Sashe 111
Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunda ya isa gida kafatanin al'umar dake cikin gidan suka fuskanci akwai wani gagarumin al'amari na farinciki da ya faru da mai gidan,tun daga manyan ma'aikata na gidan har qananu,take ya yiwa kowa qarin albashi sabida tsananin farinciki da nuna tsantsar godiyarsa ga Allah.
Bai samu ganawa da matan gidan ba sai bayan sallar magariba,ya warware musu komai,babu abinda ummee tace,ita kanta tasan yaron nata yana da buqatar sauyin rayuwa,kawaici kawai irin nata yasa basa tsomala baki cikin lamuransa,saidai sauyi wanne iri?,sauyin zai yiwu kuwa ta wannan bangaren,bayan kowa yasan ra'ayim almustapha wajen zabar matar aure?,kai hasalima kaf tarihin rayuwarshi bashi da muradi ra'ayi ko sha'awar yin mata biyu sam sam,bata manta yadda ya dinga qananun maganganu sanda yayansu adam zai sake aure na biyu,saidai a tarbiyyarsu sam babu musu ko jayayya kan duk hukuncin da jagoran gidan ya yanke,saidai su tayashi bin dokarsa ko hukuncinsa,bangaren anty maamaa ma tayi farinciki,don a dan zamanta da sumayya ta karanci halayenta,ta kuma san ta sha banban da halayyar su'ad,saidai itama tata fargabar ta yaua almustaphan baqin bature dan ra'ayin riqau mai doka da qa'idoji zai amshi wannan lamarin,gashi uwa uba baban yaja kunnen kowa da kada wanda ya sanarma almustapha maganar shi da kansa zai sanar masa,kome meye tasan na dan lokaci ne zai wuce,to baki dayansun masu biyayya ne gareshi,sannan babu wanda baida burin ganin farinciki cikin rayuwar mustaphan.
Anty farida da huda kam da suka ji lamarin har wani ihun farinciki suka saki,kasa zama sukayi sai da suka dangana da baabaan suka yi masa godiya tamkar su ya yiwa,murmushi kawai yayi yasan lamarin na damun kowa,koma dai meye shi ya fisu farinciki da shigowar jinin sule cikin tashi zuriyar.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
7⃣4⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*
*Allah S W T yana cewa*
*KACE HAQIQA MUTUWAR DA KUKE GUJE MATA MAI RUSKARKU CE,SANNAN KUMA KU KOMA IZUWA GA MASANIN ABINDA KE FILI DA NA BOYE YA BAKU LABARIN ABINDA KUKE AIKATAWA*
Ya Allah kasa ta ruskemu kana masu farinciki da mu,muna masu farincikin haduwa da kai
______________________________________
Gaba daya ta koma ta zama wata irin cikin kwana biyu kacal,duk wani kuzari da buri data ci na bikim zainab yayi nashi wuri,tsantsar tashin hankali take shiga a duk sanda ta tuna lamarin dake tunkarota,ko ya zata qare?,ko meye zai faru da ita wannan karo?,shine tambayar da take yawaita yiwa kanga,uwa uba Abdallah da ya tsaye mata a rai,ana ya gobe kamu nafisa ta iso gidansu,wani kallo take binta da shi tana tabe baki
"Ke yanzu sai kace wadda zatayi auren fari kamar wadda yau zata fara zama da kishiya shine kika bi kika susuce haka?,a haka zaki qwaci kanki duk kin fafa zabgewa kina ramewa?,amma wallahi kin bani kunya" cewar nafisa,daga kai tayi tana kallonta tare da mamakin wanda ya gaya mata zancan
"Me kike kallo na,munyi waya da amira ta gayan komai,ta kuma ce tana kiran wayarki amma kullum switchoff,na gaya mata zan shigo kanon tace na duba mata ke don Allah" ta sake fadi tana duban sumayya,fada ta zarce da yi maga,kuka ya qwacewa sumayyam,wau su don Allah ita kadai take gano abinda take ganowa,su basu hangen komai,ta gama fadanta sannan ta koma lallashinta,inda daga qarashe ita ta tilastata ta miqe tayi wanka tace zata rakata siyayya,jiki babu qwari haka ta shirya,ga zazzabin dake sakadarta a hankali,bugu da qari ga wani ciwon mara da ya saukar mata,wanda bata sani ba ko tashin hankalin da take ciki ne ya jawo shi oho.
Wani katafaren shago wanda ke saida kayan jiki na zamani nafisa ta kaisu,da idanu sumayya ke kallonta sanda take loda kayan tana zaba,harda wanda sumayyan yanzu ke amfani da shi tun wanda ta taba siya mata a uk har yau da shibtake amfani da yake ya karbeta,suna cikin mota take shaida mata yadda zata yi amfani da sauran,haushi ya kama sumayyam,yamzun suna nufim wami namiji zata yiwa hidimawa jikinta saboda za'a daura mata aure da shi
"Wallahi da kin gayan ni kika siyawa bazan barki ba,sabida asarar kudinki kawai kika yi babu abinda zanyi amfani da shi cikinsu" a fusace nafisan tace
"Wallahi baki isa ba kinyi kadan,amfani da su wallahi ya wajabta a kanki" ganin yadda nafisan ta hasala ya sanyata yin shiru,saboda ko qwaqwaqwarar magana bata sonyi yanzu kanta zau fara sara mata.
A bangaren baabaa kuwa shirin daurin auren yake babu kama hannun yaro,kai kace wannan shine karon farko da za'a yi daurim aure cikin familyn baabaa prof din,ana ya gobe daurin aure suka baro abuja suka sauka gidanshi dake kano,saboda ya kasance kusa da abokinsa,duk wanda ya dace ya san da daurin auren babu wanda baabaa bai aikawa ba.
Duk abinda ake idanu ne nata sai ta koma 'yar kallo sabanin daa da itace amara,katunan daurin aure masu dan karen kyau tsari da tsada baabaa ya sanya aka buga ya baiwa malam wani shima ya raba wani,duk wanda yaji daurin auren ya zama na mutum biyu harda sumayya sai yayi mamaki,saboda kowa yasan babu ita a batun,da kansa baba ya sanya cikin kwanaki hudu aka yima sumayyan akwatu uku na suttura wadanda zata sanya kawai bawai lefe bane,lefanta yace sai almustaphan yayi kamar yadda ya yiwa su'ad,kaya ne masu kyau da tsada dinkakku,kama daga shadda laces atamfa material sa sauransu.
Da ido kawai take binsu lokacin da aka zo yima amarya zainab lalle,almara kawai take ganin komai,wai ita za'a daurawa aure nan da kwana uku?,abinda ko cikin mafarki bata taba hasashensa ba,qememe taqi bada hannunta ayi mata komai,anty dije tace a barta kada a matsa mata,tasan cewa akwai lokacin da ita anty dijen da kanta zata sanya ayi mata kuma dole ta bada hannunta.
Ana ya jibi daurin aure kwana tayi tana kuka saboda nasihar da mama tayi mata,ta gaya mata duk wanii motsi da zata yi wanda bai dace ba tamkar ta watsawa mahaifinta qasa a ido ne,ga gidan ya fara amsar baqi,haka ta tashi washegari da zazzabi da ciwon kai amma haka ta dinga cijewa tana shiga jama'a,wanda hakan bai amfana mata komai ba face sake qaruwar ciwon kanta.
Bayan sallar isha'i tana kwance cam uwar dakan maman kan abun sallah,hasbunallahu wa ni'imal wakil kawai take ambata babu qaqqautawa saboda yadda taji nugun zuciyarta na daduwa,sallama taji anayi tsakiyar gidansu wadda ta sanyata miqewa dungur gur ta zauna tanq raba idanu kamar wadda aka ritsa da wuqa a maqogaro,muryar abdur rahman ce,sai gabanta yaci gaba da faduwa ta fashe da kuka qasa qasa tana cusa kanta tsakanin cinyarta.
Daga airphort direct gidan ya zarto ko gida bai nufa ba sakamakon mummunan labarin da ya sameshi ta bakin bahijja,kai tsaye aka yi masa iso falon malam wanda shigowarsa gidan kenan,a mutunce suka gaisa saidai kallo daya malam yayi masa yaga sauyi tattare da yanayinsa
"Ina fata lafiya malam abdur rahman" cewar malam din,kai ya girgiza cikin sanyin murya
"Malam,na jima ina neman yarda da amincewar sumayya tun kafin rasuwar yaya mukhtar har kawo yau din nan,na fara samun hadin kanta a kwanakin nan,saidai ta nemi alfarmar na bar maganar har ka kammala aurar da zainab,kwatsam sai jiya na samu labarin wai za'a aurar da sumayya malam haka ne?" Kai ya jinjina kafin yace
"Wannan haka yake abdur rahman,zan aurarwa dan aminina sumayya,sam banyi tunanin kana ci gaba da neman sumayya ba abdur rahman,ban kawo haka a raina ba" sosai ya girgiza da jin amsar malam din,idanunsa suka kada ya dubi malam din
"Malam ni nafi cancanta da sumayya,ka yimin alfarma ka aurar min da ita" cikin tausayawa malam din ke dubanshi
"Kayi haquri abdur rahman,wannan wanda zan baiwa sumayya wa familynsu sunfi qarfin na musu haka,idan da wani ne can daban babu abinda zai hana na maida auren kanka,amma zan gaya maka kadan daga labarin muntari,zan gaya maka kadan daga cikin waye muhtari a gurina" warware masa yayi DANGANTAKAR dake tsakaninsa da baabaa prof,dangantakar kuma da suke fata da burin ba zata sake katsewa ba har ABADAN,wanda hakan suna burin ya zama hanyar ci gaba da yado da qarfafa zumunci da dangantakarsu.
Cikin gamsuwa abdur rahman yakw gyada kai,babu shakka irin wannan dangantaka dake tsakanin malam da muhtari ko shine idan yana da diya abinda zai iya faruwa kenan,ba zaiso ya zama silar datse wannan kakkaurar tsohuwar igiya ba da ka qullata tun duniya na kwance,tun basu gama sanin su waye su ba kawo yau,saidai rabuwa da sumayyan ba abu bane mai sauqi tattare da shi,wani mugun ciwo ne da zai ci gaba da illata shi
"Shikenan malam,ina muku fatan alheri,saidai mu a tayamu da addu'a,Allah ya bamu haqurin jurewa" ya fada cikin karyewar murya
"Allah ya yi maka albarka,ya sanya juriya a zuciyarka,ya musanya maka da wadda ga fita alkhairi a gareka"
"Amin malam,na barka lafiya" ya fada yana mai miqewa,cikin tausayawa malam din ya bishi da kallo,har ya kai qofa ya kirashi ya dawo ya tsugunna kansa a qasa
"Abdur rahman"
"Na'am malam"
"Idan har babu takura kuma ba zaka damu ba,mai zai hana ka nemi halimatu 'yar uwar sumayyan,a tunani kamar zata iya maye maka gurbinta"
"Indai malam kana ganin hakan yayi daidai bazqi haifar da wata matsala ba na karba,ina kwadayim zuriyarka ne malam,na tabbatar akwai alkhairi ga dukkan wani d'aa da ya fito daga gidan nan" murmushi malam din ya saki cikin jin dadi
"Kayi tunani a nutse,kada kayi abinda kasan zaka takura,idan halima tayi maka ka dawo zan baka ita,idan bata yi maka ba babu komai zan biku da kyakkyawar addu'a"
"Ta yaya malam zanqi jininka,halima jininka ce jinin sumayya,na karba malam,kuma in sha Allahu a gobe zan bada sadakina nima kada itama na rasata"murmushi ya subucewa malam,sosai ya sanya musu albarka tare da jan doguwar addu'a ta fatan alkhairi a garesu baki daya,yace yaje sitting room a bude yake zai turo masa haliman,miqewa yayi kansa a qasa yana yiwa malam din godiya,abun mamaki cikin qanqanin lokaci tashin hankalin daya tsinci kamsa kaso dari sai yaji babu hamsin ciki,ya taka ya fice sitting room din gidan yana jiranta.