sayi kaji biyu gasassu da ice cream,sai damammiyar fura ya dawo ya tada motar yana dubanta,hira suke qasa qasa duk ya wani sukurkuce,wani kallo yake jifanta da shi,sai taga ya dauke kan motar ya sauya hanya,shuru tayi ta kasa tambayarsa hakanan sai ta biye masa har suka isa qofar gidansu,gidanta ne a da wanda a yanzu ma ya sake zama mallakinta
"Bismillah muje ciki ko?"
"Ya mukhtar na bar abdallah a gida fa"
"Babu komai,minti talatin kawai ina son ganinki ne sumayya" nan ma bata ce komai ba ta fita suka shiga gidan,tayi mamakim ganin komai a tsaftace a killace,bai tsaya ko ina ba sai dakin gadonsa,ya dubeta sanda yake cirw hularsa tare da tattare hannun rigarsa
"Nasan bakiyi sallar isha'i ba ki daura alwala muyi sallah sai mu wuce ko?" Cikin shagwaba tace masa
"Wai nikam bansan gaggawar me kake ba ya mukhtar,saura kwana hudu fa na dawo gidan baki daya" murmushi kawai yayi bai amsa mata ba ya shiga bandakin.
Bayan sun idar ya matso inda take,hannunsa ya sanya cikin nashi yana kallon qwayar idonta
"Sumayya,Allah ne kadai yasan yadda nake jin sonki a zuciyata" murmushi tayi tana girgiza kai."ya mukhtar,sai kace yau kasan sumayya,sai sake jaddada qaunarta kake bayan ta riga da tasan hakan"murmushin shima yayi
"Hakane fa ko sumayya,amma wannan karon wata qauna ta daban nakeji,sumayya,ina so ki kasance tare da ni har qarshen rayuwata"
"Na maka wannan alqawarin"
"Na gode"
Sai kuma shiru ya biyo baya har ya qosa taji me zai sake cewa,sai daga bisani yace
"Sumayya,zaki yimin alfarma na kasance tare da ke cikin wannan daren?"idanu ta daj fiddo
"Ya mukhtar,kwana hudu fa ya rage"
"Na sani sumayya,amma so nake kimim wannan alfarmar indai ban keta iyakar ubangiji ba"
"Na maka ya mukhtar" ta fada kanta tsaye
"Allah yayi miki albarka" ya fada yana janyota ta fada jikinsa kowannansu cuke da kewar dan uwansa,kada ma mukhtar yaji labari,ji yake kamar an masa bushara da aljanna.
Qarfe goma saura na dare ta fito daga bandaki,mukhtar tuni ya kammala shiryawa yana zaune yana jiran fitowarta,binta ya dinga yi da kallo,ji yake tamkar ya hadiyeta ya maidata ciki,har yanzu baiwar nan da ya santa da ita na tattare da ita,ganin ta kammala ta yafa mayafi tana saba jaka ya sashi saurin cewa
"A'ah,amarya guda bai kamata ace bata ci komai ba" sai ta saki murmushi cikin jin kunya
"Ya mukhtar yau ka manta da abdallahnmu?,munfa barshi a gida"miqewa yayi da sauri yana fadin
"Kai kai hakane fa,jikina ya bani ma fa ya farka" dariya ta saki
"Uhmmm,sannu masu 'ya'ya"
"Wallahi kuwa,d'a ba wasa bane" ya fada yana kama hannunta suka fice.
Ihu take so ta kwarara ko zataji sanyi a ranta amma zinatu ta hanata don kada ta tara musu mutane,wadda ita ta kawo mata labarin komawar auren sumayya da mukhtar,maimakon haka saita maida dubanta ga zinatu cikin daga murya
"Wallahi wallahi sai na aikata abinda na qudurta babu mai hanani aikatashi wallahi,mukhtar nawa ne,nawa ne ni kadai,bazan juri ganinsa da wata ba ba ni ba" ta fada kamar zararriya tana mai ficewa daga layin cikin qunar zuciya kamar zatayi aman zuciyar tata.
Ko da ya sauke ta ma sai da ya sake tsareta,kamar bazaya tafi ba har sai dayaga giftawar malam da alama ya shigo gida kenan sai da safe sannan sukayi sallama bayan ya cikata da kalamai masu tsayawa a zuciyar wanda ake so.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
4⃣8⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*
*kullu nafsin za'iqatul maut,summa ilaina turja'un*
*_DUKKAN RAI SAI TA DANDANI MUTUWA,SANNAN IZUWA GAREMU ZAKU KOMO_*
_________________________________
Tana shirin kwanciya wayarta ta dauki ruri,mukhtar ne sai ta kumahe idanu tana murmushi
"Na kasa bacci my sumy,ganinki nake kusa da ni".'yar qaramar dariya ya tasa tana fadin
" baban zumudi ka zama ya mukhtar ne?"shiru ya danyi sannan ya saki ajiyar zuciya
"Bakisan me nake ji ba game da ke sumayya". Hira suka kashe lokaci suna yi,a nan yake gaya mata ran rakota tare da yaya yahanasu za'a zo,har mamaki take idan taji yadda yaya yahasun ta sauya take nuna mata qauna,basu suka rabu ba sai daya na dare,ta dubi agogo tana zaro ido ganin lokacin da suka shafe tare,sai ta fita ta daura alwala tayi sallah raka'a biyu sannan ta kwanta.
****** ******** *******
Shirye shiryen tariya sun kankama sosai,tayi gyaran jiki hadi da qunshi da kitso,kayanta baki daya ta kammalesu.
Ranar alhamis ana ya gobe zata koma,da azahar suna falo ita da halima da zainab suna hira ita kuma tana gugar ragowar kayan abdallah da bata gama shiryawa ba,sai anty salma qanwar mama wadda anam zata kwana,wayarta dake daki ta soma burari,abdallah ne ya miqe da gudunsa ya dauko ya miqa mata,anty salma ta talle masa qeya tana cewa
" kaji dan jakar uba wai yasan kayan uwarsa,sai kace wani yace zai dauki wayar ne"dariya sukayi dukansu halima tace
"Indai Abdallah ne kadan kika gani anty" ita kuwa sumayya miqewa tayi ganin lambar mukhtar ce ta fita ta koma dakinta
"Lafiya abban abdallah naji muryarka can qasa?"murmushi ya saki sannan yace
" lafiya qalau,a yanzu ma ina gida kwance ina hutawa,babu abinda nayi amma wata gajiya nakeji sosai a jikina,kewarki nake sumayya goben nan kamar ba zata zo ba"tamkar yasan abinda take ji jikinta itama kenam,sai ta saki ajiyar zuciya tana masa murmushi
"Au dariya ma kike min?,naji na gode,amma da zaki taimaka min da kinzo na ganki kinji my sumy" sai ta kasa musa masa,dama suna da agender fita karbo dinkunan sumayya gidan wata mata bayan sallar la'asar ita da anty salma
"Babu damuwa ya mukhtar,amma sai bayan la'asar"cikin zumudi yace
"Da gaske sumayya ta?,kada fa ki shirgani"dariya ta qyalqyale masa da ita
" da gaske nake mana abban abdallah,ka jirayeni,amma fa gobe ba za'a rakoni da wuri ba tunda yau ka sake gani na"
"Babu komai,ai goben ta Allah ce,Allah yayi miki albarka sumayya ta" tana jin dadi ya sanya mata albarka don haka da sauri ta amsa da amin.
A gidan mai dinki ta bar anty salma tace zata je ta dawo,ta riga da tasan inda zata din saboda haka tayi tayi abdallah ya zauna qememe yaqi har da kukansa ammi zai bi tace madallah yayi ta binta din sai sun dawo.
A qofar gidan mai adaidaita sahu ya sauketa,ji tayi ana malam ga kudinka,tana waiwayowa sai taga mukhtar ne,cikin mamaki take tambayarsa
"Ya akayi kasan na qaraso"
"Jikina ne ya bani" ya bata amsa yana amsar abdallah daga hannunta yana masa cakulkuli suna qyalqyala dariya tana biye da su har zuwa falon gidan,kallon gidan take ya sauya komai kamar wanda zai kawo budurwa,komai fes gwanin sha'awa,zubewa sukayi kan kujera mukhtar na biyewa abdallah suna ta wasanninsu yayin da sumayyan ke zaune gefe guda
"Wai nikam 'yar kallo kuka maidani ne,nazo amma ba'a tani,bayan nemana akayi" ta fada tana murguda baki,dariya mukhtar din ya saki yana duban abdallah."lah,abdallah kaga mamanka na kishi da kai"sai ya kada kai kawai yaron don bai fahimci me yace ba,juyawa yayi gunta
"Dama taimaka mana kika yi kika dafa mana wani abun madam"
"Kamar me?" Ta tambayeshi
"Abinci mai sauqi da dadi"
"An gama" ta fada tana miqewa
"Ammm,madam,amma da kin taimaka kin cire wannan hijabin tunda gaban mijinki kike ko?" Dariya ma ya bata yadda yayi maganar a dake,bata ce komai ba ta cire din,sai ta miqawa abdallah hannu
"Muje kayi fitsari sai ka dawo ko?" Lafewa yayi jikin mukhtar din qememe yaqi yarda da ita
"Barmin yaro na ana dole ne,yayi fitsarinsa babu komai cinyar babanshi ce".don haka ta juya zuwa kitchen ta barsu nan.