Sashe 48
So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ko gobe ba tou tabbas za a samu babbar matsala! Shima sai yanzu ya ke ganin wannan result d in bayan ya tsananta bincike Kasa magana Abba yayi tsabar mamaki da takaici dan haka kawai ya turawa commisioner of police message tare da adress d in asibitin daga nan ya cewa Baban Sakina ya zo su je.. Suna fita ya ce mishi su wuce gidansu Ashraff. A motar Abba ya yiwa Baban Sakina k arin haske akan abunda ya fahimta game da Ashraff d in kuma aka ci sa a Baban Sakinan ya fahimceshi. Ba Baban Sakina ba hatta Abba sai da ya cika da mamaki da suka k arasa k ofar gidan suka tarar da tafkeken masallacin juma an dake a jikin gidan cike da jama anata shige da fice. A hankali da kamala suka kutsa kai suka shige ciki, sakamokon hango Mahaifin Ashraff ya gilma ciki sanye cikin shiga ta alfarma. Ba su gama tunanain meke faruwa ba suka ji a loudspeaker ana An d aura auren Ashraff Muhammad Bashir Da Suhailat Yusuf Tanko a kan sadaki naira dubu d ari uku lakadan ba ajalan ba. Kallon kallo suka hau yi kafin su hau kallon jamaar one by one Chaan! Suka hango Baban Ashraff d in da suka biyo cikin masalllacin, yana ta fara a yana gaisa wa da wasu Abokanayen sa na jiki jiki waenda suka samu damar halartar d aurin auren gaggawan da aka gaiyyacesu. Yana ganin Baban Sakina hankalinshi ya d an tashi! Dan a iya saninshi bai gaiyyaceshi besides auren ma ai secret aka yishi to me kuma ya faru?! Bai gama dawowa dede ba suka k arasa wajen shi da Abba suka zauna a kusa da shi. Abba ne ya iya bashi hannu suka yi musabaha Baban Sakina kuwa da kyar ya iya ce mishi Barkanmu.. Dan Allah d an yi min elaborating abunda na ji an fad yanzu. Sai da Baban Ashraff d in ya d an kalli gefe da gefen shi tukunna ya mik e ya ja su gefe ya fara magana k asa k asa Kasan me ya faru ne? Yaron yanzu sai a hankali wallahi Sai kuma ya d an yi shiru kafin ya fesar da numfashi ya ci gaba da cewa Shi Ashraff an d an samu matsala ya je ya yaudari wata Yarinyar oga na wanda shi ya siya min takardar kujerar sanatan da nake mulka a yanzu! Hatta campaign shi yake taimaka min da komai. Kaga ni d an siyasa ne In na yi mishi butulci ban kyauta ba kuma siyasata za ta samu matsala tunda party d inmu d aya. Jiya Yayar Yarinyar ta kira Mahaifiyarshi direct To kasan mata abun nasu sai a hankali, a take sai ta yi mata fata fata kuma ta ce ba dai Ashraff d inta ba Tofa shine Yaran su kuma suka je suka samu Mahaifinsu da Mahaifiyarsu suka fad i komai. Adress da sunana kawai ya karb a ya gano Ashraff d ana ne! Yau da safe sai ganin shi na yi. Baban sakina ko kaine a situation d in da nake na san dole ka yi abunda nayi. Amman ka kwantar da hankalinka Aure tsakanin Ashraff da Sakina babu fashi! In sha Allah lokacin da muka d iba yana cika za a d aura musu aure. Jiya sai cikin dare Ashraff ya dawo gidan nan a hargitse wallahi ya bani tsoro kuma hakan ya sanya na sake fahimtar yana tsananin k aunar y arka dan na san tabbas labarin ta ji suka d an samu matsala shiyasa ya damu har haka.. Kar ka ce za ka yi interfering dan Allah kar kace za ka yi komai ka barsu, dan Ashraff jiya har d an k aramin hauka ya yi! Idan ka ce za ka hanashi Sakina ban san ya za ai ba Cikin tsananin b acin rai Baban Sakina ya ce A jiyan da ya dawo muku a haukace ka san me ya je ya yi? Bai jira jin amsarshi ba ya ce wamushe mini y a ya je ya yi! Ya kaita wani asibiti suka had a baki da mai asibitin aka manna mata ciwon hauka! Yanzu haka da ka ganmu da farko shirin d aura musu aure shi da ita muke yi saboda ya ce ya san wani k warerren Likita A New York Inkuma aka barta ba a kaita wajen Likitan da wuri ba to zata iya mutuwa. A firgice Baban Ashraff d in ya ce Innalillahi wa inna ilaihirrajiun Sai kuma ya dafe kanshi kafin ya d ago ya ce Kayi hak uri Alhaji Muhammad Ashraff yayi laifi amman wannan yana yi maka nuni da abunda hanashi ita ka iya jawowa! Na tabbatar tsorata yayi shiyasa yayi hakan! Yanzu ka kwantar da hankalinka zan yi mishi magana ba zai k araba In sha Allah Lokaci yana yi za a d aura musu aure a samu a zauna lafiya Shi kam Abba dariya ma Mutumin ya so ya bashi Yana shirin yin magana ya ji Baban Sakina ya ce Unfortunately, Alhaji ka yi hak uri amman itama Sakina akwai wanda na ga ya fi dacewa ta aura! Za mu dawo muku da duk wasu kud en ku da kaya dan na janye maganar aurenta da Ashraff gaskiya! Bawai saboda Ashraff ya yi aure ba..not at all. Zan yi hakan ne saboda yadda na ga kana shakkar Mahaifin Yarinyar da ka aurawa d anka a yau na tabbar idan ya ce kar a yiwa y arsa kishiya to ba za ka bari ba. Cikin b acin rai mutumin ya ce Wai Alhaji Muhammad ya mutum kamar ni da girma na ina yi maka magana har da magiya amma kana yi min musu??? Ciki sauk e ajiyar zuciya Baban Sakina ya ce Shiyasa zan barka In bar maka d anka dan ba zan iya musun rashin gaskiya da kai ba Yana gama fad in haka ya wuce inda ya ga limama, ya same shi ya gaya mishi wata magana kafin ya dawo inda Abba yake tsaye shi da Baban Ashraff ya ce masa Kana da sadakin da zaka bayar na Auwal ko sai ka je banki? Kallonshi Abba ya yi a d an rikice sai kuma ya sauk e ajiyar zuciya yana murmushi kafin ya ce akwai a mota, bara in je in d auko Ko minti biyar bai yi ba ya dawo Alokacin limamin har ya d an tara jama a an zazzauna. Yana zuwa bayan an shirya komai ya mik a sadaki ya yiwa Auwal wakili a take aka d aura auren Auwal Yusuf Umar Farouk MT Amaryarsa Sakinat Muhammad a kan sadaki naira dubu d ari biyu lakadan ba ajalan ba. Ana gamawa Baban Ashraff ya juya ya fita fuuuuu! Daman tun d azu ko zama kasa yi yayi yana mamakin tsaurin ido da taurin kai Irin na wannan talakan mutumin............ Ana shafa Fatiha Abba ya bayar aka siyo alawowi a shagon gefen su aka zo aka rarraba aka watse.. A take ya kira su Dad ya sanar da su good news. Kasa hak ura suka yi suka ce ya bawa Baban Sakina wayar Shi kam har d an kunyar irin godiyar da suka dinga yi mishi ya ji, daga nan suka yi sallama suka nufi wajen Granpa domin sanar da shi. Su Abba kuma suka koma asibiti wajen Sakina. Suna shiga dede suka tarar ta farfad o amman Mama da Ummu sun danneta Likitan yana k arin sake sank ama mata wata allurar yana cewa Ai dama na gaya muku! Ku duba fa kugani irin abubuwan da take yi if possible a wuce da ita kawai Yau! Tunda na ji Yaron ya san garin da Likitan, shi zai yi komai dan haka komai zai zo da sauk Da sauri Baban Sakina ya je ya kwab e allurar daga hannunshi! Yana shirin yin magana y an sanda suka shigo. Babban su ne ya k araso ya karanto mishi laifinshi.... Tabbas Likitan ya san Ashraff zai fito da shi tunda ba ayau suka fara harka da shi ba! Yasha kawo mishi mata ya cire musu ciki amman duk da haka sai da ya ji gabanshi ya fad Da kyar ya dake ya bi bayansu salin alin bayan ya turawa Ashraff d in message Suna fita Sakina ta ce wallahi Abba k alau nake, Ashraff munafuki ne! Shi ne ya shak a min hanky d insa wanda Allah kad ai ya san girman kwayar da ya saka a jiki shiyasa nake jin k ayi a kaina kuma yanzu na daina. Dan Allah ku fahimceni Munafuki ne! Baba dan Allah kar ku kaini wajen Likitan mahaukata Matsawa inda take Baban nata yayi a hankali ya dafa kanta ya ce ba komai komai ya wuce ki kwantar da hankalinki kin ji? Mun yarda da ke Aaima ta fad a mana komai ai Kallonshi kawai Ummu da Mama suke yi A hankali cikin nutsuwa ya karanto musu yadda suka je suka tarar ana d aurawa Ashraff aure da komai da kuma yadda suma suka d aura auren Sakina da Auwal a yau Wani sassanyan murmushi ne ya sub ucewa Mama a hankali ta ce Alhamdulillah Abba da yake kallonta ne ya ce Ma sha Allah. Yana sakin nashi murmushin. Sakina kuwa wani irin kuka ta saki....... Direct parlourn Granpa Dad da Daddy suka nufa. a nan suka iskeshi shi da Gramma yana jik a towel yana d aura mata a ajiki. Ba yadda suka iya haka suka sanar da y an nasu rashin lafiyar Gramma d wanda hawan jinine yake neman yi mata illa tun rasuwar Ummi Ba k aramin tashin hankali su Dad suka shiga ba kuwa. Da kyar! Granpa da Gramma d in suka lallab asu suka d an nutsu bayan sun gama shiryawa akan za a fitar da Gramma d in waje ta d an huta ta samu change of environment ko da na wata d aya ne ta yarda. Sai da Granpa ya tambayesu tukunna suka tuno da zancen Auwal da Sakina dan haka suka zaiyyano musu labari tiryan tiryan ewa Gramma ta yi ta zauna tana murmushi ta ce Alhamdulillah na samu another grand in-law Allah ya sanya albarka dama inata addua wallahi saboda Yarinyar ta shiga raina tun a ranar da suka