← Book details So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 69

Sashe 29

So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tace sannan ta kashe wayar ta ajjiye flask d in ta rufe had in nata ta fita. Tana fita wani mutum ko wata mata ta/ya shigo ta k ofar baya sanye cikin bak en kaya kamar irin na leda d innan na tare ruwa an rufa har hular saman fuska. Ta chan ciki a fuskar da mask bak irin, baka ganin komai hatta idanuwan a rufe suke da bak in glass. Tafin hannu da k afa kuma duk da bak en socks Wani ruwa aka zaro a cikin syring aka bud e had in coffe d in da Hudan ta gama had awa aka b alle kan syringing kamar za a matsa sai kuma aka tsaya aka yi shiruuu! Da alama mutumin ko matar is having second thoughts. Ahankali aka ja wani d an siririn tsaki aka mayar da murfin aka rufe aka ajjiye syringing a gefe kamar ana tunani Motsin mutum ya ji ko ta ji dan haka aka yi saurin d agowa ana kallon k ofar bayan ta inda aka shigo ai kuwa aka ci sa ar ganin giftawar inuwar mutum! Lalle kuwa ko waye ya gifta to ta/ya san ya ganshi ko ya ganta! Dan haka da sauri aka ofar bayan aka bi Inuwar da aka gani amman ko da wasa babu alamar mutum a wajen Har bayan compound sai da ya/ta zazzagaya amman ba kowa. Ya/ta dad e a tsaye tana/yana tunani kafin chan ya/ta nufi hanyar kitchen d in da niyyyar d auke syringing da ta/ya manta akan kanter kitchen d in kusa da tray da coffe d in da ya/ta had Tana/yana zuwa tayi/yayi saurin ja da baya sakamokon hango Huda da Ummi a cikin kitchen d in! Hudan tana juye coffe d in a cikin flask Ummi kuma ga wani abu a hannunta tana sha suna d an hira.......... BULAMA So da Buri Free Book Mikiya Writers Association. Da d an saurinta ta fita ta nufi gate saboda ta ji Sakina tace mata ta yi sauri Kuma ta ji muryarta dishi dishi sannan kamar maa fa ba muryar Sakinar ta ji ba! Gidan ba kowa shiruu, bak in duk an watse kasancewar kowa da motarsa yazo wasu kuma drivers ne suka kawosu suka tsaya suka jira su shiyasa ana gamawa kowa ya kama gabanshi. Sai da ta kusan kaiwa gate tukunna ta danna kiran Sakina. Bugu uku ana hud un ta d auka, tana d auka Hudan tace In fito ko za ki shigo? Da mamaki Sakina ta zare wayar daga kunnenta ta kalli sunan sanann ta mayar tace Ki fito Ina? Ina zan shigo? Turuss! Haka Hudan taja ta tsaya itama ta zaro wayar ta kalli sunan kafin ta mayar tace on fa da kika ce za ki bani? Cikin rashin fahimta Sakina tace Wanne sak Ahankali Hudan ta sauk e ajiyara zuciya tace Dan Allah Sakina bar wasa, yanzun nan ki ka kirani kika ce in fito kin manta sak o in zo in karb a da sauri Cikin katseta a d an firgice Sakina tace Hudan yi sauri ki koma gida maza maza yanzun nan! Inaga kidnappers ne suka yi hacking wayata sun ga yau kuna taro. Yi maza ki koma ciki da sauri kar ki sake fitowa. Da sauri kuwa Hudan ta juya k irjinta yana dukan uku uku! Har da d an gudu ta shiga had awa da shi. Parlourn ba kowa shiruu, nan ma duk an watse Haka nan ta wuce kitchen d in jikinta yana karkarwa tana salati. Tana shiga taga kamar an fita ta k ofar baya! Dan haka tsoronta ya sake nunkuwa. A hankali ta shiga takawa tana kallon k ofar da aka bi aka fitan dan gani take yi kamar har yanzu ana tsaye jikin k ofar ba a matsa ba! Huda Ummi wadda ta shigo yanzu taga tana sand a ta kira sunanta. A mugun tsorace tace wayyo Allah!! Sai kuma ta juyo jikinta yana karkarwa. Dariya Ummi tayi kafin tace Matsoraciya!!! Ai kuwa gara tun wuri ki yakice wannan tsoron saboda gidan da za ku zauna a UK inaga ya kusa rabin wannan azun Dad yake gaya mana Granpa although yana fushi da Aslam akan ki amman ya kasa jurar fushin da yaji labarin zaku koma UK ya bashi kyautar gida da mota a chan. A hankali ta kalleta kamar za tayi magani sai kuma ta sunkuyar da kai kawai kafin ta juya ta nufi inda ta ajjiye had in coffee d in Aslam. Murmushi Ummi tayi, ganin kamar Hudan bata son maganar yasa itama ta kawar da zancen ta hanyar cewa Yauwa coffe d innan na biyo! Gaba d aya drinks d in nasu na yau zak iii sosai kaina har sarawa yake yi idan nayi sipping. Allah yasa baki saka sugar da yawa a wannan ba, bana son sake saka wani abu mai sugar sosai a baki na. A hankali Hudan wadda duk jikinta yayi sanyi daga fitarta zuwa yanzu tace Naga kamar shima baya so sosai shiyasa dama zan ajjiye mishi a gefen tray d in in yana so sai ya k ara. Murmushi Ummi tayi sannan tace To za a zuba min inshaa ne ko sai na jira an fara kai mishi ya d iba? Ta k arashe tambayar cikin sigar tsokana. Murmushi mai had e da y ar dariya Hudan tayi kafin tace Haba Ummi Tana mai juyawa ta d auko cup mai d an girma, ta dawo ta hau tsiyaya mata. Sai da ta kusan cika kofin tukunna Ummin tace Okay tam ya isa haka na gode dota, Amaryar Aslam. Sunkuyar da kai Hudan tayi Ta lura Ummi so take sai taga ta saka ta tayi walwala shiyasa kawai ta d an sake suka hau hirar yadda birthday d in ya kasance, suna hirar tana juye coffe d in a cikin flask Ummin kuwa daman hakan take so dan ita kunyar Hudan ma take ji akan abunda aka yiwa Sakina yau gashi saboda su Shuraim takanas ta zo shiyasa ta dinga janta da wasa har sai da taga ta d an sake tukunna ta shirya bata hak uri akan abunda ya farun! A lokacin Huda har ta juye ta had a tray ta d aura cup da spoon da sugar tana shirin d auka Ummi tace Amm Huda iwant to apol.... Kamar an mak ale ta haka maganar tata ta tsaya cak! Da sauri Hudan ta ajjiye tray d in ta nufeta saboda yadda tana juyawa taga Ummin ta damk i wuyanta kamar zata shak e kanta sannan ta runtse idanuwanta. Da kyar Ummi ta iya cewa ya subahanallah! Sai kuma ta zube a wajen ta fara tari Innalillahi wa innailaihirrajiun Hudan ta ambata a firgice da k arfi! Sakamokon ganin jini yana fitowa daga bakin Ummi wadda take nan k asan tiles d in kitchen d in kwance tanata tari. Da sauri ta durk usa ta hau jijjigata tana Ummi! Ummi!! Ummiii!!! Abbaaa! ya Aslam! Ya Arshaad! Ummi ki tashi.. Kuka take tana ihu tun k arfin ta dan tun lokacin da ta durk usa akan Ummin ta ga ta daina motsi sannan jikinta ya sake. Da gudu ta mik e ta nufi k ofa da niyyar fita ta kira jama a azo a kai Ummi asibiti Tana gudu tana juyowa tana kallon Ummi bata yi auni ba taji ta fad a jikin mutum! Da sauri ta d ago tana kallon Arshaad wanda shima ita d in yake kallo bakinsa yana d an rawa da alamun magana yake son yi amman ya kasa. Cikin kuka ta hau juyawa tana nuna mishi Ummi wadda ke nan kwance a k asa kan tiles! Sannan ta juya da gudu ta nufi Ummin tana cewa Harda jini! Tama daina motsi tana mugun kuka. Da kyar Arshaad wanda gaba d aya ilahirin jikinsa ya d au karkarwa tun lokacin da ya ga Ummin nan kwance, ya taka ya k arasa inda Hudan da Ummin suke. Da sauri ya durk usa a wajen a mugun rikice yace Innalillahi wa innailaihirrajiun Kawai kuma sai hawaye ya biyo ta idanunsa. Da sauri Hudan tace Ya Arshaad dan Allah kar ka ce ta mutu! Wallahi bata mutu ba! Bata mutu ba!! Ka kaita asibiti zata farfad Dan Allah ka kaita asibiti.. Ummi ki tashi! Abbbbbaaaa!!! Ta sake kwala kiran Abba dan taga Arshaad d in yak i motsi kwata kwata so ba lalle ya iya tab uka komai ba, da alamun ya yi mugun firgita da ganin Ummin. A rikice Aslam ya afko cikin kitchen d in sanye da bathrobe a jikinsa da alamun ma bai gama wankan ba dan har da y ar kumfa a gefen kumatunsa. Ganin Ummi yasa shima ya k araso ciki da mugun gudu ya durk usa a inda suke dai dai nan su Shuraim suma suka k araso cikin kitchen d in. Sai ga Mom itama ta shigo tana cewa Ife ifen me nake ta ji ne wai hak Muryarta ce ta katse sakamokon kitchen d in da taga cike da jama a a nata ihu ana kuka! Dan su Shuraim suma suna shiga suka yi kanta sukai joining Hudan a kukan. Da sauri ta k arasa tana cewa waye ba lafiya ne mai ya far.. Maganarta ce ta katse sakamokon had a ido da tayi da Aslam! Sanye cikin bathrobe Da mamaki take kallonsa har da y ar kunfar sa a gefen fuska, har zata yi masa maganar fitowar dayayi half naked dan bathrobe d in bata da wani tsayi sosai sai kuma kawai ta shareshi dan jin dalilin kukan da take ji ne priority yanzun. auke kanta tayi ta maida inda su Hudan suke durk ushe Dishi dishi ta fara gani sakamokon Ummi da ta gani kwance bakinta duk jini! A hankali jikinta na mugun karkarwa tace Innalillahi wa innailaihirrajiun Sai kuma ta tafi luuuuuuu ta sume a wajen Sudais da Shuraim ne suka fara k arin ciccib ar Ummi dan haka Hudan ma ta sa hannu suka d auketa. Aslam yana ganin haka ya bisu a baya duk ya rikice Da gudu ya wuce su ya shiga d aki ya d auko mukullin motarsa ya mik awa Huda yace su jira sa Sannan ya koma ya zura jallabiya mai kauri daman already ya saka
Chapter 29 · 0% Book details