Sashe 36
So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
asibitin da ya kamata a kaishi. Ba abunda ya fi bawa Jalila mamaki irin kyan asibitin da mak udan kud en da Ya Junaidun ya bayar daga nan suka amshi Ya Ja afar d Kusan kamar gidan mahaukata haka wajen yake amman ana basu kulawa da treatment mai ma ana. Suna dawowa washegari ya fara da case d in Baba shima wanda tun ranar da ya dawo yaje ya ganshi a gidan Kaka don tun dawowarshi a wajen Baba talatu yake. To anan ma an kashe kud i wajen bincike da ragowar abubuwa, duk kuma tare ake zuwa da Jalila wadda babu abunda tafi sakawa ido irin aljihun Junaidun dan haka tana dawowa gida take sayarwa da Umma Jarida! Nan kuwa suka maidashi atm Tun abun yana burge Anty Zainab har yazo ya fara bata tsoro saboda yadda Junaidu yake wasa da kud ya kamata a bincikesa. Ita kuwa Umma ba abunda ya dameta, da Anty Zainab tayi mata maganar ma cewa tayi Kar su yi mishi magana yayi tunanin zarginshi suke yi ya rage basu kud Tun daga nan Anty Zainab taja bakinta tayi shiru bata k ara magana ba. Su Umma duniya ta dawo sabuwa! Hatta shinkafa basmati ake ci a gidan Kaji kuwa ba a magana.. Wani zubin ma da daddare sai dai a siyo tsire ko pizza da fresh milk aci a kwanta. Har gidan su Kaka da Abba Madu junaidu bai bari ba alkhairi na yau daban na gobe daban Tabbas zama da Sadiya sai mutum mai d ankaren hak uri! Dan wannan duniya da jin dad in da ta samu sai ta mayar da Anty Zainab kamar wata bola! Idan an kawo kaji sam ba zata bari ta tab a ba ma, ita da kanta za ta gyara ta soya su d ibar mata dan wulak anci a nata kason kai da k afa suke fitowa, sam basa la akari da shi Junaidun nephew d inta ne itama Idan ya zo fita suka ce suna buk atar kud i har da na Anty Zainab yake ajjiyewa amman sai su hanata! Abubuwa kala kala haka ta dinga fuskanta wanda daman ance ba a gane asalin halin mutum sai an zauna tare ko an yi yunwa Gashi wani abun mamaki sam Umma tak i yarda su koma wajen malaminsu tare! Kullum sai sun bari ta fita aiki sai su je ita da Jalila, idan ta dawo sai ta tarar sun je sun karb o mata sak o. Gashi kullum ita ke bada kud i su basa bada ko sisi wannan watan tun kafin wata ya zo k arshe an bita bashi ba dan Khadija da Yayarta sun aiko mata kud i ba to da bata san ta ya zata dinga zuwa aikin ba ma. Haka kurum yau taji bata yarda da bayanin su Umma ba dan agaskiya so take a san yanda za ai ta koma gidanta! Shiyasa tana tashi a aiki ta wuce wajen mutumin da kanta. Hankalinta ba k aramin tashi yayi ba da taji bayanin mutumin .tabbas ashe shiyasa ko waya idan tace su kira a gabanta sai suce an sace wayar mutumin bashi da waya yanzu. Jiki ba kwari haka ta yi mishi sallama dan ita kasa ma yi mishi bayanin komai tayi ta mik e kawai ta tafi...... A tsakar gida ta samesu Suna gashin zabi akan abun gashi, gaba d aya gidan ya d au k amshi. A hankali ta k arasa ta zauna a kan tabarmar da suka shimfid e a tsakar gidan ta kalli Jalila ta ce Auta dan Allah d an kawo min ruwan sanyi a fridge d in Junaidu in akwai Ba tare da ta kalletaba tana chattn a wayarta tana nan kwance akan tabarmar bata motsa ba tace Babu! Ajiyar zuciya Anty Zainab ta sauk e kafin tace Je ki duba Ta yi maganar cikin d an tsare gida. Banza Jalilan tayi da ita. Hmmm Umma wadda take zaune akan kujerar tsugunno a gabn abun gashin tace sannan ta juya ta kalli Jalilan tace Auta dan Allah je ki duba mata mana. Tsaki tayi ta ajjiye wayar sannan ta mik e ta wuce d akin. Tana wucewa Umman ta juya ta ci gaba da abunda take yi, ba tare da ta kalli Anty Zainab d inba tace Zainab y an yanzu fa sai hak uri, in ba da Allah ka had a su ba ba zuwar maka aike suke yi ba. Murmushin takaici Anty Zainab tayi kafin tace an da aka b ata dai! an da son zuciyar iyayensu take kaisu ga halaka A zabure da mamaki Umma ta juyo tana kallonta sai kuma ta kwashe da dariya ta rangad a gud a! Kafin ta ajjiye brush da man hannunta ta juyo gaba d ayanta ta gyara zamanta ido cikin ido ta kalli Anty Zainab d in kafin tace Kin san Allah! Bar ganin wai kin san cikina na san naki Bar ganin mun yi Abotar sama da shekaru talatin da ke! Billahil Azim kin ji rantsuwar y ar musulmi ko? Yanzun nan zan murzawa idanuna toka in gurza miki rashin mutunci, har makofta sai an jiyomu. Ta k arashe maganar tana d aga murya. Cikin tsananin b acin rai Anty Zainab tace Murzawa ido toka kuma na nawa Sadiya? Banda tsantsar son zuciya da son kai da rashin sanin ya kamata mai kuka sani? This time around mik ewa tsaye Umma tayi cikin kad a hannuwa tana gyara d aurin zaninta tace Oya oya Zainba shiga d aki yanzun nan ki d auko kayanki ki yi waje! Tun kafin mu kasa sheda juna ni da ke. Dai dai nan Jalila ta k araso wajen da gorar ruwan sanyi a hannunta, ba tare da ta san dalilin hayaniyar da ta tarar ta d an fara tasowa ba tace Ko baki ji abunda aka ce miki ba ne? ta ce!!!! Anty Zainab d bata kulata ba dan ba saar yin ta bace ba, ta kalli Umman tace Ko baki koreni ba Sadiya na gama zama da ke, dan ba zan a zama kina yi min zagon k asa ba, amman kafin In tafi ina so ki san na san abunda kukayi ke da y arki.. Yau naje wajen Malan yanzu haka ma daga chan na ke Bata damu da yadda maganar tata ta girgiza su ba taci gaba da magana Sadiya da kika san ba zaki bari ayi min abunda nace ba ai da kin fito kin fad amin na chanza shek a, tunda na san dalilinki na hana ayi aiki na saboda kina gani ata dalilin aikin Jalila ne na samu matsala so kar azo a gyara nawa azo ita kuma Jalila ta rasa Arshaad ko? Haka ne ko ba haka ba? Haba Sadiya!! Wacce irin zuciya ce da ce? Wacece Ummul aba isin fad awata wannan matsalar tsofai tsofai da ni? Ko kina tunanin ban san abunda nake yi ba? Sarai fa na fahimci komai kuma duk dan kar ku ji ba dad i shiyasa na ja bakina na yi shiru. Abun naki ma ni sai na ga kamar har da mugunta saboda a ganina Idan kin ce nace na hak ura da Baban su Khadija bana son komawa gidansa a bar aikin mene kuma zaki d aura da cewa ayi abunda ba zan koma ba? Haka muka yi da ke? Haka alk awari ya ce Sadiya saboda Allah? Anty Zainab ta k arashe maganar tata tana fashewa da kuka saboda wani takaici da dana sanin biyewa Sadiya da ta dinga yi tun Yarinta da ya lullub eta lokaci d Da kyar ta samu ta lallashi kanta ta share hawayenta sannan ta d ago ta kallesu! Su na nan a tsaye sun yi cirko cirko tace Bari ku ji in gaya muku.. Wutsiyar rak umi ta yi nesa da k asa! Ba na duba bana buga k asa dan bin malaman ma ke kika saka ni amman wallahi tallahi ku rubuta ku ajjiye in dai Arshaad kuke jira ya dawo ya auri Jalila to kuwa zata k are ne a haka har abada babu Miji! Ku d auki maganata as curse a matsayina na k anwar Mahaifinta, bi ana baki ne na yi mata Wani wawan tsalle Umma tayi ta dira kan Anty Zainab ta shak o wuyanta wanda sai da ta kaita k asa Ba su yi wata wata ba suka rufeta da duka ita da Jalila Tun Anty Zainab tun tana daurewa har ta ware murya ta hau zunduma ihun neman agaji Da kyar mak ofta suka kwaceta a hannunsu bayan sun shishshigo.. Still inbanda zage zage da tujara ba abunda Umma da Jalila suke zubawa. Wata mata ce tace mata Ta zo su wuce ta kaita wajen Talatu ta d an kimtsa daga nan sai ta wuce gidanta saboda gaba d aya jikinta sun yi mata jjina jina. Ba wanda ya iya tanka musu dan an san halinsu, haka nan matar ta kama Anty Zainab wadda take tafiya da kyar ta jata sukai waje Mutane ma aka fara watsewa. Wani tsohone ya kasa hak ura ya juyo ya kalli Umma yace anwar Mijinki ce fa! Kuma k awarki tun kuna Yara saboda Allah idan ke kin daketa ai bai kamata ki bar y arki ta d aura ko da yatsa a jikinta ba. Wannan rashin sanin ya kamata har Ina? Ki bi duniya a sannu fa, Sadiya. Yunk urowa ta yi zata yiwa tsohon rashin mutunci wasu samari biyu da suma basu kai ga fitaba suka yo kansu d ayan ya ce Kun san Allah In rashin d a ne mu har certificate muke bayarwa! In kuma kanku na hayak i to ku tanka mu gani Shiruuu, suka yi ba wadda tace uffan. Girgiza kai kawai tsohon yayi ya juya ya fita. ananan marasa kunya kawai Samarin suka ce kafin su juya su fita, daga nan aka watse aka barsu su biyu suna huci. Su Baaba Talatu suna tsakar gidansu na ciki wajen d akinta a kan darduma gaba d ayansu hankalinsu a mugun tashe dan yanzun nan aka shigo da results d in tests d in da aka yi wa Baba! Suna a haka aka shigo da Anty Zainab. Da sauri Ya Jamilu ya mik e ya k arasa kusa