Sashe 52
So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwarewa Mammy ta yi da k arfi wanda duk ya janyo hankalin jama a kanta. Da sauri Aaima ta je ta matso ruwa a dispenser ta kai mata suka shiga shafa mata baya ita da Mommy tana sha tukunna ta d an dawo dede. Ajiyar zuciya Granpa ya sauk e kafin ya ci gaba da cewa Bincike yana tafiya bayan an yi testing tukunyar an tabbatar da poison mai k arfi ne a ciki sannan har da shinkafar b era. Sai kuma still aka samu gidan allura a cikin dustbin d in kitchen d wanda ba komai ne a cikin wannan allura ba face poison d in da aka yi amfani da shi aka zuba a cikin coffe d in. Tou a jikin syringe d inma kuma sai aka sake samun wani sabon tombprint d in wan.......... Shigowar Arshaad ce ta katse Granpa da kowa na wajen gaba d aya sai kallo ya koma kansa. Shiruu parlourn ya d auka na y an mintuna kafin ya ce Assalam alaikom, sorry I m late Bai jira jin me za su ce ba ya k arasa gaban officer d in kawai ya mik a mishi hannayensa duka biyu. Kuka Dad ya saka kawai ya mik e ya fita. A hankali Granpa ya sunkuyar da kanshi k asa wasu zafafan hawaye suka zubo masa. Da mamaki Mommy ta mik e ta k arasa wajen ta kamo hannun Arshaad cikin zaro ido ta ce Arshaad me ye haka ? Da kyar ya samu hawaye ya zubo masa a ido d aya! A hankali yana kallonta ya ce Mommy ni ne! Duk wannan bayanin da Granpa yake yi muku a k arshe suna na za ku ji a matsayin mai laifi! Ni na yi poisoning Ummi wanda Aslam naso kashewa tashi d aya abun ya fad a kan Ummi dan haka dan Allah taron nan ya watse haka, ku daina kwana kwana kowa ya tafi officer please arrest me Ya k arashe maganar yana sake juyawa ya mik awa officern hannuwanshi duka biyu kamar farko. ewa kawai officer d in ya yi ya zaro ankwa. Ba k aramin tashin hankali Mommy ta shiga ba bata san lokacin da ta shiga tsakaninshi da officer d inba cikin fushi ta cewa officer meyene haka yake faruwa? Kafin ta juya ga Arshaad ta ce Arshaad ba zan bari ka tafi gidan yari ba! Ta fad i haka tana nunashi da yatsanta dede fuskarshi alamun warning tana hawaye sannan ta ci gaba da cewa Ko meye ka aikata ba zan bari ka tafi gidan yari ba wallahi! Na san ba halin ka baneba pushing d inka aka yi kayi hak uri ka dawo Arshaad d in da muka sani Cikin kukan ta k arasa gaban Granpa ta ce Granpa Ummi kanta na san ba zata so haka ba! Dan Allah in domin ita kake yi to ka yafewa Arshaad ransa ne ya b aci zuciya ce ta kaishi ba laifinsa bane ba. Gani tayi kawai mutumin yana k arin sakawa Arshaad wanda ya tsaya kawai yana hawaye ankwar, da sauri ta mik e ta koma wajen ta fincike ankwar ta yar sannan cikin fad a ta cewa mutumin Wallahi bar ganin aikinka kake yi, na rantse da Allah idan ka saka mishi ankwa sai na tsinka maka mari! Runtse ido Arshaad ya yi da k arfi kafin ya samu ya bud e ya juyo da Mommy ya ya kama kafad unta duka biyu ya fara magana cikin d aci Idanuwanshi jajawur Mommy ba laifi d aya bane a kaina okay?! Ko kin kawar da wannan dole zan tafi jail saboda Junaidu ya yi filing complaint a kaina and all evidences are against me so just let it go this is wat i deserve. Dan Allah. amewa kawai ta yi tana kallonshi. A hankali Aslam ya k araso wajen ya dafa shi ya ce Arshaad! Ka juya ka fita a parlourn nan zan san abun yi please. Dan Allah ka tafi kawai! Meye ma ya kawo ka nan in the first place?! Ya fad i hakan cikin d an d aga murya. A hankali Huda wadda ta k araso wajen yanzu itama tare da Aaima ta ce Ya Arshaad me ya had aka da Ya Junaidu? Lumshe idanuwansa ya yi a hankali ya juyo yana kallonta ya ce Kin tuna sharrin da aka yi masa akan case d in Chief Justice!? Sannan akaso a sake d auke shi bayan an sakeshi? Those that ring a bell?? A firgice wani kalan kuka yana taho mata ta ce Ya Arshaad dan Allah kar ka ce min kaiine! Dan Allah Ya Arshaad Sai da ya matsa dede setin fuskarta tukunna yana kallon cikin idonta ya ce It was all me! Wani irin kuka ta fashe da shi ta durk ushe a wajen cikin kukan ta ce How?? Why??? Ranshi a tsananin b ace ya ce Why? Tambayata ma kike yi Bara ki ji dalili It was all because of you And bari ki ji abunda ya faru Naga take taken Junaidu At that very day kuma kema naga kamar kina k aunar sa, nuna miki ne ban yi ba amman hankalina a matuk ar tashe na bar wajen ki. Na biya ta wajen friend d ina Jamil! Sai na samu suna tattaunawa akan wata magana Yanayi na yasa ya tambayeni dan haka ban b oye mishi komai ba na fad a mishi damuwa ta. Ya san ki ya san yadda nake sonki shiyasa ya ce in bashi number da information d in Junaidun kawai Abun ya zo mana da sauk i saboda already best friend d in Junaidun Yaron Abokin nawa ne Jamil. A time d in ban san me za su yi ba kawai ni dai nace a san yadda za a yi min da Junaidu Sai da aka kashe mutumin tukunna na fahimci me sukayi. Cikin d aci ya ce Kinsan wani abu? Be jira jin me zata ce ba ya ce Ban damu ba! Kwata kwata ban damu da kisan kan da aka yi ba saboda Idanuwana sun rufe I was just selfish and bad! And happy tunda Junaidu ya b ace kenan babu abunda zai sake shiga tsakaninmu ko ya yi yunk urin raba mu. Ban damu da yadda ya sha wahala a Prision ba bayan an sake shi na sa a d auko mini shi. Yana kallonta ya sake cewa Kinsan wani abu? Nan ma be jira amsa ba ya d aura da cewa Ko da aka ce motar su ta kama da wuta Hudan ban ji haushi ba ban ji babu dad i ba ban kuma fad awa kowa na san wani abu ba! Na take komai na rufe idona duk dan inga na mallakeki! I was bad! Ban yi deserving freedom ba so pls dan Allah ku bari kawai su tafi da ni. Cikin fushi Aslam ya ce Ba za a bari ba! Da kasa aka kama Junaidun ai kuma still kai kasa aka dinga bashi shelter da abinci mai kyau Kaga hakan yana nuni da still akwai good in you Arshaad you felt guilty which is good. A hankali ya juyo ya kalleshi kafin ya ce For your information nine na janyo aka rufe maka company d in takalman ka! Is there any good in me left? Ya fad i hakan yana kafeshi da dogayen idanuwanshi. A hankali ya ji Aslam d in ya ce I know Arshaad na san komai! Tun kafin In tafi a time d in da aka kirani na fahimci kai ne dan Allah maganar nan ya wuce please Cikin katseshi ya ce Na so In kashe ka! Ka bar duniya gaba d aya In auri matarka! Is there any good in me? Still kana da hope a kaina ........ Ina za ki je? in da Granpa ya ce ne yasa gaba d ayansu suka juya suna kallon k ofar da Mammy ta nufa sad af sad af zata fice. A hankali Mom wadda tun d azu take magana ba a jinta tace I have something to say Da d an k arfi. Duk juyawa akayi aka zubawa screen d in ido, suna kallonta Idonta sharkaf da hawaye ta ce Arshaad baka so kashe Aslam ba! Ka dai yi yunk urin yin hakan amman kuma baka aikata ba saboda baka so ba.... A ranar birthday d in su Shuraim! Bayan Dad ya gama yi mana fad a akan Sakina da abubuwan da muke yi..I was furious! Sannan burin da na d aura akan Auwal ya mallaki MT duk sai naga yana shirin tab arewa tunda na lura shi soyayya ce a gabanshi a yanzu! Hankalina bai sake tashi ba sai da Mammy ta sanar min da cewar ta ga copies d in takardun MT da Granpa ya mallakawa Aslam a d akin ka a ranar Lokacin da ta shiga kai kuma ka fita ka barta a d akin, wanda bamu san ma an mallakawa Aslam d inba kuma bamu san ya aka yi kai ka sani ba. A take take ce min Komai ya zo mana k arshe ni da ita! Amman ta samo mana solution dan daman tun da taji labarin kyautar gidan da Granpa ya yiwa Aslam ta gama cire hope akan MT a Yaranmu muddin Aslam yana raye!.. Dan haka yanzu it s either I m with her ko kuma I m doomed Sai da muka keb e mu biyu tukun ta yi min bayanin abunda za a yi shine Ga shinkafar b era nan daman ita da shirin ta ta zo gara kawai a yita ta k are! Dukda a lokacin i was furious amman ban yi amanna da shirin nata ba, sai da ta yi mini cikakken bayani kuma na lura komai ya kusan zuwa mana k arshe tukunna na yarda but still sai na ce mata Gara mu zuba iyaka wadda zata la antashi ko ta sakashi doguwar jinya dan ni gaskiya ba zan iya kashe Aslam ba ari bisa d ari ta nuna min ta yarda, ban tashi sanin Mammy yaudarata ta yi ba sai da na ga gawar Ummi a kan cinyata Ta fad i hakan tana fashewa da kuka. Da sauri Mammy ta k araso wajen ta ce bana son munafurci! Munafuka