Sashe 3
So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sannan hankalin shi yafi kwanciya da Aslam d dan bakiga irin farin cikin da yake yi ba a lokacin da aka goya mishi baya aka kuma d aura auren. To who are we to reject? Besides Ni a ganina ma it s for the best In sha Allah Tunda kullum zab in Ubangiji muke nema shi ya shirya hakan. Dan haka sai mu runguma mu kuma gode mishi mu bita da fatan alkhairi. Banaso inji wata magana ta taso! Ku saka a ranku kawai Arshaad ba shine Allah ya tsara zai zama Mijin Huda ba Aslam ne!. Sai kuyi mata nasiha ku shiryata, Yahaya yace min k arfe biyar na yamma za su zo su tafi da ita in sha Allah.. Allah yayi muku albarka gaba d ayanku. Yana gama fad in haka ya mike suka fita shi da Baba Bashir. A hankali sautin kukan Mama ya fara tsananta a cikin d akin.... Ganin Huda ta mik e ta nufo inda take tana kuka ne ya sanya Maman ta mik e da sauri ta fice daga d akin tana kuka. A tsakar d akin Huda ta zame ta zauna ta fashe da wani kuka mai ban tausayi Shuwa ce ta umarci Ummu da ta je ta d auko mata laffayar da za a nad a mata Sannan ta taho da turarukan wuta da kasko Ummu na fita Shuwan ta k arasa inda Huda take zaune itama ta zauna sannan ta kamo hannunta duka biyu Nasiha mai ratsa jiki tayi mata wanda ko Maman iyakar abunda zata gaya mata kenan! Duk wani abunda ya dace sai da Shuwa ta fahimtar da ita dalla dalla. A haka Ummu ta shigo ta samesu dan haka itama ta nemi waje ta zauna ta d ora mata da nata darussan Ita dai Huda zuwa yanzu muryarta ta disashe, hawayene kawai yake fita daga idanuwanta, sai faman sauk e ajiyar zuciya take yi, a ranta tana tunanin Tayaya zata fara zama da mutumin da ba ya sonta bata sonshi? Mutumin da ta lura ko inda take baya son zama... Umartarta suka yi da ta mik Tana mik ewa suka hau shiryata.. Suna mata ruwan turarurruka Khumra da na wuta............... A gigice Anty Zainab ta k arasa gidan Baba. Tana shiga ko sallama bata yi ba ta fad akin Umma. A kan gado ta sameta ta bararraje tana shan lemo da bredi da gyada Ya Ja afar kuma yana gefe a kwance yana bacci. auke bredin tayi ta jefar Umma na shirin yin magana Anty Zainab ta katseta ta hanyar cewa Jiya! Sai da nace miki kar ki k arawa mutumin nan kud yaudarar mu zai kuma yi amma da yake kunnen k ashi gareki kika d auki mak udan kud e kika bashi saboda kinji Jalila duk ta rikice tana kuka ko? To albishirinki kice mini goro! Ga Huda chan ana shirya ta In sha Allah nan da k arfe biyar za azo a tafi da ita gidan Arshaad! Aure kam ya d auru, ba d an borin da yayi nasarar lalatawa. Kwarewa Umma tayi da d an ragowar bredin bakinta wanda bata gama had iyewa ba. Da kyar ta dawo dai dai Cikin tsananin tashin hankali tace Innalillahi wa innailaihirrajiun! Wacce iriyar masiface ni kam ta fad amin? Ni sadiya ina zan saka kaina? Yanzu mutumin nan ya kyauta min kenan? Tsofai tsofai da shi amman ya karkace yayi ta faman gilla mini k arya? Kin san tun yaushe muka sanshi kuwa? An dad efa ana tare. Haba dan Allah Allah ya isa kud ina da lafiyata. Kiga fa jiya cikin dare muna barin asibiti haka muka je wajen shi. Har da cewa ko dan halin da nake ciki zai yi mini aiki mai zafi! Shege ashe yaudarata ya kuma yi ya saka min rai Allah sai ya saka min wallahi Ta k arashe maganar tana fashewa da kuka.. Duk sai tausayinta ya lullub e Anty Zainab, a hankali tazo ta zauna a gefenta kafin tace Yanzu menene abun yi? Kuka ba zai kawo mana solution ba. Hawayenta ta goge sannan ta mik e tace komawa za muyi! Ai ta inda aka bi aka hau tanan ake sauk Wallah ko dai ya lalata auren kafin ta tare ko kuma ya biya ni kud Ta fad a haka tana mai yafa mayafinta wanda ta d auka yanzun. Da sauri Anty Zainab ta mik e ta tsaya a gabanta sannan tace Sadiya ki nutsu dan Allah. Na tabbata kafin mu k arasa wajen nan mai uban nisa Huda ta riga ta shak i iskar gidan Arshaad. Yanzu ni dai indai zan baki shawara ki d auka to ki hak ura da raba auren nan! Kinga fa yadda muka yi ta k arin rabawarnan yak i rabuwa to maybe wani babban rabo ne a tsakaninsu Allah ne ma yake son mu shiyasa ya barmu da ranmu, kar muje mu sake yin wani yunk urin, muje garin neman gira mu rasa idanuwanu. Cikin tsananin b acin rai Umma tace To matsoraciya! Kin san Allah wallahi sai dai duk abinda zai faru ya faru amman aure kam na raba shi na gama billahilazim! Ai In na barsu ma Maryam taci riba kenan! Idan zaki ci gaba da taimaka min to na gode, idan kuma ba za ki ci gaba ba to kina iya yin tafiyarki dan ni nan kin ganni wallahi sai inda k arfina ya k are! Na tabbatar inda ace Khadija ce take cikin halin da Jalila take ciki da kema sai inda k arfin ki ya k are! Anty Zainab taji zafin maganar amman kawai sai ta basar duba da halin da Umman take ciki kwana biyu..Jafar a haukace! Junaidu ya b ata!! Baba ya gudu!!! Jalila kuma gata chan itama sai a hankali, sannan duk fad in duniyar nan ita kad ai Umman ta gayawa Jalilan cikine da ita amman har Laraba bata sani ba Umman tace In ta fad a mata tana iya gayawa su Hansai, daga nan su kuma su yayata ayi ta munafurci a cikin unguwa da dangi Waennan dalilan su suka sanya itama Anty Zainab d in tayi sticking by her side take taimaka mata sannan tana tsananin jin tausayin k awartata, shiyasa yanzu ma Mta kaawar da haushin da taji tace Sadiya yadda na d auki Jalila haka na d auki su Khadija. Ki kwantar da hankalinki ki nutsu kar muje muyi ba daidaiba cikin rashin sani. Da sauri Umma tace Hankali na ba zai tab a kwanciya ba Zainab! Ina cikin tsananin tashin hankali.. Jiya da Jalila ta kira ni gaya miki ne ban yi ba dan kaina ya d au chaji ba kad an ba! Cikin jikinta ya zube, garin haukarta taje ta fad o daga matattakala. Kinga yanzu shi Yaron Auwal babu maganar karb ar kud i a hannunshi kuma na tabbatar nan da kwana kad an uwar nan tashi mara mutunci itama tsayayyiyar kanta zata auno Jalila gidan nan! Ni na ma yi mamakin da ta barta har yanzu dan kwata kwata ba shiri suke yi ba! Gashi ke kin san yadda Jalila take matuk ar k aunar Arshaad sannan a haka kike tunanin zan bar Huda taje ta zauna tare da Arshaad a gaban idon Jalila? Tana ji tana gani? Da wanne Yarinyar nan za taji saboda Allah? Sannan ni kaina me nayi ne haka a rayuwa da mugayen abubuwa suketa fad o mini haka? Ta k arashe tana mai fashewa da mugun kuka. Rungumeta Anty Zainab tayi ta shiga lallashinta Sai da taji tayi shiru tukunna tace Sadiya ki nutsu ki bani hankalinki dan Allah mu yi magana Kamar wata k aramar Yarinya haka Umma ta hau share hawayenta tana d aga kai duk ta rikice, ta manta rabon da ta shiga kwatankwacin tashin hankali irin wannan. Sai da ta nutsu sannan Anty Zainab tace Anjima idan na dawo daga raka Huda zan zo mu koma wajen mutumin nan, akwai wani ma shima za muje wajenshi. m sorry to say amma raba auren Huda da Arshaad ba zai yiu ba Sadiya tunda an riga an d aura. Yanzu mu bar Huda mu ji da Jalila duk bala i idan za muyi yawo tsirara mu san yanda za ayi a sati mai kamawa a aurawa Arshaad Jalila. Ke kin san wacece Jalila da kuma yadda take son Arshaad da taimakonta da taimakonmu na tabbatar Huda ba zata yi wata biyu a gidan Arshaad ba. Na tabbatar hakan sai yafi yiwa Maryam zafi akan yanzu a fasa kai Huda gidanta kai tsaye!. Yanzu ki cewa Jalila ta daure ta jure ta kauda kanta, za mu yi nasara in shaa Allah. BULAMA So da Buri Free Book Sakina ce ta yi knocking aka bata izinin shiga, tana shiga tace musu Masu d aukar Amarya sun zo, suna k asa. Dumm!! Haka k irjinsa ya buga hatta Shuwa. Cikin dauriya Ummu ta cewa Sakinan ta je, ga su nan zuwa Kallon ta Hudan tayi da idanuwanta da suka k ance suna zubar hawaye, da sauri ta juya ta fita tana share tata kwallar.. Shuwa na hannun damanta Ummu kuma ta ruk ota ta gefen hannun hagu, a haka suka sakata a tsakiya suka sauk o parlourn da ita fuskarta a lullub Kauda kai Mommy ta yi ta share kwallar farin cikin data zubo mata! A hankali ta mik ta k arasa wajensu ta kamo hannun Huda ta kawota kan kujerar da take akai gefenta ta zaunar da ita sannan itama ta samu waje ta zauna kusa da ita. Ummi ce ta mik e itama ta isa 3 seater da suke zaune su biyu ta zauna a kusa da Huda ta kamo hannunta tana murmushi (ya zamana sun sakata a tsakiya ita da Mommy ) Tsakin da Mom ta yi sai da ya d an fito fili ba tare da ita kanta ta san zai fito d inba! Da sauri ta wayance ta sake yin wani sound kamar wadda abu ya mak alewa a hak ori sannan ta shiga gaida su Shuwa tana mai arewa gidan kallo! Dukda cewa gidan yana da girma gashi mai bene amman hakan bai hana Mom yiwa gidan kallon k anci ba. Gaggaisawa aka shiga yi cikin barkwanci da mutunta juna, daga nan aka damk