← Book details So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 69

Sashe 35

So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya bud ewa Granpa ya shiga ya rufe mishi sannan shima ya zagayo ya shiga ya tada motar kansa a d aure yake! Ga dai abun farin ciki, abunda yana d aya daga cikin abubuwan da yake mafarkin son ganin sun tabbata amman kuma Allah yasa babu wata matsalar da zata kunno kai ta b angaren su Madu dan nan kam a b angaren su Granpa ya gama gyara komai............. Mama tana shiga ta tarar da Shuwa a yadda ta barta, suna a ido ta sake fashewa da kuka ta k arasa inda take ta tsugunna a gaban kujerar da take ta d aura kanta akan cinyarta. Shafa kanta Shuwa tayi kafin tace Lafiya Maryam, mai ya faru? Nifa daman yadda naga Abban ku ya shigo na san akwai matsala. Mai ya faru? Tayi mata tambayar cike da fargaba. A hankali Mama ta share hawayenta ta d ago tace Hajiya matsalar ba daga kowa bane ba, daga mu ne! Matsalar daga ni da Abba ne! Faith d inmu a baibai yake duk lokacin da muke so ko ya dace mu kasancewa da juna sai a samu matsala ta yadda indai muka zamo tare wani sai ya k untata Mai yasa farin cikin mu yake tahowa a tare da bak in cikin wasu? BULAMA So da Buri Free Book Mikiya Writers Association. 39 DAYS AGO! Gandun Albasa. Gidan shiruuu, gaba d ayansu suna zaune kowa yayi jugum! Kamar anan ake zaman makokin. A hankali Shuwa ta juya ta kalli Ummu kafin tace Gaskiya fa Mama ta fad a Ummu, ku je kawai ke da Sakina.. Ai ta ce ta kirashi ko? A hankali Mama ta d aga kai alamun Ajiyar zuciya Ummu ta sauk e kafin tace To shikenan Hajiya. Sakina taso mu je, Babanku yana waje. A hankali Sakina ta d an kalleta sai kuma ta d auke kai tace Ummu, dan Allah ki je kawai ko da Sumayya ne bana son zuwa gidan wallahi an k ura mata ido Ummu tayi kafin tace Taso mu je! Ba na son shirme.. Ba zaki yiwa su Abba da Aslam gaisuwa ba ko me?? A hankali Mama tace Ummu barta kawai ku je ke da Sumayya. Shiruu Ummun tayi kamar za tayi magana sai kuma tace Sumayya mu je Ta fad i hakan tana mik ewa ta d au mayafinta ta nufi k ofa da alamun ranta ya b aci. Suna fita ita da Sumayya Hajiya Shuwa ta mik e ta fita tsakar gidan don yin zagaye saboda kumburin da k afafuwanta suke yi idan ta zauna shiru. A hankali Mama ta mik e ta koma kan kujerar da Sakina take zaune 2 seater.. Tana ganin ta dawo kusa da ita ta tashi ta zauna da kyau sannan ta d an sunkuyar da kanta a hankali tace Bara inje d aki in kwanta Tana shirin mik ewa Mama ta kamo hannunta ta rik Ajiyar zuciya ta sauk e kafin ta sunkuyar da kanta k asa. Sai da Mama ta gama k are mata kallo ta gama nazartar ta tukunna tace Nima b oye min za ki yi? Da sauri Sakina ta d ago tana kallonta kafin ta juyar da kanta tace Me ne zan b oye miki Mama? Tana k arin danne kukan da taji ya taho mata. A hankali Maman ta sa hannunta ta juyo da fuskarta sannan ta ce Tun ranar da kikace kin bawa Ashraff go ahead ya turo Sakina har yau ban ga walwala a kan fuskarki ba! In akwai wani abun ki yi magana a samu a gyara Idan mai gyaruwa ne.. oye b oye ba abunda yake janyowa sai dana sani a rayuwa. azu Ina jinki a band aki ke kad ai kinata kuka! Meye ne yake damunki? Ko na tashi daga Mama na koma wata daban wadda ba zaki iya gayawa damuwarki ba? Duk k arin Sakina na ganin ta tsayar da kukanta kasawa tayi, tashi d aya ta hau ambaliyar hawaye ta shiga kuka tsakaninta da Allah.. Janyota Mama tayi zuwa jikinta ta rungumeta. Sai da tayi me isarta tukunna ta yi shiru da taimakon lallashin Mama kafin a hankali ta fara magana Daman akan Ya Auwal ne cousin d in su Hudan............ Tun ranar da suka fara ganin juna har kawo yanzu ba abunda Sakina ta b oyewa Mama Kallon ta Maman take yi tana sake wa kafin a hankali ta ce Sakina wa ya gaya miki ana aure saboda a yakice soyayyar wani daga cikin zuciya? Bata jira jin me zata ce ba tace to bari kiji in gaya miki.. Shekarata goma sha takwas tare da Ya Usman matsayin mata da miji amman har yau ba abunda ya shiga zuciyata game da shi ta fannin soyayya sannan ba abunda ya ragu a cikin soyayyar Abba a zuciyata. Da sauri Sakina ta d ago tana kallon ta sai kuma ta fashe da kuka ta ce Mama dan Allah kar ki yi min fatan in yi dakon soyayyar Ya Auwal haka har k arshen rayuwata! Wallahi tallahi In dai yadda nake ji akanshi haka zan ci gaba da ji har abada bayan bana tare da shi tabbas mutuwa zan yi Ta k arashe maganar tana kifewa akan cinyar Mama tana sakin wani sabon kukan. A hankali Mama take shafa kanta Sai da taji ta d anyi shiru tukun tace Sakina ba zan b oye miki ba, kin yi mistake! A hankali ta d ago tana kallon Mama da dara daran idanuwanta da suka rine sukayi jazir. Jinjina kai Maman tayi alamun tabbatarwa. Cikin share hawaye Sakina ta ce Mama kin ji fa abunda Mom da Mammy suka yi min still in aureshi? Daman ni saboda family d insa shiyasa na k i tun farko bana san issues sannan Sai da ta d anyi k asa da kanta kafin tace Sannan womanizer ne shi ne ya yiwa Jalila ciki fa Ajiyar zuciya Maman ta sauk e kafin tace Sakina Ubangiji ya halicci bayinshi kowa da irin yananyin tashi k addarar! Idan Allah yayi wannan ce k addararki kina ganin kina da wayon da za ki kufce?. In dai Auwal yana sonki tsakani da Allah to zai daina abubuwan da yake yi, za ki iya gyarashi besides ai Auwal d in ya shiryu ke kanki kin ce Arshaad tun ba yau ba ya cewa Hudan ya ga changes a tare da shi sannan kin ce Mahaifinsa shima yace ya shiryu! Ni a ganina zaki iya sake gyarashi tunda yana son ki wanda Allah kad ai ya san d umbin ladan da za ki samu. Tabbas ban so ki aura irin Miji mai halinshi ba ko da ace ya shiryu amman in dai haka Allah ya tsara yana sonki kema kuma kina son abunki to ya za ai?. Kuma Mahaifinsa ma baya k in ki yana son ki wanda shi ne yake da say a gidan! Tabbas Mom matsala ce amman ni a ganina zugar Mammy ce yadda kika ce tanata kuka ta rikice a lokacin da ya suma na tabbatar inda ba a kawo kud in auren ki ba to da tuni yanzu tazo nan gidan saboda farin cikin d anta dan tana tsananin sonshi wanda hakan shi zai sakata ta sauk o ta so ki In sha Allah. Yanzu kam ba abun yi sai dai hak But by any chance kar ki sake yunk urin toshe hanyar da za ku bi ku mallaki juna ke da Auwal! Ko da wasa, tunda kuna son juna. Kukan da Sakina take ne yasa Mama ta janyo ta jikinta, a hankali ta shiga lallashinta kafin tace Ki yi hak uri Allah ya zab a miki mafi alkhairi. Ku yi ta addua Allah ya zab a mafi alkhairi. Da kyar Mama ta samu ta lallab ata ta yi shiru dann ita kam ta san inba wani tsananin rabo ba to Auwal yayi mata nisa! Ta riga ta datse duk wata igiyar da zata k ullasu su kasance tare k ashin inuwa d aya da hannunta A Cikin kwanakin da ba su kai wata d aya ba da Anty Zainab ta yi da Sadiya tabbas ta fahimci ba zaman amana take yi da ita ba! Mamaki k arara take yi game da yadda Abotar tasu take k arin juyewa ta koma wani abun na daban. Haka nan ita za ta yi musu girki da kud inta saboda duk wani ragowar gari ko abun dafawa da suke da shi Umma ta tattare tace babu ya k are! Sai ta fita aiki ita da Jalila su dafa su ci. Tun bata gane ba har tazo ta fara fahimta.. Ga shegiyar k azanta daga Umma har Jalilan sannan wani lokacin Jalila har yada mata da magana take yi wai anzo an zaune musu a gida! Sannan Ya Ja afar kwata kwata basa kula da shi dan wani lokacin wandonshi har tsutsa ne suke binshi gashi kullum cikin datti kacha kacha especially gashin kansa sak mahaukacinsa! Haka nan zata tartare kitchen da band aki dan idan zai yi tsutsu ba za su gyara ba! Sannan ta gyara Ya Ja afar ta fita aiki ta je ta dawo ta dafa kuma su ci tare. Ana cikin haka Junaidu ya dawo Ranar suna zaune a d aki suna d an tab a hira kawai suka ganshi ya shigo! Da farko Umma tsorata ta yi dan ihu ma ta yi, fahimtar da tayi ba ita kad ai ce take ganinshi ba yasa ta tashi ta k arasa ita da Jalila inda yake. Sai da suka d an tab a fuskarshi da jikinshi suka tabbatar da shi d inne tukunna suka rungume shi a tare suka fashe da kuka Tabbas shima yayi matuk ar kewar gida shiyasa bai san lokacin da hawaye suka wanke mishi fuska ba. Da taimakon Aanty Zainab aka samu suka yi shiru ita ma ta rungume shi tana d an nata hawayen sannan suka nema waje suka zazzauna......... Tun daga lokacin duniya ta dawowa Umma da Jalila sabuwa! . Hankalin Junaidu ba k aramin tashi yayi ba ganin halin da Ya Ja afar ya ke ciki. Bai yi k asa a guiwa ba haka suka kinkimeshi shi da Jalila suka sa a mota suka nufi asibiti Bayan y an dube dube Likita ya basu sunan
Chapter 35 · 0% Book details