Sashe 66
So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da Sakina ta fara kukan gida tukunna Auwal ya yarda suka dawo a lokacin watansu biyar a k asashen waje. Ya so ta tsaya su biya Paris dan nan ne kad ai basu je ba a cikin k asashen da ake yawan zuwa a d an shak ata (Har Hajji da Umaara sun yi) Amman ganin yadda ta d aga hankalinta sannan ga yanayin condition d inta yasa kawai ya hak ura suka dawo. Direct gidansu, Daddy ya ce su wuce dan ta samu ta d an huta. Tabbas Daddy ya san in ba da kyar ba to kuwa za a yi irinta Granpa da Aslam shi da d an cikin jikin Sakina saboda yanda yake jin son jika ko jikar tashi tun kafin su zo duniya a ransa Allah kad ai ya sani. Ita Sakina har mamaki da kunya ma take yi, haka nan fa takanas! Zai kirata ya yi ta jero mata adduo i ita da babyn sannan ya yi ta turo mata important things akan condition d inta abunda ya kamata ta ci da wanda bai kamata ta ci ba saboda lafiyarta da babyn Wasu lokutan ita kam har kukan farin ciki take yi dan gata da soyayyar da Auwal yake nuna mata bata jin she could ever ask for more. Tunda ta lura yana d an wasa da sallah ta kafa ta tsare sannan ta nuna mishi b acin ranta! Yanzu sam Auwal ya manta rabon da ya bari lokacin sallah ya wuceshi. Zaman lafiya da k aunar juna shine definition d in rayuwar su ga families d inshi suma hatta Granpa da Mom kiranta suke yi su ji ya lafiyarta da babyn dan Auwal a ranar da ya sani washegari ya kasa rufewa farin ciki yasa sai da ya fad awa su Mom da Gramma har su Abba tukunna hankalin shi ya kwanta, sai da ya gama sanarwa kuma sai ya d anji kunya. Idan ka gansu tsaf da su sun yi k iba sun yi fresh in banda glowing ba abunda suke yi! Gashi sun yi mugun dacewa da juna, kamar ka sace su ka gudu. Gidan da Arshaad ya siya zasu zauna da Huda nan ya mallakawa Auwal, hatta lefe da kayan d akin suma su Daddy duk suka bashi. Sakina taso biyawa ta ga Huda amman jin yadda Daddy ya damu akan ta huta wai ta hawo jirgi ta yi jigila jigila yasa kawai ta hak ura suka wuce gidan ba dan ranta yaso ba. A hakan ma kuma Daddyn ya ce zuwa gobe su je asibiti a tabbatar da komai dai lafiya A chan suka tarar da Gwaggo Asabe tana gyaggyara musu gidan ita da wata mai aiki har girki sai da tayi musu. Suna gama oyoyo d insu ta sulale ta fice ko sallama bata yi musu ba dan karma su rik eta saboda ita tun kwanakin baya da Mommy ta tilastamata zama a wajen su Hudan ko kwana d aya bata iya yi ba ta gudu ta koma gidan Mommy a ranta kuwa ta raya ta gama zama gidan sabbin Amaren nan gaskiya .......... Aslam, yana tuk i yana d an satar kallonta. Ganin tak i ta yi shiru yasa ya sauk e ajiyar zuciya ya yi parking a d an gefen titi kad an ya kashe motar ya juyo ya kamo hannunta. Kamr za fashe da kuka ya ce Hudatie, kukan nan ya isa haka dan Allah. Saboda ke fa na je wai dan ki d an samu ki shiga mutane amman ni kam na jima ma rabona da shi. Da ace na san kuka za ki d ebo Allah da ba za mu je ba gaskiya. Ki share hawayenki Come here. Ya fad a hakan yana mai janyota izuwa jikinshi. Da kyar ya samu ta d an yi shiru kafin ya ce Ya Aslam matar nan ta bani tausayi..wallahi ba ita ta d auka ba! Sannan Yaron ina ganin lokacin da Maman shi ta bawa wannnan maid d in shi a wani lungu wajen ba kowa time d in ni kuma na fita yin waya da Sakina ne. Da sauri Aslam ya ce are you sure? Cikin tabbatarwa ta d aga mishi kai alamun A hankali ya sauk e ajiyar zuciya kafin ya ce Tun farko daman maganar sark ar nan na fahimci makircin mata ne. Wannan maganar Babyn kuma da kika fad a min yanzu ya sake tabbatar min. Zan je in samu Yash d In fad a masa sannan In tsaya har sai naga an fitar da ita tun kafin a shiga kotu ma. Amman wacce iriyar dak iyar uwa ce zata yiwa d an da ta haifa a cikinta haka? Cikin share hawayenta ta koma gefe ta zauna ta ce Nima dai abunda na ce kenan, amman wallah yadda naga ta bawa wannan maid d in Yaron Allah yasa In ga Annabi. Sannan jakar MANNUBIYAn a hannuna take! Ta bani bayan ta d auki abu a ciki ta ce in rik e mata bara ta je ta yi chanjin ta dawo A gabana ta bud e ta d auka abun da zata d auka, ba komai a cikin jakar sai y ar k aramar fasashshiyar wayarta da abunda ta d auka sai d ari biyu wallahi. Tana dawowa ko tab a jakar bata yi ba na ajjiye mata akan cinyarta. Kuma ko da ta dawo d in babu komai a hannunta haka nan ta nemi waje ta zauna da jakar a gefenta. Tana zama wayarta ta d au ringin ta bud e ta d auka Tana gama wayar muka ci gaba da hira take ce min Babanta ne a yi sadakar arbain d in Mahaifiyarta jibi. Daman tun zama na na fahimci tana cikin damuwa, tun farko ita kad ai a gefe na hango shiyasanya ma na je na zauna kusa da ita Ashe dalilin kenan....... Cikin jinjina kai Aslam ya ce shikenan, zan je In samu Yash d I wonder why ya yi believing da sauri haka har ta kai shi ga yi mata wannan wulak ancin! Yanada zurfin tunani ban san me ya shiga kanshi ba Anyways zan je in sameshi. Yanzu ki daina kuka share hawayenki kin ji honey Cikin share hawaye Hudan ta ce Ta bani tausayi ne sosai wallah, har da kukanta dama tana bani labarin Mahaifiyarta sai kuma kawai muka ji sanarwa. Ni a ganina lokacin da wajen ya hargitsene aka saka mata sark ar a cikin jaka saboda tabbas a k asa muka hango jakar a jefe tana d auka kuma aka k araso kanta. Hmmm, makircin mata ne kawai. Cewar Aslam yana mai kunna motar. A hankali Hudan ta ce an Indiya ne? Friend d in naka, na ji sunansa Yash Murmushi Aslam ya yi kafin ya ce sunanshi Yashjub, Itama MANNUBIYAn baki ji Manu ake ce mata ba. Cikin son faranta mata rai da kawar da zancen ya ce Good news sannan surprise Bara dai mu je In munje za ki gani...... Tunda suka shiga gidan suka zauna Aslam ya yi waya ya ce suna parlour ta kasa nutsuwa, in banda gyara zama da kalle kalle ba abunda take yi. Ta so ta gane wasu items a cikin gidan kamar waenda suka zab a ne ita da Sakina lokacin bikinta da Arshaad. Da sauri ta kalli Aslam ta ce Laaa Ya Aslam Sakina ce ta dawo ko? Dai dai nan suka k arasa sauk owa ita da Auwal. Jikinta ne kawai ya bata tana bayanta ga kuma Aslam yana kallon wajen yana murmushi. Da sauri ta juya sai kuma ta mik e da gudu ta zagaye kujerar ta tafi zata fad a jikin Sakinar. Da sauri Auwal ya shiga gaban Sakina tsakaninsu ya tsaya ya ce a,a,a,a careful!! Yana d an zaro ido da d aga gira da d an murmushi akan fuskarshi. Da sauri Huda ta ce Au sorry na manta, Daddy ya Auwal tana d an dariya. Dariyar shima ya yi yad an matsa ai kuwa da sauri Sakina ta rungumeta ta na share hawayen murnar ganin y ar uwartata. Cikin farin ciki da k aunar juna suka hau gaggaisawa da tambayar bayan rabuwa. Sun jima suna hira kafin Sakina ta ja Huda suka yi sama. Auwal kuma ya kira Arshaad suka hau video call su uku! Ba k aramin dad i suka ji ba da ganin yadda Arshaad d in ya sake sakewa ya ware sosai kamar komai bai tab a faruwa ba Suna hawa saman Huda ta fara tab a cikin Sakina tana murna har da kwallarta Nan suka zauna Huda ta fara zab an sunayen da zxata sakawa Babyn In sakina ta haihu. Ganin da tayi kamar Sakinar is moody ne yasa ta shiga tambayarta da damuwa akan fuskarta. A hankali Sakina ta ce Ni inata mita mu ba a cikin estate za mu zauna kusa da ku ba, ashe ba ma a garin zamu zauna ba gaba d aya. Ajiyar zuciya Huda ta sauk e kafin ta ce Ai kin san Ya Auwal shi ke da MT d in Abuja, dole kinga a chan za ki zauna kusa da shi mana Sakina. Za mu dinga zuwa ai ku ma kuma na san za ki dinga zuwa sannan na san maybe ma ya dawo dashi Kano gaba d aya ko? A hankali Sakina ta ce Ai cewa yayi wai a chan Cairo zan yi karatu kuma de! Ni duk kaina a d aure yake ban ma san wajen zama d aya tak ameme ba, ya ce min dai wai zan ji dad in karatun sosai. Dariya Huda ta yi kafin ta ce ashe ya yarda kenan.. Ya Aslam ne ya sama mana karatun mu biyu ni da ke, da yayi mishi maganar da farko sai kamar bai yarda ba ya ce shi yana Abuja family suna Kano ke d in idan kika yi masa nesa aganinshi abun zai d anyi wuya Shiyasa Ya Aslam ma ya ce min kar In gaya miki yet ki d aga mishi hankali tunda bai riga ya amince ba. Kinga yanzu kuma ashe ya amince Da sauri Sakina ta rungume Huda ta ce Na ji dad i da za mu yi karatu tare Sai da dare ya yi sosai tukunna su Huda suka kama