← Book details Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 226

Sashe 70

Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tuni aka sanya kayanta a mota saidai ta tsaya sallama da mama,hawaye ne ya balle mata sanda suke sallaman,dariya maman tayi
"Saikace wadda aka ce idan ta tafi ba zata dawo ba,jeki don Allah sunata jiranki kada ku bata lokaci a hanya" halima da zainab ne suka rakota har bakin motar,tana shirin shiga halima tace
"Yaya sumayya,me za'a cewa yaya abdur rahman idan yazo,baki sanar masa ba fa,sannan baki bar saqo ba"
"Ki fada masa duk abinda kika ga ya dace" dariya sukayi don sun fuskanci gatse take musu,tana shiga yaran suka fara raba gardama,kowa na fadin kusa da shi zata zauna,motar akwai yalwa,sit uku ne da ita harda gun mai tuqi na hudu,hakan ya sanya ta tattara ta koma sit din cab qarshe ita da laila da minal,khalifa da hafiz na sit na biyu,anty dije ita kadai na sit na uku wanda ke kusa da driver tana rubuce rubucenta da lissafi na siye siyen da tayi don ta taba kudinta sosai har ta so shiga kudin abban lailah shi yasa tace su barta tayi lissafi,saidai duk da ita daya ce a sit dinta hayaniyarsu bata barta tayi aikin da take so ba,sun cika motar da karadi sumayya na biye musu,duk da zuciyarta babu dadi amma haka ta dinga biye musu har suka hau kwalta sosai,minal ita ta fara bacci sannan hafiz da yake bashi da son hayaniya sosai,khalipha shima yabi sahu sai laila ta dinda dariya tana cewa
"Yauwa kwa qyalemu ni da anty sumayya ta muyi hirarmu",su biyu suka dinga hirarsu tafiyar tasu naci gaba da gangawarawa,kafin a kai zaria sai ya zamto motar babu kowa sai sumayya da anty dije wadda sai lokacin ta samu sukunin yin aikinta.

Suna shiga kaduna suka farka baki dayansu,nan anty dije ta sanya salihu direban nasu ya wuce da su wani gidan cin abinci (restaurant)da sukan tsaya suci abinci duk sanda zasu taho kano ko zasu koma abuja,cikin mintina qalilan suka isa da yake kamar kan hanya yake,sai da suka fara shiga masallacin dake daura da wajen suka bada farali sannan duk suka fito sumayya na dauke da minal take ta saje da 'yan garin,tun a hanya ta dinga qarewa yanayin garin kallo,akwai yawaitar mata masu dogon hijabi da niqab kamar nata,sai kuma qabilu data lura suna da wani kaso na musamman cikin garin,baka tafiya daya biyu baka gansu ba cikin irin nasu shigan,hakan ya sanya ta yiwa garin hasashen gari mai tarin mabanbantan qabilu da yare.

Table biyu suka kama kowanne nada kujeru uku uku,daya sumayya laila da minal,sau dayan kuma anty dije hafiz da khalipha,salihu kuma na can wajen wani tsohon abokinsa ya karbi nashi abincin yana ci suna hira.

Kowa cin abincinsa yake cikin kwanciyar hankali,saidai sam ita ta kasa cin nata,hasalima jinta take a takure tamkar ita kowa yake kallo saboda bata taba zama gu irin wannan taci abinci haka cikin guri dake cakude da maza da mata ba,ko da can ita mai kunya ce rashin sabo da rashin saurin sakin jiki,don haka minal kawai take ta bawa abincin idanuwanta na kan minal din duk motsin da take,don a tsarge take.

tunda ta shigo gun ya zuba mata na mujiya,sau biyu suna hada idanu yana jifanta da murmushi,hakan ya sanya ta saka hannunta ta maida niqabin fuskarta,duka anty dije na ankare da yadda take a takure,saidai bata san dalilinta na sakin niqab din ba,ta dai dauka rashin sabo ne na shiga irin wadan nan wuraren,laila ce ta dubeta tana dariya
"Wai anty sumayya anan din ma sai kin rufe fuskarki,wurin cin abinci ne fa kowa abinci yake ci,duba ki gani" ta fada tana waiwayawa tare da yi mata nuni da ido,sai itama lailan idanuwanta ya kai kansa,matashine wanda zaiyi shekara talatin da biyu,fari ne sosai,yana sanye da shadda ruwan madara dinkin yarbawa,kansa babu hula,kallo daya zaka masa kasan cewa hutu ya ratsa jikinsa,su uku ne saman teburinsu shi da wasu matasan da aqalla zasuyi shekaru daya,biyun cin abincinsu suke suna duba wayar da take hannun na kuaa da shi,sam basu ma lura da yanayin da dan uwansu ke ciki ba
"Anty sumayya,kinga wani sai kallonki yake ya sanki ne?" Laila ta fada cikin sigar gulma murya qasa qasa taba ranqwafowa kan teburin
"Ku da kuke wucewa ta gun baki sanshi ba sai ni da yau na fara zuwa" sumayya ta fadi tana gogewa minal baki da tissue bayan ta gama bata abincin
"Ku taso mu wuce ko?" Anty dije tace tana daukar minal don ta ragewa sumayya tayi gaba suka bita a baya,da kanta taje wajen biya da yake har sun saba da su sosai,tasa aka hado takeaway saboda sumayya don ta lura bata ci komai ba ta amsa sannan suka wuce.

Suna shiga motar laila tace
"Lah,wallahi anty sumayya kinga har ya biyo mu ya koma,ta fada tana qyalqyala dariya"
"Waye ya biyo mu" anty dije ta tambaya tana qoqarin maida atm dinta jaka
"Ba kowa" sumayya ta fada da sauri sannan ta juya tana kallon laila,harararta tayi sannan tace
"Bana son surutu komai kika gani kiyi magana kai,idan ba haka ba bazamu shirya ba"
"Sorry anty sumayya" ta fada tana narke fuska don ta cikawa su hafiz baki ita ce ta gaban goshin anty sumayya bata son su gansu a rana
"Shikenan" ta fada tana gyara zamanta,sai da suka sake daukar hanya sosai sannan ta lalubi wayarta da niyyar kiran yaya yahanasu,sai taci karo da misscall din abdur rahman,sai kuma saqon SMS
_garin masoyi baya nisa,ina miki fatan alkhairi_ abinda kawai ya rubuta kenan,bata fahimci zaurencen nasa ba saboda haka ta share ta lalubi lambar yaya yahanasun ta danna kira,ringing biyu ta daga,cikin mutunci suka gaisa sannan aka nemo mata abdallah aka hadata da shi,hira ya dinga mata wani shirme wani abun dariya haka ta dunga dariya,daga bisani su laila suka amshe wayar suka yita shirmensu su da shi sai da suka cinye nata credit dinta tatas sannan suka haqura,bayanta ta maida makarin kujerar ta lumshe idanuwa zuciyarta fes tana jin dadi da jin muryar abdallah da tayi,tabbas d'a ba wasa bane,ababe ne masu wanke zukatan mahaifansu koda da shirme da quruciyarsu kadai,tunanin mukhtar shi ya ratso cikin farincikinta ya gusar da shi cikin yab sakanni qalilan,taje fuskarta ta sauya,damuwa ta lullube zuciyarta,taso abdallah ya rayu da mahaifinsa,yaci gaba da cin gajiyar gata da mahaifinsa ya tanadarwa rayuwarsa saidai ina,tsarin ubangiji shine daidai,tana jin hayaniyar su laila amma tayi fakare kamar mai bacci,bata sake bude idanuwanta ba har suka shiga garin abuja.

Qarfe biyar da rabi suka isa garin,bata mance yadda unguwar tasu take ba saidai an sake samun sauye sauye,sabbin gine gine da kuma sabunta tsoffin.

A falo suka zube baki dayansu wanda basu tashi ba sai da lokacin sallar magariba yayi sannan kowa ya debi kayansa zuwa daki,a dakin laila da minal ta zabi zama,kasancewar gado uku ne a dakin,daki ne madaidaici wanda ke shimfide da tiles da labulaye sai fenti dukkansu kala daya,wardrobe ce irin ta jikin bango wadda ta cinye bango guda,sai madubi a wani bangon daban,daya bangaren kuma gun ajitar takalma ne zuwa su jakankunan makarantarsu,daura da nan kuma qofar bandaki ne,sallah ta sanyasu suka fara yi sannan suka bude kayansu suka koma maidasu muhallinsu,a wanke a goge suke dawo da kayansu kamar yadda suka tafi da su.

Anty dije ce ta turo qofar dakin ta shigo,wannan karon ta sauya kayan jikinta da alamu ma wanka tayi don sai qamshi take zubawa ta dubesu tana zama gefan daya cikin gadajen dakin
"Sannunku da himma,hala ma ko wanka ba wanda yayi a cikinku ko?"
"Ummi sai mun gama gyaran kaya"inji laila
"eh kam bakwajin yunwa ne" anty dije ta sake fada,murmushi sumayya tayi din itakam ba yunwa tattare da ita,miqewa anty dije tayi
"Idan kun gama ga takeaway can da abban laila ya shigo da shi sai ku dauka kuci,nikam ina ga sai da safe zamu sake haduwa da ku"
Minal ce ta miqe da sauri
"Ummi zani gun abba"
"A'ah,ya shiga daki shima a gajiye ya dawo,abba sai da safe ki kwanta ga anty sumayya nan sumayya sai da safe,ayi kwanan baqunta lafiya" dariya duka sukayi sumayya tace
"Allah ya bamu alkhairi anty"
"Amin" ta amsa tana ficewa.
Chapter 70 · 0% Book details