← Book details So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 69

Sashe 19

So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wuce kije ko? Kar Aslam d in yaga kin dad e, yau ma na san da wurwuri za su fita. Kiyi sauri kije ki tayashi shiryawa, ko? Kuka kawai taji Hudan ta kece dashi kamar wadda akace za a yankata! Cikin kukan tace Ummi dan Allah karki bari in koma, Allah ba zan iya had a ido da shi ba, baki san meh.... Kamar kuma wadda aka datse harshenta sai ta tsaya da maganar chak! Tana mai ci gaba da kukanta. Murmushi Ummin tayi ranta fess. Tace mata to shikenan jeki ki yi alwala ki yi sallah ki daina kuka haka. Anjima sai muyi magana ko? Muje d akina. Tayi maganar tana jan hannunta..... Bayan, Ummi ta gabatar da sallar Asubah, ta yi azkar, ta zauna ta hau nazari Wani sanyi da dad i take ji a ranta..ta san Huda Arshaad take so amman tabbas kamar yanda su Dad sukace Ko bayan auren Mammy bazata barta ta zauna lafiya ba Aslam shine wanda take gani zai bata cikakkaiyar kula da soyayyar da take buk ata, bayan haka sun yi mugun dacewa sannan ita daman ta d an fahimci kamar Aslam d in yanas son Huda! In dai kuwa hakanne Allah Ubangiji ya barsu tare ya k ara musu k aunar juna ya sanyasu farin cikin da basu yi tun tasowarsu ba A zaune taga Huda ta fara gyangyad i dan haka tace mata ta tashi ta kwanta a kan gado Da sauri kuwa Hudan ta mik saboda daman addua take tayi kar Ummi tace mata taje ta had awa Aslam breakfast. Tana kwanciya bata dad e ba bacci ya kwasheta Ummi kuma ta mik e ta fita dan had a musu breakfast d in.. Tana cikin bacci taji muryar Abba yana kiran sunanta, a hankali ta bud e idanuwanta. Zaune ta ganshi a gefenta yana mata murmushi dan haka itama ta d anyi murmushin sannnan ta mik e ta zauna tace Abba Ina kwana Lafiya, Alhamdulillah. Kin tashi lafiya? Alhamdulillah Tace ewa taga yayi tsaye kafin yace Zamu wuce UK ni da Daddy. Urgent tafiya ya taso, akwai abunda kike buk ata? Murmushi kawai tayi tace Ba komai. Allah ya kiyaye ya tsare hanya ya dawo daku lafiya A hankali ya d an matso ya shafa kanta yace Ameen princess, take care. Sai mun dawo ko Yana gama fad in haka ya juya ya nufi hanyar fita, har ya kama handle d in sai kuma yaga rashin kyautawarshi dan haka ya juyo ya kalli Ummi dake gefe a tsaye yace Na tafi. Zan saka miki kud i ta account ko akwai abun buk ata. In akwai wani abun you can call me Wani kalan murmushin farin ciki ne ya baiyyana a kan fuskarta, tana murmushin tace Nagode. Sai kun dawo Murmushin daya mayar mata ne ya bata kwarin guiwar binsa a baya domin tayi mishi rakiya. Hudan ma taso ta rakasa amman ganin sun fita da Ummin ya sanya ta bari kawai, dan ta barsu su samu alone time su biyu. Kallon agogo tayi taga har 10 ya d an gota. Ta san by now Aslam ya fita dan haka ta sauk e ajiyar zuciya ta zuro k afafunta k asa tana tunani da mamakin guts! Kalar na Ya Aslam .mai yasa yayi mata hakan? Ya san ba sonta yake yi ba mai yasa zai dinga yi mata wasu abubuwan kamar waenda sukayi auren soyayya!? She definitely has to stay very far away from him har sai ta gano inda relationship d insu ya dosa da ita kanta dan gaba d aya Aslam ya juya mata lissafi kwana biyun nan kanta duk ya d aure s like bama ta san me take so ba! Tabbas ta san tana son Ya Arshaad sannan tana son rabuwa da Ya Aslam Amman kuma when ever she s with him she feels complete and safe! Da farko bata fahimci hakan ba sai a jiya da yayi hugging d inta ta kasa kwace kanta daga k arshema bacci ya kwasheta Ajiyar zuciya ta sauk e, a chan k asan ranta tace A complicated marriage is enough! I can t deal with complicated and confused relationship. Tun d azu idan ta tuna da moments d insu na tsakanin jiya da yau da safe sai taji tana feeling somehow bata k aunar wannan feeling d in at all bata son abunda zai na janta garesa shiyasa gara tun kafin ta gama zama confuse tabbas ya kamata ta d au mataki A haka Ummi ta shigo ta sameta. Tunanin me kike yi? Taji muryar Ummin. A hankali ta d ago ta kalleta sai kuma ta maida kanta k asa tace Ina kwana Murmushi kawai Ummin tayi tace Lafiya sannan tace Oya tashi ki shirya mu yi sauri mu tafi ko? Ai tun kafin Ummi ta ida rufe bakinta Hudan ta sauk a ta fita daga d akin cike da d oki. Murmushi kawai Ummin tayi itama ta hau nata shirin Sai pass 11 sannan suka shirya suka fito Hudan bata wani yi kwalliya sosai ba, Abaya ce a jikinta nude colour mai kyau sosai, tayi rolling ta d an saka lipstick, sai zobe da bracelet a hannunta. Ummi kuma lace ne mai kyau da tsada a jikinta peach da farin mayafi da jaka da takalmi. Suna baya suna d an tab a hira driver yana jansu, haka suka kama hanya A wani babban mall Ummi ta cewa drivern an tsaya Dai da suka fita tukunna ta bawa Hudan kud i, tace azu Aslam yace abata ta yi siyayyan tsaraba ta kai gida Angode kawai ta iya cewa daga nan suka shiga sukayi y ar siyayayr tsarabar suka fito Ummi tana lura da yadda mood d in Hudan ya chanza tun daga lokacin data ambato sunan Aslam So take ta fassara yanayin nata amman ta kasa a haka driver yayi parking a kofar gidan Madu.... Fita suka yi, Driver ya tayasu kai kayan har bakin k ofar parlour daga nan suka sallameshi bayan sun yi da shi akan 3:00pm zai dawo ya d auke su. A parlourn k asa suka tarar da Mama tana zaune tana kallo. Sallamar su ce ta sanya ta maida hankalinta bakin k ofar, kamar a mafarkin haka taji nan take wani farin ciki ya lullub eta. Cikin farin ciki Huda ta ajjiye ledojin hannunta a farkon parlourn ta k arasa da gudu ta fad a jikinta ta yi hugging d inta. Tabbas Mama tayi farin cikin ganin d iyar tata amman sai ta maze ta zarota daga jikinta ta fara yi mata fad mai yasa ta fito? Dududu yaushe ma aka kaita? Ummi ce ta k araso inda suke tace Ayi hak uri Mama ni nace sai ta rakoni Murmushi Maman tayi dan ita ta ma manta Hudan tare take da bak uwa hakan yasa ta d anji kunyar barinta da sukayi a tsaye ita kad Cikin fara a tace Bismillah ki zauna. Yi hak uri wannan ta gudo ta barki bama ta tsaya kun k araso tare ba Murmushi Ummi tayi sanann ta k arasa ta ajjiye ledar hannunta a gefe tukun ta zauna a kan d aya daga cikin setin kujerun da Maman tayi mata nuni da. Tana zama Mama tayi kitchen.. Sai da ta cika mata gabanta da kayan kwalama da su lemuka tukunna ta nemi waje ta zauna tana raba d ayan biyu Ko dai babar Auwal ko kuma matar Abba! Amman anya kuwa matar Abba zata yarda tazo kuma tana mata fara a haka sosai? Ina su Hajiya? Na ji gidan shiru Muryar Huda ta katse mata tunani. Sai da ta d anyi jimm! Tukunna tace Tana gidan Baaba Talatu, Baba ne aka dawo da shi wai bashi da lafiya sosai Allah ya bashi lafiya Shine abunda Huda tace kawai dan jiya ma sai da suka yi maganar ita da Sakina A yanayin take taken Baaba Talatu so take ta fake da rashin lafiyar Baba a maida Mama gidanshi..... Kafin ku tafi ya kamata ki shiga ki dubo shi Hudan taji muryar Mama. Kawai tace kafin tace mata Sakina fa? Jiya tace min tana nan Cikin sigar zolaya Maman tace Amarya dai zaki ce! Ta tafi. Gobe suka ce za suje gidan dangin Babanta da shi da Yayansa Babansu yayi tafiya. Nan da sati biyu kuma in sha Allah za su koma har da su kawunnansa da Mahaifin nasa a saka rana Murmushi suka yi daga Huda har Ummi, a tare suka ce Allah ya tabbatar mana da alkhairi Kafin Ummi ta d an nisa tace Dota d an bamu guri, ko? A hankali Hudan ta mik e ta wuce sama ta bar su su kad ai a zaune. Gyaran murya Ummi tayi suka d an sake gaisawa kafin tace Maryam ni ban ma san ta Ina zan fara ba! Abu biyu ne yake tafe dani wanda duk biyun alfarma ce nazo nema daga gareki amman inaga gara in fara dana farkon dan shi yafi hanani sukuni a rayuwata. Tabbas tun lokacin da taji ta kira Huda da dota ta fahimci Zainab ce! A hankali Mama ta gyara zama ta fuskanceta da kyau kafin tace Ina saurarenki, Allah yasa zan iya taimokonki Za ki iya In sha Allah Shine abunda Ummi tace kafin ta cigaba da cewa Sunana Zainab, na san kin sanni a bad ini a zahiri kuma yau gani a gabanki. Da farko ina mai neman alfarmarki Maryam dan dan Annabi ki samu ki yi creating space a zuciyarki ki yafe min laifin da nayi miki shekarun baya sannan ki yafe min laifin da nayi ta maim aitawa Ina nanatawa duk akan Abba kar ya dawo gareki! Ba dan ni ba, tare da taimokon su Adama to da tuni tun a karon farko lokacin da kika tura mishi da sak o na san da kun koma kun ci gaba da zaman ku cikin kwanciyar hankali da k aunar juna, amma biyewa zuciya da son kai suka kaini ga aikata makircin da wallahi ni kaina idan na tuna kunyar kaina nake ji! Na san I m asking for a lot, na san da wuya ki yafe min, na san ko da ace kin yafe min to ba lalle ki daina ganina da abun ba A hankali Ummi ta
Chapter 19 · 0% Book details