Sashe 14
So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
asa ko globes d in bata tsaya kashewa ba.... BULAMA So da Buri Free Book Tana sauk asan ta ga shiru ba kowa. Da alama ma har masu aikin sun tafi side d insu dan har an rufe main door sannan an kashe globes. Hasken fitilun barander waje da suka ratso ta windunan parlourn ne suka taimaka mata ta k arasa bakin k ofar d akin nasu. A hankali ta d anyi knocking, ita bama ta yi tunanin za aji ba amma sai taji yace Come in Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauk e sannan ta sa kai ta shiga A zaune kan sofa ta sameshi, da alamun wanka yayi dan ya chanja kaya zuwa wata jallabiya ruwan zuma mai dogon hannu da hula, bai sanya hular ba ya barta ta fad a baya ba k aramin kyau yayi ba. Yana a zaune yana latsa computer ga tea a gefe kan d an stoll d in da ya d aura computer. Gaba daya hankalinsa yana kan aikin da yake yi shiyasa ta yi mamakin ta yadda ya ji d an mitsitsin knocking d in da tayi, kuma kamar ma ba shi ya amsa ta ba dan tunda ta shigo be ko kalli inda take ba! Haushi abun ya bata yadda ko d agowa bai yi ya kalletaba kamar ba d an Adam ne ya shigo d akin ba dan haka itama ta d auke kai bayan ta d an hararesa ta shige tayi wucewarta Inda ta ajjiye akwatinta ta nufa cikin closet, ga mamakinta sai taga wani akwatin wanda ta tabbatar nasa ne! ata rai tayi kawai ta hau zabgawa akwatin harara wanda ita kanta bata san dalili ba.. Sai da tayi me isarta tukunna ta d auki inner wears, toothbrush, tooth paste, hijab da sleeping dress ta shiga toilet d Wanka tayi ta d auro alwallah, a nan cikin toilet d in ta chanja kayanta..sai kuma ta fara tunanin a ina zata shanya bra da pant d inta (waenda ta wanke yanzun) inda ba zai gani ba. Babu inda bata duba ba amman ta rasa mab oya, k arshe dai shanyawa kawai tayi a wajen shanya sannan ta d aura hijabinta akan rigar barcin jikinta ta fito. Still yana zaune a yadda yake har yanzun.. Tsayawa tayi dan so take ya tashi ta kwanta! Tafi minti biyar a tsaye chaan! Ta tsinkayo muryarsa Kina buk atar wani abun ne? Yayi mata tambayar ba tare da ya kalleta ba Itafa gaskiya ya fara k ular da ita! Ta tsani ayi mata magana ba tare da an kalleta ba, wato ba ma ta kai ya kalletan ba kenan ko me? Huda ta aiyyana hakan a ranta. Gani tayi kawai ya d ago kyawawan idanuwansa ya zuba mata su! Da sauri ta sunkuyar da kanta a ranta tace Ko dai a fili na yi maganar?? Shi kuma Aslam shirun da tayi ne yasa ya d ago ya kalleta, ganin ta sunkuyar da kanta ne still bata ce komai ba ya sanya shi kiran sunanta, a hankali taji yace Huda Da mugun k arfi k irjinta ya buga! Saboda yanayin da ya kira sunan nata da muryarsa mai mugun dad in sauraro sannan very calm kamar baya son maganar ta fito. Ita kam, tunda take anya akwai wanda ya tab a kiran sunanta da dad i kamar haka kuwa? Ta aiyyana hakan a ranta. Ajiyar zuciya Aslam ya sauk kafin ya rufe computer ya mik ya nufi inda take tsaye Tunda ya mik e ta d ago ta fara kallonsa, ganin ya nufota gadan gadan yasa ta rikice tashi d aya, da sauri tace sofa, sofa! Sofar nake buk ata zan yi bacci Kafin ta rufe bakinta ma already ya riga ya k araso inda take! Da kyar ya iya danne dariyarsa, yana kallonta yana mamakin yadda duk ta duburce kamar ba ita ta gama zuba masa harara yanzunnan ba. Hannunsa yasa ya kamo nata! Da sauri ta d ago ta na kallonsa, shima itan yake kallo ido cikin ido! asa tayi da kanta tana jin yadda zuciyarta take bugawa! Haka kurum taji hawaye sun tarun mata a ido .Tunda take da Ya Arshaad ko da wasa bai tab a kama mata hannu ba 4 years! Amman shi wannan she just knew him amma bashi da aikin da ya wuce ya shafa mata kumatu ko kuma ya kama mata hannu.. Tabbas! Ta san akwai difference tunda shi wannan Mijinta ne amman kuma duba da yanda basu wani saba ba sannan kuma basa k aunar juna ai bai kamata ace yana saurin tab ata haka ba! Ko da yake ai ance daman a uk ya girma ta tabbata inda Ya Arshaad ne aka yi musu irin wannan auren had in da shi da ba zai tab a yunk urin rik e mata hannu ba har sai ya bari sun d an saba tukunna A take case d in Jalila ya fad o kanta, ta tuna yadda ta d aura masa laifin da ba nasa ba bawan Allah har da AlQurani ya zo zai rantse mata gaskiya Ya Arshaad yana sonta ba kadan ba! Tana cikin wannan tunanin bata yi auni ba kawai taji kuka ya kufce mata!. Ajiyar zuciya taji Aslam yana ta faman sauk ewa akai akai kamar shine yake kukan! Be hanata yin kukan ta ba, sai da ta gaji dan kanta tayi shiru afafuwanta har sun fara zafi saboda tsayuwa. Har tayi shiru bata ji ya daina sauk e ajiyar zuciyar ba, chaan, taji yace Ki tabbatar duk lokacin da tunanin Arshaad yazo miki, kika yi, kin yi istighfari! Yana gama fad in haka ya ja hannunta ya kaita har kan gadon sannan ya ajjiye ta yace sleep daga nan ya juya. Huda gaba d aya tsoron sa ne ya rufeta! A ranta tace Anya wannan ba alhaji bane ba kuwa? Har ya d anyi gaba sai kuma ya juyo, ganinta yayi still a zaune bata da niyyar kwanciyar.. Yunk urowa yayi zai yi mata magana kawai yaga da mugun sauri ta juya ta d aura k afafuwanta akan gadon ta kwanta ta lumshe ido Tabbas ya san me ta tuna dan haka kawai ya girgiza kai ya juya ya koma yaci gaba da aikin shi Itama Hudan a tunaninta kwantar da ita zai yi k arfi da yaji kamar yadda ya durk usa zai kinkimeta ranar a asibiti shiyasa ta shafawa kanta ruwa ta kwanta tun kafin ya sake matsowa kusa da ita zuciyarta ta tarwatse! Dan har yanzu bata bar uban bugun da takeyi ba. Bata san lokacin da yayi bacci ba dan ita kam tana kwanciya bacci ya kwasheta. Ta riga sa tashi dan tun kafin assalatu ta farka ita akin da duhu ba kamar yadda tayi bacci ta bari da haske ba. Jinta ta yi a lullub e cikin lallausan bargon da ta gani a gefe kan gadon. A hankali ta karanto addua kafin ta mik e ta zauna sakamokon kiran sallar farko data fara ji, dan ita da a tunaninta ma farkawar tsakar dare ta yi. Sai da baccin yad an ragu a idonta sannan ta yaye bargon ta mik e bayan ta d auki wayarta. Flash ta kunna sannna ta nufi hanyar bathroom..idanuwanta ne suka sauk a kan Aslam wanda yake kwance akan sofa! Dogo ne shi d in sosai shiyasa sofar tayi masa kad an, saboda kujerar ba wata mai girma bace ba dan da kyar In tafi 3 seater. Ya tankwashe k afafuwansa akan sofar duk dan ta ishesa amman duk da haka a takure yake da alama kuma sanyi yake ji, gashi taga kamar blanket d aya ne a d akin kuma ya rufa mata Pillow kawai ya d auka ya kwanta a kai ya turo k ananan throw pillows d in sofar k Hasken fitilar ta ne ya farkar da shi .ya farka amman bai bud e ido ba. Tsintar kanta tayi da komawa gadon, a nan ta ajjiye wayarta still bata kashe flash d inba (dan ta ga haske) ta d auko blanket d in ta dawo wajen da yake kwance. A hankali gudun kar ya farka ta d an sunkuyo ta lullub a masa blanket d in tun daga k afafuwansa har zuwa wajen wuyansa Ajiyar zuciya taji ya sauk e dan haka ta yi saurin kallon fuskarsa a tunaninta ko ya farka ne amma sai taga baccinsa yake yi peacefully.. Gaba d aya sai taji tausayinshi ya rufe ta ta tabbata d umin ne ya sanya shi jin dad i har cikin baccinsa yana sauk e ajiyar zuciya ya san yana jin sanyi amman ya hak ura ya lullub a mata shi ya kwanta a haka A hankali take nazarin tana kallon kyakkyawar fuskarsa. Durk usawa tayi sosai a gabansa kamar mai zaman tahiyya. A hankali ta shiga kallon fuskar tasa tun daga kan sumar kanshi zuwa straight girarsa..duk da idanunsa a rufe suke amman hakan bai hana ta ganin kyawun da idanun suka k arawa fuskar tasa ba, ga wasu kyawawan zara zaran lashes, dogon hancinsa ta kalla tana mamaki da girmama kyawun halittar Ubangiji Ta dad e tana kwad ayin son ta yiwa fuskarshi nutsatstsan kallo saboda ita har ga Allah tunda take a rayuwarta bata a ganin kyakkyawan Namiji kamar Ya Aslam ba! Komai nasa mai kyau ne, ga muryarshi idan yana magana kamar kar ya daina Kallonsa kawai take yi sosai tana nazarin, dan har an matsawa ta yi kusa da shi sosai ba tare da ita kanta ta sani ba! So take ta gane me yafi kyau a fuskarsa! Hancinsa ne ko kuma idon ko cikakkaiyar straight brows d insa, amma ta kasa, taso ace idanunsa biyu ta samu ta yiwa idanuwan nutsatstsen kallo kamar haka. So take ta d auke kai ammman kwata kwata ta kasa A hankali take bin skin d insa da kallo, fuskarsa tass babu alamar k urji ko zanzana ko wani tabo! K ayataccen sajensa ne kawai ya bambanta fuskartasa da ta babies. Ahankali idanuwanta suka kai kan d an mitsitsin pink lips d insa wanda yake a zagaye da lallausan siririn saje! Ta jima tana kallo chan ya ji tace Astaghfirullah!! kafin tayi saurin runtse idanunta sai kuma ta mik e da sauri ta juya ta fad