← Book details Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 226

Sashe 141

Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

     bai samu baabaa ba saboda ya fice wajan aminin nashi malam kan maganar yadda zai gabatarwa da malam dukkan gidajen gonanshi wanda yakeao a yanzu su dawo hannunshi ya karbi dukiyarsa,yaga kamar malam din yana bagarar da zancan yaqi tsayawa su tattaun,yau yake so ayita ta qare,saboda haka anty maamaa maan kawai ya gaisar ya wuce wajen ummee,tana kwance ta fito ya gaidata ta amsa tana dubanshi,basai an gaya mata ba tasan da walakin goro a miya,ta gabatar masa da break fast,bai iya cin komai ba sai coffe da yayi qoqarin sha don kada ya daga hankalinta,yana sha tana gefansa a hankali tace da shi
"Dukkanin mai biyayya zaici ribarta a gaba,bijirewa iyaye koda kan gaskiyarka ne bashi da wani alfanu,zaiyi wuya idan baka ci karo da tashin hankali ba a gaba sanadiyyar wannan bijirewar,almustapha,na roqeka ka riqe musu yarinya da mutunci,ka fiddani kunya kada ka watsan qasa a ido,yanzu ne lokacin da zaka nuna irin tarbiyyar daka samu daga gareni" jikinsa duk sai yayi sanyi,shi wai iyayensa da suka isa da shi ke roqo?,akan me?,duka akanta?,akan yarinya qwara daya tal,cup din ya dire yana fadin
"In sha Allah" cikin sassanyar murya sannan ya fice yana dauke da brief case,tuni drivanshi ya gama shirya komai,maimakon baya da yake shiga wannan karon gaban motar ya shiga,baice komai ba don shima ya lura akwai abinda ke faruwa da ubangidan nashi ya shiga ya tada motar masu tsaron qofa suka bude masu wakekem get din suka fice.

       Daga kadan kadan ciwon marar ke sake yawaita mata,wanda hakan ya sanya maama ta takurata kan lallai yau sai taje taga likita,itakam baki daya bajin dadin rayuwar ma take ba,amma tilas ta shirya zuwa don cika umarninsu da samun kwanciyar hankalinsu,qarfe tara ta gama shiryawa bayan sun gama waya da anty dije ta bata adresa din wani asibi,ta gaya mata komai kyauta ake saidai akwai tsantsar kulawa tamkar asibitin da ka fidda kudinka ka biya,ba kyautar ce zata kaita ba,kulawar data fada shi yasa zata,don bata da matsalar kudi,don baabaa ya ajjiye mata su tamkar baisan zafin su ba,hatta da abinda zata ji bai yarje taci na gidan ba,sabida yace yanzun ba dolensu bace.

        Sai data shiga ta gaida baabaan a kunyace sannan sukayi sallama da malam kan zata asibitin da yake baaban yace izinin fitarta ya damqawa malam din kafin qarasowa mijinta,dakatar da ita baaba yayi ya fidda wayaraa ya kira daya daga cikin direbobin dake dakon fitowarsa ya bashi umarnin kaita ganin likita,cikin girmamawa ya amsa,shiru tayi cikin lafiyayyar motar wadda idan ba gargada ta kai gargada ba ba lallai ka fahimci ana tafiya ba,ire iren motocin da suke mallakin familyn professor mukhtar,motar da ada ko a mafarki bata darsa shiga irinta ba,ajiyar zuciya ta saki sannan ta fidda wayarta ta duba kiran dake shigowa amira ce,murmushi ta saki duk ciwon marar dake neman sake tsananta mata,amsa wayar tayi ta kara akunnenta.

Masu karatu muje zuwa,wanne asibiti sumayya zata????.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

7⃣6⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*la haula wala quwwata illa billahil aliyyul azim*
_____________________________________

        Cikin babbar haraban asibitin motar ta ajjiyeta a muhallin da aka tanada saboda ajiyar motoci,cikin rashin qwarin jiki ta bude murfin motar ta fita sanda drivan ke kashe motar yana sake daidaita tsayuwarta,kai tsaye reception ta isa,aka bude mata file kasancewar komai kyauta ne,tayi mamakin kyau da tsaruwar asibitin,wanda ta tabbatar da cewa inda mamallakin asibitin yayi shine saboda kudi ba shakka ba qananun kudi zaya samu da asibitin ba,tsarin ya burgeta,ba qaramar dabara yayi ba,saboda tasan ladan da zaya samu ba kadan bane,d'aya daga cikin abubuwan da masu kudinmu basa ganewa kenan,sun gwammace suyi saboda kasuwanci,ba don ya zame musu sadaka mai gudana ba wadda zata yita bibiyarsu har bayan rayuwarsu ba,abune wanda koda sunyi ba komai bane cikin dukiyar da Allah ya basu ba,Allah madaukakin sarki yana cewa
"Yaku wadanda kuka bada gaskiya da Allah ku ciyar daga abinda muka azurtaku tun kafin ranar da babu fansa a cikinta(da zata yi maka amfani),ba abokantaka (a cikinta da zata yi maka amfani),ba ceto(sai da izinin ubangiji)tazo muku(wato ranar qiyama",bayan mai bada katin ya gama cike mata ya miqa mata yana nuna mata inda zata kai a saka ta a layi yana fadin
" kinyi sa'a kuwa malama,yau oga ne da kansa ya zauna,ba kowa ke samun sa'a irin haka ba ranar garkonshi"ya fada yana washe baki,don tunda ta shigo tayi masa,duk da kasancewarta cikin zabgegen hijabi har qasa amma hakan bai gaza bayyana kyawunta ba
"Na gode" kawai ta fadi ta amshi folder din ta kai inda yace mata,akwai mutane kusan goma sha biyar a gabanta,saboda haka dole ne tayi zaman jira,bata jima da zaman ba kiran nafisa ya shigo wayarta,wanda shine ya sake dauke mata hankali da radadin da take ji,don a qalla sun bata kusan minti talatin suna waya kafin su rabu.

       Sannu sannu suka soma raguwa,duk wanda ya fito fuskanshi qunshe take da fara'a saboda an duba shi yadda ya kamata,uwa uba zai samu magunguna masu kyau fiye da kullum,wanda kusan yawancinsu masu ciki ne,duk na gabanta suka qare layi yazo kanta,wanda bayan fitowar matar qarashe ta miqe ta isa qogar office din ta tura ta shiga.

      Lafiyayyen office ne wanda yake a tsaftace sannan a tsare kamar yadda ilahirin asibitin yake,office ne mai girma wanda daga hannun hagu ke dauke da rukunin wasu irin kujeru kusan guda hudu da table dinsu a tsakiya,kana shigowa kuma table din likitan ne wanda ke dauke da tashi kujerar da kuma kujeru guda biyu a gaban table din suna fuskantar juna wanda anan patient ke zama yayi bayani,daga bayan tashi kujerar wami dan katako ne a tsaye wanda yake rataye 'yar saman suit dinshiba jiki,sannan gaban table din kadan dan gado ne wanda ke hade da na'urar sacanning ta musamman da sauran tarkacen likitoci,daga hannun dama kuwa qofofi biyu ne kulle,daura da su freezer ce girke a kanta akwai set na warmers da cups na tea da na ruwa,sai coffe maker daga gefe.

      Tsaye yake gaban gadon scanning din inda ya baiwa qofa baya,hannunshi dauke da takardar da ya gama yiwa wata mata scanning yana dubawa,ranshi a bace yake sosai har hakan ya nuna saman fuskarshi,yana mamakin yanda a yanzu maza ke wasa sa haqqunanau kan matayensu,kana da mata tana dauke da cikinka,wanda rayuwarta na cikin qila wa qaala ne,ko ta mutu ko dan ya mutu ko a rasa su baki daya idan kuma ta kasance daga cikin masu sa'a su rayu baki daya,amma ka kasa tsayawa ka bata kyakkyawar kulawa?,abincin da zata ci mai kyau ya gagareta?,kullum tana cikin tashin hankali da masifa,tayi wahalarka tayi ta yaranka?,akan me?,saboda me?,duka cikik zuciyarsa yake wannan maganan.

       Turo qofan tayi sallama a bakinta,ya amsa ba tare da qwaqwalwarsa ta bashi wace ba,dan tsayawa tayi saboda batasan inda zata zauna ba,ga faduwar gaban sata rusketa lokaci daya sai daga bisani ganin ba'a ce mata komai ba sannan ta taka ta isa gun kujerun ta zauna.

        Takardar ya nade ya ajjiyeta gefe yana sakin tsaki sannan ya juyo a hankali ta tako zuwa nashi muhallim ya ja kujerar ya zauna ba tare da ya dubi wadda ke zaune din ba,duk da yana shaqar wani qamshi da kamar yaso ya sanshi,ya jawo file dinta ya bude,ganin sabo ne alamun zuwanta na farko ne ya sanya shi fadin
"Uhm,meke damunki?",ita din ma bata dubeshi ba har sai da sautin muryarshi ya daki kunnenta,da sauri ta daga kanta idanunta suka sauka kanshi,tsabar ciwon dake murda mata ya hadu da firgitar da tayi ya so riqe numfashinta,qoqarin miqewa take amma ta kasa,har ya kammala rubuta date din da zaiyi baiji an amsa ba,hakan ya sanyashi daga kansa yana tsammanin ko kurma ce,idanunshi ya dan ware a kanta,kafin yq maidasu yadda suke,wanda hakan ya taimaka wajen sanyata miqewa da hanzari dom barin ofishin,ta gwammace ta haqura da ganin likitan baki daya,cak ta tsaya jin sautin muryarsa kuma muryar mukhtar yana bata umarnin dawowa inda ta tashi din,har cikin zuciyarta tana jin ba zata iya tsayawa ba,a inda daga shi sai ita?", sai ta sake daga qafarta don cikin yunqurin cimma ficewa daga office din ba.

       Batasan ya akai ba,yaushe ya iso inda take?,sai kawai ji tayi an tado qafafunta,wanda hakan yayi sanadiyyar wancakalar da jakarta sannan ta tafi zata fadi dama jikin babu qwaru,tuni ya tarota da hannayenshi,bai cikata ba har sai da ya kaita kan rukunin kujerun nan guda hudu ya zaunar da ita,tsaye yayi a kanta hannayenshi harde cikin qirjinsa yana dubanta,qare mata kallo yake yana sake shaidawa kansa cewa matarka ce,duk abinda zakayi kayi controlling kanka,duk da bai iya kallonta yadda ya kamata sakamakon hijabin da ya lullube dukkan jikinta,tafin hannayenta kawai yake iya gani sai fuskarta wadda itama bata fita ba saboda kanta na sunkuye ne a qasa,so yake ya gani ta inda ta dace da shi,so yake ya gani yadda zaiyi ya zauna da ita,ya kuma gano ta inda zata iya taimakonsa ko amfanarsa,bai gani digon wayewa ko dis tattare da ita ba,hasalima shi tunda ya santa cikin hijabi yake ganinta,sau daya ya taba ganinta ba cikin hijab ba ranar bikin amirarsa,wannan itace zata iya zama da shi ta samaasa farinciki wanda ita kanta bata samawa kanta ba?,ya tabbatar gwara su'ad sau dubu da ita,wanda ko ita su'ad dinma data san ta kan duniya ta kasa iya tafiyar da shi,ta kasa shayar da shi soyayya mai zafi irin wadda yake muradi balle wannan da kullum take a qunshe?.

       Idanuwansa ya lumshe sannan ya hadiye wani abu mai tauri daya tsaya masa a wuya sanda ya fuskanci kuka take,qaramin tsaki ya ja cikin zuciyarsa yana cewa
"Ko uban me nayi mata oho?" Motsa bakinsa yayi da niyyar daka mata tsawa sai kuma ya tuna ita din wacece wajen baabaa?,me baabaa ya gaya masa game da ita,hannunsa ya dunqule ya daki daya tafim hannun nasa wanda hakan ya darsa tsoro a ranta,sai ta runtse idonta tana jira taji mai zai faru.
Chapter 141 · 0% Book details