← Book details So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 69

Sashe 22

So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ki d agamin hankali da yammar nan! Bana son irin wannan maganar in sha Allah babu inda zaki je ki barmu muna tare... Kukan da ya kufce mata ne ya hanata kasa k arasa maganar tata. A hankali Shuraim ya yi hugging d inta sannan ya d ago idanuwanshi da suka taru da kwalla ya kalli Ummi yace Ummi Ki daina irin wannan maganar please, muna tare happy family together forever in sha Allah Ya fad i hakan yana murmushi. Murmushi Sudais yayi sannan yace Group hug! Ya had asu duka yayi hugging yana dariyar son ganin ya kawar da sad moment d in. Suma duk dariyar suka saka suna sharar kwalla. Sun d an jima a haka tukunna Shuraim ya jaa kujerar ya zauna yana cewa Let me eat small.. Yau haddar pages biyu nayi, tunda muka tashi a English section nake abu d aya amman dukda haka sai da Mu allim ya rankwasheni, duk cikina ya zuge Tray d in Aslam ya shiga k arin janyowa, nan Ummi ta hanashi ta hanyar buge masa hannu. Hudan na dariya ta shiga ta d auko musu nasu wanda ta saka a cooler. Nan kuwa suka hau ci suna santi dan ana bud e cooler Sudais ma ya dawo yace ya fasa tafiya saman Dariya kawai suka yi musu daga nan Ummi ta d an jaa ta gefe tace One last thing Taje ta yi wanka ta shirya.. Yana zuwa idan ya ga ta yi miishi kwalliya nan da nan zai barta maybe ma ya barta ta kwana, haka ake yiwa maza .tayi sauri maza maza taje ta shirya yana.. Tun kafin Ummi ta gama magana Huda ta wuce sama d auko kayanta kunya da kuma son aikata abunda Ummin tace ne ya sanya ta kasa tsayawa taji k arshen maganar. Kamar yadda ta had a akwatinta ta hau da shi saman hakanan ta had oshi harda kayayyakinta waenda ta d an d auraye ta shanya, ta kwaso ta sauk o da su. Ba iya d akin ba Hatta parlourn zuwa yanzu ya d auki k amshin turaren wuta. Tana shiga ta ajjiye akwatin ta fad a tayi wanka tayi brush ta d auro alwallar Magrib dan ta gabato, ta fito d aure da d an guntun towel saboda bathrobe d in da ya had a ya wanke a washinne machine ya shanya tare da inner wears d insa har yanzu bata gama bushewa ba. Wani had en d inkin doguwar riga A shape ta fitar, kalar atamfar royal blue an yi mata d inki irin mai stones d innan A hankali ta ware bra da pant sannan ta kinkimi akwatin nata ta nufi wardrobe ewa tayi ta sa akwatin nata a chan k asa sakamokon kayansa da ta gani a jere a side har biyu! A ranta tace Wato har wasu kayanma ya sake kwasowa Ummi tana chan tanata cewa In dawo d akin bayan shi gashi partyn shi ma yake yi ya samu freedom Kamar tana ganinshi haka ta ke kallon kayan tana zabga musu harara Idanunta ne suka sauk a abkan wata takarda kamar poster haka a ta chan k asan takardar taga an rubuta 2021 tournament mathematics competition Winner NTIC Da k arfi taji gabanta ya buga! Da sauri tasa hannu ta zaro sticker ..tun bata kai ga k arasa zarowa ba ta fahimci ita d in ce da gaske! A hankali ta cirota daga k asan kayan nasa tana kallo tana sake kallon hotonta da sunanta b aro b aro a sama Maryam Huda Muhammad Ga award d inta a hannunta da medal d inta tana murmushi Kanta ne ya d aure ta fara k arin juya takardar dan kamar da tana zarowa taga rubutu a bayan da biro. Bincike fa babu kyau Taji muryarsa a bayanta daff da ita!. Bata san lokacin da ya shigo ba amman ta d anji k amshin turaren da yake tashi ata jikin kayanshi ya k aru a d akin. Kwakwalwar ta already a cunkushe take ga tarin mamaki gashi dama duhu ya d an farayi bata kunna globe ba tana d anjin tsoro hakan ya sanya da taji mutum da murya a bayanta ta kwala ihun da ita kanta sai da ta d an tsorota Da sauri ya juyo da ita ya sa tafin hannunshi akan bakinta yace Shiiii. Da sauri itama ta sanya dukkanin k arfinta ta b intike hannunshi daga bakinta kafin tace Ya Aslam banaso Allah ka daina Ta fad i hakan tana k arin kare jikinta a rikice dan ba k aramin kunyar towel d in take yi ba. Dariya ma shi ta basa Yarinyar da ya gama k arewa kallo ba tare da ta san ya shigo ba itace take wani kakkare jikinta Wani d an guntun murmushin gefen baki yayi sannan ya kama towel d in ta sama yace Idan ban daina ba fa? What will you do? Yaji za ki sake yi min ki gudu sama , ko me? Ya fad i hakan yana d an jan towel d in kad an kamar zai fisge. Cikin tsananin tashin hankali ta sake kurma wani ihun a karo na biyu Ido cikin cikin suke kallon juna, so take ta d auke idanunta a cikin nashi amman ta kasa sakamokon sak onnin da yake aika mata daga kwayar idanuwan nasa. A hankali ya bud e baki zai yi magana yaji an turo k ofar d akin da d an k arfi an shigo..................... 5 MINUTES BEFORE NOW. Ummi, sauk owarta kenan daga sama zata d auki abu a kitchen, sam bata san Aslam ya dawo ba. Tana shiga kitchen d in taji kamar an shigo dan haka ta d au abunda take buk ata ta fito tana kallon k Sakin lemon hannun nata tayi ya fad asa cike da mamaki da murna tace Arshaad!! Sai kuma ta k arasa da sauri bakin k ofar inda yake tsaye ta hau dudduba shi tana murmushi fuskarta cike da murna da farin ciki. BULAMA So da Buri Free Book Mikiya Writers Association. Murmushi Arshaad ya yi kafin a hankali yace Ummi, na same ku lafiya? Sai a lokacin Ummin ta yi laakari da yadda bashi da lakka a jikinsa da kuma tsananin ramar da yayi. Alhamdulillah tace, sannan ta d aura da cewa where have you been? Still yanzun ma murmushi ya sake yi, a hankali yace Bara in d an huta Ya fad i hakan yana mai wucewa ya shige cikin parlourn, wanda sai da ya zo wucewar ne tukunna Ummi ta lura da akwatin da yake tafe da shi! Gabanta ne taji yad an buga! Gashi babu damar ta tsayar da shi ko ta hanashi wucewa, a k asan ranta tace Anya kuwa zaman su Aslam da Arshaad zai yiu a waje d aya? Tana cikin wannan tunanin ta jiyo ihun Hudan! Dakatawa Arshaad yayi ya juyo ya kalleta kafin yace Kamar muryar Huda.. Shiruuu, Ummi ta d anyi, chaan kuma ta sauk e wata nannauyar ajiyar zuciya tace Eh, suna nan, Granpa refuse to accept them Ya bud e baki kenan zai yi magana suka sake jiyo ihunta a karo na biyu.. Ita Ummi har ga Allah tayi tunanin wani abun ne ya sameta dan batayi zaton Aslam d in ya dawo ba! Shiyasa tayi saurin nufar d akin, ba tare da b ata lokaci ba shima Arshaad ya bi bayanta da sauri NOW. Wardrobe d in a setin k ofar yake a ta tsaye! Shiyasa suna shiga suka gansu Da mugun sauri Arshaad ya juya Ummi kuwa da kyar kunya ta barta ta iya jan y an k afafunta ta bar wajen. Ko kyallin Arshaad bata gani ba, ga de akwatinsa nan a tsakar parlourn inda ya barshi Wucewa tayi sama da sauri dan ji tayi kamar za a bud ofar d akin su Hudan a fito. Achan d akin kuwa su Ummi suna fita Huda tasa kuka! Ba abunda yafi d aga mata hankali irin Ya Arshaad wanda suka had a ido dashi! Shikenan ta san yanzu zai ce taci amanar sa ta gama! Bayan ko sati uku ba ayi da yin bikin ba Shiruu, Aslam ya d anyi yana kallonta ta rufe idonta tana kuka ta duk une a tsaye waje d aya, ajiyar zuciya ya sauk ..a hankali taji kamar ya bar wajen. Addua take yi Allah yasa fita zai yi, ai kuwa a hankali taji ya bud ofar ya fita. Tana bud e ido taga ita kad ai, ajiyar zuciya ta hau sauk ewa a jejjere, da kyar ta samu ta d an nutsu tukunna ta soma k arin barin wajen.. Poster da ta sub uce a hannunta d azu ta taka! Kalla tayi ta sake kallo kamar tanason yin nazarin wani abun chan kuma sai ta lumshe idonta ta bud e kawai ta d auka ta mayar inda ta ganta. Jikinta duk a sanyaye hakan nan ta samu ta shirya da kyar ta nemi waje ta zauna. Aslam yana fita ya fara k arewa falon kallo kamar akwai abunda yake nema. Yana cikin kallon parlourn Idanuwanshi suka sauk a akan trolley madaidaici. Wani yawu ya had iye mai d an d aci tukunna ya furzar da iska ya nufi d akin da yake da tabbacin Arshaad d in yana a ciki. Knocking ya tsaya ya d anyi, jin shiru yasa ya tura k ofar ya shiga Ganin ba kowa ya sanya yayi tunanin to ko dai ba nan d in ya shigo ba, har zai juya sai ya jiyo motsin ruwa a toilet. A hankali ya sauk e wata siririyar ajiyar zuciya kafin ya koma ya nemi waje ya zauna a bakin gadon. Morethan 10 minutes Arshaad ya d auka a band akin bayan shigowar Aslam. Har Aslam d in ya fara tunanin lek awa a ransa yana tunanin maybe ko baya ciki an yi mistake d in barin fanfo a kunne ne sai kuma yaji an kashe tap d in! Still sai da ya k ara 2 minute tukunna ya fito ya na tsane fuskarsa da towel A tunanin Aslam wanka Arshaad d in yayi amman fitowar da yayi sanye da kayan jikinshi ne ya sa ya fahimci ba wanka yayi ba sai dai ko alwallah dan gashi
Chapter 22 · 0% Book details