← Book details So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 69

Sashe 1

So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry WordDocument 0Table Data Normal So da Buri Free Book A hankali yake bud e idanuwansa.. Hasken da ya gani tarr!! A kansa ne ya sanyashi maida idanun nasa ya rufesu dan lokaci guda yaji kanshi yayi wani mugun sarawa. Da sauri Mommy ta matso ta kama hannunshi tana murmushi tana goge hawaye tace Dad, kaga ya farka, yanzunnan naga ya bud e idanunsa. Da sauri Dad ya matso ya d an shafa fuskarshi sannan ya juya da sauri yana cewa bara in kira Likitan, Alhamdulillah. A hankali yad an damk i hannun Mommy da yake a cikin nashi, da sauri itama ta d aura d ayan hannunta a kai tace Aslam, sannu mai kake so? Ya jikin?. Sai da ya sauk e ajiyar zuciya sannan yace Hasken yayi min yawa Da sauri ta mik e ta rage hasken d akin sosai sannan tace Na rage A hankali yake bud e idanuwanshi da sukayi mishi nauyi sosai. Fuskar Mommy ya gani tana kallon shi tana murmushi. Murmushin shima ya sakar mata sannan ya fara k arin tashi. Da sauri tasa hannu ta taimaka mishi, sannan ta saka mishi pillow a bayanshi ya d an jingina. Yana gama gyara zaman shi tayi huggin nashi sannan tace Congratulations Son Shiruuu, yayi chan kuma yasa hannu ya zarota daga jikinshi kafin yace Mommy dama ba mafarki na yi ba? Murmushi tayi ta kama kumatunshi ta d an ja sannan tace Ba mafarki bane! Angon Huda. Dai dai nan Dad ya dawo da Likita yana binshi a baya. an gwaje gwaje Likitan yayi sannan ya tambayeshi ina ke yi mishi ciwo? Ya yake ji a jikinshi? A hankali yace Nothing much.. Kawai kainane yake d an sarawa kad an kad an rubuce rubuce Likitan yayi daga nan ya basu discharge yace su yi signing daga nan suna iya wucewa bayan an siya mishi waennan drugs d in. Ba wani abun bane yake damunshi Like he said before Kawai shock ya shiga, shiyasa ya suma! But he s okay now. Allah ya kare gaba Daga haka ya juya ya fita. A hankali Dad ya nemi guri ya zauna a kan kujerar daf da gadon sannan yace Aslam I m sorry! So sorry. Ban yi tunanin abun zai b ata maka rai har ya kaika ga haka ba! Shiyasa kawai da Abba ya zo mana da wannan shawarar muka amince daga mu har iyayen Mahaifiyarta. Aure an riga an d aura! Ina rok on k a da kayi hak uri ka danne zuciyarka kar kayi wani abun da zai musguna mata kaga itama Yarinyar ba so take yi ba! Wannan zab in mu ne. Ku zauna lafiya, in sha Allah wata rana za ku so junanku. Kar kayi anything da zai saka mu a kunya ko dan y an tsofaffin nan Mahaifin Mahaifiyarta wallahi har ga Allah nayi tunanin idan aka gaya musu sauyin da aka samu da matsalar data taso ta wajen Arshaad ba za su yi farin ciki da kai ba amman sam ko a fuskarsu bamu ga komaiba a take suka goya mana baya d ari bisa d ari. Sannan, na san Abba kamar uba yake a wajen ka kaima amman dan Allah Aslam ka daure kaga dai yanda ya daure dukda iri k iri ya kusan jin kunya saboda d a na amman bai damuba haka ya sake yunk urin ya k ulla aure tsakanin y arsa da kai! Kar ka bani kunya Aslam dan Allah Dad ya k arashe maganar yana mai had e hannuwanshi biyu yana kallon Aslam d in alamun, roko. Da sauri Aslam d in ya matso ya kama hannun Dad d in ya sauk ar k asa: Shiruuu, d akin yayi kowa ya kasa cewa komai. A hankali Dad ya mik e yace Mu je. Idan mun fita sai Ado ya tsaya a karb a maganin a pharmacy Yana gama fad in haka ya juya ya fice. Gaba d aya hankalin Aslam baya cikin d akin har sai da Mommy ta d an tab a fuskar shi tukunna ya juyo yana kallon ta. Tana shirin yin magana ya riga ta ta hanyar cewa Ina Arshaad? Ita kanta Mommy sai da gabanta ya fad Sam murna da farin cikin da take ciki sun hanata tuna Arshaad d in ita kam tun d azu da sukazo asibitin In ba yanzu da Aslam yayi mata maganar sa ba! A hankali ta sauk e ajiyar zuciya kafin tace ll be okay. Ka ji? Kar ka damu. A hankali ya lumshe idanuwansa yana shirin yin magana kiran Dad wanda ya shigo wayar Mommy ya katse su. Tana d auka yace Akwai damuwa ne? Naga baku fitoba har yanzu Da sauri Mommy ta mik e tsaye sannan tace Babu, muna tahowa Sannan ta ajjiye wayar ta kama hannun Aslam wanda yake jin gaba d aya jikinshi yayi sanyi. A hankali ya mik e ya bi bayanta suka fita tare. A hanya aka tsaya drivern ya siya drugs d in daganan suka wuce Har suka isa gida kowa da abunda yake tunani! Suna shiga ya nufi side d inshi yana mai cewa Mommy yana d an buk atar ya huta kawai tace suka wuce ita da Dad sama. Yana shiga d akin shi ya fad a toilet yayi alwala ya fito ya hau jero nafilfili Su mommy suna hawa, Dad ya kira Daddy yace mishi ya cewa Auwal Mom da Ummi su taho da drivers da motocin mansion d in duka a had u a bakin estate za aje a d auko Amaryar Aslam. Ya yiwa Granpa bayani ta watasapp, Granpa d in ya ce masa okay he ll get back to him later So kawai a kawota estate d in idan an tashi. Cikin mintunan da basu gaza ashirin ba Mommy da Gwaggo Asabe suka shirya tsaf suka fito. Suna fita a estate d in suka had u da su Mom da tawager su don haka suka yi convoy suka nufi gandun albasa 12:00pm(earlier) Tun lokacin da su Dad suka fita Arshaad ya kasa zaune ya kasa tsaye! Gashi wani abun takaicin still Mammy ta hanashi fita. Yana ganin kiran Auwal yak agawa dan kwata kwata baya buk atar wata hayaniya.. Tunani kawai yake yi akan me zai yiwa Mammy ta barshi ya fita sannan a tunaninshi ya san Auwal d in ce mishi zai yi yayi sauri ya san yadda zai yi ya fito kawai.. Duk da dai ya san cewa su Dad ba za su tab a fasa d aura auren saboda Mammy ba amma yana buk atar zuwa He needs to be there dan bai kamata ace ya zama absent a rana mafi soyuwa a rayuwarshi ba. Suna a haka yaji wayoyinshi gaba d aya ukun sun haukace da k ara!!! Anfi minti goma amman duk ciki babu wadda ta huta, kiran yana katsewa wani yake kuma shigowa. A hankali ya k arasa kan gadon nashi inda ragowar biyun suke zube ya fara dubawa... Jamil ne da ragowar Abokanayensa suke ta antaya mishi kira Haka kurum yaji jikinshi ya d au rawa sannan zuciyarshi ta fara wani kalan mahaukacin gudu! Da kyar ya iya amsa kiran Jamil, tun kafin ya kaita ga kunnuwanshi ya juyo muryar Jamil d in yana cewa Garin ya haka ta faru Arshaad??? Da sauri ya kai kunnenshi kafin yace Sorry Jamiel, wani abu important ne ya taso ya hanani zuwa Kamar ya Wani abu important shi ya hanaka aurenta? Cikin rashin fahimta yace ban gane ba! Ba a d aura auren namu ba har yanzu? Fahimtar da Jamil yayi Arshaad d in bai san halin da ake ciki bane yasa yace Haba! Biri yayi kama da mutum.. Ni daman na san kamar da wuya ace wai ka hak ura da Huda! Anyways aikin gama ya riga ya gama yanzu kam An d aura wa Huda aure yanzunnan nima shaida ne Amman ba da kai ba Yayanka Aslam... Diff!!! Haka Arshaad ya d auke wuta! Hello helloo helloo Haka Jamil yake ta maimaitawa amman shiruu! Yadda ya k ame ya k i motsi sai da hakan ya d an tsorota Mammy dan haka ta taso ta matso kusa da shi ta tsaya tace Kaii lafiyar ka k alau kuwa?? Sai a lokacin ya samu damar jan numfashi lokaci d aya kuma ya saki wayar hannunshi ta fad asa ta tawarwatse! Da sauri Mammy ta shiga gabanshi da kyau tayi cupping fuskarshi tace Kaii, ba dai hatsari suka yi ba ko? Ka yi min magana ni duk kabi ka d aga min hankali Wani irin jan numfashi yake yi wanda yayi mugun tsorata ta! Cikin tsananin b acin ran da bata tab a ganin shi a ciki ba yace Abunda kike so ai kenan! Kowa ya mutu kowa ya lalace kowa ya shiga tashin hankali! Ko ba shine abunda kike so ba? Ya k arashe maganar cikin tsawa! Cikin b acin rai Mammy tace Kai! Dan ubanka ni uwarka ce! Kar In sake ji ka d aga mun murya idan ba haka b...... Kafad unta da ya kama duka biyu da mugun k arfi ne ya sanyata tayi shiru Girgiza ta yayi da k arfin gaske sannan yace Uwa! uwa!! uwaaa!!! Shine kalmar da kika yi amfani da ita kika tarwatsa mini rayuwa Tarwatsawa ta har abada! Ki kasheni kawai Mammy na rok eki da girman Allah ki kasheni in hutu! Kin riga kin kasheni a bad ini saura na zahiri. Yana gama fad in haka ya cika mata kafad un nata da k arfi wanda har sai da tayi baya kamar zata fad i, ji yake yi kamar ya d agata sama ya kauce! Da k arfi ya fincike hular kanshi sannan ya cire babbar rigar ya jefar! Yana juyawa yayi facin mirrow d in jikin wardrobe d inshi wanda gaba d aya k ofar wardrobe d in mirron ne da mugun k arfi ya dunk ule hannunshi ya daki mirrow d in rabi ya tarwatse! Hakan bai yi mishi ba ya sake rarumo stool ya buga mirror d in ya k arasa tarwatsewa! Da sauri Mammy wadda abun ya fara bata tsoro ta k araso ta rike shi ta baya tayi hugging d inshi.., Gaba d aya d akin ya b aci da jini
Chapter 1 · 0% Book details