Sashe 68
So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta lura da yadda yad an tsorata, aikuwa tana gama parking a compound jikinshi ya fara karkarwa ya ce Ummi dan Allah kar ki gayawa Ammi komai. Ko kallonshi Huda bata yi ba ta ce Ai naga ni ka rainani! Jiyan nan ka gama yi min alk awari amman fad a har biyu yau kad ai? Haba Arshaad! Shiruu ta yi kamar mai tunanin wani abu kafin ta ce Ka san wani abu? Bata jira ya Bata amsa ba ta ce Na ma daina kiran ka da Arshaad daga yau dan baka yi halin mai sunan ka ba wallahi, dan haka chanja maka suna zan yi In maidaka mai sunan me gadi! za ka sha mamaki. Takaici da zafin zuciya dan har yanzu fushi yake da waenda sukai fad a yau bai gama hucewa ba yasa ya fashe da kuka. Dai dai nan Auwal Aslam da Arshaad suka shigo compound d suna hira suna raha da dariya Arshaad, yad an yi k iba kad Auwal kuma ya tara k asumba da gemu kamu d aya Aslam kam ba abunda ya k ara ba abunda ya rage. Tun kafin su k araso Yaron ya tafi wajen Arshaad da gudu ya fad a jikinshi ya ce Uncle kaga wai Ummi za ta maidani mai sunan me gadi! Sai da sukayi dariya k asa k asa tukunna Arshaad d in ya d an b ata rai ya d auke shi ya ce Eh to Ni na bata shawara saboda naga ka cika fad a sosai. Ai kuwa nan ya rikice da kuka. Dariya kawai Aslam da Auwal suka yi sukai gaba suka barsu. Sai da Aslam ya k arasa wajen Huda ya d an shafa fuskarta da tirtsetsen cikin ta tukun ya ce Baki je wajen Jalilan ba kenan Sai da tad an kalli Arshaad da takwaranshi tukunna ta ce Abhu, Gaskiya ya kamata yau a saka Yaron nan a gaba a yi mishi fad a sosai wallahi, saboda shi na dawo, dambe har da almajirai a waje sabida Allah. A hankali Auwal wanda ya d auka mai sunan Dad ya ce Mu je ciki yau inga har duka sai ya sha Ya fad i hakan yana mai wucewa ciki. Dariya Aslam ya yi ya ce Kiga yadda yake wani had e rai kamar ba a wajen shi ya gado ba Um um fa! Yarintar shi kad ai ka gani baka san na mamansa ba Hudan ta bashi amsa. Murmushi duk suka yi Huda ta wuce shi kuma ya juya wajen su A ish waenda suka gama kwasar lunch box da jakankunan su. Murmushi ya yi ya d aga A ish sama ya ce Mamana ya school ke ba kya fad a ai ko? Sai kuma da sauri ya sauk eta ya d auki Anum yana cewa sorry kakata yi hak uri na manta na yi alk awarin yau ke zan fara kulawa. Da d an k arfi Huda ta ce Kar ki yarda ya yi miki dad in baki Tana mai wucewa bayan ta kamo hannun Abbakar k anin su Arshaad wanda yake a kindergarten suka shige ciki Sakina taso ta yi mishi shegen duka bayan ta gama jin bayanin abunda ya yi yau dan ta zo wuya da halinshi amman sai Aslam ya jata gefe ya yi mata Nasiha.. Nutsatsen fad a sosai suka taru suka yi mishi dan har Jihad Arshaad ya kira ta zo itama saboda Yaron yad an shak u da ita itama dan tun yana zuwa hutu wajen Arshaad a Uk suke video call da ita, lokacin da su Sakina suka tafi course d insu kuma a gidansa ma ya zauna gaba d aya ko da yayi aurenma tare suke har lokacin da suka dawo Nigeria tukun ya gudu gidan su Huda dan sam baya san zama waje d aya da Ammi saboda ya san zai yi laifi itakuma zata dake shi ta yi fushi da shi duk da yanayin rigimarshi amman yana tsananin k aunar iyayenshi shiyasa baya son yaga tana fushi da shi. Sannan baya son fad a da duka. Haka nan suka had u su shidda! Da turanci da Hausa da larabci duk aka yi mishi fad Kuma da alamu fad an ya shige shi sosai. Tun daga ranar an d an samu ya nutsu amman ba a yi cikakken wata d aya ba ya koma ruwa dan haka kawai suka bishi da addua..... Sai da bikin su Shuraim da Sumayya ya rage saura sati tukunna Aaima suka zo dan a Abuja itama take tun aurenta. Ya yanta uku biyu maza Farouk da Bashir sai auta Aisha. Tun aurensu har kawo yanzu cikin kwanciyar hankali suke sai dai y ar rigimar Mata da Miji wanda wannan normal ne a ko wanne aure. .... Sai da Ya Ja afar ya yi shekara biyar tukunna aka samu ya dawo dai dai, idan ka ganshi yanzu ya nutsu sosai kamar ba shi ba. Yana fitowa Junaidu ya bashi jari aka nema mishi mata ya yi aure shima y ar bazawarar da Baba ya aura y ar garin Katsina dutsanma bafulatana. Umma har yau tana nan jiya i yau! A nan gidan Baba da Junaidu ya rushe ya sayi filin bayansu ya had e ya yi musu ginin zamani take itama amman b angarenta daban ita da masu aikin da Junaidu ya d auko suke kula da ita. Wani lokacin Huda idan ta je dubata har kuka take yi saboda Umma ta zama abun tausayi. Duk k asar da take ji da kwararrun likitoci Junaidu sai da ya kaita an yi maganin Hausa da turanci amman har yau babu ci gaba sai ma abun da ya k aru dan wasu lokutan har duka take yi. Anty Zainab itama bata koma gidan Mijinta ba! Ganin tana zaune haka ba wanda ya fito mata yasa itama Junaidun ya bata nata jarin suke zaune ita da Baaba Talatu a gidan Kaka wanda nan ma ya gyara musu sosai. Idan ka ga Jalila ba zaka ce ta tab a yin rashin ji ba! Ta nutsu sosai. Bayan aurenta sai da ta yi sauk a yanzu haka a islamiyyar da Mijinta ya bud e take koyarwa. Ta rungumi Mama a matsayin Uwa Sakina da Huda da Sumayya kuma a matsayin y an uwa sannan ta rik e Mijinta wanda ta fahimci shine gatanta kuma shine masoyinta na gaskiya. Tabbas Jalila tana cikin matan da za ace sun yi sa ar samun Miji mai tsananin k auna da tausayinsu tsakani da Allah. Wani lokacin har ce mishi take yi ya k ara aure saboda duba da a yanda ya sameta ita! Amman duk sanda ta yi mishi wannan zancen sai taga fushinshi a cewarshi shi ita yake so ba wani abun ba kuma ya tabbatar ba zai tab a iya had ata da wata y a mace a zuciyarshi ba. Ibraheem irin mazan nan ne masu zuciya Mahaifiyarsa ta rasu itama two years back k anwarsa ma ta dad e da yin aure. Dukda Ubangiji ya rubuta mishi rayuwar middle class zai yi hakan bai hanashi siya mata y ar k aramar mota ta mata ba! Sannan ya tashi daga gidan Junaidu ya yi gidansa Ita ma kuma tana business d in kaya daga India Dubai wanda Junaidu ne yake kawomata duk zuwanshi, itanma kuma ta tab a zuwa sau d aya da kanta ta je ta sari kayan ta dawo bayan Hajji da Umara da Junaidun ya biya musu suka je ita da Mijinta tun farko farkon aurensu. yan ta biyu mace da Namiji, ta farkon sunanta Maryam mai sunan Huda tana ce mata didi na biyun kuma mai sunan Kaka, Bashir. Sai kuma tsohon cikin jikinta maybe su haihu tare da Huda ko kuma Huda ta rigata. Tsakaninta da Aaima akwai zaman lafiya da friendship da mutantanta juna ga zumunci...... Tunda aka fara bikin su Sumayya Hudan take nak uda sama sama.. Sanin da ta yi lokacin haihuwar ta bai yi ba yasa kawai ta yi shiru a tunaninta juyi ne! Sai dai ranar da za a kawo Amarya jikinta ya motsa sosai! Dama Sakina ta fahimceta tun jiya dan haka ta yi rushing nata zuwa asibiti ba tare da ta gayawa Aslam ba dan ya ce ba a nan yake so ta haihu ba, tunnda haihuwa ta uku tana zuwa da complications gara ya fita da ita waje . Kuma ta san in dai ya ji Huda tana nak uda ne amman ta yi shiru to zai ji haushi sosai. Tun kafin su k arasa asibitin faya ta fashe, ko minti talatin baayi da shigar da itaba ta haifo y anta biyu kyawawa maza masu kama da Aslam sak..... Sai after one week tukunna Granpa ya had a walima iya family kawai na welcoming Sumayya da twins waenda suka ci sunan Arshaad da Auwal (Abhi da dada). Takanas Granpa ya aikawa su Shuwa nasu invitation d in. A compound d in tsakar gidanshi aka yi decoration manya manyan dining table masu seat 20 guda biyu aka k awata aya na manya d ayan kuma na Yara jikokin gidan. Wajen 5:00pm kowa ya hallara, tun rasuwar Kaka Granpa ya zama shine Abokin Madu, shiri suke yi sosai .Allah ya arawa Granpa tsahon rai tubarkallah, sai dai fa ya tsufa sosai dan baya ma iya takawa a kan wheelchair yake. Haka aka fara gabatar da walimar bayan Madu ya bud e taro da addua. In ka gansu kowa cikin farin ciki da walwala da annashuwa Mama na zaune kusa da Abba Mom da Anty Kaulat sun saka Daddy a tsakiya Mommy a kusa da Dad Hudan kusa da Aslam sun d au twins d insu a hannu Arshaad da Jihad Sakina da Auwal Aaima da Junaidu sai Jalila da Mijinta. ayan dinning d in kuma Yaran ne tun daga kan Arshaad har kan Abbakar Saddik. Ana gama cin abincin Granpa ya yi gyaran murya ya ce Hudan Maryam Aisha inaso in sake baku hak Da sauri Madu ya ce Dan Allah ka yi shiru. Yanzu haka kana ganin akwai grudges? Komai ya wuce, mu yafi juna Allah ya yafe maana. A hankali ya sauk e ajiyar zuciya yana kallonsu Mama one by one Cikin had in baki Mama da Mommy suka ce Granpa