← Book details So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 69

Sashe 25

So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

k oshi Ji tayi kawai ya kamo hannunta ya d an matse a cikin nasa a hankali ya sake cewa Yana sake matso da cokalin. Ya subahanallah! Wannan wanne irin mutum ne? Ta yiwa kanta tambayar a cikin ranta. Ji tayi ya murza tafin hannunta da nashi hannun still a hankali taji ya sake cewa Da sauri ta juyo ta bud e bakin ta lumshe idanunta numfashinta na fita da sauri sauri. Murmushi yayi ya saka mata cokalin a baki ita kuma ta karb a ya juye mata tukunna ya zare. A hankali ta shiga taunawa, har yanzu idanuwanta a lumshe suke. Kamar wanda ya samu tv haka ya nutsa ya maida hankalinsa wajen k arewa kyakkyawar fuskarta kallo. Sai da ya ga ta had iye tukunna ya mayar da cokalin ya fara k arin d ebo wani, da sauri ta d aura hannunta a kan nasa ba tare da tayi laakari ba, tace Nafa ci abinci Mai yawa. Please Ya Aslam kar in yi amai Sannan ta fara k arin bud e kyawawan idanuwanta da suka taru da kwallah. Tana gama bud ewa taga ya ajjiye spoon d in ya na k arin bud e robar ruwa Ba yadda ta iya haka ta yarda ya bata a baki ta sha tukunna ya mik e ya d auke plate d in da ta ajjiye a kan side drawer ya had a da wanda ya shigo da su ya fitar. A yadda ya fita ya barta a haka ya dawo ya sameta, bai kalletaba bai ce mata komai ba ya nemi waje ya zauna ya ci gaba da aikin da yake yi d azun kafin ya fita sallah. Ya d an jima yana aikin, kafin yaga ta taso ta k araso ta zo inda yake. A hankali ta zauna a gefensa tace Ya Aslam Um, Anty Huda Ya ce ba tare da ya kalleta ba, yana mai ci gaba da typing d in da yake yi. Ajiyar zuciya ta sauk e kafin tace zan je dan Allah, goben. Yace, still bai kalleta. Turo baki tayi kafin tace Na dawo fa d akin This time around dariya yayi kafin ya rufe computer gaba d aya sannan ya juyo gareta yace Ki yi hak uri, baza ki je ba. Kamar da wasa kawai sai yaga ta fashe ta kuka! Ajiyar zuciya ya sauk e kafin ya matso ya kama hannunta yace Mama ce tace kar a barki ki sake fita sai nan da wata d aya. Idan kina son fita ki kira Hajiya Shuwa idan ta barki sai ki je. Da mamamki take kallonsa tana rage sauti da yawan kukan nata. Jinjina mata kai yayi alamar tabbatarwa. A hankali ta shiga share hawayenta tana sauk e ajiyar zuciya a hankali. Yanzu zaki kuma yin wani yajin kenan? Tunda dai kinga ba damar fita gobe Ba ni zan barki ba Hajiya da Mama ne A hankali ta girgiza kanta tace Ka yi hak uri, a kan abinda nayi Murmushi yayi yace Ai kuwa na hak ura! Tunda har kwalliya da turaren wuta aka saka duk dan saboda ni. Ko ba dan ni akayi ba?? Murmushi kawai tayi ta sake sunkuyar da kanta k asa. A hankali yana kallonta kafin yace Je ki kwanta. Gobe tashin asuba ne, ko? Ba tare da ta d ago ba tace Kaje ka kwanta kai, ni a nan zan kwana. Da bananan ai a gadon kake kwana. Sai da yad an k ura mata ido tukunna yace A nan d in nake kwana.. Har gyara miki gadon nake yi kullum thinking you will come back A haka bacci yake d ibana kullum. Shiruuu suka yi duk su biyun kafin yaji tace Ka fini tsayi, ina gani kullum kujerar bata isar ka, ka je ka kwanta don t be stubborn Dariya taji yayi kafin yace In da acting stubborn nake miki yanzu ai da na san tuni kin fita a d akin nan da gudu Bata fahimci kan zancen nashi ba dan haka kawai ta basar da zance ta sake cewa Ya Aslam barci nake ji, ka je ka kwanta. A hankali yan kallonta yace Are you sure? In je in kwanta ba damuwa? Da sauri ta d ago ta d aga mishi kai sannan tace Sai ka fi sakewa achan da kyau Ajiyar zuciya ya sauk e kafin yace Thank you Hudatie Haka kurum ta tsinci kanta da murmushi dan ba kad an ba sunan ya yi mata dad i matuk Murmushi shima yayi kafin ya mik e ya fara d ibar throw pillows d in kan sofar.. Iya yadda hannunshi zai iya d iba ya kwasa ya nufi gadon. A ranta tace Ikon Allah! Neman magana yake yi wannan ko mee? Bayan pillows d in da suke kan gadon wajen guda 4 masu laushi mai kuma zai yi da throw pillows?? Tunaninta ne ya katse ganin yana jera throw pillows d in yana raba gadon gida biyu da su. Tuni! Kwakwalwarta ta bata me yake shirin yi dan haka tana gani ya gama ya tunkaro ta ta mik e ta fara magana ba tare da ta kallesa ba Ai ni nace maka anan zan kwanta Allah kar ma kayi tunanin haka! Idan kuma neman maganata za ka yi to wallahi zance na fasa sai da ka dawo ka cigaba da kwana a sofa kuma ko zanga k afafuwanka suna lankwashewa kana tafiya da kyar ba zan sake y...... Dip! Maganarta ta d auke sakamokon d aukarta da yayi tashi d aya in a bridal style Ba tare da ya kalletaba ya fara tafiya da ita towards the bed. Tsoro da mamaki da kuma yanayin da ta tsinci kanta a ciki ne suka sanya ta kasa magana ko yunk urin zamewa.. In banda kallon gefen fuskarsa ba abunda take yi har ya isa bakin gadon ya sunkuya ya kwantar da ita rigingine a kan gadon ya d aura mata kanta a kan pillow ya zame hannuwansa. Ba tare da ya d ago daga sunkuyon da yayi a kanta ba fuskarsa dan da tata ya d ago da idanuwanshi ya sanya su cikin nata a hankali yace Sleep here. Dan Allah Sannan ya mik e tsaye ya zagaya d ayan side d in ya kwanta. Sai a lokacin ta samu ta sauk e wata siririyar ajiyar zuciya mai vibration kamar mai jin sanyi. A hankali taji yace Ki yi addua, good night ............ Ita dai Hudan a yadda ya barta nan rigingine tana kallon sama a haka ta farka ta ganta lullub e da bargo, daga cikinta zuwa k asa..ba ta san lokacin da barci ya kwasheta ba. Ko ba a fad a mata ba ta san Aslam d in ne ya lullub eta. Kiran sallar da ta ji ne ya sanya ta fahimci tabbas yau ta d an makara dan kamar ma har an shiga masallaci, ta ji. Addua ta yi tukunnan ta d an juya ta kalli side d in da ya kwanta. Ga mamakinta sai ta gansa kwance a kan gefen damanshi yana facing d inta.. Bacci yake yi peacefully kamar kuma da murmushi a kan fuskarsa. Kamar yadda ya rufe mata rabin jikinta haka nan shima ya rufu da bargon. Jin an tada ik ama yasa ta d an matsa kusa da shi ta fara kiran sunanshi A hankali yake bud e idanuwansa, kafin ya k arasa bud e su tarr a kan fuskarta! Murmushi ya sakar mata a hankali taji yace Lucky Morning Shiru tayi taana kallonshi shima itan yake kallo chan ta d auke idonta da sauri tace Zaka makara fa, har an shiga sallah. Da sauri ya mik e ya d an dafe kansa yana mutstsika idonshi kafin ya sauk a akan gadon ya fad a toilet. Ko da yaje har an tafi ruku dan haka raka aya ya samu. Haka nan suka dawo tare da su Shuraim da Arshaad Sudais yana cewa Arshaad Ya kamata ya yiwa Ya Aslam bulalar makara sallar asuba yau Murmushi kawai Arshaad d in yayi ba tare da yace musu komai ba ya wuce d akinsa. A shirye ya tarar da Huda, suna gaisawa ta fice zuwa kitchen don had awa Abba abunda ta san yafi so. A kitchen d in ta tarar da Ummi don haka suka taru suka had a masa lafiyayeyyen breakfast.. 6:30am, Aslam ya fice tare da Sudais suka tafi d auko su bayan shi da Hudan sun yi wishing d insu Happy birthday sun basu gifts d insu shi da Shuraim. Kafin 8:00am suka dawo, Daddy direct side d insa ya wuce Abba ma suka nufi side d inshi shi da su Aslam. Da gudu Hudan taje ta yi hugging d inshi tana murna haka ma Shuraim, daga nan aka shiga gaggaisawa. Ummi, ba kad an ba tayi matuk ar jin dad in yadda Abba ya yi mata faram faram! Dan haka ta samu kwarin guiwa ta hau gabatar masa da abinci kala kala ita da Hudan. Cike da farin ciki yake karb a yana ci dan Huda da Shuraim da Sudais ke bashi a baki one by one duk da Sudais yana ta yi musu kwange A haka suka ciyar da Mahaifin nasu cike da tsananin so da k aunar juna. Sai da ya k oshi aka tattare wajen ya fara shirin mik ewa tukunna Arshaad ya fito. Cike da kulawa Abba yayi welcoming d insa daga nan ya wuce sama bayan ya bawa Ummi briefcase d insa yace ta kai masa dakinsa Shuraim kuma ya ja masa trolley d inshi. Bai tarar da Shuraim a d akin ba, sai Ummi ita kad ai ya tarar ta juya baya tana k ara turaren wutan da ta saka tana d an fifitawa akin ya sha gyara ba kad an ba gwanin sha awa. A hankali ya k arasa inda take tsaye yayi hugging d inta ta baya. A mugun zabure ta juyo dan sam! Ko da wasa bata yi expecting haka daga Abban ba. an guntun murmushi ta gani kwance a kan fuskarsa, a hankali yace Ko ba a shirya yi min wannan tarbar ba? Ummi bata san lokacin da ta fashe da wani kuka ba, ta fad a jikinsa cikin kukan tace Abba ka yafe min dan Allah kayi hak uri
Chapter 25 · 0% Book details