← Book details Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 212 OF 226

Sashe 212

Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari suka shirya shi da ita tsaf don su'ad na nade bata ga wajen fita ba,wani qauye a 'yar gaya dake kano nan ya dauketa suka tafi shi da ita da driver,sai wata motar guda daya a bayansu akwai PA dinshi da kuma wanda ya barwa aikin da zasu je gani a hannunshi,gonaki ne masu fadi da tsaho wanda iya ganinka auduga ce,sosai taji dadin zuwa wajen don ko ba komai zata tattaka,uwa uba kuma ranar garin babu rana,sai da ya gama zagayenshi sannan ta fito suka fara takawa tare,wajen da matan dake musu aikin cire audugar zaije yaga yadda suke,hannunta cikin nashi yana dan tsokanarta yana mata dariya,murmushi take tanajin dadi qasan ranta,tana godewa Allah kullum kwanan duniya da irin mijin da ya bata,bakin wata bishiya suka nufa,Allah sarki matan karkara,rayuwarsu abar dubawa ce,cincirondon mata ne,wasu na aikin wasu na qasan bishiyar suna baiwa yaransu nono,yayin da wasu ke gefe suna hutawa,sosai ta tsurawa daya daga cikin matan dake bawa danta nono tana hira data kusa da ita,yanayi take mata da fa'iza sosai,duk da wannan ta soma komawa tamkar tsohuwa,saidai ga mai dogon nazari da tsinkaye yana mata kyakkyawan duba zai san wahala ce ta maidata hakan da tsantsar rashin kulawa ci sha sutura da muhalli mai kyau.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽

✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

1⃣0⃣4⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*la ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin*
_____________________________________

       Har ta qarasa wajen basu lura ba,sai data tsaya dab da su sannan hankalinsu gaba daya ya dawo kanta,idanu kowa ya zuba mata yana mata kallon qurilla
"Fa'iza?" Sumayyan ta fadi tana dubanta,jin tayi shiru bata amsa ba ya sanyata sake cewa
"Ko ba fa'iza bace?"
"Nice,nice mana" ta fada tana yanqare haqora tare da cire yaronta daga bakin nonon,farinciki fal ranta yau cikinsu su wajen goma 'yar gayu ta mata magana ita kadai har tana nuna ta santa,har ga Allah sam bata gane sumayya ba
"Fa'iza kece haka?" Sumayya ta fada cikin mamaki da al'ajabi
"Eh wallahi...amma na kasa heda fuskar taki"
"Sumayya ce fa....sumayya kishiyarki wadda kuka taba auren mukhtar tare" miqewa fa'izan tayi dafe da qirji tana cewa
"Keeee.....sumayya?,da gaske?" Ta fada tana matsowa kusa da ita ta soma shafa kayan jikinta tana qare mata kallo,sai kuma ta fashe da kuka tana cewa
"Kina nan dama sumayya?,naji labari ashe mukhtar ya rasu?" Cikin raunin zuciya ta gyada
"Mukhtar ya rasu fa'izw,shekara kusan shida kenan"
"Wayyo Allah,dama mukhtar na raye na roqeshi gafarar cusguna muku da nayi" gefe fa'izan ta janye sumayya,kan wasu duwatsu guda biyu dake wajen suka zauna,nan take sanar mata labarinta,bayan fitowarta gidan mukhtar kamar wadda aka yiwa baki ba wanda ya taba zuwa taya aurenta,ko dama can bata da farinjinin samari ko kadan,hakanne ma ya sanya aka hada ta da mukhtar din,sai daga bisani baban yaron dake cinyarta ya fito neman aurenta,wanda yanzu yaransu uku,wannan ne qarami,bayan auren ba komai ta tsinta ciki ba sai wahala,matanshi hudu kowacce ita ke dauke da dawainiyar kanta data yaranta,zai zube musu hatsi ne kawai a rumbu saura kuma ya rage nasu,sosai taji ta tausayawa fa'izan,wato rayuwa kowa da irin jarrabarsa,hakan duk abinda ka shuka dole wataran saika girba,ko ka jawa yaranka gadon wahala su su girbe abinda kaine ka shuka shi,gashi dai taqi uarda ta zauna gidan mukhtar dake cikin birni,yana da matarshi daya da rufin asirinsa qwarai,babu abinda bai dauke musu ba na dawainiyar gida,sai gashi ta fada gidan mai mata uku,banda hatsi bai kula da komai naku ba,ga haihuwa tanayi
"Ya taki rayuwar sumayya?,da alama komai ya miki kyau" ta fada tana qare mata kallp,tun daga takalmin qafarta zuwa lafiyayyen material dake jikinta,dankunne agogo sarqa da jaka,murmushi kawai ta saki sannan tace
"Kowanne bawa da kalar tashi qaddarar,kuma ba shakka duk inda kayi sai ta bika,saidai Allah yakan yiwa bawa sakayya gwargwadon abinda ya shuka,idan alkhairi ne bayan Allah ya gama jarrabaka sai ya maka sakamako mai kyau,haka idan sharri ne ma" a taqaice ta bata labarin komai,ta dinga jinjina kai tana sake nutsuwa tare da dana sani kan abinda ta aikata a baya,nan ta nemi gafarar sumayya,bata da riqo sam ballantana ma ita bata ga abin da za'a riqe fa'iza da shi ba,don baki dayarta abar tausayi ce,yafe mata tai sannan ta bita da alkhairi,ta tambayeta nawa take buqata na jari,wanda zata bar wannan aikin taje ta riqe iyalanta
"Dubu uku ma ni ta isarmin" ta fafa cikin zumudi,baki dayanta kalar tausayi ce,jakarta ta bude,ta zaro dubu goma 'yan dari biyar biyar sababbi ta miqawa fa'izan,ai batasan sadda ta dire danta dake kan cinya ba hannu na rawa
"Don Allah kada kice min da wasa kike" ta fada bayan ta gama qirga kudin,murmushi sumayya tayi tausayinta na kamata
"Ba wasa nake miki ba fa'iza,ki riqe kija jari,don Allah ki baiwa yaranki tarbiyya da kuma ilimi,shine kadai gatan da zaki musu"
"Da izinin Allah sumayya na gode na gode na gode" sai ta fashe da kuka tana sake jaddada godiyarta.

       Daya daga cikin matan ne ta iso wajen tana sanar da fa'iza ta taso za'a biya su kudin aikinsu na yau,sannan mai gonar zai basu wani abu,daa tace ba sai taje ba,sumayya tace haqqinta ne taje ta karba ta hada,baki dayansu suna tattare waje daya,tare suka isa wajen,almustapha na tsaye jikin motarshi,tun dazu yake raba ido yaga ta ina zata bullo,gefan matan itama ta tsaya cikin tausayi take dubansu,tana godeww Allah matuqa kan ni'imar da yayi mata,ba tare da wayo ko qarfinta ba,da idanu ya dinga binta,tausayin da ya gani zallah cikin idanunta ya sake burgeshi,ko da yaushe dabi'arta tasha banban data saura daya saba gani masu shekaru irin nata,take yayi wani quduri cikin ranshi,ba shakka zata dace da a bude mata wata qungiya ta tallafawa mata marasa galihu da koyon sana'o'i,da alheri almustaphan yabi kowaccensu,dukkansu ko sai da suka dara saboda kudin da ya basu,shi kanshi tausayi suke bashi,ina mazansu da haqqin ciyarwa da shayarwa ke kansu suka barsu suna wahala da fadin tashin ci da kansu,sai da suka gama kaf sannan sukayi sallama fa'iza na sake jadda da mata godiya,ta karbi lambar sumayyan tace ko cikin gari zata dinga shiga tana kiranta suna gaisawa lokaci zuwa lokaci.

         Yana nade saman gado yana duba saqonnin hotuna da lamin ke turo masa na gonakin da suke nema yadda noman yayi kyau,lokaci lokaci yakan daga kai ya kalleta sanda take shirin bacci gaban madubi,ya lura tunda suka dawo jikinta a sanyaye yake,haka yake,tana tuna wato rayuwa garanbawul ce,haka sharri tamkar jifa ne,duk sanda ka yishi komai daren dadewa sai ya dawo ya sauka tsakar kanka,a hankali ta hauro gadon,sai ya bar abinda yake ya zuba mata idanu kafin daga bisani ya bude mata hannayensa,dama abinda take jira kenan,ba bata lokaci ta isa jikinsa ta lafe tana shaqar tattausan qamshin da yake fitarwa,bugu da qari tafin hannunta na kan singalalin hannunsa dake cike da gargasa tana shafawa,hakan ya sakashi lumshe ido saboda yadda tsigar jikinsa ke zubawa
"Babe....mai ya sakaki mutuwar jiki haka?,ko baby ne?" Kai ta girgiza sannan ta soma kwatanta masa fa'izan da ya gansu tare,yace ya ganeta,nan ta bashi labarin yanayin da take ciki,shiru yayi yana jinjina mata,ba shakka ba kowacce mace bace haka,ya tabbata da wata ce dariya zatayi tayi shewa kafin ta shelantawa duniya,zata ce Allah ne yasaka mata abinda fa'izan tayi mata,sau gashi ita neman hanyar da zata fiddata daga cikin qunci take
"Kin taimaka mata ai ko?,ba sai an sake wani abun ba"shiru tayi kaman ba zata yi magana ba sannan tace
"A'ah....ranka ya dade da zaiyiwu a qara mata jari,a baiwa mai gidan wani qwaqwqwaran sana'a da zau kula da iyalinshi baki daya"
"Babe.....ta cutar min da rayuwarki fa?" Kai ta kada
"Na sani...amma na yafe mata,tunda gasji daga qarshe ni naci riba,Allah ya yimin kyakkyawan sakamako da gwarzon miji kuma masoyi irinka,daya tamkar da million" ta qarashe maganar cikin wani salo mai kwantar da rai,dariya ya dinga saki sannan ya ruqunqumeta cikin jikinsa yana jinta har cikin bargonshi
"Duk abinda kika ce shi za'a yi" ya rada mata akunne cikin salo na rada kaman wanda zai shide.

  ********   *****   ********

       Washegari shi da su'ad suka wuce jigawa,yayin da ita kuma ta tattara ya nata ta nata sai gida.

       A falo ta tadda mama ita da anty meena suna hiransu tamkar uwa da da,cikin farinciki suka tarbeta,mama kam kallon sumayyan take taba sambarka tare da godiya wa Allah,yaran meena biyu suna makaranta sai qaramin yasir sulaiman mai sunan malam ne,wanda baifi wata uku ba,gida kam yayi kyau masha Allah ya burge sumayya qwarai,ta dinga shiga tana fita tana godewa Allah,har da tsokanar mama cewa bata ga dakinsu ba,dariya anty meena tayi
"Kukam ai an gama yayinku tunda an yaye ku" suka sa dariya baki daya,a nan ta yiwa mama barka,da anty meenan ma baki daya.

      Kusan itama anty meena nan ta zauna da su,ranan bata je gidansu masu jego ba duk da kusan kullum sai taje,sai da zata dora abinci ta fita ta barsu,kafin sannan yaran sun dawo daga makaranta,abin mamaki duka sun santa,don yaya abbakar na nuna musu ita akai akai yana gaya musu sunanta,abinka da yaro da riqe abu,saidai basu sake da ita sosai ba kaman yadda suke sakewa da su halima.

       Tare malam suka shigo da yaya abubakar,kowannensu murna fal cikinsa da ganin sumayyan,sun sha hira sosai har ya abbakar ya gaji ya wuce bagarensa ya bar sumayyan da malam,labari yake ta bata kan irin ci gaban da rayuwa ta samu,yana sake jaddada mata irin soyayyar dake tsakanin baba prof da shi,da kuma yadda ko da yaushe zumuncinsu ke sake gaba yaba habaka,sosai take sake ganin qimar baban cikin ranta,ba shakka shi aboki ne kuma masoyi ne daya tamkar da dubu.
Chapter 212 · 0% Book details