← Book details So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 69

Sashe 64

So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kai ga zuwa inda za mu je ba cikina ya b aci! Dan haka na nemi alfarmar su tsaya in d an yi uzuri. Suna tsayawa na fita Ina kutsa kai cikin d ajin kamar an ce in juyo nan na ga wasu maza da mask su uku sun nufi motar. Duk sai da suka fito da y an motar suka dubasu amman sam babu abunda suke nema wanda sai daga baya na gane waenda Arshaad ya tura ne kuma ni suke nema. Kamar na sani a lokacin sai na b oye kaina. Bayan na b oye kaina su kuma suka gama dube duben su suka tafi. Su kuma Abokanan tafiyar tawa inaga tsorata suka yi dan ina shirin fitowa naga duk sun shige motar suna shirin tafiya. Da sauri na yunk ura zan tafi na ji an rik e min k afa! Sai da gabana ya fad i da na juya dan ni sam ban lura akwai tsoho ma a wajen ba a durkushe sai da ya rik o nin. Cikin kuka tsohon ya ce bawan Allah ko baiwar Allah dan Allah taimakon musulunci zan mutu yunwa nake ji. Da sauri na ce Baba dan Allah Abokanan tafiya ta za su tafi ka cikani In wuce. Cikin kuka tsohon ya ce yunwa nake ji ka taimakeni dan Allah Haka nan inaji ina na gani na kama hannunshi ya mik e su kuma Abokanayen tafiyar tawa suka wuce dan maybe sunga na dad e su kuwa a tsorace suke. Na ji takaici sosai amman yadda tsohon nan yake karkawa da kuka yasa kawai na yanke shawarar In taimakeshi. Sai da muka fara tafiya na fahimci ashe makaho ne! Haka muka yi ta kutsawa dan hanyar ba jama a sosai har muka iske wata mai k osai da kunu na siya da d an kud in da aka bani in yi na mota na bashi ya ci ya sha. A hankali muna zaune a wajen ya ce in bashi labarina Haka kurum ban sanshi ba amman na tsinci kaina da fad a mishi komai na rayuwata har kawo yanzu. A hankali ya ce kuma kana ganin ba kai ake nema ba kuwa!?. Ka zo mu je Gidana ka d an b uya kafin kwana biyu sai ka wuce gudun kar ka je suna nan har yanzu ka fita a kamaka. Tsoro ya sanya ni na amincewa wannan tsohon, dan a yadda naga mutanen nan babu kalar imani a tattare da su. Gidan nasa y ar bukka ce sai band aki wanda aka yishi da langa langa a gefe sai wani murhu da rijiya. Sam babu wani katanga ko wani abun da yake nuni da wajen keb antacce ne. ar bukkartashi muka shiga muka zauna anan yake ce mini Matarsa ta rasu watan da ya mutu, Allah bai bashi d a ba! Danginsa kuma duk sun guje shi saboda basa son d awainiya. Atake na ji tausayin bawan Allahn nan ya rufe ni, kuma a take muka saba shak uwa ta shiga tsakaninmu Kwana na biyu a wajensa, na siya mishi abinci da d an abun da ba a rasa ba duk a cikin kud in da aka bani a lissafina idan na tashi ni sai In d auki drop har gidan Abokina ya biya. Ban b oyewa tsohon nan ba na ce masa muma ba wasu masu arzik i baneba, ba daban haka ba da na tafi da shi dan na lura yana cikin kad aici da buk atar taimako kuma akwai abubuwa da dama a kaina amman dai bara mugani in shaa Allah idan na koma gida na yi settling zan dawo in duba shi. Dan nima a yanzu Ina matuk ar buk atar kud Daga nan na nemo wata mata a gefe na rok eta akan dan Allah ta d an dinga lek ashi Ita kam Matar mamakima ta dinga yi dan a cewarta duk zaman ta a k auyen ita bata san da shi ba Bayan Matar wuce ne muka yi sallama muna ji kamar kar mu rabu A bakin bukkar tashi Ina fitowa na ci karo da wani mutum cikin suite! Da akwati a hannunshi, kamar yana cikin sauri, ya nuna min hotonshi da wannan tsohon kamar lokacin tun suna samari ya ce min an ce yana nan! Da kyar da wuya ya samu location d insa, dan Allah na san shi? Ba tare da b ata lokaci ba na ce masa Dan haka mutumin ya ce mini sun tab a yin businesses da tsohon ne, tsohon ya aminta da shi amman shi sai ya gudar masa da kud insa so tun daga lokacin abubuwa basu yi mishi kyau ba! Shiyasa ya yanke shawarar dawo mishi da dukiyarsa. Ya d aura da cewa Dan Allah in bashi in ce masa ya ce sunanshi Kabir, Alhaji Kabir. Ya taimaka ya yafe masa Yana min maganar ne shi duk a tunaninsa ma ni d an tsohon ne. Jin muryar tsohon ya fito yasa ya yi sauri ya yi min sallama a cewarsa ba zai iya facing d insa ba dan kunyarshi yake ji. Duk da nace ya d an tsaya ko ruwa ne ya sha saboda naga inba magana ya yi ba tsohon ba zai gane shi ba dan ba gani yake yi ba, amma sam yak i yarda, ya damk a min akwatin yana d an waiwayowa yana kallon tsohon har ya shige motarshi driver ya ja suka tafi. Akwatin na ja na kai d aki na fito na kama hannun tsohon muka shiga ciki na zauna. Na zuge akwatin ba tare da na ce komai ba. Sai da gabana ya yanke ya fad i dan gabaki d aya akwatin cike yake da mak udan kud e dollars! A hankali na ji tsohon ya ce Kai da waye d azu a waje? Cikin In inaa na ce wani mutum ne ya zo neman ka! Ya ce kun tab a yin buisiness kai da shi ya gudar maka da kud Shirruuu tsohon nan ya yi kafin chaan! Ya yi murmushi ya ce na kasa tunawa Kafin ya sauk e wata nannuyar ajiyar zuciya ya ce Akwai abunda ban gaya maka ba Inada sabara a kwakwalwata shiyasa ma kaga wasu lokutan Ina zama ina yin kuka ni kad ai. Wani makwafcina anan ya d auke ni satin baya ya kaini asibiti aka tabbatar da cewa ba zan k ara sati uku a duniya ba! A take wani tsananin tausayinshi ya lullub e ni! Ga dai kud e nan ya samu bayan ya sha wahalar rayuwa amman a lokacin da kud en suka riskeshi sai ya zamana ba za su yi mishi amfanin komai ba. Ban san lokacin da kuka ya kufce mini ba!. Jin ina kuka yasa tshon ya hau tambayata menene? Mai ya faru? Me ye a cikin jakar? Ko wani abun tsoron na gani? Shiru na d anyi kafin ince mishi i ne a ciki, Dollars. Shiruuu na ji ya yi Ya jima tukunna ya ce Ka taimakeni ko masallatai ne in gina dan Allah. Saboda kaga ni ba ido da lafiya gare ni ba. Bana bukatar ka gina min gida ko wani abu daga kud in tunda kaga ba lallae inga k arshen aikin bama kawai dai ka rik e Allah ka tayani gyara lahirata ta hanyar gina masallatai da islamiyoyi a k auyukan nan. A lokacin tabbas ina son komawa gida amman kuma wannan tsohon yana buk atar taimakona a yanzu sannan inaso a ida auren Huda da Arshaad kafin In koma dan tabbas na kasa cire ta a cikin zuciyata kuma na riga na d auki alk awarin ba zan aureta ba! Tunda na lura sam bana cikin zuciyarta tun ranar da ta ce min Arshaad zata aura ari kawai nake yi inga na fitar da ita a raina saboda no matter how much I love her ba zan tab a iya zama da ita idan bata ra ayi na ba! Amman kuma bana buk atar a aurar da ita a gaban Idona sannan still ina jin fargabar fitowata duba da sharrin da aka yi min da kuma waenda nake tunanin ni suke nema..A ganina gara In d an fahimci abubuwa daga b oye kafin a kaini lahira tun da ban san waye yake farautata ba! Sannan aikin da zan yiwa wannan tsoho tabbas lada zan samu Shiyasa a take na yanke shawarar jifan tsuntsu biyu da dutse daya.... ...Haka nan na tsaya tsayin daka wajen taimaka masa kamar yadda ya buk ata aka shiga gina masallatai a duk k auyukan da makarantun islamiyya gini mai kyau da had uwa, na ban mamaki. Tabbas Ina da buk atar kud amman ban tab a yunk urin d aukar ko naira biyar ba! Apart from kud in motar da yace In dinga d auka a ciki dana abinci da shelter. Akwai kud i sannan na samu maaikata masu yawa sosai dan ko wanne k auye masu ginin daban suke shiyasa kafin wata uku aka fara shirin kammalawa. Ba abunda yafi sakani farin ciki irin yadda Allah ya arawa wannan tsohon tsawon rai har na tsawon lokacin da aka zo kammalawa duk da dai jikin nashi sai a hankali. Ranar da na kammala aikin da washegari ya tashi da tsananin ciwo wanda kana gani ka san sai a hankali kawai. A wannan bukkar tashi muke har kawo wannan lokacin amman fa muna cin mai kyau mu sha mai kyau. Ina ganin yana yin jikin nashi na ce bara inje In nemo mai abun hawa a kaishi asibiti cikin gaggawa Amman sai ya rik eni ya rok eni akan in tsaya akwai maganar da yake so ya yi da ni. Abu na farko da ya fara tambayata shine sunana! Duk tsawon lokutan nan Yaro yake kirana da shi ni kuma in kirashi da Baba. Sai da mutanen last k auyen da aka yiwa masallaci suka tambayeni suna son rubuta sunanshi Tukunna da kyar ya ce min sunanshi Alhaji Kabir mai fetur ....Ahankali na ce mishi sunanan Junaidu Da kyar cikin tsananin ciwon da yake ciki ya iya ce min in d auko masa wata y ar jaka Ya yi maganar yana mai yi min nuni da wajen da jakar take! Tabbas na shiga rud ani saboda yadda ya juya
Chapter 64 · 0% Book details