← Book details So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 69

Sashe 20

So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

share hawayen da suka zubo mata sannan ta d an zamo daga kan kujerar ta durk Da sauri Mama itama ta sauk a akan kujerar tace Dan Allah kar ki yi haka! Already ni kam na dad e da yafe miki besides ba kece kika saka Abba ya sakeni a wannan ranar ba kawai dai kun had amu fad a ne wanda yanzu ya riga da ya wuce, komai ya wuce! Dan haka na yafe miki Ubangiji ma ake masa lefi anemi gafara kuma ya yafe mana ballantana ni? Ki manta da komai ki saki ranki In dai dan ta ni ne inaso kisa a ranki kamar komai bai faru ba! Dan Allah. Sannan ki daina d aura laifin da ba naki ba a kan ki ke kad ai dan Allah. Ummi bata san lokacin da ta fashe da kuka ba! A hankali Mama ta rungumeta Itama tana nata hawayen da bata san dalilin sa ba. A hankali ta share hawayen nata sannan ta cika Ummi ta gyara zaman ta ta hau lallashinta Da kyar Mama ta iya lallashinta aka samu ta yi shiru. A hankali Ummin ta kamo hannuwanta duka biyu a cikin nata tace Na gode kwarai! Sai alfarma ta biyu Ina rok on ki ki daure! Na ji kuma na san yadda Abba yake ta faman biko amman kin k i amincewa! Na san kina da gaskiya ta wani b angaren amman kuma duk inda akaje aka dawo Abba ya fiki gaskiya. Ki yi hak uri ki daure ki koma gidanki na farko na tabbatar har yanzu kina son Abba kuma a cikin shekaru goma sha taran nan da nayi da shi a matsayin Miji na fahimci zuciyarsa ba tawa bace ba taki ce! Ba zan tab a mallakar abunda ba nawa ba kuma indai bakya tare da shi to ba zai samu nutsuwar da ni kaina zan samu koda ace 1/10 d in kulawar da ya kamata ya bani ba. Ki daure, kar ki cuci kanki ki cuce ku. Ki dawo kusa da y arki kusa da masoyinki ku k arashe rayuwar ku just like it was soppose to be Kar ki damu da kowa ke dai kawai ki yi abunda zai sanyaki farin ciki, dan Allah. Da sauri Mama tace a zainab gaskiya wann..... Cikin katseta Ummi tace Na san alfarma nace Ina nema a wajen ki amman In kikai duba zakiga kamar a cakud e take da shawara! Shawarar da duk wani masoyinki na gaskiya zai baki. Sanann idan kikai haka za ki sanya mutane da yawa farin ciki.. Kinga na farko Abba Ta biyu Huda Sannan ta uku Da mamaki Mama take kallonta. Murmushi Ummi tayi sannan tace tabbas! Dan ni gani nake yi ma ko Abba ba zai kaini farin ciki ba saboda kinga na farko Zan ganshi cikin farin ciki Sannan zai daina blaming d ina akan na rabaku sannan idan ba gani nayi na gyara abunda na b ata ba to wallahi har abada har In koma ga mahaliccina ba zan iya samun nutsuwa ba! Ganin ku tare a yanzu living together happily zan iya ce miki shine abunda nake da kwad ayin gani a yanzu fiye da komai a rayuwata Zuwa yanzu Mama kam tama rasa bakin magana A hankali Ummin tace Ki yi tunani mai kyau. Dan Allah Maryam A hankali Mama ta sauk e wata nannauyar ajiyar zuciya tana kallonta kawai.. Sai a lokacin Shuwa wadda shigo tun d azu tayi musu sallama. agowa sukai suna kallonta, itanma su take kallo har ta k araso tsakiyar parlourn inda suke, jikinta duk a sanyaye. Cikin mutuntawa Ummi ta shiga gaisheta, Itama ta amsa mata cikin karramawa da kulawa kafin ta k araso ta nemi waje ta zauna tana tambayarta ya mutan gidan? Sun d an jima kafin Huda ta sauk Shuwa na setin staircase dan haka da ita ta fara tozali! Salatin da ta rafka sai da ya firgita su Mama dan haka suka juya suna kallon inda sukaga tana kallo Ita kanta Huda sai da ta tsorata. Tun kafin ta k araso ta rufeta da fad Dan mai yasa za ta fito? Aslam d in ne ya bata izini saboda shima sakare ne irinta! Ko dai satar hanya tayi ta fito? Da kyar ta iya tsayawa ta amsa gaisuwarta daga nan tace su kama hanya maza maza su koma gida! Wannan shirmen ba da itaba.. Ita tunda uwarta ta kawota duniya bata tab a ganin amaryar da ta fito bata yi sati biyu ba! Da kyar ta yarda suka d an jira driver bayan sun kirashi amman da cewa tayi bara ta yiwa Abban Ya Jamilu magana ya maidasu Ai bai dad e ta kawo Baba ba akwai mota shima a hannunshi. Ba a wani dad e ba Drivern nasu ya k araso: Ba yadda Hudan ta iya ta fara k arin tafiya ba dan taso ba haka nan ta yi wa Shuwa sallama ta basu tsarabar da Aslam ya bata kud i suka tsaya suka siya daga nan ta cewa Mama za suyi waya anjima dan da akwai maganar da itama ta shirya za suyi da Maman. Har mota Maman ta rakasu, haka nan ta tafi tanata kumbure kumbure.. Sai da Shuwa taga fitarsu tukunna hankalinta ya kwanta, yadda tabi ta d aga hankalinta zaka ce Huda wani gagarimin laifi tayi Mama tana dawowa daga rakasu ta zo ta nemi waje ta zauna a gefenta kan 3 seater tace Kiyi hak uri Hajiya nima sai da nayi mata fad a wallahi. Wai Ummi ta rako ne shiya sanya. Kin san su family d in nasu boko ta ratsa su da yawa basu wani damu da al ada ba amman duk da haka na san inda ace a waje d aya suke da Mommy da ba zata barta ta fito ba. Ta k arashe maganar tana d agowa ta kalli Hajiya Shuwa wadda tunda ta fara magana ta tsareta da idanu. A hankali taji ta sauk e ajiyar zuciya kafin tace Maryam Naam Maman ta amsa a hankali. Wata ajiyar zuciyar Hajiyan ta sake sauk ewa sannnan tace Naji duk abunda Ummin tace miki yanzu shigowa ta Wani yawu Mama ta had iye kafin tace Hajiya na gama deciding tun tuni Ba zan koma wa Abba ba! Ba kuma zan komawa Baba ba! A barni kawai, itama Ummin dan tak i yarda ta saurareni ne da abunda na shirya gaya mata kenan tun da hakan ne ra ayi na, bana jin kuma zai chanja ko da nan da shekaru nawa ne A hankali Shuwa tace Mai yasa? Da tsananin mamaki Mama ta d ago tana kallonta kafin ta sake yin k asa da kanta tace Hajiya dan girman Allah kar ki biyewa Baaba Talatu wannan karon har yanzu wasu lokutan ina jin rad i a k afata idan abun ya motsa, bayan k afata har a cikin zuciyata ina jin tsananin rad in azabar da na sha a hannun Ya Usman. Dan Allah Hajiya kar kice In koma gidansa Ta k arashe maganar tana me d ago kanta ta kalli Shuwan da idanuwanta da suka fara zubar da hawaye. Ahankali Shuwa tayi wani sassanyan murmushi sannan ta kamo hannunta duka biyu a cikin nata ta bata dukkannin attention d inta tukunna tace Gidan Abba fa? A zabure Mama take kallonta saboda bata tab a yin tunanin jin wannan maganar daga gareta ba. Kasa magana tayi bakinta ya hau rawa da alamun akwai abunda take son cewa amman ta kasa. A hankali Shuwa tace Maryam, ko ni na kawo taurin zuciya duniya ba zan tab a bari ki koma gidan Usman ba indai inada rai a doron k Wani kuka ne ya tahowa Mama lokaci d aya ta sakeshi! Tana sauraron Shuwa tana cigaba da magana A baya na yi kuskure, idanuwana sun rufe da takaici da kuma bak in cikin ganin kina y ata amman kin kasa yi mini biyayya! Wanda hakan ya kaini ga jefa rayuwarki cikin taskun da na kasa taimokonki kuma na kasa ganin hakan har sai ranar da aka kawo min ke a karye. Ban san da wannne baki zan baki hak uri ba Maryam ban san ta yaya sannan ta ina zan fara baki hak uri ba dan laifukan da nayi miki sunada yawa Ina jin takaicin yadda na kasa fahimta da ganin laifi da badaidan da na ke ta faman aikatawa da wuri ba. Ki yi hak uri ki yafewa mahaifiyarki Maryam dan Allah Da sauri Mama ta d ago tasa hannu ta toshewa Shuwa baki tana kuka bilhakk i da gaskiya. Cikin kukan ta hau girgiza mata kai alamun ta daina rok on ta. Da kyar ta iya cewa Hajiya dan Allah ki daina rok ona, ke fa Mahaifiyata ce, tayaya za kiyi ta rok ona haka. Laifin in dai kece kikayi min to na riga na saka a raina na yafe miki tun kafin ma ki aikata laifin. Kuka itama Shuwa ta fashe da shi, a hankali tasa hannu ta janyo Mama ta rungume ta suna kuka duk su biyun gwanin burgewa gwanin ban tausayi. Muryar Abba Madu wanda basu san da shigowarsa ba suka ji yace Ni fa? Za a iya yafe min nima? agowa suka yi duk su biyun suna kallonsa. Murmushi yayi ya k araso inda suke zaune ya zauna akan kujerar shima A gefen Mama (ya zamana sun sakata a tsakiya shi da Shuwa) A hankali yasa hannu ya dafa kafad arta yace Za a iya yafewa Abba Madu shima? Da sauri ta fad a jikinsa tana kuka at the same time tana d aga masa kai alamun A hankali ya sauk e ajiyar zuciya, wani hawaye mai cike da tarin k aunar y arsa da dana sani ya samu nasarar zubo masa ta ido d aya! Hannu yasa ya janyo Shuwa wadda itama take nata kukan ya had asu guri d aya da Maryam d in ya rungume Mama, ta manta rabon da taji kwatankwacin wannan farin cikin a rayuwarta a ranta ta shiga aiyyana.. ashe zata ga wannan rana? Ashe zata sake samun wannan opportunity d in a rayuwarta? Allahu akbar! Ubangiji mai zamani duniya juyi juyi mahak urci mawadaci Tabbas komai in yayi zafi maganinsa Allah sannan duk nisa jifa k asa
Chapter 20 · 0% Book details