← Book details So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 69

Sashe 45

So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sa hannu ya janye hular alkyabbar. Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk e kafin yace Ma sha Allah Sai kuma ya sake cewa Kukan me kika yi? A hankali ta girgiza kanta alamun ba komai Tana jin bugun zuciyarta yana kara tsananta!. Cikin son ya tashi a gaban ta ta ce Akwatunan menenen wannan? Murmushi yayi yad an sunkuyar da kanshi k asa ya ciji lips d inshi kafin ya d ago da kanshi yana kallonta tukun ya fara magana Ai dama sai da na cewa Mommy ta yafe min a barni ba sai na yi ba amman ta saka ni kashe uban miliyoyi akan lefe! Yau kusan wata biyu kenan tana ta tatsemin aljihu. Ga shi ke kanki bama ki so ba ko? Mu mayar mu karb o kud in mu? Sai yanzu ta d ago ta kalleshi Ma sha Allah ta fad a a ranta.. Tunda ya shigo dama ta lura da fararen kaya ne a jikinshi kaftan, sai yanzu taga ashe har hular kansa itama fara ce tas! A ranta ta ce Manyan kaya sun fi yi maka kyau Cikin katseta ta ji ya ce Kwalliya ya biya kud in sabulu kenan! Tunda gashi har an saki baki ana kallona Ya fad a yana murmushi gefen baki da d age mata gira. Da sauri ta d auke idonta da kyar. Cikin son kawar da zance ta ce Ya Aslam wasa wasa fa kanada rowa, tun ba yau ba na fuskanci haka Dariya sosai yayi kafin ya ce Ai kin fini rowa! Tunda gashi ana ta yi mini rowar zuciya. Ya fad i maganar yana k arin yin zaman dirshen akan kafet d in gaban gadon ( a gabanta) Yana zama, bata san lokacin da ta yi sauri itama ta sauk o ta zauna a gabansa ba har guiwowinsu suna gogar juna. Sai kuma ta fara k arin janyewa Hannuwanshi ya saka ya rik e cinyar tata ta yadda ba zata iya motsawa ba! Yana jin wani yanayi na daban ya na shigar shi A hankali yana d an murmushi ya ce I love this respect da kike min Hudatie, Thank you. Sunkuyar da kanta ta yi kawai ta kasa cewa komai. A hankali yana kallonta ya ce Baki ce komai ba. Akan maganar mu da muka fara a d akin Gramma Da sauri ta ce Ya Aslam dan Allah ka daina bana son maganar. Kuma ni dai ka d auke hannunka. Gefe ya kalla yayi wani murmushin gefen baki.. Bata gama fahimtar murmushi da jinjina kan me yake yi ba ta ga ya mik e tana shirin yin magana ya sunkuya ya d auketa! Sai da ya k arasa wajen sofa tukunna ya zauna ya d aura ta a kan cinyarshi kafin ya ce e idon sannan ki ja numfashi Matsoraciya kawai In kika sake yi min musu ko kika ce kar In tab aki Allah sai na nuna miki matsayina a wajenki. A hankali ta bud e idonta tana kallon k asa.. Hankalinta In yayi dubu tou ya tashi! Tanajin yadda jikinsa yake d an rawa kad an kad ga zuciyarshi tana iya feeling bugunta! A hankali ta ji ya ce Unhm ina jinki. Say something anything i told you how I feel. s talk about us, Um?? Yayi maganan yana ruk o hannunta. Zuwa yanzu kam Huda ji ta yi ba zata iya jurar wannan torture d in ba dan apart from heart d inta da yake over racing! Ta rasa fahimtar meyene game da hannun Aslam da yake sanya touches d inshi suke zautar da ita. igar hawayenta ya ji dan haka ya sauk e ajiyar zuciya ya mik e da ita a jikinshi ya ja hannunta Sai da suka je inda ya ajjiye ledojin d azu tukun ya d auki wata ledar bag y ar babba mai zip lock mainkyau sosai ya bata ya ce Gashi ki shirya ki sa wannan kayan ki yi alwalah..please ki saka rigar ciki Har zai juya sai kuma ya ce If not Ya matso da bakinshi kusan kunnenta ya fara magana Da mugun sauri ta juya ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta jikinta na karkarwa. Kisa rigar kin ji, pls Ya fad i maganar kamar ba shi ya gama zuba mata maganganu a kunne ba yanzun nan. A hankali ta ce dan ita Allah Allah take ya fita ya bata guri ta samu ta shak i isashshiyar iska. Yana fita ta sauk e wata nannauyar ajiyar zuciya tana dafe k irji sanann ta nemi waje ta zauna akan gadon. Ta jima a haka kafin kawai ta mik e ta fad a toilet dan daman wanka take son yi tun kafin ya shigo: Ta d an jima tukun ta fito bayan ta yi wanka da ruwan turarrukan da Ummu ta jere mata a toilet d in, da brush duk sai da ta yi sannan ta fito. Rigar, dan kyau ta yi kyau sosai sai dai spaghetti hand ke gareta. Ba wani rashin d a a rigar dan doguwar gown ce har k asa Slim mai bin jiki sai wasu stones masu shek i na azaba k anana a saman edge d in wuyan rigar da kuma dede k asan boost sai kuma chan k asan edge d in rigar shima an zagaye da stones d in. Ko bra bata saka ba dan rigar irin me bra d innan ce ta ciki. Sai da ta saka rigar ta zuge zip d in da kyar tukunna ta ga rashin d ar rigar dan kusan rabin k irjinta a waje ne sannan bayanma gaba d aya ashe akwashe yake dan ma Allah ya taimaka gashinta ya rufe kusan rabi. Da sauri ta fara k arin zuge zip d in domin ta samu ta chanza rigar kafin ya shigo. Bata kaiga zugewan ba kuwa ya shigo! Sanye cikin jallabiya fara tass! Mai k aramin hannu. Suna had a ido da shi bata san daliliba kawai sai ta fashe da kuka. Da sauri ya k araso gaban madubin dan shi a tunaninshi yadda ya ga ta rik e wajen zip d in ta na jaa ya d auka had ewa ta yi da fatarta. Sai da ya duba ya ga ba komai tukunna ya sauk e ajiyar zuciya ya juyo da ita ya fara lallashinta yana dariya k asa k asa dan sai yanzu ya fahimci dalilin kukan nata. Da kyar ta yi shiru tana sauk e wasu tagwayen ajiyar zuciya tana nok ewa: A hankali yake binta da wani irin kallo kafin ya tattara gaba d aya gashin nata ya zubo mata shi ta gefen fuskarta suka fad a a kan k irjinta gefe d aya. Tunda ya fara kallonta har ya gyara mata gashin kan nata ta sunkuyar da kanta k asa. A hankali ya zaro wata red rose ya sak ala mata a jikin gashinta ta d an saman kunnenta kafin ya zaro wani tsadadden pendant necklace an mitsitsi mai shape d in heart ya ware shi ya bud e ya kara mata a wuyanta sannan ya matso sosai ya lek a ta baya ya manne mata sark a ya saketa ya gyara mata gashinta. A hankali ya na nan a yanda yake dan baya son motsawa daga position d insa ya ce Open it Da kyar ta iya bud ewa hannunta na gogar k irjinsa Bata san lokacin da murmushi ya sub uce mata ba Right side d in an rubuta Left d in kuma A hankali ta mayar ta rufe sark ar tana d an murmurshi. Jin yayi shiruu yasa ta d an motsa sai kuma ta tuna ashe a jikin madubi ta ke! Da sauri ta juya ta katseshi daga k are mata kallon da yake.. Dariya ya yi ya ce To ai nan d in ma zan ganki Da sauri ta koma ta kanannad e shi ta baya ita ala dole kar ya sake ganinta. Ganin tana shirin kunce mishi lissafi yasa ya ce Tsaya In d auko miki hijabi mu je mu yi sallah Da kyar ya samu ta sakeshi ya k arasa wajen akwatunan ya bud e wanda yake kyautata zaton akwai hijabin a ciki.. Cikin sa a kuwa ya samu ya d auko harda darduma ya dawo ya mik a mata hijab d in ya ce Ungo, saka A hankali ta karb a ta saka tana sauk e wata nannauyar ajiyar zuciya.. Daga nan ya ja hannunta ya ce mu je, i have a surprise for you. Yana rik e da hannunta suka fito suka nufi d akinsa Yana bud ewa! A hankali ta ce Woow.. Tana murmushi. Sai da ta k arasa shiga cikin d akin tukunna ta fahimci abunda ya rubuta da y an k ananan candles d in da ya kunna a tsakiyar d akin Love You Hudan!. Kan gadon ma wanda ke nan shimfid e da white bedsheets haka ya rubuta da wasu k ananan red roses. Murmushi kawai take yi tana kallon yadda d akin ya k awatu matuk a! Ya burgeta sosai. A hankali ta ji yayi hugging d inta ta baya sannan ya ce Do you like it? Ya yi kyau? Murmushi ta yi a hankali ta ce Ya yi kyau Juyo da ita ya yi ya d an b ata yayi kalar tausayi fuska abun dariya ya ce Ya yi kyau but you don t like it ko? Sai da ta yi k asa da kanta tukunna ta ce Ni Ya Aslam kana confusing d ina ne idan na ji ka ce you love m me Ta k arashe maganar da d an inda inda. A hankali ya sauk e ajiyar zuciya kafin ya ce Cikin runtse idanunta ta ce Ya Arshaad fa k anin ka ne! Amman kuma how kake sona bayan ka san shi zan aura? Idan kuma ba haka ne ba to tayaya zaaka ce ka fara sona ana d aura auren mu? Tunda na lura tun lokaci ka fara nuna intrest. Ta fad a tana sake sunkuyar da kanta sosai. Ya ji zafin zancen Arshaad da ta kawo amman sai ya basar, ya ce Dole ki sunkuyar da kai ai Ya fad i hakan yana d an jan hancinta, kafin ya sa hannu ya sake jawota jikinshi tukunna ya fara magana
Chapter 45 · 0% Book details