← Book details Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 226

Sashe 6

Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

    Murmushi ta sakar masa kamar yadda ya sakar mata
"Kinyi kyau sumayya ta" kanta ta sunkuyar cikin kunya tana murmushi
"Na gode yaya na,sannu da zuwa" ta fada tana cire masa hular kansa da bai samu cirewa ba
"Ya kasuwar" ta sake fadi tana qoqarin ajjiye masa ruwa mai sanyi
"Kasuwa alhamdulillah......kinga ai my sumy abinci zaki kawomin don yunwa nake ji",ta dan zaro ido tana dubansa
" da wuri haka yau?,na zaci sai ka dawo daga sallar magariba",shafa cikinsa yayi yana murmushi
"Salla bazata yiwu cikin nutsuwa ba ina fama da yunwa,taimakeni ki bani sumayya magaribar da sauran lokaci,idan na kammala ko masallacin sun idar mayi jam'in da ke"
"To" ta fada tana miqewa zuwa kitchen.

     Bayan ta gabatar masa da komai tuwon semo ne miyar kuka sai qamshin daddawa take duk da babu nama amma tayi dadi qwarai,taasa bismillah sannan ta koma gefansa ta zauna.

     Sai da ya kai loma biyu sannan yace
"Ga kayanku nan ki duba kiga" ya fada yana mata nuni da akwatunan dake jere gefe,da to ta amsa masa sannan sannan ta sauka qasa ta janyo akwatunan ta soma dubawa.

    Tana dubawa yana zuba mata santin tuwo,yayin da itama ke santin kayan,komai yayi kyau,sai data kammala tas,lokacin har ya gama cin twon ya jngina da kujera yana kallonta tana ta daga kayan tana yabawa,ta rurrufesu yadda ta gansu sannan ta dubeshi.
"Nayi zaton ma har an kai kayan ne naga lokaci ya qurato"

"Um um" ya fada a taqaice

"Sunyi kyau sosai ya mukhtar,Allah ya qara budi,saidai komai naga bibbiyu ka saka kala daya,nufina kayan dake cikin akwatin kayan sawa sune a daya akwatin,under wears da mayafai ma"

"Eh,akwatin uku naki ne uku nata", idanu ta zaro a firgice tana dubansa
" aini yaya ka manta ka yimin lefe na tun sanda zaka aure ni?"
"Na fiki sani,kayan fadar kishiya na miki".

    Tsoro ne sosai ya kamata,tsoron su yaya yahanasu,ina zata sa kanta idan suka ga wadan nan kayan,komai iri daya ita da amaryarsu,hatta da man lebe iri daya ne?,tabdi lallai ya mukhtar so yake ya janyo mata bayan lallabawa takeyi.

" gaskiya ya mukhtar ba'a haka,itafa amarya ce ya zaka hadamu kayi mana abu iri daya?bayan kayan kitchen da kayimin,ka sauya min kayan kallo,kasan su yaya yahanasu sai sunce wani abu idan ma basu ga laifina ba lo sun zargeni ba"

"Eh,saboda kin fiye min ita,ke din zabi na ce,kuma raino na ce,tun kan kisan ciwon kanki kike zaune da ni,tun ana ciyar da mu bana daukar nauyinki,ita din ban santa ba,bansan halinta ba bansan ko zata iya irin zaman da kika yi da ni ba,sannan idan su yaya yaha da kike zance ai basu suka yimin ba,da kudina nayi balle a ce don me?,kufi na ne kuma iyali na ne,saboda haka bana buqatar ki sake cewa komai".

    Tun asali ita ba mai musu bace da ya mukhtar din ba,girmansa take gani,kallon yaya take masa saboda haka cikin sanyin jiki tsoro da sanyin murya tace
" hidimar ce naga kamar taso tayi yawa,na gode Allah ya saka da alheri,Allah ya jiqan magabata ya basu aljanna madawwamiya"cike da jin dadin yadda ta yiwa mahaifansa addu'a yace
"Amin,Allah yayi miki albarka"
"Amin ya mukhtar na gode sosai".

     Tun qarfe takwas washegari ta kammala komai saboda da wuri mukhtar yace zai fita saboda masu jere,qarfe tara ta sallameshi,har ya fita ya dawo ya dubeta
" idan kinga babu dadi zaman gidan,na baki izini kina iya tafiya duk inda kike so,idan yaso idan sai kimin waya ki gayan inda kike,idan na taso daga kasuwa sai na biyo na daukeki"murmushin yaqe kawai tayi,don hakanan tunda ta tashi yau take jin fargaba da bacin rai
"Babu komai ya mukhtar zan iya zaman ma,me zai hana"
"Kada dai ki takura kanki idan ba hali kiyi ficewarki"
"To,a dawo lafiya",ya amsa mata da " Allah yasa"ya saka kai ya fice.

      Tayi wanka ta shirya tsaf cikin atamfarta da abbanta ya dinka mata ita kwanaki,dark brown ce da adon mint green ajiki,sosai ta mata kyau dinkin ya zauna mata das a jikinta,falo ta koma ta zauna,jikinta a sanyaye bata san dalili ba,gidan ya mata shiru kasancewar 'yan hirar tata duka ana makarantar boko sai sha biyu da rabi suke tashi.

     Ganin akwai wuta ya sanyata jona kayan kallo,tashar arewa 24 ta kama,cikin sa'a suna maimaicin shirin agent ragab,tana son film din sosai,kusan shi ya dauke mata hankali har sha daya da rabi.

    Gamawarsu yayi dai dai da bugun qofa da ta soma ji,ta miqe ta fito tana tambayar waye tare da nufat soron,tun kafin ta kai ga budewa taji cikin kakkausar murya
"Malama ki bude bana son salo kin wani kama qofar gida kin rufe,bayan kinsan akwai wadanda zasu zo,dadin abun saura 'yan kwanaki naga ta iyayi" da sauri ta qarasa bude qofar domin tuni ta dauki muryar wace,yaya bara'atu ce sai fadima tsaye a bayanta,dai sauran da bata san su waye ba,tasan dai ba zasu wuce dangin amaryar ba tunda ita daga amaryar har 'yan uwanta babu wanda ta sani,iyaka dai tasan cewa amaryar 'yar aminiyar yaya yahanasun ce.

      Saura kadan yaya bara'atun tayi gaba da ita badan tayi gaggawar matsawa gefe ba ta wuceta saura suka biyo bayanta suka bar mazan da zasu shigo da kayan katakon da kujerun.

     Bata qosa ba tabi bayansu zuwa dakin da aka bawa fa'izan wanda tuni yasha fentin farar qasar data siya tayi da kudinta,babu komai a dakin a share yake fes kasancewarta gwanar tsafta ce,tun kafin tace wani abun yaya bara'atun ta galla mata harara yayin da sauran suka mata caa da ido
"Uban me kuma kika biyo mu ki mana?" Ta tambayeta tana huci,qasa tayi da kanta saboda yaya bara'atun ta girme mata nesa ba kusa ba cikin ladabi tace
"Zuwa nayi mu gaisa ne"
"Riqe gaisuwarki bama so"
"Uhmm,wallahi kuwa" fatima tayi caraf ta karbi zancan
"Allah ya baku haquri" ta fada sannan ta juya ta fice kai tsaye falonta ta shige taci gaba da kallonta.

       Miqewa tayi zata dauko wayarta dake uwar daki tana ringing ta hangosu suna kici kicin budw kwadon dake rufe da dakin ya mukhtar wanda da kansa yasa ya rufe ya tafi da abinsa,da taga a kulle yake sai ta saka tana fadin
"Lallai,kaddai yaya mukhtar daki daya ya bayar,tabdi lallai,yana nufin ita a falle daya zata zauna waccar tana da ciki da falo....haka ne....mu shirya mata kayan idan muka koma ma sanar da yaya yahan",bata ce uffan ba don ba mas'alarta bace,ko tata din ce ma basu sako da ita ba.

      Ya mukhtar ne ya kira yana tambayarta komai lafiya ko tace eh sannan sukayi sallama ya kashe wayar.

      Kafin wani lokaci gidan nasu ya cika da 'yan jeren,ko ina sai shewa ke tashi da qananun magan ganu,take tsoro ya cika sumayya,ta dinga kiran lambar maman naana kan ta shigo ta tayata zama amma wayar a kashe take,ta dinga leqe ta window dinta taga ko akwai hanyar da zata ratsasu ta fice.

      Bata samu sararin gurin ba sai da suka fara daura alwalar sallar azuhur,tayi hanzarin shiga uwar dakanta ta dauko hijabinta tare da padlock  ta sanyawa qofar dakin nata ta fice.

     A qofar gida ta tarad da su naana suna tsaye,suna ganinta suka nufota da sauri,ta dubesu tana cewa
" me kuma yau kuke tsaye a qofar gida?"bilkisu ce tace
"Hanamu shiga anty akayi?"
"Waye ya hana ku shiga?"
"Masu jeran amarya"inji nana,take taji ranta ya baci,sam bata son abinda zai taba mata yaran,ba zata juri haka ba sam,bata ce misi komai ba sai
" kuzo muje,qila fitina zaku shiga kuyi musu shi yasa suka hanaku shiga don kada ku bata masu kaya"
"Wallahi anty a'ah" inji aysha
"Shshshshah" sumayya tace da su,sun san me take nufi ko batayi magana ba,bata da son su kawo mata hirar wani dama.

      Gidan mamam naana ta shiga,ta taras da ita tana kwashe abinci cikin kula
"Ina zaku haka ke da gayyar yaran naki,ina kika baro baqin naki,ai yanzu nake shirin shiga kinga girki ya tsayar da ni ina so na kammala na turasu islamiya sannan na shigo" murmushin yaqe tayi ta ja kujera 'yar tsuguno ta zauna daga bakin qofar falon maman nanan,yaran nata suka zazzauna kusa da ita
"Eh wlh,na gaji da zama ni daya nace bari na leqo"
"Banda abinki sumayya aiko baki aiko na shigo miki ba kyayi waya a turo miki halima da zainab ko su tayaki zama"
"Wallahi maman naana bansan haka akeyi ba ai" murmushi tayi tana tausayawa sumayya da quruciyarta
"Ai shikenan,Allah ya bada zaman lafiya,ya kade fitina tsakaninku"
"Amin" sumayyan ta fada cikin faduwar gaba.

     Duka yaran ta zubawa abinci suka ci sannan ta tura kowa ya gida saboda ganin lokacin tafiya islamiya yayi,ta shirya su naana ma suka tafi sannan suka daura alwala sukayi sallar azahar ita da sumayyan.

     Shinkafa da miya har da salad da kifi abinda ta dafa ta zubo musi cikin plate
"Sauko sumayya maza muci" kai ta girgiza don a cunkushe take jin cikinta babu space din abinci
"Na qoshi maman nana" tausayinta ya kamata amma ta dake tayi murmushi
"Sauko muci akwai abinda nakeson gaya miki" bata da jan doguwar magana saboda haka ta sauko ta sanya hannu suka soma ci.

      Cikin hikima maman nanan ke kwatantawa sumayya dabarun zama da kishiya,qissa dabara da wayo kala kala,ta dora da yi mata nuni da haquri,kau da kai kara da alkunya,gaskiya da amana,zama na tsakani da Allah,sai gashi sun tashi da abincin tas,har sai da hannayensu ya fara bushewa da miya saboda sun kasa tashi a gun darussan maman naana sunqi su qare,saiga sumayya na kwasar dariya saboda wani abun idan maman nanan na gaya mata kunya ce ke kamata ko mamaki.

     Hararta maman nana tayi dariya itama nason qwace mata itama amma ta dake saboda yadda taga sumayya na dariya wani abu da ta gaya mata
"Au dariya ma nake baki ko?,zaki ci gidanku wallahi idan baki dauke duk abinda nake gaya miki ba" cikin dariyar ta dafe baki
"Yi haquri maman nana,abunne wallahi" ta kuna saka dariya,kada kai maman nana tayi itama dariyar ta qwace mata,ba shakka sumayya danyace har yau,ta miqe ta dauke plate din da suka gama cin abincin ta fice da shi.
Chapter 6 · 0% Book details