← Book details Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 194 OF 226

Sashe 194

Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai ya moreta tamkar wani mai biyan bashi,sam bata isarshi ko yaji ya gaji da ita,kamar ana sabunta masa ita ne,tana kwance jikinsa baki daya gabbanta sun mutu,amai ya dinga taso mata,ga yunwa da take ji,bata ankara ba ta soma sheqashi,ya miqe da hanzari ya riqeta gam,sai data amayar da duk abinda taci,tana jikinshi bai damu da yadda ta bata shi ba,sai daya gyara mata jikinta sannan ya gyara gadon ya sauya zanin gado ta koma can,yace ta zauna ta huta kafin ta sake kwanciya
"Abinci" ta furta a hankali,da kanshi ya shiga kitchen karon farko ya dumama mata a na'ura sannan ya kawo mata,yana zaune opposite dinta yana kallon yadda take cin abincin hannunshi rungume a qirji,zallar tausayinta ke ratsashi,bai taba zaton haka mata ke dawainiya da shan wahala da ciki ba sai yanzu,a haka har wasu ke iya yadda ayi musu cikin shege?,su haifan yaro su iya yarwa?,ko su bayar?,ko su kashe shi da kansu?,sai ya tuna gidajen marayunshi da irin yawan yaran da ya qunsa,
"A irin wannan halin kikeso na tafi na barki ke daya?" Ya samu kanshi da furtawa a sanyaye ba tare da yasan furucin ya fita ba,dubanshi tayi itama cikin sanyi tace don kewarshi ta fara bugunta tun jiya
"Haka ummi suka tsara,nasan saboda qaruwarmu sukayi hakan,kuma na tabbata ummi zata kula da ni fiye da yadda zaka yimin,dukkanmu ta fimu sanim zafin haihuwa" ko yaushe kalaman girmama iyaye daga bakinta sune gaba dan komai,idanunsa ya lumshe yana jin kamar yace ya fasa tafiyar,ji yake kamar zasu rabu ne ba zasu kuma ganin juna ba,da sauri ya kori wannan mummunan tunanin daga ranshi tare da yin ta'awizi.

*saura naji an zage mustapha tsaf,lol😂😂kada kuyi qorafi,duk dadin zamanku wataran dole a samu sabawa juna*

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽

✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

9⃣7⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah madaukakin sarki yana cewa*

*haqiqa Allah ma'abocin falala ne abisa mutane,saidai,yawancin mutane basa gode masa*
______________________________________

        Wani dare suka gabatar wanda kusan rabinshi basu samu bacci ba,sai da suka idar da sallar asuba wanda shi yayi limanci sannan wani bacci mai nauyi ya dauketa,dubanta ya dinga yi saman abun sallahn,tausayinta yake ji,daren jiya kawai amma sai yaga ta fada baki daya,kanshi ya dauke a hankali yana ci gaba da karanta azkar dinshi.

         Bugun qofan aka soma yi a kai a kai,wanda hakan yayi sanadin farkawar sumayya,a hankali ya miqe yana mamakin waye wannan,bude qofan yayi,su'ad ce tsaye cikin kayan bacci tana jifarshi da murmushi
"Lafiya?" Ya tambayeta cikin mamaki,fuskarta dauke da murmushi tace
"Cewa nayi ko zaka zo muje ka shirya" waiwayawa yayi ya dubi agogon dake manne bangon dakin,baki daya qarfe bakwai da minti hamsin da hudu na safe,sai ya maida kanshi wajenta
"Halan baki ji qarfe nawa nace miki zamu tafi ba ko?,sha biyun rana shine har zan fito ma shirya yanzun?" Kasaqe tayi,tayi nufin janyeshi ne,yadda sumayyan ba zata sake ganinshi ba,wataqila ma sai bayan sun dawo
"Shikenan" ta fada gwiwa a sage tana juyawa,ya maida qofar ya rufe sannan ya tako zuwa cikin dakin,tana zaune tana murza yatsunta a inda ta tashin,da alama ba isarta baccin yayi ba bugun shi ya tasheta
"Ina kwana" ta gaidashi kanta a qasa
"Lafiya lau,ya jiki" ya tambayeta yana komawa inda ya tashi ya sake zama
"Alhamdulillah" ta maida masa tana miqewa,toilet ta nufa ya bita da kallo har ta shige.

*Bayan awa hudu*

Kwance take lamo cikin dakin dake bangaren ummi wanda ta ware mata,tun bayan awanni hudu da tafiyarsu babu abinda ta iya tsinanawa sai juyi da take daga farkon gadon zuwa qarshenshi,ba wani loko ko saqo dake jikinta wanda kewarsa sonshi da qaunarshi basu bi sun illata mata ba,hango sallamarsu take da kuma sallamarsu tsakanin shi da ita,hawaye ya gangaro mata ta sanya hannu ta sharce,har ya tafi tana iya hango damuwa qarara kan fuskarshi,furucinsa na qarshe sanda ya sanyata cikin jikinshi suna sauraron bugun zuciyar junansu
"Ki taimakeni ki bini.....ki cewa ummi zaki" a sanyaye ta girgiza kai duk da tana kwance qirjinshi
"Bazan iya ba.......kunya nakeji....kayi haquri" bai sake cewa uffan ba face zareta da yayi daga jikinshi,ya fiddo kudi da kuma daya daga cikin ATM dinshi ya ajjiye gefanta,ya tsugunna gabanta a hankali ya yaye rigar jikinta zuwa saman cikinta,ya dora tattausan lebbansa ya sumbaceta sannan ya miqe,duka wannan abun da yakr yaqi yarda ya dubeta kamar yadda take nacin duban qwayar idanunshi,a hankali cikin takinshi ya juya har ya fice daga dakin idanunta na kanshi.

Ba irin sallamar da takeso suyi ba kenam,saboda haka tunda ya fita take faman kiran layinshi saidai ba'a daga ba,bata daina kira ba har sai da aka tabbatar mata wayar a kashe take,abinda ya sake karyar mata da zuciya kenan har yanzu yake fidda hawaye,zuciya da gangar jikinta baki daya a quntace suke,wunin ranar baki daya a quntace tayi shi,duk da yadda ummi ke nan da nan da ita,duk abunda take buqata dama wanda bata buqata ta tanadar mata shi.

Bata sake tabbatar da cewa lallai almustapha ya zama wani sashe na rayuwarta ba sai da dare yayi,baki daya bacci ya gudu a idanunta,fafur yaqi zuwa,dole ta shiga bandaki ta daura alwala ta yi sallolinta yadda zata iya,duk juyin da zata yi sai ta dibga hangoshi gefanta sanda yake bata kulawa,cikin jikinta take jin tamkar ta rasa wanu babban sashi daga jikinta.

Washegari kallo daya ummi tayi mata ta fuskanci batayi bacci ba,wannan dalili ya sanya ta sanyata gaba sai data tabbatar ta samu isashshen bacci,ta sani fushin mijinta ke damunta,saidai baki dayansu kuwa suyi haquri,don ba zata taba bari wani abu mara dadi ya faru ga sumayya ba,idan da ace su'ad din mai aiki da tunaninta ne babu abinda zai sanyata rabasu,zata barau suyi tafiyarsu tare,amma a irin wannan qadamin da ake ba zata lamunci tafiyarsu wata uwa duniya ba a sanda sumayyan ke da buqatar taimako,a yammacin ranar iyalan adam suma suka shirya komawa lagos wajen mijinsu,sumayya na zaune falon ummi tana kallon wani comedy,babu abinda ya dauke mata na daga kewarshi da take,saidai ya dan dauke hankalinta,anty ni'imah ce ta shigo cikin shirinta,sanye take da doguwar riga ta atamfa da yalwataccen mayafi,bayanta hibba ce da hibban,sai nasrin da take riqe da hannunta,yaran baki dayansu sanye suke da qananun kaya,sam gori da rashin mutuncin fahariyya bai hana anty ni'imah riqon 'ya'yan tamkar ita ta haifesu ba,bugu da qari ya adam din tsayayye ne a tsaye yake hakan shi ya sauqaqa tsiya da wariyar launin fata da fahariyya taso koyawa yaran,fuskokinsu ita da sumayya dauke da murmushi suke gaisawa,su hibba suka gaidata suka shige kitchen kiran ummi,murmushi ni'imah ta sakeyi tana duban sumayya
"Sannu anty amarya(yadda yaran sukan kirata wani lokaci kenan),ashe qaruwa muka samu" a kunyace sumayya tayi murmushi ba tare data amsa ba
"Allah ya inganta ya raba lafiya ya kawo na 'yan baya" nan ma bata masa ba saboda kunya,dubanta tayi
"Ina miki addu'a kice amin wallahi,haihuwa ai babbar ni'imah ce" ta fada wani abu na taba ranta,yanayin fuskarsa ya dan sauya,dubanta sumayyan tayi tana karantar yanayinta,wani yanayu data taba tsintar kanta can baya shekaru biyar zuwa shida a baya ya soma dawo mata,tasan me take ji,ba shakka ba kowanne mutum ke iya fuskantar yanayin da mata irin su ni'imahn ke ciki ba sai wanda ya taba tsintar kanshi ciki,al'amari ne mai taba zuciya da tsayawa a ran dukkan wata diya mace sata tsinci kanta cikin irin wannan jarabawar,sai ta tsinci kanta da kamo hannun ta,ta daga kai suka hada idanu,tuni qwalla ta cika idanun ni'imah,qaqalo murmushi tayi sumayya ta maida mata
"Kada ki damu anty ni'imah,lokaci wataran sai kinga gamkar ba'ayi ba,kinsan na taba tsintar kaina cikin yanayin da yafi naki muni?" Cikin mamaki take duban sumayya,kai ta jinjina mata alamar tabbatarwa
"Kan na samu abdallah na sha wuya anty,ba wanda ya taba tsammatar abdallah zaizo duniya....amma yanzu fa.....kinga kamar ba'a yi ba ko?,to kema kusan hakane in sha Allah"
"Allah ya amsa amiran yaya musty...don yanzu bata umman khalipha bace" ta fada tana qoqarin maida qwallarta tare da jin sanyi cikin zuciyarta da addu'ar da sumayyan tayi mata,daidai sanda ummi ta fito tana cewa
"Wai tafiyar ce ne?"
"Eh wlh ummi" anty ni'imah ta fada cikin girmamawa tana murmushi,qarasowa ummin tayi ta zauna sukayi sallama,sannan ta miqe suja fice sumayya na dagawa su hibban hannu.

Da dare sai ga babbar 'yar anty farida sajida,ummu tasa aka daukota duk don sumayya taji dadin zaman gidan,tunda gidan ya dade babu kowa,sajida akwai hankali nutsuwa da wayo,hakan ya sanya sumayya ta fara jin dadin zama da ita sosai,akwai surutu,a qalla zatayi shekara goma sha biyu,ta nan gidan take tafiyarta makaranta,idan ta dawo sumayya tayi mata qarin karatun addini,tunda a sannan an musu hutun islamiyya.

*Bayan sati daya*

Sha biyu saura na sare tana saman gadonta,sajida na gefanta kwance,tuni ta jima da yin bacci,kamar kullum tunaninsa ke faman yi mata kaikawo cikin zuciyarta,idan har cikin sati gudan tace ta samu walwala ta minti biyu tayi qarya,duk da tsantsar kulawa da take samu daga bangaren mutane ukun nan,ummi anty maamaa da shi kanshi baba prof,tun daga randa ya kira ummi ta sanya dukkan kulawarta kan wayarta ko zata ga kiranshi amma babu shi ba alama,ko saqon tafi da gidanka bata ci nasarar ganin gilmawarsa ba daga gareshi balle kira,kusan sau uku tana jinsa suna waya da ummi amma bai taba nemanta ba,wayar tata ta janyo ta bude tana duban lambobin wayarshi data dauka daga wayar ummi,amma gefe daya na zuciyarta ya hanata kiranshi,akan me ma zata nemeshi bayan shine a haqqu daya nemeta,ya sani ai tana son binsa amma dole subi umarnin na gaba da su,haka taci gaba da juya wayar a hannunta wanda ba jimawa wani zazzafan a mai ya taso mata,tuni ta miqe cikin hanzari,saidai bata kai ga kaiwa toilet ba ta durqushe a nan ta soma kelayashi ba qaqqautawa.
Chapter 194 · 0% Book details