← Book details So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 69

Sashe 34

So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

suka k arasa duk su biyun suka shiga Aslam ya kunna ya ja suka fice daga estate d Gidan Madu Mahaifin Maryam za mu je! Granpa ya fad a yana mai gyara zamanshi ba tare da ya kalli Aslam d in ba. Wata nannauyar ajiyar zuciya Aslam ya sauk e wanda har sai da Granpa ya jiyo shi kafin ya lumshe idanuwanshi ya bud e ya gyara zama suka d auki hanyar gandun albasa. A dede k ofar gidan ya yi parking ya kashe motar ya juyo yana kallon Granpa wanda yake kallon gidan yana sake kalla, a hankali Aslam d in yace Mun iso Granpa Lumshe idanuwanshi Granpa ya yi, kafin ya bud e ya sauk e ajiyar zuciya yace mu je Yana mai sa hannu ya bud ofar motar. A hankali Aslam wanda tsananin farinciki da fargaba suka lullub e a lokaci guda yasa hannu ya bud ofar side d inshi ya fito zuciyarshi cike da fargabar abunda ya kawo Granpa nan sannan kuma yana addua da tsananin farin ciki In Allah yasa alkhairin da yake tunani ne ya kawo su.. Kame kame Aslam ya fara yi da dibi dibi dan shi dai ya san bai kamata su shiga kai tsaye ba! Rashin sanin kan al ada da lamarin garin Hausawa kuma yasa ya rasa abun yi. Suna tsaye Junaidu ya bud ofa ya fito.. Kallon kallo aka tsaya kafin Junaidun ya k arasa ya mik awa Aslam hannu. Bayan sun yi musabaha yace mishi Dan Allah suna son ganin Abba Madu idan yana nan. Da mamaki Junaidun ya kalleshi kafin yace Wa za a ce mishi? Sai da yad an kalli Granpa wanda still har yanzu gidan yake ta kalla tukunna ya d an sunkuyar da kanshi kafin ya d ago yace Kace mishi Mijin Maryam ne, Huda. Murmushi Junaidun yayi ya sake bashi hannu suka gaisa sannan yace Ashe k anin namu ne Ya fad a cikin raha da barkwanci sannan cikin ladabi ya juya ya gaida Granpa! Ba yabo ba fallasa ya amsa shi daga nan Junaidun ya juya da d an sassarfa yace Minti biyu dan Allah ya shiga cikin gidan. Bai rufe second talatin ba suka ga ya bud e wata k ofa ta waje ta cikin gidan sannan ya fito ta k ofar yace musu Ku shigo, bismillah Sai da suka zauna ya d auko ruwa da lemo a cikin babban fridge d in da yake a parlourn bak in ya jere musu tukunna ya juya ya fita ya ce bara yaje ya kira musu Abba Madun, yana gidan Kaka. Ba ayi minti biyar ba Madu da Kaka suka shigo da sallama. Cike da kamala suka k arasa cikin parlourn suka nemi waje suka zauna a kan 3 seater d in su biyun wadda take facing 1 1 seaters d in da Aslam yake zaune a k asan d aya Granpa kuma ke a kan d aya. A hankali cikin girmamawa Aslam yad an sunkuyar da kanshi ya shiga gaidasu Da kulawa suka amsa shi kafin su maida hankalinsu a Granpa suka soma gaidashi cikin girmamawa zuciyoyinsu fal mamaki da tunanin abunda ya kawo shi garesu. Ba yabo ba fallasa ya amsa su kafin yayi gyaran murya ya gyara zama sannan ya kalli Madu yace Ina son ganin ku ne amman first Ina buk atar Maryama a nan Ajiyar zuciya Madu ya sauk e kafin yace Ok ba damuwa daga nan ya mik e ya fita. A parlourn k asa ya sameta ita da Shuwa suna tattaunawa a kan al amarin Junaidu! Bai bi ta kansu ba yace mata ta taso ta d auki hijabinta ta zo Ganin yanayin shi ta san koma menene it s serious dan haka ta mik e ta nufi sama, bata wani dad e ba ta sauk o daga nan suka fice a tare. Suna fita ya kalleta ya ce Kun yi magana da Abba ne? Akan aure ko wani abun? Kuna magana da shi sosai yanzu? Da mamaki ta d an kalleshi kafin ta sunkuyar da kanta tace Na dai kirashi washegarin ranar da Ummi ta rasu nayi mishi gaisuwa A hankali ya sauk e ajiyar zuciya kafin yace Tou Allah yasa lafiya Dede nan suka k arasa bakin parlourn dan haka bata samu damar tambayar shi komai ba suka kutsa kai suka shiga yana gaba tana biye da shi Da Granpa suka fara had a idanu tana shiga dan an ci sa a k ofar yake kallo. A take gabanta ya yanke ya fad i! sannan ta fara tariyo had uwarsu da irin kalar warning d in da yayi mata! Sai yanzu ta gane dalilin tambayoyin Abba Madun da kuma dalilin damuwar da ta hango shimfid e akan fuskarsa. Shigo mana Mama Muryar Kaka ta katse mata tunani A hankali ta taka ta k arasa cikin parlourn k irjinta na dukan uku uku!!! asa kan kafet ta zauna gefen kafar Madu, muryarta na d an rawa tace Ina wuni Daddie Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk e, kafin ya ja wani yawu ya had iye sanann ya d ago ya zuba mata idanuwanshi yace Alhamdulillah, Maryama A hankali ta sake cewa Ya hak Bata jira jin amsarshi ba dan bataso maganar tasu tayi tsayi kar ya ga zak ewarta kuma bataso ya kasance batayi mishi gaisuwa ba dan ta san yanda yake da Ummi d dan haka tace Allah ya gafarta mata yasa Aljannah ce makoma Ameen ya ce. A hankali Aslam ya gaidata cikin girmamawa, da kulawa ta amsa kafin Granpa yace Marigayiya ta bani sak o wajenki Da sauri Mama ta d ago kai tana kallon shi.. Shima itan yake kallo kafin yace A ranar da zata rasu tace In sake nema mata yafiyarki Da sauri Mama tace Na riga na yafe mata tun ba yau ba mun gama wannan maganar da ita. Mun yafe mata daga ni har Huda fatan mu Allah ya ji k anta da rahama A hankali Granpa yace Ameen Sannan yad an sake muskutawa ya gyara zamanshi kafin yace A ganina ya dace ace nima na zo na nema yafiyarki tun kafin azo a nema min Ba Mama ba hatta su Kaka da Aslam Granpa suka kalla fuskokinsu d auke da tsananin mamaki! Bai damu da yadda suke kallonshi ba yace Shekaru 29 ko ace 30 baya! Na san na baku wahala ke da Abba Ban san halinda za ku shiga ba na biyewa b acin rai da zuciya na turaku chan wata k asa sannna bayan shekaru goma duk irin shak uwar da kuka yi ban duba ta ba na sa Abba ya sake ki! Ki yi hak A hankali ya kalli su Madu yace Kuma ku yi hak yri ku yafe min abubuwan da na aikata muku Da kyar Madu wanda ya shiga shock yace Ba komai ya wuce Allah ya yafe mana gaba d aya. Na gode Granpa yace, sannan ya maida idanuwansa kan Mama wadda ta kasa cewa komai. Ganin ta yi shiru yasa ya sake cewa Ki yi hak uri Maryama ki yafe min dan Allah.... Da sauri Mama wadda sai yanzu ta dawo haiyyacinta tace Daddie dan Allah ka daina bani hak uri.. Gaba d aya am not comfortable with you apologizing. Ka yi hak uri dan Allah ka daina bani hak uri. Na hak ura na yafe na manta komai, mu yafewa juna muma mun yi laifi ni da Abba dan kamata yayi ace dole muma mun tsaya mun bi zab in iyayenmu Ku yi hak uri ku yafe mana Ta yi maganar tana kallonshi sanann ta juya ta kalli su Madu. Ajiyar zuciya Granpa ya sauk e kafin yace Na gode Maryam amman in dai da gaske kin yafe min ke da iyayenki a yanzu Ina so mu d aura aurenki da Abba! This time around k amewa Mama tayi k Hatta numfashinta sai da ya kusan d aukewa Ganin ya sake yunk urowa zai yi magana yasa kawai ta fashe da kuka sai kuma ta tashi da sauri ta fita a parlourn tana kuka sosai. Da sauri modu ya mik e zai bita Granpa ya hanashi ta hanyar cewa Barta, kyaleta. Dawo ka zauna mu k arasa magana. Ahankali ya koma ya zauna jikinsa duk ba laka. Ajiyar zuciya Granpa ya sauk e kafin yace Ka lallab ata. Na san dama dole ba lalle ta amince lokaci guda ba. Amman yau! Ni, a matsayina na Mahaifin Yakubu na zo nema mishi auren Maryam. Ina fata za a bamu. Tun kafin ya rufe bakinsa Kaka yace na baku, za ku jimu nan ba da jimawa ba in sha Allah. A firgice Abba Madu ya juya yana kallonshi yana shirin yin magana Kaka ya mik e tsaye yace Mun gode kwarai Granpa. Ba ka san yadda maganganun ka na yau suka sanyani cikin tsananin farin ciki ba! Allah yasa ka gama da duniya lafiya In sha Allah ni da kaina zan samu Maryam mu yi magana da ita, daga nan zan tsayar da rana kawai a d aura aure A hankali ya kalli Aslam yace Ina so ka yiwa Abba albishir d Baba Bashir ya sake bashi Maryam a karo na biyu! Sannan ba zai yi k asa a guiwa ba wajen ganin ya mallaka mishi ita cikin sauk Daga haka ya kallesu yace Bara in je gida na barku lafiya Yana gama fad in haka ya juya ya fita yana share wasu hawaye da shi kanshi bai san dalilinsu ba. Kana ganin Madu ka san yana cikin tsananin rud ani! A hankali ya koma ya gyara zamanshi da kyau ya hau kame kame kafin ya daure yace Mun gode Granpa.. Kwarai za ku jimu in sha Allah Ya fad i haka wani gumi yana keto masa. Tashi d aya Granpa ya fahimci akwai wani abun a k asa haka ma Aslam, amman ganin da suka yi tunda har suka b oye kuma ga abunda suka gaya musu sai kawai suka bari akan bara kawai suma su bisu a hakan. Dan haka Granpa ya dogara sandarshi ya mik e tsaye sannan yace Na barku lafiya Daga nan ya juya ya kama hanyar fita. A hankali Aslam ma ya mik e ya yi wa Madu sallama ya fice. Har ya isa mota
Chapter 34 · 0% Book details