← Book details So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 69

Sashe 58

So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

soyayya? Ajiyar zuciya Ummu ta sauk e a hankali ta matsa kusa da ita tasa hannu ta rungumeta, a take kuka ya taho musu a tare su biyun. Suna a haka Shuwa ta shigo. Murmushi kawai ta yi cikin dakiya ta k arasa inda suke ta d an b ata rai kafin ta ce Yanzu dan Allah Maryam kema sai kin saka mu kuka? Su Huda sunayi kema kina yi? Sannan cikin d an fad a ta cewa Ummu tashi ki fita, yi maza ki fita kije kin bar Zainab da had a abinci ke kin zo nan. Oya Maryam kema tashi ki shirya yanzunnan za ki ga an fara zuwa Bata Ida rufe bakinta ba Hudan ta shigo ita da Mommy. Da d an sauri ta k arasa ta fad a kansu Ummu tana murna. Jujjuya kai kawai Shuwa tayi ta ce Nikam wannan alada taku ta turai ban santa ba! Dan tsabar rashin man kai Huda yanzu keda za akai miki Maman naki inda kike shine kika fito? Kalleki ko nuna baki gama yi daga jinin amarcinba amman dan fitina har kin fito? Murmushi Mommy ta yi suka gaisa ita da Shuwa kafin ta ce Hajiya ayi mana uzuri, nima naso in hana amman ita da Mijin suka kafe! Wai zata yi mishi kuka idan na tafi. Cikin d an fad a Shuwan ta k arasa ta sakar mata rankwashi a kai tace ira!! Sannnan kin zo kin wani wuce ni kin fad a jikin iyayenki.. Murmushi Huda ta yi ta mik e ta yi hugging Shuwa kafin cikin dariya da zolaya ta ce Hajiya kawai ki fito ki ce daman kishi kike yi ban kula ki ba ba wai kiyi ta kame kame ba . Dariya duk akayi. A hankali Shuwa itama tana d an murmushi tasa hannu ta yi hugging Huda tukunna ta cika ta ta juya ta fita da sauri tana cewa su tabbata sun sa Mama ta shirya yanzu Already Maman ta yi wanka tun sassafe dan haka kayanta kawai ta shiga bathroom ta saka Sky blue lace da white jaka takalmi da jewelry Ummu ce tayi mata d auri nan take ta fito rass Amarya Anyi hotuna sosai Allah sarki sakina a video call Huda ta kirata ta saka fuskarta akan screen din full aka d auki hoton da ita su Ummu suna ta yiwa shirmen nasu dariya gashi Sakina ta dage sai an yi da ita. A masallacin unguwar kusa da gidan Madu anan za a d aura aure dan tun kafin lokaci ya cika manyan motoci suka cika layin tap! Har layin baya saboda Abba gayya yayi kamar wannan ne na farko. Lokaci yana cika dubban mutane suka shaida aurin Auren Yakubu Umar Farouk Mt (Abba) Da Amaryarsa Maryam Muhammad Madu (Mama) Akan sadaki naira dubu d ari uku. Ana shirin watsewa Kaka ya cewa Limamin ya sanar za a sake wani d aurin auren Tun lokacin da Kaka ya bada sanarwar Jalila wani mai d an kantin ana ce mishi Abdullahi ya ce yaji ya gani! Shi da Mahaifiyarshi basu wani dad e sosai da tarewa a anguwar ba kasancewar Mahaifinsa ya rasu kuma anata rigima tsakaninsu da dangi da iyayen uban a kan gado yasa suka baro Katsina suka dawo Kano da shi da Mahaifiyarshi da k anwarsa Aminatu tsarar Jalila. Da farko Hudan ya so sai da mazan layin suka zaunar da shi suka yi mishi lecture a kan indai ba gudumar late comer da heartbreak yake son yasha ba tou ya hak Tukunna ya hak ura ya koma kan Jalila wadda sai da ya fara sonta ne ma ya lura yama fi k aunarta akan Hudan, dan haka ya je ya sameta ya gaya mata.. iri k iri ta fito mishi ta k i amincewa da shi sannan ta wankeshi tass!! Ta yi gaba abunta. Babu yanda bai yi ba amman ya kasa cire ta aranshi har rashin lafiya yake yi saboda Jalila tun ba ma lokacin da Auwal ya fara kwasarta ba sai da ya yi k aramin hauka. Har gida Mahaifiyarsa ta je ta samu Sadiya amman tijarar da Sadiya ta yi mata har yamafi wadda Jalilan ta yiwa Abdullahin kumafa idan ka ga Abdullahi bashi da laifi sam! Bak in saurayi dogon gaske mai fad in k ashi bashi da wani muni a fuska sam ya kammala degree d inshi bai samu aiki ba shiyasa ya bud e shago saboda d awainiyar Mahaifiyarsa da k anwarsa dole shi ne zai yi. Yana jin labari ya tafi wajen Kaka.. Ba abunda Kaka ya b oye masa gameda cikin da Jalila tayi amman wannan Yaro ya ce yaji ya gani. Kaka ba k aramin farin ciki yayi ba dan bai tab a tunanin Jalila zata samu Miji saurayi kamar Abdullahin ba amman still sai da ya sake tura Baaba Talatu wajen Mahaifiyarsa da bayani Itama ta amince Dan haka aka bashi Jalila ba tare da an gayawa ita kanta Jalilan ko Sadiya ba Baba ne kawai ya sani Su Sadiya suna gidan Baaba Laraba sai uban hayak i suke yi dan Malamin nasu yace in dai sun yi wannan hayak in a anguwar in da Maryam (Mama) take tou ba za a d aura auren Maryam da Yakubu ba. Suna hayakin suna ta uban tari kawunan su na ciwo suka jiyo an d aura auren Maryam da Yakubu! Fatali Umma ta yi da kaskon kafin ta fashe da wani matsanancin kuka!. Jalila kanta sai da ta yi kwallar tashin hankali. Ba a yi minti talatin ba suna cikin jimami da tashin hankali suka ji ana sanarwa An D aura Auren Abdullahi Muhammad Da Amaryarsa Jalila Usman Bashir BULAMA So da Buri Free book Mikiya Writers Association. A hankali Mama ta lumshe idanuwanta wasu hawaye suna zuba. Dai dai nan Ummu ta shigo, ta na Isa gareta ta sa hannu ta yi hugging d inta ta ce congratulations Ajiyar zuciya kawai Mama ta sauk e daga nan d akin ya fara cika da jamaa.. Banda hayaniyar mata babu abunda ke tashi. Suna cikin hira suka ji d aurin auren Jalila itama, nan take kowa ta hau tofa albarkacin bakinta wasu su ce Allah shi k wasu kuma su ce Ai ta ma yi sa a data auri Abdullahin, Mutum mai kirki da hankali da zuciyar nema wallahi ta tsinci dami a kala... Kowa idan ya ga Abba a wajen d aurin auren nan tashi d aya zai san yau d in fa yana cikin farin ciki. Ba shi kad ai ba hatta su Granpa idan ka gansu fuskokinsu tap! Cike da annuri. Ba a jima ba suka shiga parlourn Madu aka yi musu hotuna suka wuce bayan sun ce nan da anjima in an d an watse Abba zai dawo ya d auki Amaryar shi da kanshi. Madu ya ji dad in hakan dan dama shima ya gama deciding akan ba sai an yi wani reton kai Amarya kamar wata Yarinya ba Hakan kuwa aka yi, Hudan ta so tsayawa amman awa uku kawai Aslam ya bata daga nann ya dawo ya d auketa a cewarshi gidan yayi mishi girma ya kasa shan ko ruwa tunda ya koma Tunda ta ji haka dama ta b aro jirginsa! Dan haka ta yi murmushi kawai ta girgiza kai tana mamakinsa. Tunda aka idar da sallar Magrib Abba ya shirya tsaf! Ana idar da sallar isha ya kama hanyar gandun albasa bayan ya samu Dad ya cika shi dakyar dan da farko rik esa ya yi ya ce akwai wani important aiki da zai tayashi dan Allah Kamar Abba zai yi kuka haka ya yi mishi sai kuma ya ga Dad d in yana dariya k asa k asa dan haka ya gano tsokanace! Amman dukda haka sai da ya yi da gaske tukunna Dad d in ya cika mishi riga ya wuce mota Dad d in kuma ya nufi gidanshi yana dariya Yana zuwa ya tadda Madu zai shiga gida ya fito kenan daga masallaci dan haka suka shiga tare har parlourn Shuwa. Nan Madu ya d au waya ya kira Kaka da Baaba Talatu suka zo suka had u suka yi musu Nasiha! Daganan suka sanya musu albarka Sai da suka zo tafiya ne Mama ta ji kuka ya taho mata. Murmushi kawai Baaba Talatu da Shuwa suka yi daga nan Baaba Talatu ta mik e ta k arasa ta mik ar da ita suka yi gaba Abba shima ya yi musu godiya da fatan alkhairi ya bi bayansu Da shi da mai aikin ne suka ja akwatunan Mama guda biyu da ta had kayanta a ciki suka kai mota suka sanya mata a booth... Har k ofar mota Baaba Talatu ta raka Mama ta bud e ta saka ta a ciiki tukunna ta ce Allah ya miki albarka Tana mai rufe mata motar ta koma ciki. Dede nan Abba ya shigo ya rufe motar ya kunna ta, a hankali ya sauk e ajiyar zuciya sannan ya juyo ya sa hannu ya jawota ya yi hugging d inta wasu hawaye suna zubowa daga idanunshi.. Da sauri ta ce Abba mutane fa suna wucewa Tana mai d an k arin janyewa. Bai cikata ba sai da ya yi niyya tukunna ya matsa amman still yana rik e da hannunta yana kallonta ta cikin mayafin da ta d an ja. Murmushi kawai ya yi yana sauk e wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ya koma ya zauna rik e da hannunta ya tada motar suka wuce. Sai a sannan tukunna Baba ya share hawayenshi ya juya ya nufi cikin gidan Kaka yana ganin uku uku...... Tunda suka isa bakin estate d in ta lumshe idanuwanta. A hankali ya yi horn aka zuge makeken gate d in suka shige ciki. Direct gidan Granpa Abba ya nufa da ita. Yana kashe motar ya d an murza hannunta wanda tun d azun da ya rik e bai cika ba ya ce Maryama Sai a sannan ta bud e idon ta d an juyo ta kalleshi. Murmushi ya yi ya ce mu je ko? Jinjina kai kawai ta yi daga nan ta fara k arin fita sai kuma ta juya ta ce hannuna Sai a sannan ya d anyi murmushi ya sakin mata hannun da
Chapter 58 · 0% Book details