← Book details Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 226

Sashe 45

Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

       Tun safe take addu'ar kada Allah ya dawo da shi,a haka har lokacin tafiya makaranta yayi ta shirya ta tafi tare da abdallah wanda yau ya tubure sai ya bita.

      Yau sai kusan biyar suka taso,tun daga qofar gidan ta hangi motarsa,a hankali ta dinga takawa jikinta a sanyaye har ta isa gab da motar,qofar mazaunin direba a bude take alamun mamallakin motar yana ciki,tuni abdallah ya gane motar waye,ya zame daga jikinta yayi wajen motar yana kiran abba,hankalin abdur rahman yayo wajen ya waiwayo yana murmushi sannan ya fito ya dage shi sama ya cafe suna dariya,sanye yake da yadi irin na maza blue black,hula da takalminsa sau ciki duka baqi,yayi kyau sosai. Ya sauke idanunshi a kanta yana kallonta
"Yau kam kin dade,kinsan tun nawa nake nan ina jiranki?" Kai ta girgiza ba tare da tace komai ba,yatsun hannunsa ya daga guda hudu ya nuna mata,sannan ya dora da fadin
"Shine yau kika dauke abokin hirar ko?" Kai ta sake kadawa sannan tace
"Shine ya nace yau sai ya biji,nima bana son tafiya da shi"
"Mukam muna maraba da shi ko yaushe,shiga ki kintsa kafin naje can qasan layinku na dawo na baki minti talatin"
"Amma dai da ka shigo ciki ko?"
"Amma dai kinsan gunki nazo ko?"ya bata amsa da salon yadda tayi tata maganar,ta lura jan magana yake ji saboda haka ta sanya kanta gida tana fadin
"A dawo lafiya".

       Salla kawai tayi wadda lokacinta ya kubce mata,ko abincin ta kasa ci tanaa zaune tana nazarin hanyar da zata bi abdur rahman ya janye zancansa salin alin ba tare da an kai ruwa rana ba,don gaskiya bata jin zata iya maida kanta cikin familyn su mukhtar,an gudu ba'a tsira ba kenan,ko kuma tsugune bata qare ba?,cikin haka zainab ta shigo dakin ta gaya mata taje ya abdur rahman na waje ta karbi abdallah.

      Kamar wancan karon wannan ma haka ya tilasta mata shiga motar tasa,shuru ya ratsa motar na wasu daqiqu ba wanda ya sake cewa uffan bayan abdur rahman ya gama jaddada bayanansa a gareta
"Da farko abinda zan fara cewa shine na gode na gode matuqa,na yaba da qaunata da kace kana yi,har ka nuna sha'awar zamantowa abokiyar rayuwarka duk da ban cancanci wannan darajar ba,amma abdur rahman kayi haquri,bazan iya aurenka ba,saboda wasu dalilai wadanda ni da kai duka mun sansu wasunsu kuma ni da ubangiji na ne kawai muka sansu" kai yake jinjinawa yana dubanta sannan yace
"Ban gamsu da baya nanki ba ko kadan,babu wani abu da zai sanya ni janyewa daga batun neman aurenki sumayya,ina sonki babu wanda zai hanani"so take ya fahinceta bilhaqqi don su bar maganar sun wuce gun,sai ta sake fuskantar sosai wani abu na taba zuciyarta na daga abubuwa da suka faru da ita a baya
" ta yaya abdur rahman kake so na sake komawa cikin danginku,bayan kaima kana daya daga cikin mutanan da zasu shaidi irin rayuwar da nayi a cikinsu,ya kake so ka sake maidani rayuwar baqincikin da nayi bankwana da ita?,ko kuwa zaka sauya dangi ne saboda zaka aureni ni sumayya 'yar gwal,ko ka manta waje mijina na baya,ka manta alaqar da take tsakanin ku,don Allah abdur rahman muci gaba da mutunci mu ajjiye zancan soyayya a gefe"ta qarashe maganar tsohon mikin dake zuciyarta na taso mata,sai ta sanyo qafafunta waje ta fito daga motar,da sauri shima ya fito ya zagayo inda take tsayen,kafin yace mata komai suka ji tsaiwar mota,waiwayawa sukayi dukkansu don ganin waye.

       Mukhtar ne,tun yana cikin motar tasa yake qarewa motar kallo,babu shakka wannan motar yake tawan gani a qofar gidan su sumayyan,kenan yau zai ga waye mamallakinta zaiga wake zuwa gunta,amma idan idanuwansa na nuna masa dai dai kamar abdur rahman yake gani tsaye tare da sumayya,to meye yake haka a gidan?,meyw hadinsu?,shine mai motar da yake gani kullum na ficewa daga layin?,don samun amsaoshin tambayoyinsa sai ya balle murfin ya fito bayan ya kashe motar ya nufosu idanuwansa a kansu zuciyarsa na azalzala tare da ayyana masa wani abu wanda baya fatan kasancewaraa.

        Sallamarsa ita ta katse abdur rahman daga kallon sumayya da tuni idanunta suka cika da qwalla,sannan suka katse shi dag fadar abinda yake shirin fada,dukkansu waiwaya suka yi suka dubeshi,fuskar abdur rahman din dauke da murmushi ya miqawa mukhtar hannu yana fadin
"Ah,ya mukhtar kai ne?" Baiqi miqa masa nasa hannun ba suka yi musabaha yana fadi tare da tsareshi da wani irin kallo
"Eh,ya kawu da sauren mutanen gidan"
"Duka lafiya alhamdulillahi" ya fada yana sakin hannun mukhtar din sannan ya juya ga sumayya
"Ki nazari a nutse,kada ki ruda kanki,kada ki cuci kanki ki cuceni,gobe in sha Allah zan dawo" ya fada yana juyawa zuwa wajen motarsa,dukkansu ita da mukhtar din suka yi masa rakiyar idanuwa,saidai kowa da abinda ke kai kawo cikin zuciyarsa,ya bude motar ya shiga bayan ya bawa abdallah 'yar madaidaiciyar baqar leda cike da biscuite da choculet ya saukeshi ya tada motar ya wuce.

Busy kuyi haquri da wannan

*mrs muhammad ce*

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

3⃣8⃣

____________________________
*Bismillahir rahmanir rahim*

*wala taqulanna li shai'in inni faa'ilun zalika gada,illa ay yasha Allah,wazkur rabbaka iza nasit*

_kada kace ni zan aikata wani abu gobe,face sai ubangijinka yaso,ka tuna ubangijinka idan ka manta_

______________________________

        Wani abu ne ya tokare masa wuya yana jin wani irin bacin rai na taso masa,sai yayi qoqarin dannewa ta hanyar daukar abdallah da ya nufo gunsa kai tsaye yana fadin daddy daddy,motsawa sumayya tayi don shigewa cikin gidan cikin hanzari ya sha gabanta
"Me abdur rahman ke zuwa yi gunki?" Idanunta ta dora a kansa kanta tsaye tace
"Alheri"
"Alheri wanne iri?,kada kice min gonata yake son shigowa?"wani irin kallo ta masa
"Yaushe ka fara noma?,dama kana da gona ne?,alheri kuma duka alheri ne babu wani banbanci" ta fada tana rabeshi zata wuceshi ranta a bace,baisan ya riqo gefen hijabinta ba hakan ya sanyata waiwayowa tana dubansa a mamakance
"Me yasa kike cutar da ni haka sumayya me na miki a rayuwa da zafi?" Ya fada zuciyarsa na zafi yayin rauni ya bayyana qarara a fuskarsa
"Cutarwa?,ni nake cutar da kai ma mukhtar!" Ta fada tana nuna qirjinta da yatsa cikin mamaki,sai ta juyo baki daya tana dubansa sosai
"Bance ka cutar da ni ba mukhtar ni da ka saka saki uku ina kwance?,bance ka cutar da ni ba ni da ka yanke min hukunci kan zato da zargi,ka yanken hukunci ba tare da kayi bincike ba?...."
"Wanne bincike sumayya bayan ba labari aka bani ba,na gani da ido na,sannan bincike na likita ya sake tabbatar min da kinsha din wanne bincike kike da buqata nayi bayan wannan" a kaikaice takw dubansa sannan tace
"Ok ko?,to shikenan,yayi kyau hakan ai,amma shawara zan baka ka fita daga dukkan harkoki na,ko da maza dari zaka ganni da su wannan ba damuwarka bane,tunda dai a yanzu ba qarqashin ikonka nake ba,gashin kaina nake ci sai ka shafamin lafiya" tana gama maganar ta juya tayi shigewarta cikin gida ta barshi da abdallah.

     Binta yayi da kallo,taushe sunayya ta koma haka,yaushe bakinta ya bude da magana haka?,saidai batayi laifi ba yana ganin baiken kansa,tabbas ba shakka gaskiya ta fadi yanzun ita din ba huruminsa bace,baisan me ya sanya ya shishshigewa lamarin rayuwarta har haka ba,jiki ba qwari ya koma mota ya dauko siyayyar abdallah ya riqoshi har bakin qofar da zata sadaka da tsakar gidan ya ajjiyeshi ya wuce,cikin mota yana tuqi yana tunanin yadda zai raba kansa da shiga lamuranta,don bisa gaskiyarta take,wani sarawa kansa yayi wanda hakan ya sanyashi yin parking motaraa gefan titi ba shiri,ya dauki a qalla sama da mintuna talatin kafin yaci gaba da tafiya.

   *****    *****    *****

    Duk yadda taso abdur rahman ya fahimci abinda take nufi yaqi fahimta,sai ta tattarashi ta janye masa jiki,sau tari takan qi dawowa daga makaranta akan kari,tana kuma dawowar lokacin sallar magariba ne,daga nan kuma suna zama karatu da malam wanda ya sanya musu wasu litattafan addini wanda suke hadda ce wasu abubuwa a ciki,sam ta daina bada wani gaf ko wata dama da zasu kadaice har suyi magana,idan ana tare cikin jama'a zasu yi magana da shi kamar kowa.

      Ta bangare daya kuwa luqman shima ya matsa lamba,tilas ta bashi dama yazo gidan sau daya,a ranar malam ya dawo ya ganshi suka gaisa,saidai malam din baice mata komai ba kamar yadda ta zata,hakanne ya sanya ta saki jiki har ta sake bashi wasu damammakin yazo wai koda hakan zai sanya abdur rahman ya janye daga qudirinsa,saidai duk da hakan babu abinda ya girgiza shi,har mamaki abun ke bata,cikin lokaci qarami ya sanyata ta saki jikinta da shi,mutum ne mai barkwanci da yawan bada labarai,ko bata son magana sai ya sanyata dariya.
Chapter 45 · 0% Book details