← Book details Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 226

Sashe 1

Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Compiled By Umar Dalha Funtua.

✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*innama amruhu iza arada shai'an an yaqula lahu kun faya kun*

0⃣1⃣

Falo ne mai matsakaicin girma wanda ke dauke da set din kujeru labulaye carfet wanda dukkansu kalolin ash ne turarre da kuma mai haske,daga bangare daya t.v plasma ce 'yar matsakaiciya reciever da kuma D.V.D  wadanda aka qawata jeransu.

     Can daga kowacce kusurwa ta falon flower ce cikin plower vase dake a tsaye masu matsakaicin kudi,sosai falon ya bada sha'awa duk da ba wani uban kudi aka narka masa ba sakamakon yadda komai yake tsare a muhallinsa,bugu da qari kuma yadda ya wadatu da tsafta yake bada qamshin turaren wuta mai sanyi

    Mamallakiyar falon ce zaune kan daya daga cikin kujerun falon,matashiya ce wadda ba zata wuce shekara sha takwas ba,fara ce ba irin qal din nan ba,tana da matsakaicin kyau wanda kwalliyar da tayi cikin shadda orange dinkin bubu ya sake fidda kyanta,dan kwalin shaddar na ajjiye gefanta wanda ya zamo sanadiyyar bayyanar kitson dake kanta qananu wadanda aqalla sun doshi guda dari da hamsin,yadda falonta ke qamshi hakama jikinta yake yi.

    A hankali ta daga kanta karo na barkatai ta sake aza su kan agogon bangon dake manne saman t.v plasma din dake gabanta maqale jikin bango.

     Sauke idanun nata tayi kana ta maida kan dan madaidaicin centre table din dake gabanta,ta miqa hannunta ta dauki wayarta samfurin tecno w3 ta sake lalubo lambar da tun dazun take ta nacin kira,duk da cewa amsa daya ake bata tun dazun cewa lambar da take nema din a kashe take amma hakan bai sanyata ta daina kira ba.

   Yanzu ma amsar duka daya ce,bai saba kaiwa war haka bai dawo gida ba,yawancin baya gota qarfe takwas indai ya dade da yawa bai dawo din ba,sau tari idan taga hakan kuma ta tabbatar ba zaya wuce gidan babbar yayarsu ba hajiya yahanasu,saidai yau duk sai taji gidan shiru babu dadi,saboda baki daya 'yan tayata zaman sun tafi gida saura ita daya.

    Sauke ajiyar zuciya tayi tare da lumshe idanunta,ta dan zame kadan ta kwanta saman kujerar tana jin kewa na ratsata,kewar yara take sosai,mutum ce ita mai bala'in son yara,saidai Allah bai azurta ta da samun nata na kanta ba tsahon shekara shida da aurenta,kasancewar tayi aure tun tana da shekara goma sha biyu kacal a duniya.

     Tayi zurfi kadan cikin tunanin nata taji ana yunqurin bude qofar gidan da muqulli,ta bude idanunta tana duban agogo,qarfe tara har da mintina arba'in da biyar goma saura kenan,zumbur ta miqe ta janyo dankwalinta ta daura kana ta fito a hankali ziwa tsakar gidan nasu wanda yake da yalwa babu laifi,bayan nata dakin ciki da falo akwai dakuna biyu masu ciki dai dai wanda guda daya mallakin mai gidan ne,dayan kuma 'yan karikicen da ba'a rasa ba take ajjiyewa ciki,sai kuma bandaki daga bangare daya gefensa rijiya ce,sai kuma yalwataccen kitchen dake kallon dakuna biyu masu ciki dai dai din wanda yayi girman dakunan nasu,fes tsakar gidan shima yake kamar yadda ilahirin gidan yake,sumuntin tamkar ka zuba abinci a qasa kaci saboda wadatar tsafta.

    Tana tsayen har ya kammala bude gidan ya turo babur dinsa(lifan)samfurin companion,a tsakar gidan ya masa matsugunni gefe daya lokacin da take qarasowa gareshi tana ambaton "sannu da zuwa" fuskarta qunshe da murmushi wanda lokaci guda ya soma qoqarin gushewa daga fuskarsa sakamakon ganin fuskarsa sam babu annuri lokacin da yake amsa mata da "yauwa sannu da gida,na barki ke daya na tsaya gidan yaaya yahanasu"
"Eh nayi zaton hakan" ta fada tana sanya hannunta ta amshi jaka da ledar hannunsa jikinta a sanyaye tana qara cika da mamakinsa saboda sam ba haka ya sabar mata ba idan ya shigo gidan.

      Tana gaba yana biye da ita a baya tare da qare mata kallo,komai na sumayyarsa na burgeshi,har yau baya manta lokacin da ya aureta da qananun shekarunta wanda za'a iya kiranta qwaila,amma a ayanzun sai ka rantse ba sumayyar nan bace wadda ya aureta shekara shida baya da suka wuce.

   A falon ta barshi ta dawo tsakar gida tana hada mishi ruwan wanka zuciyarta na sake gaya mata akwai abinda yau ke damun mukhtar dinta,mutumin da ita ke tayashi shigowa da babur dinsa ta hanyar bude masa qofa da rufewa,da ya shigo zai rungume ta yana yaba kwalliyarta,a haka zasu qarasa falo,ko da ruwan wanka wani lokaci tare suke hadawa,bai barin bakinta ya huta idan ya dawo,gwanin tsokana ne da son sanyata dariya.

   Falon ta sake dawowa tana tsane ruwan hannunta,yadda ta barshi zaune haka tazo ta tarad da shi,bata ce uffan ba ta qarasa gareshi ta rage masa kayan jikinsa,shima bai tanka ba illa kallo da yake binta da shi har ta kammala ta miqa masa towel,karba yayi ya rataya a wuyansa sannan ya fice.

   Kafin ya fito har ta kammala jera abinci zuwa ruwan wanke hannu,dakinsa ya wuce kansa tsaye ya sanya jallabiya kana ya dawo cikin falon.

    Dukkaninsu jagula abincin kawai suke da cokulansu,damuwar data lura yana ciki ita ta hana mata sakewa taci abincin,duk da yunwar da take ji saboda bata iya cin abinci sai tare da shi,hakan ya sanya ko da rana ba don albarkacin yaran dake shigo mata ba wanda ta maida tamkar qannenta da ba zata dinga cin abincin rana ba,tana son tambayarsa amma bata son masa katsalandan,saboda shi da kansa yake sanar mata damuwarsa ba tare da ta kai ga tambayarsa ba,kasancewar ya maidata tamkar abokiyar shawara gareshi,sosai zuciyarta tayi ta kasa sukuni.

   A hankali ya daga idanunsa ya dora akanta sakamakon tuna a inda yake,sai yaji tausayinta ya kamashi,baiji dadin sanyata a damuwa ba,ga uwa uba yana hasashen nan gaba kadan zata iya shiga damuwar data linka wannan.

   Ajjiyr cokalin yayi yana qirqirar murmushi tare da kamo hannayenta ya riqe
"Lafiya qalau kuwa yau kike my sumy?" Cikin raunanniyar murya tana qoqarin maida qwallar data taru a idonta kasancewarta mace marason damuwa,kanta ta langabe cike da rauni
"Kai zan tambaya yaya mukhtar" ta qarashe fada muryarta na rawa,girarsa ya dage
"Me ya faru?" Qoqarin daidaita muryarta tayi
"Ban taba ganinka cikin damuwa yaa mukhtar irin haka ba,me ya faru da kai" kai ya girgiza yana sake qirqirar murmushi yana qoqarin azawa fuskarsa,don baisan ta ina zai fara sanar mata damuwarsa ba,ya tabbatar za tayi nauyi a qirjinta fiye da yadda tayi nauyi a nasa qirjin,bai da buqatar fadawarta damuwa ko kusa,sai gashi yaya yahanasu nason jefasu damuwa duka su biyun,sonta da tausayinta wani bangare ne mai girma a rayuwarsa
"Sumayyaaaaah" ya dan ja sunan nata yana kallonta
"Babu wani abu da yake damu na,gajiya ce kawai,matso maza kici abinci don na tabbata babu abinda kika ci" ya fada yana janyo plate din gabansa tare da zare nata cokalin ya fara juya abincin da iya nasa cokalin da alamu yana nufin ciyar da ita da kansa kamar yadda yake mata wasu lokuta.

   Kan ta ta girgiza idanunta cike da qwalla"ya mukhtar kayi haquri amma wlh ban yarda cewa baka da damuwa ba,bazan ci abincin nan ba har sai ka gayamin meke damunka"cokalin ya ajjiye kana ya sauke ajiyar zuciya,baya da nufin fada mata komai amma ya fuskanci idan baiyi wani abu ba zata qi cin abincin ne kuma ta kwana cikin damuwa saboda haka yace da ita
"Naji,zan gaya miki amma ba yanzu ba,kinga dare yayi sai gobe idan Allah ya kaimu,yanzun ki matso kici abinci tukun"
"Kayi alqawari?" Dariya ta bashi saboda yadda quruciyarta ta fito muraran sanda tayi maganar
"Eh nayi" ya fada shima.

    Ko da suka zo kwanciya haka ya dinga qoqarin boye damuwarsa,ya dinga qarfin halin aiwatar da duk wani abu da ya saba yi mata su don cire zargi daga zuciyarta da kuma son ganin ta sake,zamu iya cewa barcinsa kadan ne a daren ranar,cikin duhun dakin ya dinga juyi yana sake bitar maganganun da sukayi da yaaya yahanasu a wannin da suka shude dazu,yana cikin wannan tufka da warwarar bacci yayi awon gaba da shi.

    Washegarin ranar duk da maganar da sukayi daren jiya na maqale a zuciyarta tana mata yawo wanda ya haddasa mata wata kasala hakanan da mutuwar jiki saboda har wayewar garin damuwar dake fuskar sa bata bace ba,hakan bai mata tasiri ya hanata yin duka wata hidima ta gidan ta ba,wanda ya kama da tsaftace gidan kafin tashin mukhtar daga bacci,shirya abun kari da tanadar masa ruwan wanka.

     Yana tsaye bakin gado yana sanya links din hannun rigar shaddarsa,yayin da take gaban madubi tana shirya masa ragowar kudadensa da ya taho da su daga kasuwa da zai fita da su ya kaisu banki,hira suke jefi jefi duk da ba kamar yadda suka saba bane.

     Bayan ya kammala ya tako gaban madubin yana gyara zaman hularsa a kanshi,sumayya ta dubeshi cikin zuciyarta tana yaba kyawun da yayi,ya kula da ita saboda haka cikin salon tsokana yace
"Ki fito kawai kice na fiki kyau yarinya,sai wani satar kallona kike" sau tari idan ya fadi haka kunya da dariya yake bata,har ma wani lokacin musu ya dan kaure tsakaninsu,yau din ma dariyar tayi,maimakon ta biye masa auyi musun su na ta fishi kyau da iya kwalliya yadda suka saba sai tace
"Yaa mukhtar,yau ne fa sunan fiddausin" yanayin fuskarsa taga ya dan sauya,bai ce komai ba yana daura agogon hannunsa,har ta fidda rai tayi zaton ba zaya ce komai din ba sai taji yace
"Zaki je dinne?" Murmushi tayi saboda mamaki tambayar ta bata,fiddausi ai kamar diyarsa ce saboda 'yar yaya yahanasu ce,kuma shi da kansa ya bada kudin ankon sunan harda kudin dinkin ma
"Me zai hana yaa mukhtar,saidai idan kai ka hana" shiru ya sake yi har ya kammala ya dauki jakarsa ya rataya sannan ya sanya hannu cikin aljihun rigarsa ya fiddo da dari biyar ya miqa mata kudin cefane,sannan ya sake fitar da dubu daya daban yace mata kudin mota,ya sake bata wata dubu biyun yace ta baiwa mai jego barka,hannu biyu ta saka ta amsa tana jera godiya kamar yadda ya zame mata al'ada duk qanqantar alkhairin da zaya yi mata,tako masa tayi ta rakoshi har ya fidda babur dinsa waje tayi masa a dawo lafiya.
Chapter 1 · 0% Book details