← Book details Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 183 OF 226

Sashe 183

Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana shiga ta tadda wayarta na ruri,amira ke kira da yake tun jiya almustaphan ya kora kowacce dakinta,ta ajjiye plate din ta daga kiran nata tana zama gefan gado fuskarta qunshe da murmushi,suka soma gaisawa cikin barkwanci,ta tambayeta ummee ta bata saqon wani dabino tace "eh,na meye ne?" Dariya ta sanya
"Sai kinci kawai basai na gaya miki ba"nan ta gaya mata yadda zata dinga ci kafin su shiga wata hirar kuma,tsahon mintuna talatin kafinnsuyi sallama,ta sauke wayar ta maidata silent saboda dare,idanunta ya sauka kan farfesun data shigi da shi,murmushi ya subuce mata,itakam tasan akwai dalilin yi mata tayin da su'ad tayi,bata manta lafuzan data jefeta da su ba dazu,sannan ta lura da kallon data bita da shi,haqiqa jiya ba yau ba,ita din yanzun ba yarinya bace,zata iya banbance salon kowanne kallo da kishiya tayi mata dai dai gwargwado,sai ta sake sakin murmushi tana kada kai tare da neman tsari kan duk wani sharri,sake nadewa tayi abunta ba tare data bi takan dukkan abinciccikan ba,nata da nasun ta soma danne dannen wayarta,duk yadda taso taqi cin farfesun amma sai qamshinsa ya dinga cika mata hanci,yawunta ya dinga tsinkewa,janyo shi tayi ta sanya spoon ta fara ci,idanu kawai ta dinga lumshewa dadin na ratsa harshenta,bata ankara ba ta tashi da kwanon baki daya,mamakin kanta ya cikata,itadai tasan ba wani hadi na musamman aka yi masa da zai sanyata santi haka ba har ta iya tashi da shi,hannunta ta wanke a toilet gami da yin brush,ta kuskure bakinta da hadin kayan qamshin baki sannan ta sauya kayan bacci ta dawo ta nade saman gado,wani irin bacci ya dinga fusgarta bata ankara ba tuni yayi awon gaba da ita.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 no✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

9⃣2⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Assalamu alaikum warahmatullah MY DEARS FANS*

*ina son nayi amfani da wannan damar damun wajen sanar muku da cewa,lallai ne ni da sauran marubuta 'yan uwana muna buqatar ku dinga yi mana uziri*

*nasan cewa akwai da dama da suke turon saqonni na gaisuwa da tambayoyi ta numberta,saidai wani lokaci saqon yakan iya yin kwana biyu uku sati daya zuwa biyu ma wani bai samu reply ba,hakan baya rasa naba da yawan saqonnin da nake fama da shi,nakan samu saqo wallahi sama da dubu takwas cikin wayata daga na groups zuwa private charts,banda na Wattpad,face book kuwa wannan sai na samu lokaci ma,kunga idan kuka duba abun da yawa,ka zauna kayi typing mai tsaho,kayi editing,ka tura cikin duka groups din da kake ciki,akwai masu comment ka zauna ka amsa musu,kunga baki daya wannan lamarin bazai yiwu ka iya aiwatar sa shi lokaci daya ba,sau tari wasu basa fahintar haka har wani ma kan gaya maka baqar magana saidai kawai ka shanye kayi masa kawaici*

*masu numberta kuma ta kira da sukemin plashing don son annabi su daina min plashing,wlh bana qaunarsa,sannan kiran dare,'yan uwa dare fa mahutar bawa,wasu kuma kira da asuba,su fadar maka da gaba ka dauka wani mummunan abu ne ya faru,wanda yake kira kuma bana dagawa shima yayi uziri,wayata a silent take ban fiya barinta a ringing ba,wasu lokuta kuma ina rejecting to sometimes ina typing ne idan layin yana cikin wayar da nake typing da ita.*

*ina fata fans kun fahimceni,duk wanda yaga yayi min magana baiga reply ba yayi haquri,wani saqon na danne wani idan sukayi yawa,sau tari ma idan ina online ka turo shi yana sama sama ina qoqarim amsawa,mu dinga yiwa juna uzuri,nasan duka qauna ce kuma na gode,Allah yasa mu dace ya bamu ikon ci gaba da haquri da juna*

______________________________________

      Kusan a makare ta tashi,idanunta cike taf da bacci tayi sallah,saman abun sallar ta sake bingirewa bacci na fusgarta,sama sama ta jiyo muryanshi,tsaye yake a kanta cikin farar jallabiya yana kallonta,bata tantance shi sosai ba ta gaidashi tana daga kwancen idanunta na lumshewa,cikin mamaki ya amsa yana kallonta,sai yaga ta juya taci gaba da barcinta,ya jima tsaye yana kallonta qudundune cikin hijabi,yana mamamin wanne irin bacci take haka?,tsawon wasu daqiqu yana tsaye kafin ya juya ya fice.

        Qarfe tara na safiya ta sake farkawa,barcin tamkar bai isheta ba,ga mutuwar gabbai,sai ta shige bandaki tayi wanka saboda taji qwarin jikinta,duka dai sammakal,amma dai kasalar ta ragu,gaban madubi ta shirya cikin gown mai A shape ta wani material mai kyau,ta yane kanta da qaramin mayafi wanda ya dace da material din ta wuce kitchen,falon fes yake da alama masu aiki sunzo sun gyara duk da dama ba datti yake yi ba,rasa abinda zata dafa tayi,ta jima tsaye tana tunani,sai kawai ta dauko dankalin turawa ta fere,ta dora a wuta ta dafashi,ta sauke ta murmusheshi,kifin gwangwani ta bude ta murmusheshi saman dankalin,ta zuba mai a kasko tu juye dankalin da kufin,a hankali take juyawa tsawin mintuna sannan ta kada qwai ta yanka albasa a kai da maggi ta juye kan dankalin da qwan taci gaba da juyawa har sai da qwan shima ya soyu sannan ta juye a plate,ta tsiyayi ruwan shayin da yaji kayan qamshi ta fito falo.

       Kacibus sukayi da anty ni'ima matar yaya adam,cikin fara'a ta sauya akalar tafiyar tata
"A'ah,anty ni'ima,shigo mana" itama fuskarta dauke da fara'ar ta qaraso,duka sukayi masauki saman kujerun falon,sumayyan ta janyo center table ta dora plate da cup dim hannunta suka soma gaisawa da ni'iman sannan tayi mata tayi,abun ya burgeta duk da bata san meye ba ko ya akeyi,ba musu ta sanya hannu suka soma ci,sumayyan ta tambayeta ko a zuba mata ruwan zafin tace alhamdulillah,wannan ma ya isa,suna ci suna hira tamkar sun shekara tare.

        Tas suka tashi da shi,ni'ima ta kalli sumayya
"Kai amiran umman khalipha,wannan abun yayi dadi,amma fa akwaisa kwadayi,ya ake yinshi?" Dariya ta saki
"Kai anty ni'imah,simple abu ne fa" a tsanake ta kwatanta mata yadda tayi din sannan ta dauke farantan tayi kitchen da su ta dawo suka ci gaba da hirarsu.

         Tare suka sauko tana biye da shi a baya,ji take tamkar ta dawo da kwanakin baya,bata so ta tuna cewa yau zata sallamawa waccar 'yar qauyen mijinta da tafi so fiye da komai a duniya,sam fuskarta babu walwala haka suka ci gaba da takowa,muryar ni'ima ya jiyo,ya waiwayo ya dubesu,cikin girmama juna suka gaisa,sannan sumayya ta gaidashi tana dan dauke kai,kishinsa itama take ji har cikin zuciyarta,saidai bata son ta nuna,dining din da masu aiki suka shirya da kayan kari suka nufa,yayin da ni'imah ta miqe
"Bari na wuce,ko wajensu ummee ban shiga ba" sam bata son ni'iman ta tafi,taji dadin zuwanta,sai ta miqe tana fadin
"Bari na dauko mayafi mu shiga tare,nima ban je ba" tana nan tsaye sumayyan ta shiga daki ta dauko mayafinta,hankalinshi na kansu duk da yadda su'ad ta tare gaba da baya,da biyu take yin komai,a nutse ta qaraso bakin dining din a ladabce tace
"Zanje mu gaisa da su umme ni da anty ni'imah" ba tare da ya dago ba yace
"Ni din ma banje ba,ta wuce ma taho" sam bataji dadi ba,sai ta dawo a sanyaye
"Anty ni'imah tare zamu fito" murmushi ta sakar mata
"ba damuwa sai kun fito"daya daga cikin kujerun dake falon ta samu ta zauna tana jiranshi ya kammala,tana iya jiyo duka abinda su'ad ke fadi,hirar darensu na jiya take ta sako mishi yana basarwa,jin bacin rai na neman mamayarta ya sanyata miqewa tsam tayi shigewarta dakinta.

        Tana gaban mudubi tana gyara zaman kayan makeup dinta ya shigo cikin nutsuwa,har yanzu ranta a bace yake,sai taqi dagowa ta dubeshi duk da yadda take jin tsaretan da yayi da idanunshi
"muje na kammala"ya fada a a taqaice
"Kuje na taho" itana ta maida masa da yanayin da yayi mata maganar,sarai ya fuskanci ranta a bace yake
"Muje nace"
"Nace na taho" shiru ya ratsa na wasu muntuna
"Ummu abdallah" da hanzari ta daga kai ta dubeshi,ita yake kalla da shanyayyun idanunshi masu dauke da wani irin magadisu mai qarfi da tasiri,yana kallon yadda cikin kwana biyu fatarta ta skma sauyawa tana wani qyalli,ko idanunshi ke mashi gizo?,ya tambayi kansa,shidai yaga sauyi qwarai tattare da ita,kawar da kanta tayi,saidai sunan yayi mata dadi har cikin ranta,cikin qaramin lokaci ya soma saukar da sanyi a ranta,shima sai ya dauke nashi kan,ya taka zuwa inda mayafinta yake ya dauko,ya iso gabanta,sai ji tayi ya soma yafa mata yana fadin
"Idan baki shirya takawa da qafafunki ba,am ready to carry you,komai ta fanjama fanjam" dan qanqani daga cikin aikinsa kenan,hakan ya sanya yana gamawa ta motsa tayi gaba yabi bayanta.

        Kamar jiya haka suka rankaya su ukun baki daga,saidai ita bata dawo bangaren nata ba sai wajen qarfe biyu,bayan ta bada saqon abubuwa da take ganin tana da buqatar amfani da su,bayan ta kammala sallar azahar din dakinshi ta haura,dai dai sanda su'ad ta fito cikin heavy makeup,idanunta manne da sun glasses da cogen takalminta tana karkada muqullin mota tare da taunar chewing gum ta fice bayan ta watsawa sumayyan wani banzan kallo,kau da kanta tayi itama tana jan tsaki,ya ilahi batasan ma me yasa take kishin almustapha haka ba.

        A yamutse ta tadda dakin,ita ta gyara kowacce kusurwa ta dakin,ta dauko sabon zanin gado ta sauya,ta gyara toilet,ta hada dukkan under wears dinshi ta tsaftace da hannunta ba tare da taimakon washing machine ba ta shanya cikin toilet din,tana saukowa aka kawo mata saqon,ta amsa ta nufi kitchen kai tsaye.

       Lafiyayyar sakwara ta shirya tare da water leaf soup,wadda taji ganyen water leap,ogun,ganda,tsokar na da stock fish,blander ta jawo ta niqa aya da kwakwa da dabino ta hada lemo ta sanya a fridge,nono mai kyau da aka siyo mata ta hada da fura ta dama bayan ta wats kwakwa a ciki ta saka shima cikin fridge,sai data tabbatar da kammaluwar komai sannan ta rufe kitchen dinta da key,don bata mance rayuwar da sukayi da fa'iza ba,wuyat data sha kasancewar kitchen dinsj daya,kalanzir gishiri,suger duka a girkinta,murmushi ta saki tana rayawa a ranta,duniya labari,ko ina fa'iza ta shiga yanzu ohi,Allahu A'alamu.
Chapter 183 · 0% Book details