← Book details Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 226

Sashe 51

Kundin Kaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan saman kujerar ya sameta zaune tana shafawa tare da jajjabin kuncin da ya mareta wanda lafiyayyun yatsunsa suka fito rada rada tamkar an zana su,bata lura da fitowarsa ba sai da flower vase din dake kan t.v stand ta fado ta fashe saman tiles sanadiyyar finciko wayoyin dake jikin kayan kallon ta ankarar da ita,nufota ya soma yi wanda hakan yayi matuqar firgitata,gaba daya kamanninsa sun sauya mata,ganinsa take kamar wani mayunwacin zaki yaga abun farauta
"Me kake shirin yi mukhtar,kada dai kace dukana zakayi"
"Idan akwai abinda yafi duka yau zaki dan dana shi,inaso gangar jikinki ta fara dandana azaba kafin na kai ga ruhinki,yau zakiyi dana sanin raba masoya,daga yau ko a shirin film aka ce ki fito a matsayin jarumar dake raba masoya ba zakiyi marmari ba"
"Amma dai kasan......." Sai maganar ta katse sakamakon ihun da ta tsala saboda kyakkyawan masauki da wayar ta samu a gadon bayanta,duka kota ina ya dinga kai mata,baki daya ya fice hayyacinsa kamar yadda itama ta fara dan dana kudarta,duk duka daya da zai kaimata sai ya tuno baqar azabar da sumayyan ta sha a wancan lokaci,tun zuwan zainab din gidan har ya zuwa ranar data kwanta gadon asibiti,ranar data zamto rana ta qarshe a tarihin zamantakewar rayuwar aurensu.

Duk inda ta nufa da nufin samun mafaka ko maboya sai ya bita,tuni takalman qafarta sukayi nasu guri daban,haka dankwali da mayafinta,ganin abun nasa na gaske ne babu alamun sassauci yasa ta fara bashi haquri,saidai sam baya fahimtar me take fada,sai bada haqurin ya zamo tamkar tana qunduma masa zagi ne a gurinsa.

Tun zainab na iya ihu da neman agaji har muryarta ta dakushe,tuni fuskarta ta cabe baki daya,kwalliya tayi nata guri,baka iya tantance ina kwalliyar tata bare fuskarta,babu inda bai fasa ba ajikinta har wani sashe na kayan jikinta ya yage saboda tsantsar dameta da kayan sukayi,jagaf ta jiqa kayanta da gun da ta dinga malelekuwa da fitsari,wurgar da bulalar yayi gefe kamar yadda zainab ke yashe gefe daya tana fidda qwalla hadi da numfashi,sai yau ta yarda da maganar hausawa na cewa kuka ma rahama ne,gashi a yanzun bata da qwarin ma fidda sautin kukan,azaba take ji na shigarta takowacce kafa ta jikinta,dukan da tunda tazo duniya ba'a taba yi mata kwatankwacinsa ba duk da kasancewarta yarinya gagararriya tun a wancan lokacin,yana haki numfashinsa na fita da qarfi saboda tsananin bacin rai,ji yake kamar ya shaqeta ta mutu ya daina kallonta,duk duba daya da zaiwa fuskarta tsanarta ke ninkuwa cikin ruhinsa,ba shakka wannan duka babu abinda ya rage cikin zuciyarsa na daga bala'in da yake ji,qafarta daya ya kama ya bude qofar falon ya dinga janta tamkar kayan wanki,bai direta ko ina ba sai bakin qofar gidan,ya koma ya kwaso tarkacen takalmi jaka da mayafinta ya watsa mata,yana tsaye a kanta ya nunata da yatsa
"Ba qarshen hukuncinki kenan ba,ki jirayi abinda zai biyo baya" ya fada yana juyawa cikin gida.

Wani irin jiri ya dinga kwasarsa,da qyar ya kai kansa cikin dakin baccinsa inda abdallah ke baccinsa lakadan baisan meke faruwa ba,gefansa ya zauna ya zuba masa idanu yana kallonsa cike da tausayinsa tausayin kansa da kuma tausayim sumayya baki daya,tambayar kansa yake ta yaya ya yarda sumayya zata iya aikata haka ma wai?,sumayyarsa ce fa?,rainonsa ce,tarbiyyarsa ce,yaya akai har ya gaza bincike tashin farko ya yarda ya dora zarginsa kan halittar da bai taba samunta da cutar da wani qwaro ba ballanta na mutum dan adam mutum din ma shi mukhtar,mukhtar dinta,wannw iri kaidi ne mata suke da shi haka?,wanne irin halakakken kishi ne wannan?,yunqurin kisan kai fa kenan a taqaice,ta yaya zai ga sumayya?,ta ina zai fara neman yafiyarta?,da wanne ido ko fuska zai kalleta?,shi kansa baisan amsar dukkan wadan nan tambayoyi ba,haqiqa ya cutar da ita,ya cutar da zuciyarta,babu shakka shi yasa tun daga ranar da ya saketa bai sake samun sukuni nutsuwa ko farinciki cikin zuciyarsa ba,ya sani haqqinta ne Allah bazai taba barinsa ya huta ba bayan ya cutar da ruhin dake masa qauna ta domin Allah,sai kawai ya dafe kansa da hannu bibbiyu wanda yakejin kamar zai tsage,kuka ya saki mai tsuma zuciya hawaye na bin fuskarsa,fata yake ya samu sauqin azabar da zuciyarsa ke masa,fata yake ya samu salama qirjinsa ya bar suya,baisan wanne hukunci ya dace ya sake yiwa zainab ba,ba shakka wannan hukunci yana ji har cikin zucuyarsa bai gamsar da shi ba yayi kadan.

_kuyi haquri da wannan_

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

4⃣3⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*fazakkir fa innaz zikra tanfa'ul mu'uminin*

*_KA TUNATAR DOMIN TUNATARWA TANA AMFANAR DA MUMINI_*

_______________________________

         Nan gefan abdallah ya kwanta yana ci gaba da kuka tamkar wani qaramin yaro,jin zuciyarsa yake kamar zata fashe,janyo abdallah yayi cikin jikinsa yana magana qasa qasa mai cike da kalmomin nadama yana ci gaba da kuka.

          Sai da rana ta soma bugun naman jikinta sannan ta iya miqewa a daddafe ta yafa mayafinta,takalmi kuwa basu sakuwa a hannu ta riqesu hadi da jakarta,da qyar da jan qafa ta kai kanta titi ta tari adaidata sahu ta hau duk da cewa bata da qwadalar da zata bashi,qofar gidansu ya sauketa tace ya jira ta miqo masa kudin,tana sallama ta zube a tsakar gidansu tana maida numfashi,mamarta dake wanki bakin fanfo ta dago tana dubanta,mamaki ya cikata saidai bata da ikon tambayar ta abinda ya sameta,murya can qasa da qyar ta qwalawa qanwarta kira
"Idan akwai naira dari jakarki fita waje ki bawa mai adaidaita sahu,mama dora min ruwan zafi" kowannansu da to ya amsa mata,maman ta saki wankin ta shiga kitchen.

      Gashi tayiwa kanta sosai tamkar kai jego,tanayi tana runtse ido zuciyarta na zafi da quna,tana tuna yadda mukhtar ya dinga jibgarta kamar wanda ya sayi jaki mai taurin kai,dakinta ta koma ta shafe jikinta da man zafi ta samu ta kwanta sannan ta janyo wayarta tayi kiran abokiyar shawara da shaidancinta zinatu,tana dagawa ta buqaci ganinta,cikin sa'a kuwa tana kusa.

      Cikin mintuna qalilan zinatun ta iso,suka gaisa da maman wanda ke zaune tsajar gida tana shirin dora abincin rana,da kallo tabi zinatun har ta shige dakin,
"Lafiya?,na zaci zaki cemin gaki gidan mukhtar anyi kome sai nazo na sameki kina tashi da qyar haka?"baqinciki ya sake tokare zainab,cikin bacin rai ta soma fadin
" ni malam zai ciwa kudi zinatu,ni zai ha'inta?,kalli jikina ki ga abinda mukhtar ya yimin duba zinatu"
"La la lal" shine kawai abinda zinatu ke fada tana gyada kai
"Garin yaya haka zainab" tas ta kwashe yadda komai ya faru ranta na quna ta qunduma ashar sannan ta dora
"Ba sai na warke ba gobe gobe zamu koma wajen malam,wallahi sai na nuna masa ni 'yar tasha ce,duk abinda ya buqata nayi masa,kwana nayi yana sasukata duk warin dake tashi a jikinsa amma ban damu,shine ni kuma zai rainamin wayo an gaya masa ni gara ce,to wallahi Allah ya nuna mana gobe shege ka fasa" haka ta dinga bambami zinatu na tausarta da haka sukayi sallama da niyyar gobe da sassafe zasu dirarwa malam

  *******  *******   ******

       Tana zaune bakin gadonta tana ninke kayan sawarta a hanakali,tunanin abdallah na kai komo cikin ranta tun safe,tunda ta haifeashi basu taba rabuwa daidai da kwana guda ba banda sanda ta yayeshi sai wannan lokacin,yanzu haka watanni kusan shida kenan bata sanyashi a idanunta ba,gidan nasu yau shiru yake tun safe har yammaci,hajiya na bangarenta yau bata jin dadi,tunda ta kammala mata girki sai ta barta ta dan kwanta ta huta,karima ta hada kan yaran sun tafi sunan qanwarta data haihu,bata kuma bar nuwaira ba haka ta kada ta suka tafi tare,yaran baki daya sunci ado banda ita,a haka da sauqi tunda sumayya ta tattara dukkan yagaggun kayanta ta boye ta hanata sakasu tafiddo mata da wasu,haka karima ta haqura bayan sa'insar da suka sha da sumayyan,a yanzu bata da goyon bayan hajiya lukman kuma bai gari yayi tafiya bare ta hadata da shi.

        Hudu da rabi na yammacin taji sallamarsa bakin qofar dakinta,a hankali ta daga kanta tana dubansa,ta mance yaushe rabon data sanyashi a idanuwanta tun kafin yayi tafiyar nan wadda ita kanta satinsa biyu kenan baya nan,sanye yake da shadda dinkin tazarce da hula saman kansa sai takalmi sau ciki,kafadarsa rataye da jaka ta matafiya,kallonta yake yana mata murmushi
"Sannu da zuwa" ta fada tana gyara daurin dan kwalinta
"Yauwa sumayya,ya gidan?" Ya fada yana zama gefanta yana mai ci gaba da kallonta
"Lafiya qalau" ta fada tana hada kayanta waje guda tare da miqewa ta zura hijabinta tana shirin ficewa
"A'ah,ya haka kuma,ya zaki fita ki barni"
"Au da dawa nake barinka" ta fada tana gyara zaman hijabinta gami da kallonsa
"Amma dai ai yau gidan babu kowa ko?,wa zai kula da ni?"
Qugu ta riqe tana duban idanuwansa
"Sai babu kowa cikin gidan sannan nake da amfani a gunka?,to gun hajiya zani na dubata na barota bata jin dadin"damuwa qarara ta gani ta bayyana kan fuskarsa karo na farko kan maganar da ta shafi mahaifiyarsa
" subhaballahi tun yaushe?,muje na ganta"ya ajjiye jakarsa ya miqe yabi bayanta.

       Ganin yadda ya damu qwarai ya sanyata cewa
"Ba wani ciwo me mai zafi ba,qafarta ce kawai ta motsa"tayi furucin tana kallon gabanta,ajiyar zuciya yayi bai sake cewa komai ba har suka qarasa dakin hajiyar.

      Tana kwance a falo da alama sallah ta idar,sosai tayi mamakin ganin lukman din wai tazo dubata,saidai bata nuna masa ba,suka gaisa fuskarta a sake,shi da itan duka wani dadi suke ji,sai gashi suna hira kadan kadan,hatta da sumayya sai data dinga jin dadi,ta dade da sanin dadin da iyaye ke da shi a gun d'a,hakanan zuwa yanzu tasan yadda uwa ke jin dadi a duk sanda ta daga ido ta kalli danta ko diyarta cikin kyakkyawan yanayi.
Chapter 51 · 0% Book details