Sashe 175
Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin minti qalilan ta shirya cikin riga da skert na lace,ta yafa mayafi hill shoes ne a qafarta,yana zaune saman kujera qarar takalminta ya sanyashi daga ido,ba qarya tayi kyau,kome ta sanya kyau yake mata,saidai wani kishinta ya rufeshi,gani yake idan ta fita haka kowa ma kalleta zaiyi,bazai iya barinta ta fita hakan na,da idanu yayi mata nuni shigarta bata masa ba,tq kalli jikinta sai ta juya ta koma samam,ta fidda kayan jikin nata tana tunani,bangaren atamfofinta ta nufa,ta ciro wata super,kalarta tayi kyau qwarai,itama riga da skert ne masu fidda shape qwarai,sai ta fitar da lafaya wadda ta dace qwarai da atamfar ta nannade jikinta tamkar 'yar maiduguri,takalmi da jakarta mahadin juna ce,takalmin na da tudu maimakon na dazu mai tsini,sak ta fito a bahaushiyar kanuri tun kafin ta gama nada lafayar,wajen nannadota ta baya hannunta ya gaza kaiwa,tana yunqurin janyo inda ya nade din ta hangoshi cikin mudubin,qarasowa yayi ya sanya hannunsa ya juyo da ita suna fuskantar juna,da kanshi ya qarasa nada matan sannan yaja baya rungume da hannunshi yana kallonta,yana matuqar son tayi shigar arewa,shugar na burgeshi wani lokaci har tafi ya abaya kyau,kwalliya na burgeshi,wani bangare ne na abinda yake so a wajen matarsa,kasa daurewa yayi,ya hada yatsanshi manuni da babban dan yatsansa a hankali ya furta
"Kinyi kyau" murmushi ta sakar masa tana saqala jakarta suka jero suka fito lokaci lokaci yana satar kallonta.
Ko ina mutane ke kai kawo kowa na sabgarshi,saidai duk inda suka gifta sai sun wafci ganin wasu,su burge wasu,masu hassada kuma su tanka,kacibus sukayi da fahariyya wadda tabi sumayya da kallo,tuni almustapha yayi gaba abinshi,dama idan baiso ba ba shiga shirginta yake ba,har gwara ni'imah yana ganin yanayin hakayyarta da hankalinta ya banbanta dana wannan sukan gaisa a mutunce cikin ganin mutuncin juna,fahariyya kam sai yaga dama,don bai daukar raini ko wargi,yanayin nasu ya burgeta saidai haka kawai kishin sumayyan ya soketa,fuskar sumayyan da fara'a ta qarasa wajenta tana fadin
"Ina yini maman hibba?" A yatsine kamar wadda ka yiwa dole ta amsa da
"Lafiya ya kike?"
"Lafiya qalau wallahi,tunda kika iso bamu samu mun hadu ba sai su hibban na gani"
"Oh Allah?,k'nnn,ina ciki ina hutawa"
"To yayi,ki gaida yaran" ta fadi tana juyawa sabida ganin yanayin fahariyyan,yayin da ta bisu da kallo,ba shakka ba haka aka so ba qanin miji yafi miji kyau,a da tana kishi da su'ad wadda mijinta ne kawai yafi nata mijin komai da komai,a yanzu kuma saiga wadda mijin nata yafi nata,hakanan ita dinma ta fita,shi ya bude mata sai da ya tabbatar ta shiga ya rufe sannan ya zagaya ya shiga wajenshi,hakan ya tsayawa fahariyya a wuya,su'ad suna dan dasawa wani lokaci rashin jituwarsu yafi yawa,amma sai gashi yau taba taya su'ad din kishi,ya akayibtayi sake haka ta faru?,lallai bari ta iso,ta fada aranta tana yin gaba ta bar wajen,yana yunqurin tada motar tace
"Su ummee fa,basu san bama nan ba" sai da ya tada motar sannan ya amsa
"Ba ruwansu da mu,we r free".
Baki daya gidan ya tafi da ita,kaf rayuwarta bata taba katarin shiga gini irin wannan ba,gida ne wanda idan baku manta ba yake mallakin almustaphan,wanda babu wanda yasan da zaman gidan banda shi din,a hankali suka dinga ratsawa,basu tuqe ko ina ba sai lafiyayyen bedroom dinshi,wanda kusan dukkan abinda ke jere a ciki ba daga nijeria ya fito ba,bedroom ne wanda kallo daya zaka yi masa kasan cewa mamallakinsa yasan abinda ake kira da TSARI,dole tsarin dakin ya burgeka,komai na ciki fari ne qal,tun daga qwayaye,bed lamp fenti,kayan gadon,labulaye,bedsheet,sofa guda biyu,table na galss,tiles da rug dake ajjuiye can gefe guda,hatta da qofar bayi zuwa ga ac ta girke dake tsaye kusurwa daban ta dakin,tattausan qamshi da sanyi mai dadi ke gauraye a dakin,ya matuqar burgeta,tana tsaye idanunta na kan tafkeken frame mai ruwan gold da aka rubuce ayatul kursiyyu da wani daura da shi da aka rubuta addu'o'in bacci kala kala ya qaraso gareta ba tare data sani ba,a hankali ta maido kanta gareshi,babu wani space a tsakaninsu baki daya ya hadeshi,batasan me yasa yake son ritsata haka ba,baisan nauyin da yake haifarwa zuciyarta ba,jakar hannunta ya sabule ya ajjiue gefe guda,yasa hannunshi duka biyun ya riqe kafadarta,cikin sanyi yace
"welcome to my world" murmushi na fita saman fuskarsa
"I wish zan samu wani gagarumin abun da bazan taba mantawa da shi ba" murmushin itama ta saki,hannunta ya kama yana duban lallenta
"Ya miki kyau,but daga yau jan kawai nakeso,yafi lafiya ya kuma fi yimiki kyau,at d first time da naga wannan abun hannun wata kusa da ni sosai kamar haka,yana muku kyau"
"In sha Allah" ta fadi,sai ya saki hannun ya zamw dankwalin kanta,hannunshi ya dora saman kitson yana shafawa
"Wow,masha Allah" ya fada har cikin zuciyarsa saboda yadda kitson ya burgeshi,ya jima baiga kitso haka ba kan mace,har ya manta cewa mata na kitson,inda ya qarasa girmanshi dai ba kitso suke ba,haka matarshi a nata ganin kitson wai qauyanci ne,tafi ganewa taje a sanya mata gashin da zatayi parking tamkar nata,a haka ya zarce da warware mata lafayar dake jikinta tana tsaye idanuwanta alumshe,sannan ya janyeta zuwa ni'imtaccen gadonshi wai tazo ta nuna masa yadda akayi kitson,daga nan labari yasha banban.
******* ****** ********
Yana zaune abinsa hankali kwance kan kujerun dake falon kamar wanda sam bai da niyyar zuwa daurin auren ma,zirga zirga take tsakanin kitchen da dining area cikin wani hadadden lace da aka yiwa dinkin buba,duk inda ta gifta idonshi na kanga,shigar tayi masa,shi baiqi suyita zama a hakan ba,sam baya son su je gidan,don ya tabbatar zuwa yanzu hayaniyar dake cikin gidan sai Allah,baki daya hankalinta ya soma yin gida,awa daya da rabi ya rage lokacin daurin auren yayi,amma taga shi kamar ma ko a jikinsa,sai data kammala ta tako gabanshi ta russuna
"Breakfast din ya zama ready,nd saura awa daya da rabi fa lokaci yayi" kanshi ya mirgina yana sake kashingida
"Koda babu ni ai ba za'a fasa daura auren ba,ban amshi waliccin kowa ba" kai ta rausayar ta miqe,sai ya janyota cikin jikinsa ya soma shinshinarta,yasa hannu ya ture dankwalinta yana shafa jelar kitson
"Kinyi kyau,wannan kitson ya yimin" sai ya soma yamutsata,wayarshi ita ta katse masa qudurinsa,ummee ke kira sai ya gyara zamanshi,ta tambayi lafiya ne saboda ta aika sashen anata bugu ba'a bude ba,yace komai lafiya,bata tsaya jin komai ba tace to alhamdulillahi ta katse kiran dama lafiyar take son ji,a akasalance ba don yaso ba ya karya sannan ya koma dakin don ya shirya.
Tayi ready,hatta da mayafinta na yafe a jikinta,tukunshi taji,a hankali ta daga kanta
"Fatabarakallahu ahsanul khaliqin" ta ambata har bakinta na motsawa,sanye yake da shadda fara qal dinkin tazarce sai walainiya take,hular kansa baqace kamar yadda takalminsa na kamfanin batozzi halfcover yake baqi,agogon fata dake daure a tsintsiyar hannunshi ma haka,karon farko data soma ganinsa cikin shigar manyan kaya haka,kasa daina satar kallonshi tayi har ya qaraso gabanta
"Mu wuce ko?" Ya tambayeta,ba musu ta miqe din,tana niyyar gaba ya riqota
"Wallahi baki isa ba,u have to say something,na lura shigar na burgeki,nayi saboda ke kice zaki wani fuske" yadfa yayi kicin kicin yaso bata dariya
"Masha Allah tayi kyau"
"Ita tayi kyau ko ni nayi"
"Kaine"
"Allah ya ceceki yau da babu inda zaki fita har sai jibi zamu bar gidan nan" ya fafa yana yin gaba ta biyo bayanshi tana sakin murmushi,tabbas ba qarya yayi kyau,sai ta tuna yadda su'ad ke kishinsa duk sanda ake sha'ani cikin gidan bata so taga ya gifta don kada a kalleshi?,haka zasu ratsa gidan kenan?.
Qarfe tara da rabi taxi dake zirga zirgar kai jama'a daga airphort zuwa gidajensu ta sauke su'ad din qofar gidan baba prof,ta kira layin almustapha tana son shaida masa azo a dauketa don abun kunya ne tana matar fitaccen mutum kamar doctor elmustaphan ta shiga motar haya har ta gode Allah bai daga ba,dole daga qarshe dai ta dauki drop din motar ta kawota gida,wanda ta mance when last data shiga motar haya a rayuwarta cikin nijeria ko da a america ne sai ta kama take shiga din,tun daga harabar gidan take ganin al'umma saidai babu wanda ya isheta kallo,a haka ta dinga ratsawa dauke da jakar ratayenta qatuwa,ko baba mai gadi da ya matso yana mata sannu da zuwa da niyyar kuma amsar jakar hannunta ya kai mata bangaren nata bawai don mutuncinta ba,saboda daraja da girman baba da almustapha ne,wani matsiyacin kallo ta watsa mata tana tsartar da yawu
"Kada ka soma matsowa inda nake,bastard" ta fadi tana wucewa ciki,kusan duka wadandanta taras 'yan zafin kaine saboda haka ba wanda ya kulata har ta shige bangarenta,hakan ya mata ciwo,dama ga zargi fal cikin ranta sai take ganin da gayya aka mata hakan.
Sauyin yanayin qamshi da ya samu falon ya tabbatar mata da zarginta na ba shakka almustapha na abuja,kuma tare da yarinyar,tunda ta kira layikansa na nan qasar duka sun shiga,wanda abaya idan bai naija layinsa baya shiga saidai ta gwada na wata qasar,kai tsaye ta nufi samanshi,ta tura dakin ta shiga,neat dakin yake,saidai shima akwai cakuduwar wani qamshin bayan qamshinsa data sanshi da shi,wanda bata raba dayan biyu qamshin yarinyar ne,kishi ya lullubeta,wai ya akayi haka ne?,me yasa ta tafi har ta basu sararin cakufuwa danjuna haka cikin kwanciyar hankali,me yasa bata zauna ba ta daga musu hankali,kowa ya qeaci almustaphan idan zai iya,wanda tana da tabbas ita ke da nasara,sabida tana da gogewa da wayewar da zata iya aiwatar da haka,yanzun ma ai bata makara ba(a cewarta)sai ta ja qofar dakin ta rufe ta nufi nata dakin,komai yayi qura,bata jin zata iya amfani da dakin,dole ta samu ma'aikatan gidan su gyara mata,sabida haka ta koma dakin almustapha ta sake wanka ta shirya cikin wando wanda daga same yake a dame,daga qasa kuma wajen qafafun ya bude sosai,riga ta sanya spaghetti hand wadda ta dameta dai dai jikinta,gashinta ta taje ta daureshi,sannan ta janyo takalmanta masu tsini hade da igiy kamar zata tsokale idanun duniya ta daura,'yar hula ta samu ta sanya akanta wai din idon jama'a sannan ta feshe jikinta da turare ta sauko qasan tana fatan shigowar almustapha bada dadewa ba don daidaita tsakaninsu.