← Book details So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 69

Sashe 65

So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ya nuna min jakar yasa na fahimci yana gani..... Ina d aukowa ya ce In bud Ko da na bud in wasu takardu ne a ciki da waya iya mai kyau da tsada. Wayar ya umarceni da in d auko, in yi dialing number dana ga an yi saving da barrister Haka akayi, tana shiga bugu d aya ana biyu aka d aga! Cikin girmamawa na ji ance Da mamaki na kalli tsohon wanda shi kuma yake mik a min hannu alamun in bashi wayar Kaina bai gama d aurewa ba sai da na ji kalar turancin da tsohon yake yi inda cikin harshen turanci na ji yana cewa wannan wanda suke waya Suna kusa ko? To su yi sauri suzo yanzu. Tsoro da firgici suka sanya na mik e da sauri na fara ja da baya. A hankali tsohon nan ya ce Dan Allah kada ka ji tsoron komai. Matso kusa in baka wani d an tak aitaccen labari. Da farko k in yarda na yi in matsa d in dan ni a tunanina ko d an shan jini ne ko kuma d an 419 bare ma da na tuno da mak udan kud en da aka kawo mishi gaba d aya sai na sake duburbucewa. Da kyar da sid in goshi ya lallab ani na matsa kusa da shi. Ina zama ya ce min Kar ka ji tsorona d ana, Ni ba macuci bane ba Bai bani damar yin magana ba ya cigaba da cewa Kamar yadda na fad a maka da farko Allah bai bani haihu wa ba. Na kasance attajiri na gaske dan a k asar nan idan akwai waenda suka fini kud i tou bana jin za su fi mutum biyu! Arzik i na ya samo asali ne daga sana ar man fetur, da na samu Ubangiji ya sanya mini albarka harkar tawa ta bud e sai na fad a sana Business ko wanne iri ne zan yishi kuma da ikon Allah Ina farawa sai ya habb aka ya yi albarka ta ban mamaki. Ni asalina maraya ne, tun Ina gidan marayu muke soyayya da matata da na ce maka ta rasu watan baya. Ina matuk ar k aunarta sai dai kuma kishiyoyinta suka zamo silar da ya sanya bata ji dad i a rayuwarta ba! Ta rayu cikin tsananin k unci da azabar rayuwa. Ni mutum ne wanda yake son mutane masu amana, bayan son da nake yi wa uwar gidanaa tsoron Allah da amanarta ne suka k ara min tsananin k aunarta. Apart from her bana jin akwai wanda ya tab a rik e mun amana yayi mun abu tsakaninshi da Allah sai kai Junaidu. Na sha adopting Yara in rik esu tsakani da Allah amman kowa idan ya lek a ya hango tarin dukiyata sai ya nemi cutar da ni! Rabinsu ma buri suke kawai suga sun halaka ni. Da taimakon Allah da taimakon uwar gidana nake tsere wasu tarkunan wanda fahimtar da aka yi tana taimaka min ne yasa aka shiga tsakaninmu na juya mata baya. Cikin kuka ya ce Ban tashi gane gaskiya ba sai a ranar da zata bar duniya tukunna aka samu asirce asircen suka bar jikina na ganta a matsayin masoyiyata instead of da da nake ganinta as my enemy. Na yi kuka ma yi takaici! Saboda ita take d awainiya da ni idan ciwona ya motsa Ina kyararta Ina komai ashe itama bata da lafiya. Duk da na saki ragowar mata na biyun da na fahimci laifin su ne sannan na bata hak uri ta ce ta yafe min amman na kasa yafewa kaina! A ranar da zata bar duniya maimakon ni in lallasheta A dead bed d inta sai ya samana ita take lallashina. Na yi rashi tabbas sannan na san na rasa mutum d aya tak da ya tab a rik e mun amana. Ita ce ta ce min In kwantar da hankalina zan samu wanda zai rik en amana kamar ita I should mark her words. Bayan ta rasu da kwana biyu.. daman tun kafin a shiga tsakanin mu na yanke shawarar zan damk awa mutum mai amana guda d aya rabin dukiya ta idan na samu kenan, rabi kuma in rarraba a gidan marayu, ba wai kuma masu kula da gidan marayun zan bawa in ce su raba musu ba Yaran gidan marayun zan bud ewa account each In saka musu kud insu a ciki saboda yadda duniya ta lalace tsaf mutane za su iya danne kud in dan na ga yadda mutum yake komawa akan dukiya Saboda haka na fara searching A yadda na je maka a haka nake zuwama mutane amman har da waenda suka mareni! Mutum d aya na samu kafin kai ya taimaka min kamar yanda ka yi sai dai shi ana kawo kud i kamar yanda aka kawo aka baka ya gudu! Ko lek e na bai sake yi ba....... ....... Muna cikin wannan zancen Mutannen da ya kira suka k araso. Manyan lauyoyine da kuma wani babba a efcc. Da mamaki nake kallonsu. Ban san sanda hawaye suka zubo mini ba! Jin yana musu bayani akan yadda ya yi alk awarin bawa mai kyakkaywar zuciya dukiyarsa. Hope takardun sun zama ready? Saboda gani nan Ya yi maganar yana nuna ni ya ce Nine successor d insa A take suka ce komai is ready Sannan suka mik o min takardu suka ce in yi signing. Da farko kasawa na yi saboda yadda mamaki aljabi da tsoron Allah ya lullubeni, sai da tsohon ya rik e mun hannu tukunna na dawo dede na shiga signing takardun da kwakwalwa ta ta kasa d aukar d umbin kud en da idanuwa na suke gane min!. Ina gama cike wadannan tsohon ya ce yaso ya rabawa marayun kud en da kanshi amman kuma bashi da isheshen lokaci so zai d aura wannan nauyin a kaina Nan ma wasu takardun na cike na kud i shima dede adadin wanda aka gama mallakamin wanda zan rabawa marayun nan. Jakar da d azu ya ce In d auko in bashi waya a ciki Ita kuma filayene da gidaje da gidajen man fetur d insa, ya ce min I should consider it shikuma as thankyou from him, dan bai san ta Ina zai fara yi min godiya ba! Na tabbatar da maganar matarshi sannan na bashi hope na cika mishi burinshi. Daga nan duk ya saka na yi signing Ina kuka yana kuka. Sannan ya bada will d in nine d ansa sannan ya rok eni ko bayan ranshi in dinga yi mishi addua dan Allah. Ganin numfashinshi yana d aukewa yasa na kinkimeshi muka kai shi motar da mutanen nan suka zo a ciki amman Ina kwantar da shi a seat d in baya na ji yayi kalmar shahada a hankali sannan jikinshi ya sake...... Na yi kuka matuk a..... Ban yi k asa a guiwa ba, tundaga Adamawa har Abuja sai da na je da kaina na fara rarrabawa marayun nan rabin kud en shi da na yi alk awari wanda har yau ina kan aikin. A hankali Junaidu ya sauk e ajiyar zuciya kafin ya ce Wannan shine sanadin arzik i na. Babu k arya k ari ko ragi a cikin labarina. ...... A hankali su Abba suka sauk e ajiyar zuciya bayan sun gama saurarenshi kafin Abba ya ce Tabbas Junaidu samun irinka a zamanin yanzu sai an tona. Allah ya yi maka albarka. Ka cigaba da rik e amana da alk awari Allah yasa ka gama da duniya lafiya. Idan mun gana magana za ka ji sak on mu daga wajen Aaima in sha Allah. Cikin girmamawa ya yi musu godiya daga nan suka yi sallama ya wuce......... Bayan sati d aya Aaima ta ce masa su Daddy sun ce yana iya turowa anytime idan sun shirya Tsakanin Aaima da Junaidu ba zaka iya tantance wanda yafi wani farin ciki ba. Su Kaka da Ya Jamilu ne suka zo suka nemawa Junaidu auren Aaima. A parlourn Daddy aka tarbesu tarba ta mutunci! Cikin mutunta juna suka yad a manufarsu suka nema aka basu. Wata biyar ciff! Aka saka ranar auren daga nan suka bayar da goronsu da alawa da kud i nera miliyan d aya! Aka watse cikin farin ciki barkwanci mutunta juna da nishad
Chapter 65 · 0% Book details